← Book details Diya Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 41

Sashe 5

Diya Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta fito hannun ta dauke da jakar buhu,ta ja
hannun Hajjo,ko da Hajjo ta ga Indo na
shirin shigar da su dakin ta sai ta ce Indo
wlh ni ba na so na kara ko minti biyar ne a
gidan nan,dan Allah kawai mu tafi kafin
Garbati ya dawo wlh shi ya hana ni zuwa
dandali,kuma dan iska ne wlh,jiya fa da
daddare cewa ya yi na tube….shhhh!

Indo
ta toshe mata baki,dan Allah Hajjo ki rufa
min baki,muje dakin ki bani labarin kafin mu
tafi din.

Hajjo ta ce ina gama baki lbry za
mu tafi yasin!

Indo ta ja ta suka shige
dakin.

A tsakar daki Indo ta ce yanzu Hajjo
dubi dakin nan da kyau,ki ga yanda aka jera
langa tuwo da miya,jibi akwatin karfen
can,dubi sif din can fa,dubi gadan can mai
rumfa ga kuma na ki an hado mi ki da
shi,duka na ki ne Hajjo,ke ma kin zama ‘yar
gata an mi ki aure kamar yanda ni ma aka
min..Hajjo ta zumbura baki ta ce yo ni ban
ce a min auren ba ai!

Indo ta ja hannun ta
suka zauna bakin gado,ta ce ki na nufin duk
damin kayan nan ba kya so Hajjo?

Hajjo ta
ce ina so mana,amma ni Garbati ne ba na
so,wlh jiya sai da ya yay ta min fada,ce
min yayi na tube riga ta…nan ta kwashe
yanda su ka yi da Garbati ta fada ma
ta,Indo ta saki ajiyar zuciya jin yanda ta
kasance tsakanin su,ta kuma kwabeta da
kar ta fadawa kowa ko da kuwa su Mairo
ne za su yi ma ta dariya da ihu da gori,ta
ga dai su ba a musu aure ba,komai ya faru
kar ta bari kowa ya ji,batun komawa gida
kuma babu,nan ne saban gidan ta shi ya sa
ma Inna ta ce ta kawo ma ta sauran kayan
ta,ga su cikin buhu.

Hajjo ta dubi kayan ta
kalli Indo ta ce wai shikenan an min aure ni
ma zan ta haihuwa kamar yanda ki ke yi?

Indo ta ce eh idan lokaci yayi za ki haihu,ke
ma ki sami katuwar bebin ki da ta fi ta
roba.

Hajjo ta daka tsalle ta ce wayyo farin
ciki,wlh da ko sai na yiwa su Mairo
kambo,ba zan na ba su dani ba yasin!

Indo ta ce dama mana,da ke sai abun ki
babu mai taba mi ki,har fa kudin cefane za
a na baki,da kan ki za ki na girki abun
ki,idan kin so ma sai ki na toya wainar
kwai.

Hajjo ta mayar da mugun yawu ta ce
Allah Indo?

Indo ta ce sosai ma kuwa,can
ba kwanan abuncin ki bane?

Hajjo ta dubi
kwanan da Kande ta ce eh wai ni kande ta
kawowa,Indo ta tashi ta dauko ta tisa Hajjo
a gaba,ta na ci ta na mata dan nasihohi
cikin dabara dan a samu dai ta zauna dakin
mijin ta Garbati…

DEDICATED to The Women OF Virtue
(group)
[12:43am, 5/1/2015] Khadija Sidi:
DIYA MACE
Shi ko ango Garbati kai tsaye wajan abokin
sa Nuhu ya wuce,ya tadda shi cikin dakin
sa kaca kaca kamar ba mutum ke kwana
ciki ba.

Nuhu na ganin sa ya fara ango
ango ango ka sha kamshi….!

Garbati ya
zube kan katifa ya na fadin yo wani kamshi
na sha Baba ya aura min kwaila!

Ai wlh an
bata min rai na!

Jummala ta cuce ni,wlh
kwaila Baba ya aura min,kai da ta tube jiya
ko ni na fita awk yasin ni da na ke na
namiji….hahahahahaaha!

