← Book details Diya Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 41

Sashe 10

Diya Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin su Mudi yayi saurin ba
su hannu su ka gaisa,sannan su ka yi
sallama da Hajjo,ko ta kula su,ita dai rera
kukan ta take,Garbati ya tisa ta a gaba ya
na fadin da ba ki tashi zuwa gidan ba sai
da ki ka ga kina da ciki dan ki min
asara,toh wlh ba ki isa ba.

Cikan ka ba
tace ma sa ba,suna tafe jama’a na kallan
su har su ka shige gida…

DEDICATED to The Women Of Virtue
(group)
[7/25, 9:35 AM] Salmah Ateeku: [6:18pm,
5/15/2015] Khadija Sidi: DIYA
MACE
Wasa wasa cikin Hajjo ya girma ya fito
sosai,ta sha laulayi,ga jarabar Garbati da ya
karu ba dare ba rana.

Yanda Allah ya so ta
da rahama sai warin Garbati ya dai na
damun ta,sanadiyyar cikin da take dauke da
shi.

Duk dare sai dai ya zo ya ce Hajjo
gyara,da ya sami abunda ya ke so ya zube
ya na munshari,ita ko baiwar Allah har ta
ma soma sabawa.

Sanda cikin na ta ya kai wata tara sai fa
jikin Inna yayi tsanani sosai,gashi Mudi da
Indo ne masu kula da ita,dan Ayuba dai ya
shiga layin yan shaye shaye.

Ko da Indo ta
fada ma Hajjo halin da ake ciki,ita take kula
da ita da rana,saboda yara sai ta ke
komawa gida da magrib ta barwa Mudi kula
da Innar.

Hajjo ta ce ai jinyar mace sai
mace,bari Baban Garbati ya dawo za ta
tambaye shi in ya so ita take kwana da
Innar,Indo ta ce da wannan tsohon ciki
Hajjo za ki iya?

Hajjo ta murmusa kwarai
ma kuwa,ina iya komai fa.

Da haka su ka
rabu.

Baban Garbati Alhaji Basu be yiwa Hajjo mu
su ba,dama ya san halin da Innar ke
ciki,dan haka da Hajjo ta fada ma sa
bukatar ta sai ya sa Mairo ta yi kiran
Garbati.

Ko da gogan na ta ya ji zancen sai
ya ce sam ba da shi ba,ya ce Baba ni wlh
ban iya kwana ba Hajjo,caf wannan ba ma
maganar dauka ba ne Baba!

Gaban Hajjo ya
fadi,ta fara karanto addu’oi cikin ranta,ba ta
da buri da ya wuce dai na kwana rumfa
daya da Garbati.

Garbati ya dube ta ya ce yo Baba idan ta
tafi bukatata kanwa zan na sauke ta eh
Baba?

Alhaji Baso dai da ya gane in da
Garbati ya dosa sai cewa yayi toh toh na
gane,toh ke Hajjo kin ji daga bakin mijin ki.

Hajjo ta ce wlh Baba Inna ta na bukatar
taimako!!

Garbati ya ce wlh nima ina
bukatar mata ta!!!

Hajjo ta watsa ma sa
harara,ji take kamar ta kurma ihu.

Alhaji ba so ya nisa,ya ce ina ke
Hajjo,yanda za a yi ki na zuwa wajan Innar
ta ki da safe ma na,in ya so da magariba ta
yi yar uwar ta ki ta karbe ki ki dawo dakin
mijin ki,ko kuwa?

Hajjo ta san idan ta yi
wasa wannan damar zai wuce ta,dan haka
ta amsa da toh Baba,na gode,da ga gobe
zan fara zuwa.

Alhaji Baso ya ce Allah ya
sauwake.

Bayan tafiyar Hajjo Garbati yay ta mi ta,wai
fa ana ma sa katsalandan fa,Allah ya bashi
kudi ya tashi ya bar gidan ya huta,Alhaji
Baso ya ma sa banza,Mairo ce ma ta taya
sa da ameen,mu ma ma huta da masifar
ka,ya bita zai daka,Iyalle ta hana,kawai sai
ya fice ya na ta bala’i,wai ana so a kar shi
a gidan.

