← Book details Diya Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 41

Sashe 30

Diya Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin Khalid shiru ta san ya bi ta kofar baya
ya fice,ita ma ta lallaba ta shige dakin ta ta
kwanta,tuni ta fita da ga hayyacin ta.

Da azahar ta na tunanin Neena a makaranta
dan ba ta ji za ta iya fita,sai ga ta ta shigo
dakin sanye da kayan makarantar ta,da
alama dawowar ta kenan.

Ta ce Momma
sannu da gida,ya ba ki zo dauka na ba sai
dady?

Ba ki da lfy?

Ta zauna gaban ta
kamar za ta shige cikin ta.

Hauwa ta kau
da kai ta na ban da lfy,Neena ta yi saurin
ruko hannun ta,Dady ya kai ki asibiti?

Cikin
ranta cewa ta yi ai shi ne asibitin tinda shi
ya daura min,azahiri kuma hawaye ne su ka
fara zuba daga idanun ta,ganin haka Neena
ta rude,tuni ta fara kuka ita ma,ta na pls
Momma ki yi shiru na kira Dady mu je
hosptal,bara na kira Uncle Jabir.

Hauwa na
hawaye ta ce rashin lfy na ba na hosptal ba
ne Neena,ki min addua kawai dan na kusa
zaucewa,aure Dadyn ki zai kara… a razane
ta ce aure?

Me ya sa?

Ya dai na san mu?

Hauwa ta ce ki tambaye shi da kan ki.

Ai
kuwa sai ta tashi fuuuuu ta fice,a falon sa
ta tadda shi,ganin yanda ta shigo ga fuska
shabe shabe da hawaye sai ya tsuke
fuska,ya ce ya dai?

Ta dan yi kasa da
murya ta ce Dady wai za ka kara aure?

Ya
ce haka ne.

Ta ce Dady saboda me ya sa?

Ya ce kin yi kankanta,ba za ki fahimce ni ba
yanzu.

Ta ce ka dai na san mu ne?

Ya ce
na fi san ku akan kowa…ta ce plss Dady
idan ka na san mu kar ka yi.

Ba ta taba
rokansa abu ya ki ba,amma wannan karan
ta zo da maganar da ba wacce ta isa fadan
ta ya amince idan ba Hajiyar sa ba.

Ya ce
ki yi hakuri Neena,it is for your own
gud,dukkan ku,ina san ku,amma dole sai na
yi.

Idanun ta cike da kwalla,yayi mamakin
yanda yar yarinya wai itama ta san ta ya
wacce ta dauka mahaifiyar ta kishi,kai
kishin mata daban ya ke.

Juyawa ta yi za
ta koma,sai kuma ta dawo ta ce wa za ka
aura Dady?

Ba tare da ya ji komai cikin ran
sa ya ce Hajara ce wacce ake kira Hajjo,ta
ce Anty Hajjo ta gidan Hajiya?

Ya ce eh.

Ta
ce Momma ba ta so,Allah ya sa ka fasa
Dady.

Kallan ta ya ke kawai,Hajjo kawai a
tsaye,da ta san matsayin Hajjo a rayuwar
ta,da ta fi kowa farin ciki,amma a sannu za
ta fahimta,har yanzu yarinya ce.

Sai da ta
fice,sannan ya koma ya kishingida.

Ya shedawa Hajiya,har ta fadawa yayye da
kannen Baban maza,su za su yi komai har
sa rana da kai lefe,lokaci ya canja,ya fi san
mazan su kai dan a rage bidi’a.

Sati biyu su ka dauka kafin Sani ya mu su
jagora zuwa wajan Baba,da ke dama Baban
ya san Khalid sosai,sai gashi har da
gayyato yayan sa da kuma Alhaji Baso
baban Garbati,duk da kuwa ba wai warkewa
yayi garau ba,jikin na sa na tashi lokaci
lokaci,karfin hali ya ke kawai.

