← Book details Diya Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 41

Sashe 28

Diya Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ihu ne kawai Khalid be
kurma ba,ba shakka Hajjo niyar ta ta kashe
shi,duk abun da ta san ba yayi shi ta ke ma
sa,wa ya sani ma ko guba za ta sa ma sa
a abacin ya mutu ta huta,duk duniya idan
akwai abuncin da ya tsana ya bi bayan
miyar yauki.

Ciki Indo ta koma ta na fadin
saka ma sa mana,ki hado da yajin daddawa
ma.

Toh ta amsa cike da farin ciki.

Ta kawo
ma sa tuwon.

Ga mamakin ta sai ya wanke
hannu,ya dan ci kadan,dandai ya kunya ta
ta,amma da kyar ya ke hadiya,har ya dan
bata ma sa gaban riga.

Bayan ya wanke
hannu ya zauna ya ji zuciyar sa na tashi,ya
ce dan Allah suger taimaka min da leman
tsami,da har za ta hana shi,sai ta tausaya
ma sa,ta dauko ta yanka ma sa,sai da ya
dan sha kadan sannan ya samu nutsuwa,ya
dago ya kalle ta,ya ce come here Suger,ya
nuna kusa da shi.

Ta harare shi ta ce
Hajara ce ba diyar ka ba da za ka min irin
kiran yara.

Tashi yayi ya na murmushi,ya
zo gaban ta,ya durkusa gwiwowi biyu a
kasa,ya ce Hajara yau ga Maighty Khalid
gaban ki,ya zo da kokan baran sa……baki
bude ta tsaya ta na kallan sa.

DEDICATED to The Women Of Virtue
(group)
[7/25, 5:22 PM] Salmah Ateeku: [11:38pm,
6/10/2015] Khadija Sidi: DIYA
MACE
Hajara ki yi duba da soyayyar da mu kewa
diya daya,diyar ki,kuma diya ta,ki amince
na zama miji a gare ki dan cigaba da gina
zuri’ar da za su kasance tsatso daya,idan ki
ka ki aure na,za ki raba ni da diyar ki,ta
riga ta shiga rayuwa ta,haihuwan ta ne
kawai ban yi ba.

Kuma za ki iya auren
wanda kuma zai hana ki rukon ta,tin da uba
aka sani da alhakin riko ‘yaya ba uwa
ba,kin ga kenan mun yi biyu babu.

Hajjo ta
ce dan Allah ka tashi,kar wani ya gan ka
haka na banu.

Ya ce answer me first sai na
tashi.

Ta ce ba zan iya auren ka ba Khalid…
saboda me ya sa?

Saboda am nt ur type?

I
wil try to adjust to ur type,kawai ki fada
min ya type din na ki ya ke.

I promise to b
good,zan yi respectn din ki untill my last
breath,zan kuma so ‘ya’yan mu na ba su
kulawa kamar uba na kwarai.

Hajjo ta ce ba
soyayya,ka san ba na san ka,ta ya za mu
zauna?

Khalid ya murmusa,ba soyayya,amma akwai
respect,ba kya so na,i can do wit dat,ni ma
wai san na ki na ke ba,amma ina san diyar
ki Ameena zan kuma so yaran da za mu
samu a gaba inshaAllah..duk da dai ita ta
fara furta zancen rashin soyayyar sai da
amsar ta shi ta ma ta daci,ita ta fada ne
dan ta na san ji ya yake ji game da ita,ashe
it is ol abt haihuwa da kuma diyar ta da ya
ke so.

Gashi ita har ran ta ta na jin
sa,wanda kuma ke san na ta ya raba ta da
shi.

Yawun takaici ta hadiya dan jika
makogaranta da ya bushe,ta ce ba ni kadai
ba ce mace mai haihuwa a duniya,ka ne mi
wata mana!

Ya murmusa,ai nan gizon ke
saka,ke zuciya ta ta zaba,ke ce zabin rai
na,ba dan haka ba da ina tuni ma na yi
watsi da zancen,i don’t go after gurls,gurls
come after me,nd olryt u ar an exceptional.

