← Book details Diya Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 41

Sashe 37

Diya Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin haka sai ma ya dauko ta cak ya
aje bisa gado,ta ce ni fa ban komawa
bacci,ya ce ni ina komawa,ai yau asabar ba
aiki,pls ko ba za ki yi ba ki kwanta,ina son
ki a kusa,I jst want to hold you,kan Hajjo ta
tanka tuni ya janyo ta jikin sa,ya cire hijab
din ta ya aje gefe.

Kamar yanda ya ce
din,he jst kissed nd hold her,kan kace me
tuni bacci ya sake sace su.

Sai wajen 8
Hajjo ta tashi,a hankali dan kar ta tada shi
ta zame jikin ta.

Ta shige toilet ta yiwo
wanka,sauri sauri amma kuma a hankali ta
shirya cikin kananan kaya rigar ruwan hoda
da wando da ya bi jikin ta amma ba sosai
ba shi kuma blue.

Ta sanya wata yar hular
ta,kafar ta sanye da takalmin ta flat ruwan
hoda ta fito ta shiga kitchen.

Nan ta tsaya
tunanin abun dafawa dan ta makara,ba ta
so ta bar Neena da yunwa.

Dankali ta
dauko Irish ta na barewa,kusan minti goma
sha biyar kan aikin tana yi tana tunanin
rayuwar da ta shiga jiya,saban rayuwa mai
dadi,ta na yankawa ta ji anyi hugn din ta ta
baya,har sai da ta dan tsorata.

Fuskarshi ya kwantar bisa kafadar ta ya ce
ni ne Suuuger,duk duniya ma wa ya isa ya
tabaki in ba Khalid ba,yayi kissing wuyan
ta,I love you suger…murmushi kawai ta
yi,tare da fadin aiki na ke,pls ka kyale ni.

Ya
ba za ki ce you love me to ba?

Thou na san
you do.

Murmushi Hajjo ta yi,dax Khalid for
her.

Ta ce toh tin da ka sani ba sai na fada
ba,dan Allah ka sake ni kar fa Neena ko
mamanta su shigo mu ji kunya…ya ce ba
zan sake ki ba sai kin ce you love me too.

Hajjo ta ce i love you tooo..kamar daga
sama su ka ji muryar Hauwa na fadin
amma dai kun san ba ku kadai ba ne?

Akwai yarinya a gidan A rikece cikin jin
kunya Hajjo ta cire jikan ta da ga jikin
Khalid,shi kuwa Khalid ko a jikin sa ya juyo
ya na kallan Hauwa da idanun ta tuni su ka
kada,kishi kararara ya bayyana a idanun
ta,ya ce ina manners din ki su ke Hauwa?
ba kya iya sallama or atlest ki juya mana
kawai ki tafi abun ki!

Hauwa ta ce no kai
zan tambaya ina manners din ka ya ke?

Na
zaci nan kitchen ne ba dakin ku ba da zan
fara labewa ina sallama,dan kitchen is
meant for everyone,har da diyar ku Neeena
da ta zo neman brkfast ta gan ku yanda na
ganku,ta zo ta fada min,am sure itama ba
ta saba ganin haka cikin kitchen ba may b
dax y ba ta mu ku sallamar ba,ta zo ta fita
ba ku sani ba,musammam ma ni da kai ta
tashi ta saba gani,d presence of a co-wife,b
it her mother or watever is still unsual to
her,be kamata ba,pls ake yin sara ana
duban bakin gatari…ta juya ta fice,kunya da
takaicin ya rufe Hajjo jin Neena ce ma ashe
ta kai maganar..a fusace Khalid ya bi
yanta,ba ta kai ga kaiwa falo ba ya janyo ta
tare da fadin hw dare you za ki kunya ta
‘yar mutane haka,God Hauwa she is her
daughter for crying out loud!ke zai mi ki
dadi aka mi ki haka?

Toh menene dan na yi
hugn din ta?

Ba mata ta bace!!