Lokaci guda
su ka bada kudin na gani ina so,ga kuma
kayan sa rana da lefe,su ka ce wata uku su
ke so a sa,ba mu su su Baba su ka
amince,musamman yayan Baba da ya gaji
da surutan jama’a wai kanin sa ya bar
yarinya ta lalace ta zama yar boko ta ki
aure.

Lefe ma na gani na fada da Khalid ya
hada cikin gaggawa su ka sauke su gaban
su Baba.

Su Baba sun yi mamakin yawan
akwaitinan,ko da bakin su ka tafi bayan an
basu tukwicin su daga kudin da su ka kawo
bisa al’ada tuni magana ya fara zagaye
gari,an kawo laifen birni gidan Alhaji
Mamman,an sauke arziki gidan Alhaji
Mamaman.

Shiko Baba da ya san wacece
Hajjo da irin rayuwar da ta yi a baya ya san
kadan ma ya gani daga sakayyar alkhairi da
Allah ke yiwa Hajjo.

DEDICATED to The Women Of Virtue
(group)
[7/25, 6:05 PM] Salmah Ateeku: [12:17am,
6/11/2015] Khadija Sidi: DIYA
MACE
Hajjo ta na zaune tsakar gida,ta cika ta yi
fam,fashewa ne kawai ba ta yi ba.

Sai ga
Indo ta shigo ta na guda,wato ta gano
kayan Hajjo kenan,har da takawa,ta na rai
dai,rai dai,rai dai!

Ina ma Inna ta na raye ta
ga arzikin autar ta,Hajjo?

Tin da na ke ban
taba ganin kaya,kaya dai irin na akwatin
lefan ki ba!anjiman nan ma Baba ya ce a zo
a kwasa a kawo mi ki idan Sani ya sami
lokaci.

Ko a jikin ta,Hajjo ta ce hmmm.

Indo
ta kara da wata uku aka sanya ranar
ma…..nan Hajjo ta fusata,ta ce na fasa
auren na shi!

Indo ta ce iyye?

Hajjo ta ce
eh na fasa!

Indo ta na tafa hannu ta ce ku
ga wacce ba a yiwa abun arziki dangin
gidan maza!

Akan wani dalili?

Dan an sa
rana wata uku?

Hajjo ta ce haba Indo,ki na
fa gani tun da na amince da auren mutumin
nan be sa kafa ya tako ya zo gidan nan
ba,ko waya ma be min ba,ba shawara ta ba
komai an tashi an samin aure wata uku,na
san Baba zai iya sa awa uku ma ba wata
uku ba tinda dama ba kauna ta ya ke
ba,amma shi ba sai ya tambayi shawara ta
ba!!

Indo ta ce gaskiya be kyauta ba,ai na zaci
kun yi shawara ne,amma ki ma sa uziri be
kai ga a fasa aure ba,ki yi kiran sa
mana….Allah ya sauwake!

Hajjo ta katse
ta,wlh ba zan kira shi ba Indo!

Indo ta ce
toh sai ki yi hakuri tin da ke ma na ki jin
kan ya hana ki neme shi,maganar fasa aure
babu…ta na magana ta shige ciki ta bar
Hajjo na ta faman kwafa.

Khalid kuwa Hauwa ce ta ke gasa ma sa
gurasa danya a hannu,gaba daya ta birkita
shi,ta hana shi kwanciyar hankali,tashin
hankalin yau da ban na gobe da ban.

Har ya
gwammaci zaman Abuja akan kano,ba dan
ya na so ba sai dan ya ba ta lokaci ya yi
nesa da ita ko ta huce.

Idan ya zo kano
shirye shiryen auren sa ya kai shi ko kuma
ya leka site din sa ne,inda ake dankara ma
sa hadadden gidan sa da ya yi designing da
kwakwalwar sa dan zaman mata biyu.

Hajjo
na ransa kwarai,ya na son zuwa ya
ganta,amma ba dama saboda abubuwa sun
cude ma sa,gashi ya daga waya yay ta
kiran ta,amma ba a dagawa,ashe wayar ta
ta faduwa ta yi.

Har ya yi fushi ya ce shi
ma ya dai na kiran na ta,ta zo gidan sa sa
na gaisawa gaba daya.