Jikin Inna dai ba dadi,kurji ya zame mata
ciwo mai cin jiki.

Yan da Alhaji Baso ya ce
hakan Hajjo da Indo su ke,suna ba ta
kulawa matuka,duk da kuwa ta so hana
Hajjo amma ta dage,dan haka ta kyale ta
tana ta ci musu albarka,fadi ta ke in ban da
diya mace wai zai ma ka wannan gatar?

Wanda ba su da shi Allah ya ba su.

Alhaji
Garbati kuwa da Magariba ta yi za ka gan
shi kofar gidan su Hajjo,gudun kar ma ya ji
shiru ta ce za ta kwana,kullum ta na mita
ta ke bin shi zuwa gida,wata rana ta ki
fitowa da wuri amma sai ya jira ta ya tisa
kyeyar ta zuwa gida.

Bayan an idar da sallah magariba Hajjo
zaune tsakar gida tare da Inna,Inna ta sa ta
dauko wata fanteka,kayan jarirai ne,riguna
uku da wandunan su,sai kuma atamfa da
sabulun wanka da na salo,dai kuma kayan
yaji da ga can kasa.

Inna ta ce Hajjo
wannan kayan uwa ne,gashi nan na mi ki
na fita hakkin ki na baki tin yanzu kar ki
haihu ba na nan.

Ido cike da kwalla Hajjo ta
ce dan Allah Inna ki dai na magana haka,ki
nan mana,ina za ki kuma?

Indo da tuni ta
zo ta fito daga daki ta na fadin Inna
kuwa,ai kin san zancen ta kenan Hajjo.

Inna
ta murmusa kawai,ta ce da Indo ta dai aje
kayan gun ta,hankalin ta zai fi kwanciya.

Ana haka sai ga yaro wai Hajjo ta fito in ji
Garbati.

Hajjo ta ja tsaki.

Indo ta ce sai ki
tashi ki tafi kafin ya ta jero aike,Inna ta ce
aifa!

Cikin sirniki kamar ba za ta fita ba
take shiryawa,Garbati ya yi aike har yara
biyar,sannan Hajjo ta mu su sallama,za ta
fita kenan Inna ta ce ya ki nan Hajjo,Hajjo
ta dawo ta zauna gaban Inna,Inna ta ruko
hannun ta cikin musabaha ta ce diya ta
Hajjo,Allah ya mi ki albarka,Allah ya azurta
ki da ‘ya’yaye na gari,ya ba ki diya mace
mai kamar ki wacce za ta tausaya ta ji
kanki kamar yanda ki ke min.

Idanun Hajjo
cike da kwalla ta ce amen Inna,ameen Allah
ya baki lfy.

Cikin zolaya Indo ta ce Inna yau
kuma har da musabaha..yaro ya kara
shigowa wai Hajjo….gani nan dallah!

Hajjo
ta katse shi kafin ma ya karasa.

Inna ta
murmusa,ta ce Allah ya sadu mu da
alkhairin sa Hajjo,tashi ki bi mijin ki.

Hajjo
ta saki hannun Inna ta ce amen,sai da safe
Inna,ta yiwa Indo sallama ta tafi.

DEDICATED to The Women Of Virtue
(group)
[6:34pm, 5/15/2015] Khadija Sidi:
DIYA MACE
Garbati na ma ta mitar ta jirga shi ta ki
fitowa ta ma sa shiru,gaba daya ji ta ke ba
ta jin dadi,ta rasa me ke damunta.

Washagari da asubar fari Mudi ya buga
musu gida,ya zo yayi kiran Alhaji Baso,Hajjo
na bacci ba ta ma san an yi hakan ba.

Da
tashi sallah ta ga Garbati ba ya nan tai ta
mamaki,yau wata rana Garbati an tashi
sallar asuba.

Gari yayi dan haske ta fara aikace aikacen
ta sai ga Garbati ya dawo,biye da shi Mudi
ne,gaba daya a rikice ya ke,ganin sa gaban
Hajjo ya fadi,ta daure ta ce maraba da
Mudi,fuska cike da damuwa ya ce Hajjo
shirya mu je gida jikin Inna yayi
tsanani…..wayyo Allah Inna ta na shiga uku
na lalace!!!!!