Hawaye na zuba daga idanun ta,ba ta taba
tunanin rana irin ta yau za ta tsirga cikin
tarihin rayuwar ta ba,ta ga Khalid din ta da
idanun ta jikin wata,kuma da bakin sa ya
na tuna ma ta Neena ba diyar ta bace,gashi
ya na jaddada mata cewa uwar Neenan is
his wife.

Ta ce yes ba diya ta bace,kuma
matar ta ka ce Khalid dan Allah ka kyale ni
na wuce.

Sakin ta yayi,ta shige ciki da
gudu,har zai bita sai kuma ya dakata ya
buga hannun a iska tare da fadin ya salam!

Hauwa za ta iya zarar da ni!

Ita ko Hajjo kasa cigabawa ta yi da girkin
gaba daya,sai da Khalid ya dawo ya ce da
ita kar ta damu ya yi magana da Neena,so
ba wai wani abu bane.

Duk da haka da kyar
ta gama brkfast din,amma ranar ba dadi
zaman cin abunci,kowa yayi shiri,Khalid ne
ya saki jikin sa ya na ta musu hira.

Ita
Hajjo kunyar Hauwa da diyar ta ce
damuwan ta,ta san Hauwa dole ta san
yanzu ita da Khalid ar intimate.

Ita kuma
Hauwa kishi ne damuwan ta,gaba daya ta
tsani Hajjo,haka kuma ta fara jin dacin
Neena cikin ranta.

Ita ko Neena ta manta
da komai,brkfst din ta kawai ta ke ci ta
gama ta hau kan game,fargaban ta daya
Hajjo za ta iya hana ta,ta ce sai dai ta taya
ta aiki a kitchen,dax y sam ba ta san
zaman Hajjo a gida,takura ne da ita,tai ta
sa ta aiki.

Soyayya tsakanin Hajjo da Khalid tai
karfi,idan ba ya dakin ta Allah Allah ta ke
ya dawo,idan kuma ya dawo ba ta san
kwanakin ya kare.

Haka shi ma Khalid,ya
na jin ta har ransa ko dan kwanciyar
hankalin da ya ke samu wajan ta,gaba daya
Hauwa ta fara sauya hali,wanda haka ya ke
taba daga Khalid din har Neena,hakan kuma
ya sa ya ke kwalafacin Hajjo.

DEDICATED to The Women Of Virtue
(group)
[1
[16/10 22:01] .: 12:54pm, 6/14/2015]
Khadija Sidi: DIYA MACE
Mota Khalid ya siyowa Hajjo,ya kuma ware
lokacin da ya ke koya mata,nan da nan ta
iya da ke Hajjo komai idan za ta koya da
gaske ta ke tsayawa ta koya.San da Hajjo
ta cika wata hudu sai ga ta da tsintuwa,ta
fara laulayi sosai.

Ko da Khalid ya lura da
hakan,ya kuma tabbatar da burin sa ne ya
ciki tuni duniyar sa ta zama sabuwa,Hajiyar
sa ya fara fadawa sannan su Jabir da
Nabeela.

Har gida su ka zo taya sa murna
duk da dai suna taka tsantsan saboda
Hauwa,shi ya sa ma Nabeela ba ta yawan
zuwa wajan Hajjo sai dai Hajjon ta je.

Tin
da Hauwa ta san da cikin Hajjo gaba daya
ta susuce,duniya ta mata zafi,duk da sam
Hajjo na gudun duk abunda za ta yi wanda
ta san zai motsa zuciyar Hauwa.

Zama inda
Hauwa ta ke ma dainawa ta yi saboda ta
na yawan laulayi ba dadi kar Hauwa ta ga
kamar da gangan ta ke,gashi ba ta iya
girki,ba ta kuma ta san warin gas ko zaman
dining area gagarar ta ya ke,sai dai ta yi
zaman ta bangaran ta abun ta.

Da fari
Hauwa na jurar yi ma ta girki,daga bisani ta
dai na,haka kawai ta na yiwa mace girki,ita
kuma ta na kwana da miji!

Nan ko nima na
taya Hauwa kokawa,ba zai sabu ba bindiga
a ruwa,ba za a maisheta yar aiki ba.

