Sashe 14
Diya Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sani ya ce ah ah gaskiya Khalid be da
girman kai,amma fa ya na ji da kan sa
matuka,dan duk cikin yayun sa ba wanda
ya kai sa nuna isa da tinkaho,akasali ma
ko su ma yan uwan na sa kokawa su ke,ga
tsafta ko zama a tabarma ba ya yi kar ta
bata ma sa karin guga,ga kyamkyami,be
sha ko cin abu acikin ko wace roba saboda
yan da ake sarrafa su.
Ina ga shekarun sa
ishirin da shida a duniya,be dade da gama
bautar kasa ba,ina wannan karatun na
zanen gine gine?
Ya ma ya ke da suna?
Hajjo ta ce yo ni ina na sani?
Daidai bakin shagon da zai sauke Hajjo ya
faka,ya ce yauwa Ar-chi-tec-ture!
Toh shi
ya gama,auren sa be ma kai wata hudu ba
yanzu…Hajjo na shirin fita daga motar,ta ce
ya ban taba ganin shi ba shi ma?
Sani ya
ce ya na can Abuja ai,da ke shi ma
karkashin company din na su ya ke aiki,na
ji ma da an yi auran na sa ba a kasar za su
zauna ba,can dayan bangaran company na
su da ke a kasar landan zai yi aiki.
Hajjo na
jinjina kai ta fito tana fadin manya
kenan,toh Allah ya sa a yi da mu.
Dan Allah
a gaida Indo da yara Allah ya kiyaye,Sani
ya ce amen za su ji,ta dai kula da
hanya,Allah ya tsare,ta ce amen,ya tafi ta
shiga shago ta karbo din kin Hajiya.
Ba ba
tare da bata lokaci ba ta sami dan adaidai
ta ya mai da ta gida.
Ko da ta ce nawa za ta bashi,ya ce ta kawo
naira hamsin,sai Hajjo ta kame baki,hansin
fa Mallam?
Yo ruwa ka hayar da ni?
Yo toh
ko ruwa ka hayar da ni alkur’an ban biyan
hansin bare kuma nan da nan baki da
hanci,da na sani ma silafowa na yi da kafa
abuna,yasin sai dai na ba ka ishirin!
Kut
amma fa wannan yar kauyen ma ki na
neman rigima,ya kashe adaidai ta ya fito,ya
ce ke wlh na fiki kauyengi da gidadanci ki
biya ni kudina ko na more ki!
Hajjo ta dada
gyara tsayuwa,da daure goyan bayan ta
tamau,sannan ta daura hannu a kugu ta ce
wa za ka more?
Ni?
Toh uban kuturu yayi
kadan bare na makaho!shege ka fasa!
Yasin
ishirin zan ba ka,ka ga dari ne ma a hannu
na sai ka miko min canji zan ba ka!
Kan ka
ce me?
Rigima ta kaure tsakanin Hajjo da
dan adaidai ta.
Wata galleliyar mota ta
zo,da alama gidan Hajiya ta ke san
shiga,amma tsayuwar mai adaidaita a bakin
gate ya hana shi,yayi horn amma ko a jikin
sa,da dai ya gane rigima ya ke da yar
yarinyar da ke tsaye ta ruke kugu sai tsiwa
ta ke gaban sa,sai ya ja tsaki ya fito a
hasale.
Kai Mallam da Allah ka ja gefe kai
yanzu ba ka ji kunyar sa’i sa da wannan
yar tatsitsiyar yarinyar ba?
Sai a sannan da
ga Hajjon har abokin fadan na ta su ka san
da tsayuwar sa,baki bude Hajjo ta ke kallan
sa……Dogo ne,dogo sosai wane Garbati,fari
ne amma irin wanda baki ya ratsa,fari mai
duhu kamar na bakaken turawa haka,ya na
da kyau matuka,ga hanci har baka,kan shi
ya dan tara gashi baki wuluk,amma kadan
irin dai na samarin zamani,be da kiba
amma ya na da kafada irin mai kirar zakin
nan.
