← Book details Diya Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 41

Sashe 22

Diya Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba ta yi
niyar sake ganin shi ba,raban ta da shi tin
ranar da ya zo ma ta da yashasshan
zance,wlh da ta san zai zo da ba ta tsaya
jiran Jabir ba….Nabeela ta na fadin yau
Khalid a gidan nan,tin dawowar sa ban sa
shi a ido ba,gwara ma dai Hauwa da Inna
sun zo,babbar diyar Nabeela ta ce mama
Neena ake cewa ba Inna ba.

Nabeela ta ce
aw Inna fa ta koma Neena,duk dariya su ka
sa,sallamar Khalid da Jabir da shigowar su
lokaci daya ne.

Ya na shiga idanun sa su
ka isa izuwa inda ta ke,be da buri da ya
wuce ya kalle ta ya ga yanda ta ke reactn
duk sanda ya san ya idanun sa cikin na
ta,gashi d more ya ke ganin ta d more ta ke
kara ma sa kyau,ganin ta ya yi cikin riga da
wando na pakistan ja,mayafin yane bisa
kanta gashi gashin goshin ta yayi lublub
abun sha’awa ka yi zatan irin gashin nan
ne na gaske.

Kamar ta sani sai ta ki kallan
ma in da ya ke,ta na murmushi ta ke yiwa
Jabir sannu da zuwa,ya na yauwa Sannu
my sister,ya na fama da yara da maman
su,wata ruke da hannun sa na hagu,wata
na dama,wata kafa,ga maman su ruge da
jakar sa da ta karba,sauran yaran biye da
su su ka shige ciki kowa na nashi surutun,
aka bar Hajjo da Khalid a falon.

Sai a
sannan Hajjo ta daga ido ta kalle shi,ganin
yanda hankalin sa gaba daya ya karkata ga
inda su Jabir su ka shiga,ta ga yanayin da
ya ke ciki,ta tabbata Jabir da yaransa ne
su ka bashi sha’awa,rashin ‘ya’ya sam be
da dadi,sai ta dan tausaya ma sa,amma na
kankanin lokaci saboda ita ta shagala ta na
kallan sa,har ya kama ta,sai ji ta yi yace
am i dat handsum suger?

Ta yi sauri kau
da kai cikin jin kunya ta ce sannu da
zuwa,ya aiki?

Ya murmusa,yan da ya ga ta
na kallan na sa ne ya ma sa dadi kwarai,ya
ce hamdan.

Jabir ya fito biye da Nabeela,sun hada yara
da kayan dadi sun rabu da su a daki.

Nan
ya zauna tare da Khalid Nabeela ta kawo
mu su abunci,Hajjo ta tashi za ta ba su
wuri Jabir ya ce ta zauna abun ta,yay ta
jan ta da hira,yanda ya ga ta sake da shi
ya sosawa Khalid rai,wato shi ne dai ba ta
so,ba ta ra’ayi,ko ya sa baki a zancen sai
ka ji ta yi shiru,Nabeela ce ma mai kokarin
sa shi cikin hirar.

Sanda su ka gama cin abunci Hajjo ta fara
shirin tafiya,Khalid ya ce dama dai gida za
shi bari su tafi tare.

Hajjo ta ce ah ah,ita ba
gida za ta ba,Khalid ya ce ko ina za ta ba
damu,he is free.

Nabeela ta kalli Jabir da
alamar tambaya irin wats up wit dem,ya
daga kafada ya aje lyk i donno.

Jabir ya
gyara murya ya ce my sister gwara ya aje
ki din,ga hadari kar ruwa ya taba ki.

Da ke
ta na jin maganar Jabir,ba mu su ta ce tam
yaya na.

Khalid ya kalle shi tare da fadin
toh yayan ta da fatan xa a gyara ko a
canza mota,Madam ki dena hawa motan sai
ya sake wata.

Nabeela ta sa dariya,Jabir da
Hajjo kuwa ba wanda ya dara,sai ma Jabir
da ke fadin na ki na canza din,ta dena
hawa,diyoyi na sa hau.

Da haka da haka ayi
sallama, ya sanya Hajarar sa gaban
mota,su ka dau hanya.

Sai shan kam shi ta
ke,shi kuwa zuciyar shi tas,ga iska da ke
tashi,gari yayi baki,hadari ya hadu sai kugi
yake.

Ana yayyafi kadan kadan,kamshin ta
da ya mamaye motar gami da yanda AC ke
ratsa cikin ba karamin nishadi ya kara ma
da ba.

Idanun sa kan titi ya ce an gama jan ajin ko
da saura?

Ba tare da ta kalle shi ba ta ce
ban gane ba.

Ya ce har yanzu ajin ba a
gama jan sa ba?

Ar u still nt ready to obey
ur hrt?

Dan na san deep inside u ki na so ki
aure ni,am every woman type,so don’t give
dat clumsy excuse dat am ur type!

Hajjo ta
kalle shi tare da fadin nt every woman,nd
mind you am nt in ur dat “every woman”
Khalid ya ce big lie!

Yayyafi ya karu
sosai,ya kara da na sani Suger,ko ya ki ka
so ki boye feelns din ki na sani,i can read u
lyk a novel!

U hav feelns for me,you hav
crush on me.

Rai bace Hajjo ta ce ka manta
diabates ba Suger ba,i hav no feeln or wat
so ever for you,so stop mistaking!

Shiru ya
ma ta,har ta na tunanin ya rasa ta cewa,sai
kuma ya kallo ta ta hanyar danna idanun
sa cikin na ta,yanayin fitar numfashin ta
tini ya dan tsagaita,ya ce wat abt d way u
catch ur breath wen i look at u?

Ya saki
murmushi mischievously tare da mai da
idanun sa bisa titi,ya ce let it go Suger,ke
ma kin san u lyk me!

