← Book details Diya Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 41

Sashe 38

Diya Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Juya ma sa baya ta yi ta
fara ninke mayafi,ita sam ba ta lura tare ya
ke da Neenan ba,ta ce no ban da wata
diya,ko Neenan ma ba diya ta bace,ga uwar
ta can Hajjo ta kai ta,ko na haife ta da zan
na dawainiya da ita……?

Ta juyo,sai a
sannan ta yi ido biyu da Neena da ta
karasa shigowa ta tsaya kusa da
Khalid,idanun ta cike da hawaye.

Baki bude
cike da dana sani ta ce Khalid ba ka fada
min ba…ban san tare ku ke ba…idanun sa
jajur,ya murmusa ya ce no ba sai na fada
mi ki ba,abunda ki ka yi kan ki kikayiwa
Hauwa.

Juyawa yayi ya fice a fusace.

Hajjo
da ke zaune falo sai ganin shi ta yi ya fito
cikin bacin ran da ba ta taba ganin sa ciki
ba,ko kallan in da ta ke be yi ba ya nufi
bangaran sa.

Tashi ta yi da kyar da niyar
bin sa,sai ta jiyo muryar Hauwa na kira
Neena!

Neena!

Ga mamakin ta sai ga
Neenan ta fito a guje ta na kuka,za ta shige
Hajjo,Hajjo ta janyo ta baya,hakan yayi
daidai da fitowar Hauwa,ta yi turus ta
tsaya,ita ma hawaye ne fal fuskar ta.

Cike
da bacin rai Hajjo ta tsawatarwa Neena,ta
ce ina za ki?

Ba ki jin Mahaifiyar ki na kiran
ki!!

Jikin Hauwa ya dada sanyi.

Neena na
kuka ta ce ki yi hakuri,amma ba mahaifiya
ta ba ce,ke da ban dauka a matsayin uwa
ba sai gashi ke ce uwa ta,ta fada ita ta
fada da bakin ta…..a gajiye Hajjo ta saki
Neena,maganar Neena ta gajiyar da ita
kwarai.

DEDICATED to The Women Of Virtue
(group)
[7/25, 6:15 PM] Salmah Ateeku: [1:14pm,
6/14/2015] Khadija Sidi: DIYA
MACE
Da gudu Neena ta shige bangaran Hajjo.

Hajjo ta juya za ta bi ta,sai kuma ta
tsaya,ta ma rasa ya za ta yi,Khalid za ta bi
ko Neena?

Gashi sai dada makara ta ke,ta
juyo ta ce da Hauwa,Hauwa zan mi ki
magana a matsayi na na diya mace,zan
baki shawara a matsayin diya mace.

Na
san halin da ki ke ciki,amma karya ne na ce
na san yanda ki ke ji,i undstnd ur
situation,amma you pushing dem away,kina
pushing mijin da ke son ki matuka,you
pushing him to the wall,tura idan ta kai
bango ba ta bullewa,you ar letn him go,d
more u push him,d more he get close to
me,nd am sorry to say dis the more i get to
knw him well,d more i get to love him.

Yanda ya ke san ki duk da kuntata mi shi
da ki ke ya sa na san waye mijin ki,kuma
na kara respectn din shi!

Haka diyar ki,duk
duniya ba wacce ta ke kira Momma,ta ke
kira uwa sai ke,ba kuma wai dan ba na nan
ba ne,ko ba na san ta,ina nan da rai na,ina
kuma san ta,amma saboda compassion irin
na diya mace,na runtse ido na,na danne
zuciya ta,i let u guys b,ba ma sharing din ta
na ke da ke ba,i overly let her b urs,ta na
san ki wit oll passion na diya ga mahaifiyar
ta,amma me u jst pushed her away.

Wake
up nd hold urslf,ko wani dan adam da
kaddarar rayuwar sa Hauwa,bare kuma kina
diya mace,it is part of ur destiny,jst take lyf
d way it is,Allah be cutar da bawan sa,sai
dai bawa ya cuci kansa…dan takaici Hauwa
kasa magana ta yi,har Hajjo ta juya ta nufi
bangaran ta,kai tsaye dakin ta ta nufa,jin
shi a rufe ya tabbatar ma ta Neena na
ciki,tai tai ta bude,amma ta ki,kukan ta
kawai ta ke ji,sai kawai ta juyo,ta haye
sama bangaran Khalid.

