← Book details Diya Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 41

Sashe 35

Diya Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai fa rigimar kwana ta
tashi tsakanin Indo da Hajjo,Indo ta ce
Hajjo ta bi mijin ta ta tafi gida ita za ta
kwana da Baba,Hajjo ta ce ba inda za ta
sai dai Indo ta tafi,Mudi da Sani su ka sa
baki,a dole su ka ce Hajjo ta tafi ta bar
Indo tinda ita ce babba.

Shi dai Khalid ya
na gefe be tanka ba,amma har ga Allah ba
zai so Hajjon ta kwana ba,zai fi so ya tafi
da matar sa.

Shi kuwa Ayuba cewa yayi toh
kai Mudi kai za ka kwana ko?

Dan ni ina da
abun yi.

Mudi ya ce sai na kwana din.

Hajjo ta yiwa Indo da Mudi sallama rai bace
baki zunbure Khalid ya tisa ta su ka tafi.

Sai da su ka dau hanya ya ruko hannun
ta,Hajjo ta yi saurin kokarin fizgewa,ya ruke
gam,ya ce am sorry,am realy sorry Suger!

Ta ma sa banza,ta ma ki kallan sa.

Da ya
ga haka sai ya yi shiru.

Sai da su ka isa
gida,bayan yayi parkin za ta fita ya ce diya
mace kenan,duk abunda Baba ya mi ki,ki ka
iya cire komai a ran ki,ki ka manta, ji yanda
ki ka damu da shi Hajara,diya mace daban
ta ke,Allah ya kara azurta ni da wata bayan
Neena.

Sai da ta bude motar ta sa kafar ta
daya waje ta,sai ta juyo ta kalle shi ta ce
na iya cire wanda ka min daga rai na,na
manta bare na mahaifina da na ke tsatson
shi?

Shiru yayi har ta fice bai sake tankawa
ba dan ta rufe bakin sa.

Ta na shiga babban falo ta ga Hauwa na
zaune,ta kafa ta tsare,sai cika ta ke ta na
batsewa,yau girkin ta Khalid ya fice tare da
amaryar sa har shadayan dare ba su dawo
ba,ta kira ta kira wayar Khalid din be daga
ba,ba ta san cikin aljihu ya aje wayar ba,ga
shi a silent ta ke be sani ba.

Sallama irin na
dan Musulmi kawai Hajjo ta ma ta,ta shige
na ta bangaran.

Khalid na shigowa ta tare
shi da masifa,inda ta ke shiga ba nan take
fita ba,maimakon ya ba ta amsa,gudun kar
rai ya baci kawai sai shi ma ya haye na shi
bangaran,haka kusan sa Hauwa hauka
yayi,gani ta ke Hajjo ta gama asirce
Khalid,ya mutumin da ya gama lallaba ta
dazu dazun nan,zai kuma shigo yanzu ya
ma ta haka?

Ba shakka akwai sa hannun
malami!

Sai kuwa ta shige na ta bangaran
ita ma ta na rusa kuka.

Washagari da duku duku gari ko haske be
gama yi ba Hajjo ta shirya,ta fito za ta
asibiti.

Da ke Khalid ya san halin matar ta
sa da wutar ciki tin da ya dawo daga sallar
asuba ya zauna a babban falo ya na jiran
tsammani.

Ganin ta fito sai ya tashi,ya na
Suger an fito?

Ta kalle shi cikin girmamawa
amma ba sakin fuska ta ce ina kwana?

Ya
ce lfy lau Suger,wuce mu tafi ko?

Hauwa za
ta yi brkfast zuwa anjima sai na kawo mu
ku.

Ita dai ba ta tambaye shi ba dan haka
shiru ta ma sa,shi kuwa ko a jikin sa,shi
mai laifi ne burin sa ya shawo kan Suger ya
farantawa Suger ko ta huce.

Sai da ya duba
Baba sannan ya juya zai koma,ganin Hajjo
ba ta da niyyar raka shi,ya ce Suger dan
taka min mana.

