Sashe 12
Diya Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hajjo tace la ba komai wlh dama bu ku bata
min ba,Allah ya yafe ma na gaba daya.
Gaba daya jikin su yayi sanyi,Mairo har da
kuka,ita ko Hajjo yau ta ke sallah,da haka
da haka su ka yi sallama Hajjo ta kama
hanyar ta.
Rashin Inna ya sa Hajjo maimakon ta je
gidan su sai ta tafi gidan Indo,dan ko ta je
gidan ba dadi za ta ji ba,sai ma kyara da
tsangwama daga wajan Baba.
A dakin girki
ta tadda Indo,ganin ta da kaya niki niki ta
kama ta sauke ma ta fantekar ta na fadin
lfy kuwa uwar Inna?
Hajjo ta na dariya ta
ce Garbati dai ya sau ni!
Kai kai kai amma
ba dan saki abunda Allah ba ya so bane da
na yi guda,kai amma na mi ki farin ciki,mu
je daga ki fada min garin yaya.
Ta dau
fantekar su ka shige dakin Indo.
Ko da Indo ta ji dalilin sakin sai cewa ta yi
kan sa yayiwa ai,can da su gada.
Ki
kwantar da hankalin ki nan gida na za ki
zauna,sai na gyara mi ki daki daya,idan
Sani ya dawo sai mu je mu fadawa Baba.
Dan murna Hajjo ta rungume Indo,ta ce na
gode Allah ya saka da alkhairi,yan uwa dadi
gare shi.
Indo ta ce haba Hajjo ai yiwa kai
ne.
Ya Inna?
Ta daina kukan dare?
Hajjo ta
sinto Inna da ta ke ta famar baccin ta,ta
mikawa Indo ta ce gata ba ta daina ba,ita
ta yi baccin ta da rana,da dare yayi ta hana
ni sai dai a tashi a yi hira.
Indo ta dara ta
na kallan Inna,ta ce ayya Allah sarki ina
ruwan Inna,Allah dai ya raya ma na
ita,Hajjon ta ce amen amen.
Da Sani ya dawo ya ji batun Hajjo,ya goyi
bayan zaman ta a gida,ya kuma ce maza
su je su fadawa Baba kar su yi laifi,dan
haka Hajjo da Indo su ka kwashi kafa su ka
je gun Baba.
Be mu su tarbar mutunci
ba,sai ma fadan da ya hau su da shi,wai ai
ya ji batun sakin,me zai mu su yanzu da su
ka zo su ka sa shi gaba?
Tin wuri Hajjo ta
je ta nemi afuwan mijin ta ya dawo da ita
dan shi ba zai iya hidima da ita ba ya yi da
wannan diyar ta ta ba,ka sayar da akuya ta
dawo ta na cinyema dusa.
Kai a kasa Indo ta ce dama Baba na zo ne
neman alfarmar a bar Hajjo ta zauna gida
na….yoo da shi ne ba ki yi bayani tin wuri
ba?
Baba ya katseta,ai ba sai ma kin
tambaya ba,tai ta zama har mahadi ya
bayyana,ni menene nawa a cikin tin da
aljihuna ya kubuta!
Jiki a sanyaye su ka ma
sa sallama.
DEDICATED to The Women Of Virtue
(group)
[7:20pm, 5/18/2015] Khadija Sidi:
DIYA MACE
ya ce a sauka lfy,su ka fita,sam ba
soyayyar Baba cikin ran Hajjo,bare yau ma
da ya gama fita daga ranta.
A soro suka
gamu da Mudi,shi ya raka su hanya,Indo ta
fada ma sa halin da ake ciki.
Yayi bakin ciki
da halayyar da Baba ke nunawa diyoyin sa
mata,yay ta bawa Hajjo baki har su ka yi
sallama.
Gidan Indon Hajjo ta yi zamanta,har ta
gama Idda Garbati be zo biko ba bare kuma
batun kome,diyar sa kuma ta yi wata
hudu,amma tsinke be taba siya mata ba.