Hauwa ma juyawa
ta yi ta shige na ta bangaran cike da da na
sani.

Ya na tsaye hannu cikin aljuhu gaban
window,idanun sa na kallan waje,gaba daya
hankalin sa be wajan,ya ji an taba shi,ya
saki ajiyar zuciya,duk da be juya ba ya san
wacece.

Ta ce am sorry,ka yi
hakuri,undstnd her,try to undstnd,thou ba
lalle ka fahimta sosai ba,diya mace ce
kawai za ta gane,amma itama ba haka ta
ke so ba,ba san ran ta bane,shez tyt,shez
emotionally disturbed,Khalid ya ce ban taba
canza ma ta ba,Allah shi ne sheda ta.

Hajjo
ta ce na sani,itama ba a san ranta ta canza
ba,she need you!

Juyowa yayi ya ruko
hannun Hajjo,tare da fadin no i need you,i
need you Hajara more dan ever….Hajjo ta
girgiza kai,ta ce nd we need ur wife
more,we need each other to survive,i need
her Khalid,ita ce mahaifiyar diya ta,you
need her,am a busy woman,dole za ta
zama part of ur children’s lyf,nd she need
us,we ar fmly.

Khalid ya girgiza kai,ya ce
na so Hauwa,ina san Hauwa ta kasa
ganewa.

Wani irin kishi ne ya tasowa
Hajjo,ta yi saurin kauda shi,amma duk da
haka Khalid sai da ga gani,ya saurin cewa
don’t get me wrong Suger.

Dariya Hajjo ta
yi,ta ce haba worry nt,na fahimce ka,u ar
tryn to make a point,bare kuma idan ba ka
so Hauwa ba ai sai Allah ya tambaye ka.

Hugn din ta yayi tare da fadin u ar ao
diffrnt,ya ba zan so ki ba Hajara?

Ta na
murmushi ta ce nd i u.

Maza ka je wajan
diyar ka,ta rufe kanta a daki sai ka fito mu
tafi na aje ka kar ka yi missing flight na
samu ni ma na wuce hosptal.

Hannun ta
cikin na sa su ka fito,ya na fadin ya fasa
zuwa Abujan yau,zai daga meetn din dan ya
kula da Neena,tai tafiyar ta kawai.

Hauwa kuwa gida ta tafi,ta na kuka ta
fadawa Mahaifiyar ta abunda ya faru.

Mahaifiyar ta ta ta ce ai ga irin ta,za ki yi
biyu babu,kishiyar ta ki da ki ke tinkaho kin
fita komai gashi ta zo ta fiki komai ai yanzu
tsabar rashin hakuri,ita ki ka san menene
na ta kaddarar rayuwar,kawai ganin ta ki ke
amma ki ka san yanda rayuwar ta take?

Ke
kuma ga uwa ga uba,ga gata ga arziki,ga
miji mai san ki so na gaske,ba ki haihu ba
amma Allah ya baki soyayyar diyar wata,ki
ka yi watsi damar ki.

Ta na kuka ta ce
yanzu ya zan yi?

Ta ce ya za ki yi kuwa,ki
je ki nemi yafiyar mijin ki,ku samu ku sasan
ta.

Da wannan kudirin Ta koma gidan ta.

Da dadare Hajjo ta fito da niyar zuwa wajan
Khalid,sai ga Hauwa ta ci ado mai
kayatarwa,wasu irin kaya ta sa wanda su
ka kama ta ma su jan hankalin mai kallo,ta
yi kyau kamar yar tsana,itama din wajan
Khalid din za ta,ganin Hajjo sai ta tsaya.

Ganin yanda ta yi kyau sai da zuciyar Hajjo
ta motsa,amma a zahiri murmushi ta yi,ta
gyada ma ta kai alamar go ahead,ni bara na
koma.