Gudun surutu da mitar Indo
sai kuwa ta biyo sa din,su na fita ta ce ni
fa yau ina da call,so kar ka yi expectn zan
kwana a gida.

Yayi jim ya ce toh yanzu ki
na nufin tin 8 idan ki ka fara aiki ba za ki
dawo gida ba ko kin ta shi?

Ta ce ai kasan
4 na ke tashi,so daga 4 zan fara call din,sai
kuma 8 na safe zan gama shi.

Ya ce
sannan ki dawo gida?

Ta daga kafada ta
sauke tare da fadin ya danganta.

Kai ya
gyada kawai tare da fadin Allah ya
kyauta,sai na dawo.

Ta ce a dawo lfy.

Ya
na tafe ya na tunanin Hajjo,shi fa a aikin
Hajjo babu abunda ya tsana kamar wannan
cal din na ta,dadin ta ma a wata be fi ta yi
sau biyu ba,amma dai ya na tsaya ma sa a
rai.

Ko da gari ya waye sosai,wajan 10 sai
gashi da Hauwa sun zo asibitin,wato sun
aje Neena a makaranta.

Ba su sami Hajjo
ba ta tafi ta fara aiki,sai ya bar Hauwa
wajan Indo,ya tafi office din Hajjo.

Ga
patience zauna akan layin ganin ta,ganin
Khalid ba wanda bai bi shi da kallo
ba,gaskiya ya hadu kwarai.kai tsaye ya
kutsa,ya shige office din.

Ta na duba wata
tsohuwa Allah ma ya so ta gama da ita sai
gashi tsakar office din.

Ganin shi sai da
gaban Hajjo ya fadi,dan duba tsohuwa ta ke
amma ya na ranta,missing din shi ta ke
sosai.

Idanun sa kan Hajjo da ta wani
basar kamar ba ta gan shi ba ya gaishe da
tsohuwar tare da fadin Baba mata ta ta
duba ki da kyau ko?

Tsohuwa ta ce eh,ai
akwai aiki,kai ne mijin ta?

Cikin jin dadi an
yabi Hajjo ya ce eh,tsohuwa ta ce kai
amma ka yi sa’ar mata,Allah ya sa mu ku
albarka.

Ya na dariya ya ce ameen,amma
dai Baba ai ita ta yi sa’a,dubanni fa
kyakkyawa da ni?

Tsohuwa ta ce eh wlh ga
kyau ga ado,eh ta wannan dai ta yi sa’a,ya
kashewa Hajjo ido,Hajjo ta yi rolling idanun
ta,irin kai ka sani,ta ce iya za ki iya
tafiya,sai a je a siyi magani Tsohuwa ta ce
toh madallah.

Ta tashi,tare da yiwa Khalid
sallama ta fice.

Tana fita ya zaga gaban
Hajjo ya yi kissin kumatun ta tare da fadin
u see Suger,har tsofaffi yabawa su ke da
Khalid,you should b glad am urs….ta na ji
wata za ta shigo tsohuwar na fadin ku dan
dakata ya fito,mijin ta ne.

Ajiyar zuciya
Hajjo ta yi gami da fadin dan Allah Khalid
ka tafi am too busy wlh,marasa lfy ke jira
na fa.

Ya ce ni ma mara lafiya ne,wani abu
ya fito min a baki,da sauri Hajjo ta tashi ta
na menene?

Mu gani?daga zaune ya dan
daga kai ya bude baki kamar mai nuna ma
ta abu din.

Hajjo ta dan matsa kusa da shi
kamar ta na tsoran matsawa kusa sosai,ta
ce ka ma kasa tsayawa na gani,ya ce
matso kusa sosai za ki gani,ta na matsowa
yayi saurin janyo ta,cikin zafin nama ya fara
kissing din ta,ta na kokarin kwacewa ta
kasa,dan kan sa ya sake ta,ta yi baya za ta
fadi ya yi saurin ruko ta…..

