Sashe 34
Diya Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ganin yanda kofar gidan ya
kwarabe sai da gaban ta ya fadi,bare da ta
shiga gidan,kamar ba nan ne Innar ta ke
rayuwa ciki ba da,gidan ya lalace,ya
kazance.
Muryar Indo ta ji ta na musayan
magana da matan su Mudi,Indo na fadin
wlh sam ba ku kyau ta ma na ba,amma ba
laifin ku ba ne,laifin mazajen ku ne,idan ku
be haife ku ba ai su ya haife su.
Tare su ka
ce eh mun ji din,yo ba shi ya ce a bashi
garwashin ba,sai mu hana shi?ace mun
yiwa siriki rowa?
Muna fama da yara muna
fama da tsoho,ai idan ba a gode mana ba
ba a zage mu ba.
Baba kwance gaba daya
hannun sa na dama ya kone,yatsun duk sun
durkushe,sai nishi ya ke dan azaba,bakin sa
karkace daga alama barin jikin sa ya
shanye.
Hajjo ta yi sallama jiki sanyaye.
Indo ta amsa ta na yauwa Hajjo gwara da
Allah ya kawo ki,ji yanda Baba ya sanya
hannun shi cikin garwashi ya kone dan
Allah!
Sai ta sa kuka…Matan Su Mudi su ka
rude ganin Hajjo,dake sun santa tin kafin ta
auri Garbati,tare su ka yi wasa,amma
zaman kauye sun tsufe sun tsomare kamar
ba sa’annin Hajjo ba.
Su ka fara laha’ila
Hajjo,Hajjon ce kuwa!
Ko ta kan su ba ta yi
ba,ta karasa wajan Baba da tin randa ya ce
ta zauna wajan Indo ba ta kara sa shi a ido
ba,gaba daya ya tsufe ya tsomare saboda
cuta da rashin gata.
Gaban shi ta zauna ta
na hawaye.
Jin ana Hajjo Hajjo!
Idanun sa
runtse sai yayi sauri ya bude ya na ina
Hajjo?
Ina diya ta Hajjo,ku hada ni da Hajjo
na nemi gafarar ta!
Indo ta ce yi magana
Hajjo,taba shi ya jiyo ki!
Hajjo ta sanya
hannun ta cikin na Baba,ta kasa magana
sai kuku.
Tana kuka Indo na kuka.
Su kuwa
matan su Ayuba sai abun ya zama mu su
na kallo.
Sani Hajjo ta nema,su ka yi sa’a shigowar
sa kumurya kenan,ya ce gashi nan tafe.
kafin su iso Indo ke ba ta lbryn yanda aka
yi Baba ya kone,wai cewa yayi a bashi
garwashi zai yi turare,da ke Baban ba lfy
gare shi ba,ya na cikin turaren ya yanki jiki
ya fadi,sai hannu ya fada garwashi,gashi
bangaran jikin sa ya shanye,ba daman
ihu,baki ya karkace ko ya yi ihu ba mai ji
bare a ka masa dauki,matan ‘ya’yan sa ba
sa iya kula da shi,sai da babban dan Mudi
ya gifta ta dakin ya ga Baban ya fasa
ihu,shi ne fa aka zo aka cire hannun.
Mudi
da Ayuba sun dawo,sai mita su ke wai laifin
Baba ne,shegen rigima na tsoho,ina shi ina
turare!
Abun mamaki da kudirar ubangiji a
nan shine diyoyin matan na sa da ya guja
ya ke kyama,ya ke kira da jidali su ke jin
kan shi su ke tausayin shi,su kuma ‘ya’yan
na sa maza da ya nunawa gata sam ba su
damu da shi ba,shi ne ma ya zame mu su
jidali su da matan su,sun ma daina kiran sa
Baba sai rikitaccan tsoho.
Jin yanda su ke
wa Baban ran Hajjo ya baci,ta ce da Sani
ya sa Baba a mota,su fara tsayawa a gida
ta dan wanke konuwar in ya so sai wuce
kano.
