← Book details Diya Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 41

Sashe 20

Diya Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar ta yi
kuka ta yiwa Hajiya sai ta dawo,Khalid ya
ma ta sallama,su ka fito ya na gaba ta na
biye da shi,sai watsawa bayan sa harara ta
ke.

Ko da su ka kai mota,ya bude ya shiga
sai ta bude baya ta shiga ta rufe.

Sai a
sannan kamshin ta ya mamaye hancin
sa,ya bi numfashin sa,kamshi ne mai dadin
gaske ga sanyi,da ke ta na amfani da
turaren the body shop(indian nyt jesmine)
wanda Suraj ke yawan aiko ma ta da su,sai
kuma wani hadadde kuma dadadden
Humrah da Aunty Hussaina ta ba ta,so
wani kamshi ta ke mai rikitarwa,kaji kamar
ka janyo ta jikin ka ko ka samu kai ma ka
shafa.

Ya lumshe ido ya bude,gaskiya babu
abunda ya kai kamshi dadi a duniya
dadi,zaman Hajjon a baya ya sa ya ki tada
motar,sun kai kusan minti goma a haka,shi
dai be damu ba,as long as ya na jin
kamshin nan,zaman is worth.

Hajjon ce ta
gaji,ta ce ko motar na da matsala ne?ya ce
me ki gani?

Ta ce na ga ba mu motsa ba.

Ya gyada kai, Yes ta na da matsala,as long
as u sitting der,ba za ta tashi ba.

Cikin
mamaki ta ce ikon Allah,me ya hada zama
na a nan da kuma tashin mota?

A hankali
ya juyo suna fuskar tan juna,tini Hajjo ta
daina numfashi na dan sakanni,ganin yanda
mischievous idanun shi ke kallan ta,ta yi
saurin nisar da na ta idon.

Ya lura da
yanayin da ta ke shiga duk sanda ya kalle
ta,she catches her breath duk sanda ya
kalle ta su ka hada ido,kamar yanda shi ma
his hrt beat faster dan normal duk san da
ya sa ta a ido.

Ya na murmushi ya ce am
nt a driver Hajiya…..ido a kasa ta ce nan ne
wajan zama na a motar ka 11 years ago,u
knw dat as well Alhaji… darawa yayi,indeed
ba wai kamannin Hajjo ne kadai ya canza
ba,hatta maganar ta ta sake,ta za ma
brazen!

Juyawa yayi ya na murmushi
mischievously,ya ce yes u made ur
point,noted,so dawo gaba in ki na so mu
tafi,idan kuma kina san ki ta zama ne,i wil
nt mind,cos i love ur scent,ya sunan turaren
ne?

Ta ma sa banza,ya dara tare da fadin
shi ya kamata a kira a ba rai dadi,i soo
much luv it.

Ji ta yi kamar ta fasa fitar,sai dai sakon na
Hajiya ne,kuma ba ta so Hijiyar ta ga ta ki
bin maganar ta da ta fita ta hau dan sahu.

Da wannan tunanin ta fito ta shiga
gaban,kamshin na ta ya kara shigar Khalid
har cikin ran sa,cikin zuciyar sa ya ce
Astagafirullah!

Allah ka yafe mana ni da
wannan baiwa ta ka,dan gaskiya kamshin
na ta ya ma sa,kamar ba shi ne mai sauke
glass ko dauke numfashi da ta gifta shi.

Hmmm duniya juyi juyi kwado ya fada
ruwan zafi.

Ganin ta dawo din,kuma be motsa ba,ta ce
na dawo.

Murmushi ya sakar ma ta,wacce
ita kanta ba ta san na menene ba,yayinda
ya kunna mota su ka fito su ka dauki
hanya.

Babu wanda ya sake magana har ya sauke
ta,ta bishi da Allah ya tsare.

Ya amsa
amen.

Sai da ta shiga gidan da ya kai ta
sannan ya kunna mota ya tafi,ran sa cike
da sake sake iri-iri ya karasa AKTH.