Amma ita Hajjo shigar shi ta fi burge
ta,shiga ne na kanana kaya wanda su ka
karbe shi matuka…ba fa wani kunya dan
samari,wannan ba yarinya ba ce tin da ta
san ta toye min hakki na,kowa dai ya san
daga tarauni zuwa nan GRA hamsin ake
biya,na fada ma ta ce wai ishirin za ta biya
ni,ni kuwa wlh sai ta bani kudi na daidai ko
na more ta!maganar dan adaidaita ya dawo
da ita da ga kogin tunanin da ta fada.
Tsaki
ya ja ya sa hannu a aljihu ya fiddo da kudi
naira dari biyu ya mikawa dan adaidaita ba
tare da ya kalli Hajjon ba,ya ce gashi ka
ruke har canji!
Ya shige motar ya ja gefe ya
faka.
Mai adaidaita ya ce Allah ya cece ki
yarinya,Hajjo tace yarinya na bayan uwar
ta,kai dai Allah ya ceta da yau ka yi biyu
babu!
Suna musayan magana har ya fito ya
shige gidan ba tare da Hajjo ta ankara ba.
Mai adaidaita ya tada babur din sa ya na
kiran Hajjo matsiyaciya,ta na kai ne
matsiyaci!
Sai da ya tafi sannan ita ma ta
shige gida.
DEFCATED to The Women Of Virtue
(group)
[7
[16/10 21:46] .: :49pm, 5/31/2015] Khadija
Sidi: DIYA MACE
Ranar aka yi dinnar,Hajjo da Dada da yara
aka bari a gidan,washagari aka kai amarya
gidan ta a court road.
Bayan sati daya
kuma jirgin su ya kyeta hazo.
Bayan
hayaniyar biki ya lafa,Hajjo ta je kumurya
domin fadawa Indo maganar makarantar da
za ta koma,Indo ta ce ta yi dabara Allah ya
taimaka dai,ya za ta yi da Inna?
Ta ce
Hajiya ta ce ana barin ma ta ita,ta ce toh
madallah.
Bayan dawowar ta Jabir ya kai
ta makarantar abokin sa,prestige gurls
collage,duk da dai ba ta ci test din da aka
ma ta ba aka samu aka makala ta a JS
1,Jabir ne ya biya kudin uniform da books
din ta,da ke abokin sa ne,ya kuma ce Hajjo
cousin din shi ce sai ya dauke ta on
schlarship.
Hajiya ta ji dadi kwarai,gashi
makarantar kusa ce,dan haka Hajiya ta sa
Hajjo ta yaye Inna indai makarantar ta ke
so ta yi da gaske ga shi dama babu abun
da ba ta ci kuma ta saba da Hajiyar,sai ta
ke barin ta gun Hajiya,Inna na wata tara
aka yaye ta.
Kullum da tashi da asuba ba
ta komawa bacci ta ke hawa kan aiki,kafin
lokacin makaranta ta gama kome ta tiwa
Inna wanka,sai ta je makarantar ta,2 na
rana ana taso su ta dawo gidan Hajiya,da
la’asar kuma ta je islamiyar da ke kusa da
gidan Hajiya.
Rayuwar makarantar na matukar bawa
Hajjo wahala,Hajjo ba turanci,ba ta iya
ba,ba kuma ta ji,so ko ya ta dan
jagwalgwala sai ka ji dalibai sun dare suna
ihu,gashi an hana hausa,in ka yi sai ka biya
naira goma,tin Hajjo na biya ta ga ana
shirin tatiketa abun ba na hankali ba ne ai
kuwa sai ta dage da kwaba turancin ta,a
rana be fi a karbi naira hamsin ba,shi ma
din da kyar da sudin lodayi.
In ka ji Hajjo na
told me wen I say d hausa mana!!!!!!
Toh fa
an kama Hajjo ta na hausa an rubuta sunan
ta,an zo an ce ta biya,da kuwa har dari
biyu karbe ma ta ake,wato ta yi ya taru.
Kullum in ta je gida tai ta gwarancin
turancin ta ko Allah ya sa a daina karbe ma
ta kudi.