Da
yammacin ranar lahadi Hajjo zaune cikin
dakin da Indo ta ba ta,ta na yiwa Inna
wasa,Indo ta shigo ta na umm su Hajjo ma
su diya!
Ta na dariya ta aje Inna ta ce wlh
ki ga fa har zama ta ke….Inna ta yi luuuu
za ta fadi Hajjo ta ruko ta da sauri ta na
dariya.
Indo ta ce Auta hankali!
Maza ki
karasa ma na yar Innar ta mu mu yi biyu
babu.
Duka dariya su ke.
Duk da ba wani
abu na daban ta ke ci ba,kwanciyar hankali
ya sa ta canza ta yi kyau,gashi haihuwar
da ta yi ya sa jikin ta yayi kyau,ta yi diri
mai kyan gaske.
Indo ta ce Sani ne ke kiran ki.
Hajjo ta ce
aw ya dawo?
Ai ban sani ba da na ma sa
barka da sauka,gani nan zuwa.
Indo ta ce
kar fa ki tsaya sirniki,So ya ke ya fita, Hajjo
ta ce Indo ho toh mu je gaba daya,ta biyo
ta dauke da Inna.
A tsakar gida kan tabarma su ka tadda
shi,hannun sa ruke da tasbaha.
Hajjo ta
zauna daga farkon tabarma yayinda ita
kuma Indo ta zauna sosai bisa tabarma.
Sannu da zuwa Babn Aisha,sunan da ta ke
kiran sa kenan,da ke diyar Indo ta fari
sunan ta Aisha,sunan Indon ta ci.
Cikin
sakin fuska ya amsa ma ta,su ka gaisa
sosai.
Ya kara da Hajjo za ki iya aikatau a
cikin birnin kano?
Ta na murna,abun nema
ya samu kila za ta bar kumurya ko ta rage
wasu bakin ciki da su ka sami wajan zama
cikin zuciyar ta,ta ce wlh babu aikatau din
da bazan iya ba.
Shi kan shi Sani sai da ta
bashi dariya bare kuma Indo,tace ka ji
azarbabi,kya dai yi shiru ki ji karashen
batun ko?
Hajjo ta ce tam!
Sani ya cigaba
da fadin gidan da na ke musu direbanci
ne,mai gidan ya jima da rasuwa,kusan
shekara goma kenan ma muna tare,duk
‘ya’yan Hajiyar Maza ne su uku,biyu
magidanta ne,sai kuma autan ta dan
saurayi nan da wata hudu shima zai yi
aure,kuma ba a kasar zai zauna ba shi ya
sa ma su ka damu a samo ma ta yar aiki
da za ta na debe ma ta kewa duk da de ba
wani aiki ba ne a gidan ba yara.
Baki washe
Hajjo ta ce yasin zan yi!
Ah ah toh ya za a
yi da Inna?
Tambayar Indon da ta katsewa
Hajjo farin cikin ta kenan kafin Sani kuma
ya dawo ma ta da farin cikin ta da ta jin
amsar sa na dama sai da ya fadawa
Hajiyar,ta ce ba komai indai na yaba da
hankalin ta,na kawo ta sai ta ji nawa Hajjon
ta ke so a matsayin albashin ta…ko nawa
ne wlh ni zan yi!
Caraf Hajjo ta amshe.
Indo
dai ba son tafiyar Hajjon ta ke ba,sai ta
kara da za ta na biyo ka ne kullum kuna
tafiya tare kuma?
Sani ya ce ah ah su
wacce za ta na kwana su ke so…ai ba
komai sai na kwanan ma,yaushe za mu
tafi?
Ta na magana ne yayinda ta yunkura
ta tashi,Sani ya ce duk sanda ki.ka shirya.
Toh bari na fara shiri yanzu sai mu tafi
gobe,ta tashi da sauri ta shige ciki.
Indo ta ce toh fa,ka ga rawan jiki,toh Allah
dai ya fisshe mu alkhairi.