Maimakon Jabir ya taho shi kadai sai ya
taho da abokin aikin sa,Doc Ahmad,wai za
su aje shi na’ibawa.

Khalid na driving
amma gaba daya hankalin sa ba ya
wajen,kamar daga sama yaji Jabir ya ce
wata kanwar ta wa ka ke so?

Hajara?
….kiiiiiiiiiiiii Khalid ya yi saurin ta ka
birki,dan ya kusa bugawa wani jin inda
maganar ta su ta dosa.

Jabir dake zaune
tare da shi a gaba ya daki kafadar sa ya na
dan uban ka ka goga yar motar ta ka da ka
ke ji da shi kamar kwai!

Khalid yayi karfin
hali ya murmusa gami da dagawa wanda ya
kusa bugawa hannu,cikin ba da hakuri,ya ce
ahaf tawa za ta siyi akwalar motar ka
goma,ka ga ko dole na ji da ita!

Jabir ya ce
karya ne wlh,ya rush o karya ka ke!

Gaba
daya dari a su ke,Jabir na shirin cigabawa
da maganar Doc Ahmad ya ce pls mu yi
maganar Hajara,na kusa sauka,ya za a yi
ne?

Wlh shez exactly the womon of my
dream,ga kyau,ga kwalliya irin na matan da
su ka san ciwan kan su,ga sanin darajar
mutane,ga tsafta…. o yes!

Jabir ya katse
shi,she is neat,exceptionally neat wlh,ga ga
ga ga din Hajjo da yawa su ke Alhaji.

Khalid
dai ya baza kunne,ya na jira ya ga iya
gudun ruwan su.

Jin Doc Ahmad ya ce ka
tabbata ba maganar kowa as in ba ta
sasansan ta da kowa ba?

Jabir ya ce etoh
gaskiya.. kafin ya karasa Khalid ya saurin
dakatar da shi ta hanyar tare maganar…
gaskiya nauyin bayani ya ke ma,wato kai
ma Jabir ka iya bugan cikin mutum,ka ma
sa shiru ya na ta sakin layi,baki bude Jabir
ya ke kallan Khalid,Khalid ba kunya bare
shakka ya ce Doc Ahmad,na gode kwarai da
yabon my wife to be da ka yi,amma an ba
da ita.

Jikin Doc Ahmad yayi sanyi,Jabir ya
ce kut!

A gidan ubanwa……

Jabir ka yi shiru
kawai,ya dan kifta ma sa ido,ai Ahmad wil
undstnd,kawai so ka ke na ji ana yaban
Hajarar a gabana dax y,ryt?

Jabir ya ma sa
banza.

Cikin jin kunya ya ce amma gaskiya
Jabir ba ka kyauta ba,kullum na ta ma ka
maganar yarinyar nan,ashe kanin ka ne zai
aure ta ba ka fada min ba?

Jabir ya ce
kasan Allah Ahmadu….be yi da niya ba!

Khalid ne ya kara katse shi,duk bakin Jabir
sai gashi be da ta cewa.

Doc Ahmad ya ce
na gode Khalid,tsaya na sauka a nan.

Khalid ya ce haba ai ba mu kai ga layin dan
Hassan din ba,bari na karasa da kai ma na.

Doc Ahmad ya ce kar ka damu,nan ya isa.

Innocently Khalid ya faka,cike da burin
kunya Doc Ahmad ya sauka,ko sallama be
yiwa Jabir ba.

Ya na fita Jabir ya fara
sirfowa Khalid zagi,har da kun ga shegen
maza!

Gidan ubanwa ta zama ur wife to b?

Kai wai haka ka dada lalacewa?

Karya
kuma Khalid?

Ko a jikin sa ya ce karya kuma sai ka ce
yaro Jabir?

Jabir ya ce in ba karya ba har
yau she ka dawo da za ka ce kun sasanta
da yarinyar nan?

Hankali kwance ya ce ni
na ce ma da ita na sasanta?

Toh da uban
wa ka sasanta?