Hakan ko aka yi,gidan Indo a tsakar
gida aka yiwa Baba shimfida,Hajjo ta wanke
konuwa ta ma sa dressing.
Zaune gaban sa
ta na ma sa fifita Sani ya ce bara ya samo
mai ya kara a mota sai a tafi.
Fitar shi ba
da dadewa ba sai gashi ya dawo tare da
Khalid.
Jin muryar Khalid cikin gidan gaban Hajjo
ya fadi,ta tashi da sauri ta shige ciki ba
tare da ta ko daga ido ta kalle shi ba bare
ma ta ga yanda ya ke a birkice.
Daga ciki
ita da Hajjo su ke jiwo maganar su,ya na ta
jajanta jikin Baba,gashi ganin Hajjon kan sa
ya ji dadi kwarai.
Sani ne ya kwallawa Indo
kira,ta fito su ka gaisa da Khalid,ba dan ta
na fama da ciwan Baba ba da babu abunda
zai hana ta dariya ganin Khalid ba yanda ta
saba ganin sa ba,yau takalmin ma hadin
bauta aka sako,lalle kanwar ta ta ruda
shi,dake ta ba ta lbryn abun da ya faru.
Khalid ya ma ta ya mai jiki,tare da fatan
samin lfyar sa.
Sani ya ce da Indo ta
kawowa Khalid dadduma bara ya je ya karo
mai.
Khalid ya ce ka bari mana a tafi a
tawa motar?
Sani ya ce da ke har da su
Mudi za a tafi,wajan ba isar mu zai yi ba.
Khalid ya ce eh haka ne,toh a dawo lfy.
DEDICATED to The Women Of Virtue
(group)
[7/25, 6:13 PM] Salmah Ateeku: [12:01pm,
6/14/2015] Khadija Sidi: DIYA
MACE
Daga can gefe ya na fuskantar inda Baba ke
kwance ya zauna bisa dadduma.
Indo ta
zauna ita ma daga gefe,su na dan
tattaunawa,Khalid ya kawo maganar
Hajjo,ya ce wato Yaya ta(sunan da ya ke
kiran Indo tin da ya auri Hajjo)na ji dadi
kwarai da na ga Hajjo na kula da Baba,da
har ina zargin ta da kin kula da lamarin sa
da ma lfyar sa,ki ga sanda ya kwanta
dinnan ko duba shi kin zuwa ta yi.
Indo ta
murmusa tare da fadin ai ina ga duk cikin
mu babu wanda ke kula da Baba kamar
ita,ka ga kwanciyar ta shi da ka ke magana
a kai,eh kwanciyar da yayi ba ta je ta duba
shi din ba,amma ita ta biya duka kudin
asibitin,ina sanda ka zo ka ke tambaya ta
wa ya biya kudi ka je biya aka ce an biya?
Ai ita din ce ta biya.
Khalid ya ruke baki
tare da fadin ikon Allah,wani abun sai
Hajara,a haka sai ka yi zatan ba ta damu
ba!
Indo ta ce ai haka take,ba mai gane
halayyar Hajjo,ita dai kam wuyar sha’ani
gare ta yanda ka san hawainiya haka ta ke
rikida.
Toh amma duk cikin mu babu wanda
Baba ya yiwa ba daidai ba kamar Hajjo.
Ta
ba shi lbryn Hajjo tsaf,ba ta boye ma sa
komai ba,gaba daya jikewa yayi da
zufa,idanun sa sun yi jajur kwalla fal
ciki,wani irin abu ya ke ji game da
Hajjo,tausayi ga kuma abun da ya ke ji na
game da ita da shi kan sa ya kasa ganewa.
Shiru ya yi,ya ka sa magana dan ya rasa
me zai ce yanda ya ke jin kan sa.
Baba ne ya fara tari mai karfi,fitowar Hajjo
da gudu da kuma tashin Indo da sauri
lokaci guda ne,su ka yi kan sa,Hajjo ta
tallafo kan sa hannun ta ruke da hannun sa
mai konuwa,ita kuma Indo hannu bisa kirjin
sa ta ke dan masa luf luf.