Sani ya tashi ya
na fadin ameen,kar ki damu Indo,mutane ne
ma su kirki,ba za ta sami matsala da su
ba.
Indo ta ce Allah ya sa,Sani ya amsa da
ameen,sai na dawo,ta ce adawo lfy.
Tin asubar fari Hajjo ta shirya tsaf ta shirya
diyar ta,dan dakar ta iya bacci ma saboda
zumudi da Allah Allah gari ya waye,wai
Hajjo ce za ta shiga birnin kano,wayyo dadi
abunda ta ke fadi cikin ran ta kenan.
Da
gari yayi haske sosai Indo ta kama mata
karin kumallo dan Hajjo ta gagara fita ta
dauka da kanta,sai da Indo ta tsaya kanta
sannan ta ci,ita kawai a tafi a tafi.
Indo ta
bata kayan shafa,har da turaren shafawa su
“aba rai dadi” da “danduwala” ta mata fada
sosai,ta kula da kanta da kuma Inna,birnin
kano girma gare shi,shi ake kira timbin giwa
ko da me ka zo an fika,gwara ta bi hankali.
Toh kawai ta ke cewa dan ba ma ta jin
ta,ita dai kawai a tafi.
Har mota Indo da
‘ya’yan ta su ka rako ta,suna ta daga ma
ta hannu,baki washe ita ma ta ke daga
musu,ta takure gidan baya Inna zaune bisa
cinyarta…. su ka nufi birnin dabo,gari mai
mata mai mota,gari ba kano ba dajin Allah!
/ l \
/ l \
/ l \
/ l \
DEDICATED to The Women Of Virtue
(group)
[7
[16/10 21:46] .: 25, 9:38 AM] Salmah
Ateeku: [2:41pm, 5/27/2015] Khadija Sidi:
DIYA MACE
Ko da su ka shiga garin baki Hajjo ta
saki,idanu bude kamar za su fado ta ke
kalle kalle,garin acike ya ke taf da
jama’a,kowa da irin sa da irin salon shigar
sa,ga motoci ga hayaniya,ga gidajen
sama,kai kano sai ka ce duniyar ce gaba
daya?
Tambayar da take maimatawa cikin
ranta kenan.
Ita ko Inna tinda ta ji iskar
mota ta noke jikin maman ta sai bacci.
Hotoro G.R.A sunan unguwar da Sani ya
shiga.
A gaban Wani katan gida,mai dauke
da ado da bishiyoyi na fure ya tsaya ya na
danna hon,da sauri maigadin gidan ya bude
gate,Sani ya karasa ciki.
Dan al’ajabin
kyauwun gidan ihu ne kawai Hajjo ba ta sa
ba,tin da ta ke ba ta taba gani gida irin
wannan ba,toh sai dai a kalandar da su
Mudi ke kawo gida daga boko,wai amma
yau ga ta ita ce cikin gidan.
Da wannan
tunani ta ji Sani ya tsaya ya na fadin Hajjo
ga mu a kano,a sa takalmi a sauko ko?
Cikin rawar jiki ta fara jijjiga Inna,ke Inna
tashi ki ga aljannar duniya!
Inna ta motsa
ba tare da ta farka ba,hannun ta kamkame
jikin Hajjo.
Sani ya fito ya bude mata kofar
yayin da ta sauko ta na mitar nauyin baccin
Inna kamar na uban ta Garbati!
Dariya Sani
ya ke ma ta,ya taimaka ya fito ma ta da
kayan ta da na Inna,ta saba Innar a baya ta
sa zani ta daure.
Sani a gaba hannu dauke
da ghana must go din Hajjo,ita kuma biye
da shi,ta daura fantekar kayan Inna bisa
kanta su ka shige cikin gidan,tana mamakin
yanda Sani ya san kan gidan dan lunguna
da su ke ta kutsawa dan ta san kafin ta
gane sai fa an kwala duk da Inna ta ce ta
na da kan gane waje.