In dan zai aika ma
ta da sako Sani kawai ya ke bawa,idan aka
kai ma ta ta ki karba,sai Sani da Indo sun
ma ta ca ta ke hakura.

Ana saura wata guda biki,su Doc Hussaina
da yan uwanta likitoci aka kawowa Hajjo
kayan gyara,su cikwaidi,zuman mata,tsumi
har da turarukan tsugunno.

Doc Hussaina
ta ce matso nan ki ji diya ta,dan ni fa
Hajara diya na ke da ke ba abokiyar aiki ba.

Cikin jin kunya ta matsa kusa da ita,sauran
matan ma matsowa su ka yi dan sun san
Doc Hussaina ba da ga nan ba.

Ta gyara
murya ta ce Hajara kin shirya yin aure kin
shirya zaman aure?

Hajjo ta yi shiru,Doc
Hussaina ta ce amsa min mana.

Hajjo ta
gyada kai alamar eh.

Ta ce toh saurare ni
da kyau,auren dai kin taba yi,amma ki sani
wanda ki ka yi da da na yanzu ba daya ba
ne,da bambamci,da ba ki san ciwan kan ki
ba,yanzu kuwa kin san wacece ke,kuma kin
san wa za ki aura,toh fa Hajara sai kin yi
hakuri,dan hakuri shi ke zaunar da ko wace
diya mace gidan mijin ta,Hajara da ba
hakuri da aure dayawa tuni ya mutu,ki yi
hakuri,ki toshe kunnuwan ki,ki kuma runtse
idanun ki,ki sai ta harshen ki,ki ji ki
ji,Hajara ki gani ki ki gani,kar ya hau ki
hau,idan ya hau,shafawa zuciyar ki salama
ta hanyar ambaton ubangiji,ki tuna Allah ki
ke bautawa,ba wai dan shi wanda ya aje ki
gidan na sa za ki yi ba,sai ki ga ke kin
sauko,da iyaye ma sai an yi hakurin zama
bare wani can da ya ganki da hakoran ki
ras da wayan ki.

Sauran su ka ce ba
shakka.

Doc Hussaina ta ce kin ga
watannin farko na aure,nan su ke fara nuna
isa,su a lalle sai sun gwada wannan ikon da
Allah ya ba su kan mace tin da ta zama
mallakin su,ke kuma daure ki gwada
wannan sallamawar da Allah ya yassare mi
ki,kwantar da kai,ba komai ba shi girman
sa,girmama shi,yi ma sa ladabi da biyayya
muddin be wuce gona da iri ba,kar ki yarda
ki yi abunda zai rai na ki,duk da ba ke bace
matar sa ta farko,dole da tambiyar uwar
gida zai tafiyar da ke,da kin ga abunda be
dace ba a musulunce da dabi’ance gyara
ma sa a dabarance.

Kar ki taba yarda wai
kin zama daya da miji ki saki jiki,ki na zama
anyhw,idan an yi abun dariya ki saki baki ki
ta dariya kamar shashasha!

Ah ah Hajara
raini ya ke kawowa,wlh ba ko wani irin
sakin jiki za ki yi da shi ba,kar ki yarda idea
din an zama daya ta shiga ran ki,idan ki ka
bari ya rai na ki kin shiga uku,ki yi yanda
zai yi respectn din ki,ja girman ki ki ja ajin
ki,yan da za ki yi reapectn din sa yayi
respectn din ki,reapect beget respect.

Uwar
gidan sa gaba ta ke da ke,ko da kuwa kin
girme ta,ita ma ba ta girmanta, tare ki
ganta da mijin ta,kar ki yarda daidai da
rana daya tunanin ki fitar da ita ya tsurga
cikin zuciyar ki,ke ma diya mace,kuma ki na
da diya diya mace,ki na da yan uwa,ba za
ki so a yi mi ki ko na ki haka ba,ke ma ki yi
adalci kar ki yiwa wata,amma fa kar ki
yarda ta raina ki.
Chapter 30 · 0% Book details