Sha’awa su ka
bawa Khalid,yanda su ka damu da mahaifin
na su da yanda su ke ma sa sai dai diyoyin
mata,ga mazan na shi can majalisa suna
hirar su,wai suna jira Sani ya zo su tafi.
Duk kiyayyar ta shi na diya mace gashi
diyoyin na sa mata ne ke ji da shi,su ke ta
hidama da shi,gaba daya soyayyar diya
mace ta shiga zuciyar Khalid,gaskiya duk
wanda be haihu ba abin tausayi ne,haka
kuma duk wanda ya haihu din amma be
sami diya mace ba toh be gama morewa.
Idanun sa bisa Hajjo,sun samu tarin na
Baba ya lafa,ta dauko ruwa ta na bashi da
cokali saboda yanda bakin yayi.
Hasken
farin wata da na fitilar tsakar gidan ya
haske fuskar ta,sai ta kara kyau da annuri,ji
ya ke kamar ya tashi ya je yayi hugn din
ta,kamar ya ruke ta gam ta shige har
tsokar sa,kamar ya yi kissing din ta fiye da
wanda yayi rannan…kamar kamar kamar…
God i love dis woman!
Abunda ya fada cikin
ransa kenan ba tare da ya san ya fada ba a
lokaci guda kuma ya ankare,ya fara tunanin
so yace?
Yes so ne,ya na san Hajara,ya
kuma dade da fara san ta,soyayya da sabon
da yayi da Hauwa ya sa ya kasa ganewa!
Shi kadai ya ke murmushi idanun sa kan
Hajjo,ta kwantar da Baba za ta koma ciki
Indo ta ce kin ko gaisa da mijin ki?
Wani
irin kallo a marairaice na nuna rashin jin
dadin maganar Indon ta yi ma ta.
Shi kuwa
Khalid cewa ya yi bar ta ta huta Yaya
ta,ma gaisa anjima.
Da amsar ta sa ta yi
shigewar ta ta ciki.
Sani ya dawo aka shirya
tsaf aka sa Baba cikin motar Sani,Mudi ya
zauna da shi a baya kan Baba bisa cinyar
sa,Hajjo ta yi saurin shiga gaba.
Khalid ya
ce ta sauko a tashi za su tafi,ta ce wlh ba
za ta shiga ta sa ba,aka yi aka yi ta fito ta
bawa Indo wuri ta ki,da dai suka ga su ka
biye ta Hajjo bata ma su lokaci za ta yi,sai
aka hakura,Indon ta shiga bayan motar
Khalid,Ayuba a gaba,Khalid sai kwafa ya ke
bini bini.
Su ka dau hanyar kano.
Sai wajan goman dare su ka isa kano.
Asibitin nasarawa su ka kai Baba da ke
AKTH suna yajin aikin,ita ko Hajjo haka
daidai ya ma ta,ga ta ga Baba ta fi kula da
shi.
Aka ba su daki V.I.P.,da ke baban Doc
Hajara ne har riga rigan duba shi da kula
da shi doctors din su ke,hakan ya burge
Indo,cewa ta ke hmmmm ilimi dadi,kai ilimi
yayi.
Su kuwa Mudi da Ayuba sai kallo,wai
Hajjo ce ke da matsayi haka har mutane ke
dawainiya da Baba dan darajar ta?
Shi ko
gogan na Hajjo wato Khalid cikin takama ya
ke jin kan sa,yes shine fa mijin Doc Hajarar
nan,gwara kowa ya sani,kamar cingum ya
like ma ta,ko ina ta yi biye da ita ya ke. .
DEDICATED to The Women Of Virtue
(group)
[12
[16/10 21:48] .: 13pm, 6/14/2015] Khadija
Sidi: DIYA MACE
Kan kace mai har an duba Baba an daura
shi kan medication.