Dan
haka ranar girkin Hajjo sai dai a samo
abunci gidan Hajiya da ke Hajiyar ba suruka
ta ke da Hajjo ba,diya ta ke da ita,ran da
ba aiki gidan Hajiyar ta ke zuwa ta
wuni,musammam idan ranar girkin ta ne.

Khalid na kaffa kaffa da Hajjo,ta sha
kwararo ma sa amai a jiki,sai dai ya
wanke,hakan kuma be hana shi sake
kwantar da ita jikin sa ba,Hajjo dai ta zama
yar gata.

Wasa wasa,kuma kwanci tashi,da dadi ba
dadi cikin Hajjo ya kai wata tara,yayi girma
sosai wane na Neena,gashi ta kumbura
kamar wacce aka hura,ya sake ma ta
kamanni gaba daya,dama ba tsayi gare ta
ba sosai sai ta zama kamar za ta kife idan
tana tafiya saboda cikin rinjayar ta
yake,Khalid yay ta tsokanar ta wai ta yi
muni kamar a yanka a boye wukar.

Hauwa
kuwa tuni ta bata rawan ta da tsalla,gaba
daya Khalid be jin dadin zama da ita,ta dau
kishi da bakin ciki ta ji zugan ma su ziga
hatta diyar ta ta Neena ta watsar,sam ta
dai na nuna ma ta kulawa irin na
uwa,hakan na damun yarinyar da Khalid da
ma ita kan ta Hajjo,duk da haka Hajjo ba ta
janye Neenan ba,ta barta tana addua Allah
ya sa Hauwa ta farga ta san abunda ta
ke,haka kuma ba ta ga laifin Hauwa ba,after
ol ko wace diya mace ta shiga halin da
Hauwa ke ciki sai abunda Allah ya yi.

Sau
dayawa sai ta ki zuwa dauko
Neena,mussammam idan Khalid na
Abuja,sai dai principal din su Neena ta kira
shi ta ce ba a zo daukan ta ba,idan ya kira
Hauwa sai ta ce ba ta jin dadi,sai ya kira
Hajjo,ta bar aikin da ta ke ta dauko
ta,sannan ta koma bakin aikin na ta.

Hajjo na sane ta ki daukan hutu,tafi so sai
daf da za ta haihu saboda ta samu ta na
motsa jikin na ta sosai.

Ranar da ta ke san
zuwa aiki na karshe kafin ta fara hutun
haihuwar na ta ranar Khalid shi ma ke
shiring tafiya Abuja saboda wani meeting
da za su yi.

Tare su ka shirya da
sassafe,ya sanya suit baki,yayi kyau sosai
kamar dai bakin baturen na Hajjo,ita kan ta
Hajjo ta na alfahari duk sanda ta tuna mijin
ta ne.

Team din su Hajjo na da wani
discussion mai matukar muhimmanci,dan
haka a gurguje ta shirya,by 8 za su fara.

Tare su ka fito,su ka tadda Neena zaune a
babban falo,Ta gaishe su,Khalid ya ce ya
dai?

Ina maman ta ki ba ta kai ki
makaranta ba har yanzu?

Za ki makara
ai,ko ma na ce kin makara.

Neena ta ce
Momma ba ta tashi ba.

Ba ta tashi ba?ba
ki karya ba ma kenan!,aje briefcase din da
ya ruko,kai tsaye bangaran Hauwa ya
shiga,a daki zaune kan gadon ta ya tadda
ta.

Ta ce da shi barka da asuba.

Da ga
bakin kofa Ya ce yauwa Baby-luv,diyar ki fa
ta dade da shiryawa,ke ta ke jira.

Ta ce
wata diyar tawa kenan?tambayar tata ta
bashi mamaki,ya ji kamar an tsaya a baya
san,da ya dan waigo sai ga Neena,ashe
biyo shi ta yi.

Wata diyar ta wa?

Kamin
shiru?

Dawo da kallan sa yayi gare
ta,sannan ya ce kina da wata diyar ne da
ya wuce Neena?
Chapter 37 · 0% Book details