Sam ba wani alamar Hajjo ta yi
aure,bare ta na da diya,tini ta saje da
daliban,amma kauyencin Hajjo ya sa ta yi
suna a makarantar,ko ina ka bi ka ji ana ina
spoke the hausa,sunan da aka sa ma ta
kenan.
Da aka yi exam din first term Jabir
ya zo ya karbar ma ta result,ba labari Hajjo
ta dauke ajin,da ke ya san background din it
was very poor,sai be damu ba,haka second
nd third term ma.
Ana shirin ma ta repeatn
Jabir ya roki arziki da a barta,what is
important shi ne kawai ta zo makarantar.
Da su ka shiga JS2 sai Hajjo ta ba da
mamaki,ta fara jin turanci sosai,kuma
tsabar kar a karbi kudin ta ba ta jin kunyar
kwaba turancin ta,ga ta gwana ce,kwaruwa
ce wajan maths,kan ka ce mai sai ga Hajjo
ta fito sahun goman farko,duka terms din.
Jabir da Hajiya sun ji dadin kwazon
Hajjo,da aka fara siyar da form din Junoir
WEAC na science bord abokin Jabir ya ce a
siya Hajjo ta gwada,da ke abun na Allah ne
sai sai kuwa ta ci,ta sami Gurl science
Garko.
Murna gun Hajjo be musantuwa.
Duk
da JS 2 ta ke an gwada ne kawai a ga ya
kwakwalwar ta ta take gashi kuma sun
sauke alqurani a makarantar islamiya,su na
shirin fara hadda da littafai na addini.da
Jabir ya ga ta ci sai kawai ya ce kawai ta
tafi abun ta.
Lokacin Hajjo ta cika shekara
goma shabiyar,Inna kuma an yi biyu,da
Hajjo ta ga za ta makarantar kwana sai ta
yanke hukunci mayar da Inna kumurya
wajan Indo,Hajiya ta ce a bar ma ta
ita,Hajjo ta ce ita ma za ta so haka,amma
gaskiya ba za ta iya dorawa Hajiya
dawainiya ba,sanda dai ta na prestige
zaman Hajiya da Innar na dawainiya na
awanni ne,yanzu kuwa shekaru ba wasa ba
ne.
Da haka din aka yanke hukuncin mayar
da Inna kumurya.
A wannan karan ne
Khalid da Hauwa su ka sauka gida Nigeria
domin yin hutun su na karshen shekara
bayan sun shekara biyu a london.
Murna
gun Hajiya be musantuwa,dan da saukar su
gidan Hajiyar su ka fara zuwa,sai dai har
su ka tafi ba su hadu da Hajjo da Inna ba
sun je Kumarya.
Ana saura kwana hudu Hajjo ta tafi
Garko,Jibril da Hajiya su ka ba ta kudi ta yi
siyayya,Sani ya kai ta kasuwa,a gida wajan
Hajiya.
Hauwa da Khalid su ka zo gidan.
Hauwa ta kara fari da kyau sosai, Tin da ta
kyallara ido kan Inna ta ke ta bibiyar
ta,dama tin usul ta na san yarinyar,gashi
auren su 2years amma shiru ko batan wata
ba ta taba yi ba,duk da dai shi Khalid be
damu ba ya ce lokaci ne be yi ba,da yayi
Allah zai kawo ma su albarka.
Shima din
dake Inna tashi ce,tin shigowar su ya ke
makale da ita.
Suna zaune tare da shi da
Hajiya,Inna ta yi bacci kan cinyar sa.
Hauwa ke tambayar Hajiya ina maman Inna
kuwa?
Tin da mu ka dawo ba mu hadu ba.
Hajiya ta ce kai haba?
Ai kuwa da kyar za
ki gane ta idan ki ka ganta,Hajjo ta ta zama
yar birni yar boko,ta ma tafi kasuwa siyo
provisions za a shiga Ss1,ta sami admision.
Hauwa ta ruke baki kai ya aka yi ta yi sauri
haka?