Babu yanda zan yi.

Hajjo ta ce ka raba ni
da mai sona,Khalid ya amsa da ba zai so
diyar ki ba Hajara,dan haka be dace da ke
ba!

Ajiyar zuciya ta yi,sannan ta ce zan yi
tunani a kai.

Tunani akai?

Kamar ni Khalid
na zube gwiwowi na kasa na rokeki amma
ki ce sai kin yi tunani?gaba daya kin taba
tsarin rayuwa ta,har kin min gibi.

Hajjo ta
daga kafada ta sauke tare da fadin dax in
za ka iya jira,idan kuma sauri ka ke sai ka
sake saban lale.

Tashi yayi ya na
murmushi,ya ce ba sauri,amma ki sani da
ga yau bazan sake bibiyan ki ba,da fatan za
ki yi tunani da kyau,dan Allah ki yiwa sirika
ta sallama,sai na zo maganar auren mu,ya
zira takalmi,ya na murmushi ya fice,Hajjo ta
bi bayan shi da kallo,kamar ta ce ya dawo
ta yarda,dan ba wai yardan ne ba ta yi
ba,ta na jin tsananin tsoran kishi da
Hauwa,dan ta fita komai,bare uwa uba mai
san auren na ta ba ma san ta ya ke ba.nan
ta yi zaman ta sai da Indo ta fito ta same
ta,ta yi nisa cikin tunani.

Da ta matsa sai
Hajjo ta fada ma ta damuwar ta ne sai ta
fada ma ta yanda su ka yi da Khalid.

Indo
ta ce to menene na ki na kin yarda?

Menene laifin Khalid,Hajjo kar fa ki yiwa kan
ki asara!

Mutum mai asali ga ilimi da komai
na rayuwu?

Ya na san ya aure ki,ya na
kuma san diyar ki,ba kowani namiji za ki
aura ba ya yarda ki zauna ma sa da agola
ba,shi gashi saboda ita din ma ya dage ki
aure shi,wani zancen ba ya san ki ki aje,ki
ka iya zama da Garbati ma bare mutum
kamar Khalid?

Hajjo ta nisa tare da fadin ni
fa kishi da matar shi ne bazan iya ba,ta fini
komai,ni da ita ba gami.

Indo ta ce Hajjo,ya
fa san da matar ta shi ya dage sai ya aure
ki,saboda kina da abunda ya ke bukata
matar shi ba ta da shi,yar ki da kuma
‘ya’ya tsatson ki ya so,kin ga kuwa ba ta fi
ki komai ba din kenan.

Hajjo ta ce
wulakanci ne ban so Indo.

Indo ta ce ai kin
fi karfin wulakanci Hajjo,bare ma Khalid ba
zai wulakanta ki ba,a de bar shi da jin
kai,amma ba wulakanci….Hajjo ta dara,ta ce
aw ashe ke ma kin san halin nan na shi.

Indon ma dariyar ta yi,ta ce waye be sani
ba.

Allah dai ya tabbatar da alkhairi,ki dai
kara nazari Hajjo,ki kuma cire san zuciya ki
zabi hanyar da zai fisshe ki.

Hajjo ta ce
amen amen,inshaAllahu,Allah ya sa mu
dace.

Ta amsa da amen.

Da tunanin Hajjo khalid ya isa kano,shi kan
shi ya kasa gane dalilin da ya sa ta
mamaye zuciyar sa,gaba daya ta mamaye
zuciyar sa,ji ya ke kamar ya kusa fara
numfasa sunan ta tsabar yawan yanda ya
ke tunanin ta a rana.

Duk da haka ya ki
yarda wai san Hajjon ya ke,shi a na shi
daga Hauwa ba zai iya kara san kowace
diya mace ba.

Shigar shi gida be ga Hauwa
da Neena a falo ba,kai tsaye bankaran
Hauwa ya nufa,ya jiyo su a daki.