Rai bace,bakin cikin
yanda da ta yi reactn ya sa ta fadin tsayar
da motar ka!

Fita zan yi!

Cike da mamaki
ya ce ki fita ki je ina kuma cikin ruwan
nan?

Ta ce da zama guri daya da kai gwara
dukan ruwa,ka tsaya ko na bude na fita a
haka.

Ganin fuskar ta ba wasa,sai ya sauka
gefe ya yi parkn.

Ta yunkura za ta bude
motar ya danna lock,wai ina zaki?

Shin in
kin fita ina za ki sami abun hawa cikin
ruwan nan.

Ta ce ina ruwan ka?

Zan fita
kuma zan sami abun hawa ba tare da bata
lokaci ba,idan kuma ban samu ba zan taka
daganan har hotoro GRA a kafa.. ya ce no
way!

A fusace idanun ta har spark su ke
dan bacin rai ta ce way!

Bude ka gani!

A
kasalance ya rangwadar da kai bisa kan
kujerar sa,ya ce Suger….ta ce Hajjo!

Ba
suger sunana ba,kowa da Hajjo ya ke kira
na,so ka kira ni Hajjo ko ma child abuse da
ka saba kira ko ka yi shiru!

Ya murmusa ya
ce child abuse is no more,wannan zaune
gabana is a strong woman!

Khalid ba kowa
ba ne,Khalid is unique dax y zai kira ki da
sunan da ba kowa ke kiran ki da shi ba
Suger!

Ta ja hannun kofa,tare da fadin ka
bude min.

Ganin ta matsa sai ya bude ma
ta kofar ya ga iyakan gudun ruwan ta.

Ta
ko sa kai ta fito,yayya fi ya zama
ruwa,wani irin iska mai sanyi ya buso jikin
ta,kayan ta ya fara bin jikin ta,ta ja daga
jikin motar Khalid ta sami wata yar lemar
ma su sayir da recharge cards ta
kebe,amma duk da haka ruwan na taba ta.

Daga mota ya ke kallan ta,he love d view,ta
yi ma sa kyau kwarai,ba dan ya na tsoran
kar ta kamu da sanyi ba da ya kyale ta yay
ta kallan ta a haka.

Ya yunkura zai fito
kenan sai ya ga wata mota ta tsaya a
gaban ta,an sauke glass din motar,abun da
ya dada kular da shi yanda ya ga ta na ma
mai motar murmushi mai kayatarwa!

DEDICATED to The Women Of Virtue
(group)
[7/25, 5:16 PM] Salmah Ateeku: [10:56pm,
6/5/2015] Khadija Sidi: DIYA
MACE
Ganin frnd din ta da ya dade da nace ma ta
na yafuce shi,farin ciki ya lullube ta,a asibiti
daya su ke aiki,amma shi a admin block ya
ke aiki.Cikin jin dadin ganin sa Hajjo ta ce
KB na ji dadin ganin ka wlh!

KB ya dara tare
da fadin maza shigo toh kar ruwa ya zane
min ke.

Dama tayin da ta ke jira kenan,dan
ta fara jikewa sosai,ta yi saurin bude motar
ta shige.

A fusace Khalid ya fito daga ta shi
motar,ya nufi motar KB amma ina KB be ma
san da shi,tini ya karya kan mota ya haye
kan kwalta abun sa.

Rai bace ya bi motar
da kallo,ruwa ne ke dukan sa amma sam be
damu ba saboda zafin da kuna da ransa ke
yi ya fi dukan ruwan.

Sai da ya dau kusan
minti biyar a tsaye,ya jike jagab,Hajjo sai
dan waiwayen sa ta ke ta motar KB har sai
da ya ce ko kin yi mantuwa ne?

Ah ah,ta yi
saurin ba shi amsa,mu je ba komai.

A fusace ya juya ya koma motar shi,da
juyawa zai yi kawai ya tafi gidan sa,amma
kishin ganin Hajjo ta shiga motar
wani,wanda ba mamaki ma ba ta san shi
ba dan ta kuntata ma sa ta bishi ya sa
zuciyar shi tafasa,a dole ya bi bayan su dan
ya tabbatar ya sauke ta lfy.

Har su ka kai
kofar gida ba su san Khalid na biye da su
ba,can gefe ya faka,ya na ji ana ta horn
maigadi ya ki ya zo ya bude gate,shi ma
ruwa ya buye shi,dan haka sai Hajjo da KB
su ka tsaya shawara,ya na ta zauna a
gama ruwan,ta na bari dai na shiga yanda
ruwan nan yayi yawa Allah kadai ya san
lokacin tsayawan sa.

Khalid da ga na shi motar ya cika ya yi
fam!

Wai shin mai Hajjo ta ke nufi za ta
zauna a motar wani kato!

Ta na zaune
motar wani cikin ruwan sama,sai shakar
gamshin ta ya ke!

Mtsw ya ja tsaki!

Hakurin sa ya kare,ya yanke hukunci zuwa
ya fito da ita da kan sa kenan sai ya ga ta
bude mota ta fito,ta shige gida da sauri.

Ajiyar zuciya ya saki tare da bin motar da
kallo da ta zo shige shi ya na fadin Allah ya
taimake ka kai dai,amma ka kuskura na
kara ganin ka kusa da Suger ba za ka ji da
dadi.

Be shiga gidan Hajiyar ba ya tada
motar shi cikin bacin rai da hanzari ya bar
wajan.

A hanya yayiwa Sani waya,ya ce da
shi gobe kafin ya taho kano yayi jiran
shi,zai shigo kumurya.

Cike da mamaki Sani
ya ce toh Allah ya kai mu.

Ya amsa da
amen.
Chapter 22 · 0% Book details