← Book details Diya Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 41

Sashe 16

Diya Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

DEDICATED to The Women Of Virtue
(group)
[16/10 21:47] .: /25, 9:44 AM] Salmah
Ateeku: [7:34pm, 5/31/2015] Khadija Sidi:
DIYA MACE
Budar bakin Hauwa sai cewa ta yi Hajjo na
gode kwarai,Allah ya saka mi ki da
alkhairi,wlh ba karamin gurbi Neena ta cike
a rayuwa ta ba,thanks to you da ki ka iya
yarda na tafi da ita,ta sanadiyyar haka i
knw wat it feels lyk to b a mother,to hold
nd hug a little one dat cal u mother,idanun
ta su ka ciko da kwalla,ta kara da ba dan
Neena ba ina ga da duk wannan ba zan san
su ba.

Subhanallahi!

Hajjo ta fada yayin da
ta daura hannun ta kan na Hauwa,me zai
sa ki ce haka?

Ya kamar kin sare da ikon
Allah?

Ai Allah ne ke bayarwa,dan kin yi
shekara hudu ba ki haihu ba be kamata ki
fidda tsammani ba,ma su yin goma tukun
su haihu su ce me?

Kwallar da ya makale
idanun Hauwa ne ya gangaro bisa kuncin
ta,ta ce ba fidda rai na yi ba,kuma har gobe
ina addua,sai dai mun je manya hosptals da
dama a london ana duba mu,duk sun
tabbatar ba zan iya samin ciki ba bare na
haihu,matsalar kuma ta wa ce ba daga gun
Khalid ba.

Jikin Hajjo yayi san yi,ta
tausayawa Hauwa,ko wace diya mace da
kaddarar rayuwar ta,ita na ta kaddarar
kenan,rashin haihuwa.

Ta nisa tare da fadin
kar ki damu,in da rai da rabo,
Allah mai bayarwa shi zai ba ki.

Ta na
murmushi ta goge hawaye ta ce ameen
Allah ya amsa,dan ma Khalid be da
damuwa akan maganar,ya ce ba su dame
shi ba,tin da Allah ya ba shi ni shikenan,ba
maganar kara aure,ta kare ta na murmushi.

Hajjo ta ce mashaAllahu,na ji mi ki
dadi,Allah ya bar ku tare,ta ce ameen,ta
dan yi shiru sannan ta ce ban sani ba ko za
ki yarda na kara tafiya da Neena,kamar za
ta hana,amma sai ta ga menene amfanin
hanawar?

Kar kishi da kyashi ya sa ta cuci
diyar ta,dan gashi ta zama kamar diyar
turawa dan kyau da kiba,gashi ita ma din
fama ta ke da boko,dan haka sai ta ce me
zai hana?

Ke ma din ai kin zama maman
ta,murna da farin ciki ya bayyana fuskar
Hauwa,tai ta godiya har abun ya fara bawa
Hajjo mamaki,ta tashi ta ce maza Neena zo
mu tafi mu bar Mama ta yi karatu,ta ji ta
na gani ta fita da noke jikin ta,ko daukar ta
Inna ta ki bari ta yi.

Hajjo na tsaka da jarabawa su Khalid su ka
koma.

Ta yi post UME ta ci aka bata
admssion a BUK,foculty of medicen,za ta
karanta MBBS,ta yi sa’a ta ci WAEC din
ta,Jabir ya biya kudin registratoin,Hajjo ta
zama yar Jami’a,ta waye ta goge
kwarai,nan ta hadu da wata Aysha ana
kiranta Ayush,su ka kulla amunta mai karfi.

Tin da ta fara sau biyu kawai su Hauwa su
ka zo hutu,shi ma din ba wani dadewa su
ka yi ba,ta na makaranta ne ta ga kira
international num ta wayar da Hajiya ta ba
ta,ko da ta daga sai ta ci muryar Khalid,a
dar dar ta gaisa da shi gani ta ke kamar zai
ce ma ta wani abu ne ya sami Inna,ga
mamakin ta sai ji ta yi ya ce ya na so ne
ya sa Neena makaranta,amma be san
surname din ta ba,Hajjo ta yi jim,har sai da
Ayush da ke zaune kusa da ita ta fara
tambaya lfy?

Shi ko Khalid da ya ji shiru
sai ya katse wayar a tunanin sa jin shi ne
ba ta yi,ya ce ya kira anjima.

Da Ayush ta
damu Hajjo da tambaya,a karo na farko sai
ta ba ta lbryn rayuwar ta gaba daya,Ayush
har da zubda hawaye,ta ce lalle Hajiya da
zuri’ar ta daban su ke,kin ga kuwa ni
anawa shawarar Hajjo gwara ya sa ta da
sunan shi,tin dadai a hannun shi ta ke
yanzu.

Shawarar Ayush din ta bi,da Khalid
ya sake kira sai ta ce ya sa sunan
shi,dama dai abunda ya ke so kenan,ya ji
dadi sosai,har da yar fara’ar sa,wasa wasa
dai Neena na kara zama tamkar diyar sa.

Hajjo da Ayush na ta tare rai da rai,kuma
kullum Ayush cikin ba ta lbryn wani cousn
din ta da take so ta ke,shi ma Doctor
ne,duka yan gidan su ma haka sun maida
MBBS kamar gadon gidan su,dan san shi da
ta ke ma shi ya sa ta ke course din,amma
shi be ma san ta na yi ba,kuma ta ki
fadawa Hajjon sunan shi,ita dai Hajjon abun
mamaki ya ke ba ta dan tun da ta ke ba ta
taba san wani da namiji ba,bare kuma irin
na Ayush wanda ba a ma san ta na yu ba.
tare su ka yi 3 yrz a Buk old sites (pre-
clinicals),sai kuma su ka koma teaching
hosptal na Amenu kano,sun yi 3years har
sun shiga na hudu,housemanship su ke,shi
ma din watanni kadan ya rage su gama.