Nuhu ya sheke da
dariyar mugunta,yo in ban da abun ka
Garbati me za ka gani jikin Hajjo?

Kasan
yarinya ce danya sharaf!

Garbati ya buga
kafa!

Ni wlh Nuhu Jummala ce ta cuce ni!

Ta bata min rai na!

Nuhu ya ce ka ce dai
kai ma ba ka gama lalube yan matan tasha
ba!hahaha ashe da saura!

Garbati ya ce
indai Hajjo ce mata ta yanzu na fara lalube
yan matan tasha!

Ta shi ma muje dan
Allah!

Bazan iya jira gari yayi duhu ba!

Nuhu ya tashi har yanzu be dai na dariyar
ba,ya dau wata rigar sa,dan dauda har
annakiya datti da jirwaye ta yi,ya zura,su
ka fito ya ja kufar shago ya rufe,kai tsaye
tasha su ka nufa….

Gidan su Garbati kuwa wuni Indo ta
mata,sai da ta tabbatar Hajjo za ta iya
zama sannan ta saki ranta,dama Inna ce ta
turo ta saboda hakan,kafin Indo ta tafi yan
uwa sun dan lekowa Hajjo,ita ko Hajjo tin
da Indo ta ce za ta haihu ta saki
ranta,dama yarinya ce mai san yara,gashi
za ta na girki,kuma komai na dakin na ta,ai
sai kuma lamari ya fara ma ta dadi.

Indo ta
sa ta yo wanka aka cancada ma ta ado,ta
ce haka za ta na yi kullum tin da ita matar
aure ce.

Hajjo ta ce toooh,abun nema ya
samu!

Iyalle ce ta kawowa bakin Hajjo
abunci,sai yaban ta su ke kuwa ta karrama
su.

Da la’asar sakaliya kowa ya kama
hanyar gida,ko da Indo za ta tafi sai Hajjo
ta fara shirin yin tsiya,da kyar ta lallaba
ta,ta yarda ta zauna a daki shiru ita kadai.

Da abun ya ma ta yawa sai ta zari mayafi
ta ci dammara,ta yi sa’a ba kowa a tsakar
gidan sai ko ta yi ficewar ta.

A waje ta tadda su Mairo suna enter,ta ce
ku da Allah zan yi,kun ji?

Mairo ta ce
yarinya idan Garbati ya kamaki ba ruwana!

Hajjo ta murguda baki ni ina ruwa da shi,za
ku yi da ni ko kuwa?

Hanse ta ce za mu yi
da ke mana,ai sai a fara daga fari,ta yi
saurin daga hannu ta ce fess!

Mairo ta ce
sakan!

Hajjo da Habi suka hada baki su ka
ce los!

Da kyar aka raba gardama Hajjo ta
zama los din Habi ta biyo ta a baya,sai
kuma sauran wasan suka zabi na su,ya dai
danganta da wanda ya riga fada,sun kai su
bakwai.

Kan ka ce me,enter yayi
enter,amma sai aka cinye Hajjo ta zama
kariya,ai kuwa nan aka shiga ma ta waka….

“Wacece wacece?wacece
Kariya,Hajjo ce Kariya!

Ta yi cikin dan tsako ta
Buye a gajeran wando
Kariya!ku fada mana
Ko kuna tsoran ta ne
Yar ficika ta Alhaji
Baba ta ci tuwo ta
Na mana yanga….”
Suna ma ta wakar ta na bin su za ta kama
dan ta shafa kan su ta tsira amma ta
kasa,gaba daya ta hada zufa,ko da Mairo ta
gifta ta gaban ta sai ta yi kanta da
gudu,idanu rufe ba ta ankara ba sai ji ta yi
ta yi gware da jikin mutum,azatan ta Mairo
ce,fadi ta ke yarinya na kama ki,ko da ta ga
kafar namijj sai fa ta sha jinin jikin ta,ta
daga kai a hankali,yayinda ta yi ido biyu da
jajayen idon angon na ta Garbati…..