Ihun da ta sa kenan!

Ihun na
ta ne ya fito da su Iyalle da Kande daga
daki dake da ma su sun san halin da ake
ciki,Hajjon ce dai ba a fadawa ba.

Ke dallah ba na san shashanci!

Wani abu na
ce ya sami Innar?

Za ki sa fa na fasa tafiya
da ke idan hauka za ki min!!!

Hajjo ta ruke
bakin ta tana fadin na yi shiru,wlh na yi
shiru dan Allah kai ni wajan Inna ta!

Garbati
ne ya dauko ma ta mayafin ta,su Iyalle ma
sai ba ta baki suke,su ka kama hanyar
gidan su Hajjo.

Ko da su ka Isa Hajjo ta ga Jama’a a kofar
gida,wasu suna alwala,sai ta kara fasa
kuka,Mudi ya ja hannun ta ya na fadin kar
fa ki yiwa kan ki illa,ki yiwa mutane shiru
Hajjo,shigar su gidan ta kara ganin mata a
tsakar gida,ta ns shirin faduwa Mudi ya
ruko ta,dakin Inna ya shige da ita.

An yi mata sutura dama Hajjon ake jira su
yi sallama a tafi da ita,tsakar dakin ta ke
kwance,Indo zaune gaban ta,hawaye na
kwaranya.

Mudi ya karaso da Hajjo gaban
gawar Inna ya ce ga Inna nan ki ma ta
addua ba kuka ba….Hajjo ta yanki jiki za ta
fadi,Mudi ya ruko ta,nan jikin shi ta zube
sumammiya.

Sai bayan da aka kai Inna aka dawo Hajjo
ta farfado,gaba daya idanun ta sun kafe ta
ma kasa kuka,sai dai surutai kamar wacce
ta fara zarewa.

Gidan na su tai ta
kwana,randa Inna ta yi uku Garbati ya ce ta
dawo gida,su Mudi su ka ba shi hakuri,su
ka ce ya bari a yi bakwai tin da aka yi
rasuwa Hajjo ba ta sami cikakkiyar lfy ba.

Bayan da zai yi ya hakura,amma dan an fi
karfin shi ba dan ya na so ba.

Ranar da aka yi bakwai Hajjo ta tashi da
naguda,ta sha wahala matuka har sai da
aka fara shirin kai ta asibitin gwamnati da
ke gari sai kuma Allah ya sauke ta,ta silbo
diyar ta mace,sai dai ta karu sosai
sanadiyyar girman yarinyar,Fara ce ga tsayi
ga jiki kamar dai Garbati,amma kuma fuskar
ta Hajjo ce sak,kamar ta yi kaki ta tofar….

DEDICATED to The Women Of Virtue
(group)
[7
[16/10 21:46] .: 7:11pm, 5/15/2015] Khadija
Sidi: DIYA MACE
Unguwar zoma ta ce da su Indo da Hajjo ta
sami kanta sosai sai su kai ta asibiti a ma
ta dinki,suka ce toh,ga koshi ga kwanan
yunwa,an rasa Inna an kuma sami karuwa.

Hajjo zaune,ta na ta kuka dan tin da Inna
ta rasu ba ta yi kukan ba sai yanzu,dan
haka sai su ka barta ta yi mai isar ta,dama
dai sun damu da rashin kukan na ta.

Ta yi
ta koshi,sai ajiyar zuciya ta ke,kanwar Inna
ta fara ma ta nasiha na da ta
dangana,Allah da ya bada Inna shi ya karbe
ta,ya kuma ba ta wata diyar mace.

Da haka
Hajjo ta yi shiru,jaririyar ta na ta tsala
ihu,aka ce ta ba ta nono mana,Hajjo ta ki
saboda da yarinyar ta kama sha cikin ta ke
ma ta ciwo,sai da aka sa ta gaba,ta na
kuka haka ta ke shayar da diyar ta ta.

Duk
wannan abun da ake Garbati be tako kafa
ya zo ba,kayan da ke jikin jinjirar ma kayan
da Inna ta bawa Hajjo ana gobe za ta rasu
ne.
Chapter 10 · 0% Book details