Sannan Hajjo na da shekara ishirin da da
uku,diyar ta Inna kuwa na da daya.

Tsabar kawacan Hajjo da Ayus ba wanda be
san su tare ba,komai na su daya,haka ma
group din su,da ke Ana raba whole Class
into 2 groups first Lyk internal medicine Vs
Surgery
a level 4 and 6 While a level 5…into
Paediatrics vs Obstetrics and Gynaecology
(O&G) kuma a kowani department.

Akwai
sub speacialities….sai a ka qara raba su
into no Of speacialities available Lyk into 5
or 6 haka Then sai suke rotating into
kowannen su….every 2 or 3weeks.

Kamar yanda su ka saba,yau ma tare su ke
tafe,Hajjo na ma ta mitar wani young
doctor da ke takura ma ta da kallo,sai dai
ba su hadu ba,ita ta na mamakin me ya sa
doctors ke da masifar san mata ne?

Aysuh
ta dara tare da fadin isn’t dat obvious?

Irin
wandannan docs din nay da basu yi aure da
wuri ba…sun tsaya yin boko,ko toossing din
babe ma basu iya ba….sai ta zo asibiti,kin
ga kuwa dole su duba,Hajjo ta ce toh Allah
dai ya sauwake!

Ayush na dariya ta ce da
Allah ni kuwa ki nuna min wannan Doc din
na ki…ya Salam!

Hajjo ta kau da kai,gashi
nan wlh,daga idun Ayush wa za ta gani?

Cousn din ta ne ma ashe Doc din da Hajjo
ke magana akai.

DEDICATED to The Women Of Virtue
(group)
[6:42pm, 6/1/2015] Khadija Sidi:
DIYA MACE
Baki ne,be fiya tsayi sosai ba,amma sai dai
ba a kira shi gajera ba,ya na da hanci da
manyan idanu,kuma da ka gansa ka ga
bafulatanin mutum.

Ya na murmushi ganin
Ayush din tare da Hajjo,ya karaso gun su ya
na fadin aminan juna,Doc Ayush ya ki ke ya
kawar ki?

Baki budi Hajjo ta ke kallan
Ayush,ganin yanda ta ke ma sa murmushi
ya kara ba ta tabbacin ta san shi,caf Allah
da ya so ma ba zagin shi ta yi ba,da ta sha
kunya,godewa Allah da ta ke nan,ta na ji
Ayush ta amsa da Yaya Suraj,lfy lau,kawata
ma haka,ya su Mama?

Idanun sa kan Hajjo
ya ce lfy lau,kawar ta ki ba ta magana ne?

Hajjo ta yi yake ta ce ina gajiya?

Ya na
murmushi ya ce ko kefa,lfy lau,ya kokari?

Ta ce Alhamdulillah.

Ya mayar da kallan sa
ga Ayush ya ce kanwata akwai maganar da
na ke so mu yi,so zan zo na same ki a
gida.

Cikin jin dadi ta ce toh ya Suraj sai ka
zo.

Ya kalli Hajjo ya ce sai mun sake
haduwa?

Ta ce sai anjima,Ayush ta ce a
gaida su Mama,ya ce za su ji,su ka!

Wuce
idanun sa kan Hajjo.

Hajjo ta ce Ayush?

Dama kin san shi?

Ayush ta ce cousn dina
ne fa,ina famly din su ne na ce mi ki ar ol
doctors,Hajjo ta ce aw fmly din crush din
ki?

Ko dai shi ne ma?

Ta yi saurin ce wa
nooo ba shi ba ne,yayan sa ne.

Hajjo ta ce
toh Allah ya sa dai ayi da mu.

Ayush ta ce
shi da be ma san ina yi ba,toh amen dai.

Maganar Suraj dai akan Hajjon ne,ya je ya
sami Ayush ya ce da Allah ya za a yi shi
wlh kawar ta ya ke so,nd da gaske ya ke.

Duk da maganar ta ma ta ba zata,sai ta ce
toh ba komai,za ta ma ta magana,ya kara
da dan Allah ta taimaka,da gaske son Hajjo
ya ke matuka.

Washagari da Ayush ta yiwa
Hajjo magana,sai ta ce ba wannan
maganar,ba maganar maza ko so ko aure
gaban ta…nan Ayush ta shiga ma ta
nasiha,idan ta ce za ta yi haka ta sabawa
mahaliccin ta,shi da ya halatta aure,da
kuma manzo sallallahu’alihuwasallam da ya
sunnata shi,haka kuma ta yi butulci.

Da
wannan Hajjo ta ce toh za ta yi kokari ta
canza ra’ayi.

Aysuh ta ce dan Allah for my
sake dai ki bawa Suraj dama,wlh mutumin
kirki ne,he is very differnt ko cikin fmly
ma,he is nt jst a doctor,ya yi specialising a
radiology,he is a great Radiologist.

Cikin
zolaya Hajjo ta ce ya kai Crush?

Ayush ta
murmusa ta ce He is exactly lyk him.

Hajjo
ta dara saboda ke Ayush,zan gwada ba shi
chance.

Ayush ta rungume ta ta na
godiya,wayar ta ta dauka ta sawa Hajjo
numbar Suraj din,ta ce dama shi tin jiya ta
ba shi na Hajjon,Hajjo ta ce lalle,da kuma
na ki fa?

Ayush ta ce na san ba za ki ki ba
ai.

Wasa wasa soyayya ta fara nisa tsakanin
Hajjo da Suraj,duk da kuwa Hajjon kara
kawai ta ke ma sa,she is tryn to give him a
chance.
Chapter 16 · 0% Book details