DEDICATED to The Women OF Virtue
(group)
[16/10 21:44] .: /25, 12:39 AM] Salmah
Ateeku: [11:03am, 5/5/2015] Khadija Sidi:
DIYA MACE
Gaba daya rudewa ta yi,su Mairo ma su
waka tini suka yi shiru babu wanda be
tsorata da ganin Garbati ba.

Cikin tsawa da
daga muryar nan ta sa da ya saba ya ce ke
Hajjo!Hajjo ta daura hannun ta biyu bisa
kanta,ta cure gu daya a durkushe,tana jiran
saukan duka,ya ci gaba da fadin uban me ki
ke a waje sai ka ce shashasha!

Kai ni wlh
an cuceni!

Yau sai kin gane kuranki yarinya!

Ya fizgi hannun ta,Hajjo ta sa kara wayyo
Allah Inna zai kashe ni!

Cikin takaici ya saki
hannun,a fusace yace wlh Hajjo kar ki bata
min rai na,ki wuce mu tafi na ce!

Hajjo ta ki
ta motsa,shi ko Garbati ya gama kulewa,sai
ya sunkume ta ya aza a kafada ta na ihu da
bori,gaba daya warin dadti da gumi da ya
ke ma kadai ya isa sata ihu,sai Mairo su ka
sa ihu,wooooyiii an dauke ta,ya nufuso da
sauri kowa yayi ta kansa,Mairo ta shige
gida a guje,Garbati biye da ita,a tsakar gida
su ka tadda Iyalle ta na tuka tuwan
dare,dan ko dakin girki ba su da shi.

Saura
kiris Mairo ta sa ta bari ta tsallake ta a
guje ta shige dakin Iyalle ta banko kofa
garam!

Iyalle na fadin wakika tsokano ke ko
Mairo za ki lalata min kyaure…sai ga
Garbati ya shigo,ya na huci ya saki Hajjo ta
fadi gaban Iyyale sharaf kamar kayan wanki
fuska cike da hawaye ta dada curewa.

Kai
Garbati ina ka samo wannan fitinanniyar
diyar da aka aura ma ka?

Cikin daga murya
ya ce Iyalle!

Iyalle ki bar ni na jibgi Mairo!

Mairo daga daki ta ce yo ni ina ruwana!

Ni
na ce ta fito?

Iyalle ta ce gaskiya Mairo ita
daya ta fita abunta,ita wannan mata taka
ita ya kamata ka jibga ba diya ta ba!

Ina
ruwan Mairo?

Kande ta fito daga bayan
gida dauke da buta,ta gifta gaban Garbati
ta ce kwarai ko ni ma na ga fitar ta,sannan
ta aje buta ta shige dakin Iyalle.

Cikin
takaici ya ke duban Hajjo,ya ce Iyalle,wai
ya zan yi da yarinyar nan ne dan Allah?

Ya
zan yi ta daina fita kar fa watarana kuma
uban ta ya zo ya ga abun da na gani yau?

Iyalle ta ce aiki za mu ta jibga ma ta,duka
aikin gidan nan ita za ta ke yi,ka ga ba ma
za ta sami damar fita ba.

Garbati ya ce
Iyalle ita fa wannan babu abunda ta iya sai
fitina,za ta iya aiki kuwa?

Iyalle ta ce ba
dai diya mace ba ce?

An gama
magana,koya ma ta za’a yi.

Garbati ya saki
ajiyar zuciya ya ce indai zan sami sauki a
tula ma ta aikin,dan wannan ko dukan ta
zan yi sai dai na daki kashi!

Iyalle ta ce
daga gobe ma kuwa.

Ya dubi Hajjo cikin
zafin nama ya dada cincincibar ta yay daki
da ita,kan gado ya aza ta,tini warin sa ya
game daki,Hajjo ta na so ta toshe hanci ta
na tsoro,ya nuna ta da dan yatsa ya ce ki
ka sake fita sai na jibgeki,shashasha kawai.

Ya ja tsaki ya fito ya rufo kofar dakin,dama
gashi tagar dakin yar karama,ga Garbati ya
gume daki da wari,ga shi kuma ya ja kofa
ya rufe.
Chapter 5 · 0% Book details