Da shigar
sa dakin kamshi da ya sani,ya ke balain so
ya shaka,ya bi ta hanci ya shige har cikin
zuciyar sa,be san sanda ya yi subul da baka
ba ya ce ya na ke jin kamshi Suger?

Hauwa
da ke zaune kan gado ta na yiwa Neena
kalaba,da tuni ta ankare da shigowar sa,ta
amsa ma sa zuciya daya ta ce ba Suger ba
ne,Humrah ne fa ya dade ajiye a kan
dressing mirrow na Neena ta zubar garin
tabe taben ta.

A sannan ya gane kwaban
da ya kusa tafkawa,yayi saurin bin ta ta
hanyar yin kwana shi ma ya ce aw Humrah
sunan turare?

Kai amma yayi dadi,ki na da
shi amma ba ki amfani da shi?

Hauwa ta
ce wlh be dame ni ba ne.

Khalid ya karaso
kusa da su,ya zauna tare da fadin ni ya
dame ni,ki na amfani da shi daga yau.

Hauwa ta dara,toh zan sa a kawo min
wani,ina kasan kamshin humrah?

Tambayar
ta sa gaban sa ya fadi,ya na tuninin amsar
da zai ba ta da gaggawa Neena ta ceto shi,
Daga yanda ta ke a durkushe,ta ce sannu
da zuwa Dady.

Da sauri tare da maraba da
gaisuwar ta ta ya amsa da yauwa sannu
my beloved one.

Ya kiriniya?

Hauwa ta ce
kasan ba kiriniya sai shagwaba.

Ya na
murmushi ya tashi gudun kar a koma
maganar humrah,ya ce ki yi san ranki indai
shagwaba ba ce,diyar Khalid ki ke.

Neena ta
ce yauwa Dady.

Hauwa na dariya ta ce
dama kai ka ke kara shagwaba ta.

Ya ce
ita diya tilo ya bazan shagwaba ta ba?

Hauwa ta ce gaskiya fa.

Ya ce in kun gama
kwasame ni a bangare na.

Hauwa ta amsa
da toh.

Ya fice ya na dirga sa’ar shi na
yau,amma lokaci yayi da zai sanar da
Hauwa kudirin sa akan Hajjo.

DEDICATED to The Women Of Virtue
(group)
[11:50pm, 6/10/2015] Khadija Sidi:
DIYA MACE
Kusan sati daya kenan raban Hajjo da
Khalid,kamar yanda ya ce ma ta din ya
daina bibiyan ta,amsar ta ya ke jira.

Da ya
sanar da Hajiya da Jabir yanda ya yi da
Hajjon amma be fada mu su har tsugunna
ma ta ya yi ba gudun sharrin Jabir.

Jabir
ya ce ahaf,dama na fada mi ki Hajiya,jin kai
irin na Khalid ba zai bari ya iya shawo kan
ta ba,gashi kullum rama ya ke kamar kudin
guzuri.

Hajiya ta ce Jabir ai sai ka sa baki.

Jabir ya ce toh Hajiya,gobe zan je na same
ta inshaAllahu.

Hajiya ta ce toh Allah ya kai
mu.

Ba karamin dadi ya ji ba jin Jabir zai
sa baki,ya san Hajjo ta kusa shiga hannu
kenan.

Tattaunawar Hajjo da Jabir a asibiti
Hajjo ta nuna amincewar ta kan auren
Khalid.

Jabir ya ji dadi matuka da yanda
Hajjo ta ke ma sa,komai ya ke so ta
yi,wuyan ta ya yi magana kamar yanka
wuka haka ta ke aiwatar da shi.

Ya ma ta
alqawarin tsaya ma ta a komai kan
auren,sannan kuma ta ba su sati biyu za su
zo su nemi iyayen ta dan yanke maganar
auren.

Da kamar za ta fada ma sa tsakanin
ta da Baba,sai ta ga ai kamar tonawa kan
ta asiri ta ke,gwara su je da kan su,su
ganewa idan su.

Da wannan maganar su ka
yi sallama.

Cikin dalleliyar motar shi da ya sake ya nufi
gidan Khalid.
Chapter 28 · 0% Book details