Ita ma Hauwa murmushi ta sakar ma
ta sannan ta haye bangaran Khalid.

Zuciyar
ta na bugawa Hajjo ta koma na ta
bangaran.

Dakin ta ta shiga ta na ambaton
sunan Allah dan kishi ne ya tashi,raban
shedan da ke zuciyar ta ya motsa.

Khalid na zaune ya na Allah Allah ya gama
hade papers din gaban sa ya je wajan
Suger.

Jin an bude kofa yayi zatan ita ce ya
ce Suger Allah Allah na ke fa na gama na
zo gare ki.

Jin an yi shiru be kuma ji
kamshin turaren na Hajjo ba sai ma na
Hauwa ya sa shi dagowa,Hauwar ce gaban
sa,God shez beautiful!

Abunda ya fada
kenan cikin ransa,ita kuwa karasowa gaban
sa ta yi cikin yanga da kissa ganin yanda
ya tsaya cak.

Ta durkusa gaban sa tare da
fadin dan Allah kamin afuwa,na kasance
mace mara godiyar Allah,duk soyyayar da
ka ke min amma nai ta saba ma ka,ka yafe
min Khalid.

Ganin be motsa ba,ta dago su
ka hada ido,ta ga ya na murmushi,ya ce da
gaske kike?

Ta ce cross my hrt!

Cikin jin
dadi ya aje papers,ya ce come here baby-
luv.

Da sauri ta tashi ta shige jikin sa ta na
kuka,ya ce shhhhhh is owk.

Hajjo kwance bisa gadon ta,Ta ji an bude
kofa,daga idon da za ta yi,ta ga Neena
tsaye kofar dakin,ta ce zan iya shigowa?

Hajjo ta tashi zaune tare da fadin shigo
mana.

Ga mamakin Hajjo sai ga ta ta shigo
ta durkusa gaban ta,ta ce Mama,dan Allah
zan iya kiran ki mama a matsayi na na
diyar ki?

Tashi Hajjo ta yi,ta tada ita su ka
zauna bakin gado kamar yaya da kanwa,ta
ce Ameena?

Neena ta ce na’am,ta ce ko ba
ki kirani mama ba ni mahaifiyar ki
ce,wannan ba zai taba canzawa ba,zan fi so
ki cigaba da kira na Antyn da ki ka saba,ki
kuma kira dayar maman taki da Momma da
ki ka saba,kar ki canza ma ta,ita ma
maman ki ce,ta na san ki kwarai kamar
yanda ni ma na ke san ki.

Neena ta gyada
kai tare da fadin na gode.

Hajjo ta shafa
kanta,nan fa hira ta bige,ta ma manta da
Hauwa na wajan Khalid,hira har da
dariya,ta na bata lbryn mai sunan ta,a haka
har bacci ya dauke Neena,Hajjo ta gyra ma
ta kwanciya,ta san Khalid na tare da Hauwa
ana ta soyayya,sai kawai ta yi kwanciyar ta
da diyar ta,a karo na farko kenan tin bayan
da aka dauke ta ta na shekara biyu.

DEDICA to The Women Of Virtue
(group)
[16/10 22:05] .: [2:25pm, 6/14/2015]
Khadija Sidi: DIYA MACE
Washagari cikin jin dadi aka karya,Khalid ya
tafi Abuja,Hauwa ta kai diyar ta
makaranta,Hajjo da ta daina fita ta yi
kwanciyar ta a gida,rayuwa ta fada dadi.

Da
yamma bayan Hajjo ta gama waya da
Indo,ta na tambayar yaya dai?

Ba a motsa
ba?

Hajjo ta ce tukunna,ko yau ko gobe ta
ke sa rai dan ta jin kab ta ba daidai ba,su
ka kare da fatan alkahilairi,Indo ta ce suna
nan suna jiran abun arziki dai.

Aje wayar ta
ke da wuya wani kiran ya shigo,kawar su ce
Yusrah.

Ta daga ta na Yusrah ashe ana
tunawa da mu.
Chapter 38 · 0% Book details