DEDICATED to The Women Of Virtue
(group)
[7/25, 6:14 PM] Salmah Ateeku: [12:20pm,
6/14/2015] Khadija Sidi: DIYA
MACE
Ta fizge hannun ta tana mayar da
numfashi,ta ce nan office dina ne,ba gidan
ka ba ne,ba dakin ka ba ne,pls kar ka jawo
min mutane su shigo su raina ni mana!dan
Allah tashi ka tafi.

Ya daga kafada ya
sauke tare da fadin ke fa mata ta ce,na fi
bukatar ki fiye da kowa.

Hajjo ta ce plss ka
fita.

Ya tashi ya na murmushi ya ce akwai
abunci wajan Indo,ki daure idan kin sami
dama ki ci.

Tare na ke da Hauwa,ta na mi
ki ya mai jiki.

Ya juya ya fice.

Sai da ta dau
kusan minti goma zaune sannan nutsuwa
ta dawo ma ta,ta cigaba da duba jama’a.

Lokaci lokaci ta na zuwa ta na duba
Baba,ranar har Hajiya sai da ta zo duba
Baba,su Jabir,Nabila ne,Ayush hatta su Doc
Hussaina sai da su ka shigo wajan
sa,masinjoji da nurses ma ba a bar su a
baya ba,kowa na zuwa duba baban Doc
Hajara,sai dai ba a ji ba.

Hajiya ce ta kai
mu su abuncin rana,da za su tafi Nabeela
ta ce ita za ta kawo na dare.

Jikin Baba
kuma ba laifi jikin na sa da sauki,ya na
gane jama’a,ya ga yanda jama’a ke
tururuwan zuwa duba shi,duk dan darajar
diyar sa mace,diyar sa mace ce yau ta
zama abun alfahiri ga jama’a,ta zama
kamar tauraruwa kuma ya ke cin darajar
ta,diyar da be san darajar ta ba,diyar sa
Hajjo,ina ma matar sa Ameenutu na raye ta
ga baiwa da daraja da yayiwa diyar su
mace.

Kai kawo na Khalid kuwa ba
adadi,bini bini sai Hajjo ta ga ya zo ya duba
su,har sai da ta ce ya huta haka da ta raka
shi har mota bayan magrib.

Ya ce toh gobe
da sassafe zai dawo,ta ce Allah ya nuna
mana.

Su ka yi sallama suna missing juna
gaba dayan su.

Washagari da asuba bangaran Baba da ya
shanye ya fara motsi,Hajjo ta tadda Mudi
ya dan jinginar da shi ya sallaci asuba.

Kujera ta ja gaban sa,ganin ta farin ciki ya
bayyana fuskar Baba,ya ce Hajjo,Allah ya
mi ku albarka ke da yar uwar ki,Allah ya sa
diyar ki ta mi ki yanda ki ka min,Hajjo kin
cika diya,da na san haka dadin diya mace
ya ke da ban kyamace ku ba,da na yi
addua’a Allah ya bani diya mace ba adadi,ki
yafe min diya ta,na zalince ki yafe min diya
ta.

Hajjo na murmushi,idanun ta cike da
kwalla ta ce ba komai Baba,ni ya kamata
na nemi yafiyar ka,na kaurace ma tsawan
shekaru,dan Allah Baba ka yafe ni.

Ya na
murmushi ya ce haba ai tsakani na da ku
sai albarka,diyoyi na kun min komai,hakan
zan yi kashi na yi fitsari a sitira yar uwar ki
Indo ta sa hannu ta wanke,da kuwa matan
yayyan ku sai dai su kyamace ni,su ka ma
hana yaran su jikokin na zuwa waje na,na
fada ma mazajen su sai suce na fiya
korafi…..sai ya fashe da kuka,kunya ta
kama Mudi,Indo da Hajjo su ka shiga
rarrashin Baba,har su ka samu yayi shiru.

Haka suna dan hira sama sama,Hajjo ta ce
bara ta karasa aikin ta ta zo,ta tafi ta na
murna Baba sauki ya samu.
Chapter 35 · 0% Book details