Idanun sa kan hanya ya
amsa da zuciya ta,yanzun nan na yanke
shawara da zuciya ta dat i hav no choice
buh making her my wife……ko da kuwa za a
maimaita yakin badar!

Dariya mai karfi
Jabir ya saki,ya ce ko ba da zuciyar ka ba?

Ga fili ga doki,ba ma yakin badar kadai ba,a
ma yi na uhud!caf kai rigimar ma ka ma ba
ta sallah wlh.

Na ga dai ba wanda ya kai
ka kyarar Hajjo,child abuse ma ka ke kiran
ta,amma daga dowar ka ka ga ta zama
very beautiful nd sophisticated woman har
ka fara san ta?

Cikin takama da dagawa ya
ce har akwai wani beauty da sophistication
da ya dara na ma tar sa na ke aure?

Ta
hada komai na diya ma ce,she got everyting
na diya mace,Kasan ba maganar so,Hajara
is nt even my type,kawai larula ce ta sa na
ke considering auren na ta,Hajiya ta ce na
mayar da Neena,hankalin wife dina ya
tashi,plus am getting older kullum,at 37 ban
da kids,so zan aure ta ne saboda abu
biyu,na fari ka ga Neena za ta zauna
guna,logically i wil remian her dad,na biyu
kuma d woman wil bear my kids as many
as i want…. hmmmm Jabir ya gyada
kai,very selfish nd arrogant brother i
have,ka san Allah?

Kar ka sake ka matsawa
yarinyar mutane saboda selfish interest din
ka,ta na da wanda ta ke so,u better stay
away from her.

Khalid ya daga
kafada,wannan na ka ra’ayin kenan,wat if
shez interested?

Bare na san she is,dole shi
is cos ko wata mace burin ta ta sami miji
kamar ni,ol women wants an outstanding
man as a husby,kasan ma ta nawa ke sona
ina mu su yabs bare kuma ni da baki na ce
zan aure ta,God she should even b grtful,ai
ina fada ma ta za ta hau murna,I tell u
bro!

Jabir ya murmusa,ya ce ba ko ba Hajjo ba?

Ayi mu gani,..

Da haka su ka isa gidan
Jabir,zai fita Khalid ya ce ya za a yi a min
hanyar Hajara ne?

Na ga da kai ake kama
kafa….Jabir ya ce for ur imformation,yarinya
na da correct man,a Doctor so kar ka bata
lokacin ka!Khalid ya ya yi mika ya na
mischievous murmurshi ya ce ko kai ne
correct man din,d so called doctor sai ka
saurara ka bar wajan bare kuma wani
bare,Khalid ne fa kanin ka,taba neman mace
na rasa ba!

Sai dai ban nema ba!

Jabir ya
murmusa ya ce wannan karan ka ma rasa!

Khalid ya ce no ka bani five month za ka ga
Hajara a gida!

Jabir ya na dariyar yanda
Khalid ke da gadara,ya ce get lost!

Ya na
dariya Khalid ya tada motar shi,ya na a
gaida uwar yan mata,Jabir ya daga ma sa
hannu ya shige gidan sa.

Khalid ya kama
hanya da tunanin kudirin da zuciyar sa ta
yanke,if realy goin to hav a second wife,den
she should b Hajara.

DEDICATED to The Women Of virt
Diya mace 2nd post
Posted by UMMU-ABDOUL on OCTOBER 17,
2016
[16/10 21:47] .: /25, 5:15 PM] Salmah
Ateeku: [7:32pm, 6/5/2015] Khadija Sidi:
DIYA MACE
Da zancen Hajjo cikin ran sa ya
kwana,washagari Allah Allah ya ke yamma
ta yi ya samu ya je gidan Hajiya ya ma ta
zancen Hajjo ya ji ta bakin ta kafin ya yiwa
Hajjon magana,dan ya san sai da yamman
ake samun Hajjo a gida in dai ba weekend
ba.

La’asar sakaliya a gidan Hajiya ta ma
sa,ya ko ci sa’a Hajjo ta dawo.
Chapter 20 · 0% Book details