← Book details Diya Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 41

Sashe 3

Diya Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ke tashi!

Baba ya daka ma ta
tsawan da ba ta san sanda ta saki
daddawar Inna ba ya zube kasa,jiki na bari
ta tashi,Baba yace daga yau dawainiyar ki
ta tashi daga kai na kuma ya koma ga mijin
ki,ya mikawa Inna kudin hannun sa,ta ma
kasa karba sai da ya ce ke karbi mana!

Kun
ga shashanci,jiki ba laka Inna ta
karba,Baba ya ce dubu biyar ne ba dari
uku,dari ukun na biya kudin barnan da ta yi
kin dai gani,sai ki siyo ma ta langa tuwo da
miya da kuma dai abunda ki ka san za ta
bukata,kudin sadakin ta kenan,na ce da
Alhaji Baso ba sai sun kawo lefe ba dan ni
ma ba gara zan yi ba,zan kira kafinta ya ma
tsohon gadon da ke dakin can fanti,dan
gobe za a yi jere akai Hajjo dakin ta…..

DEDICATED to The Women Of Virtue
(group)
[12:16am, 5/1/2015] Khadija Sidi:
DIYA MACE
Yauwa Allah ya sa na yar da kwallan
mangwaro zan huta da kuda!

Ya na ware
babbar riga ya shige ciki,Inna sakin jiki ta yi
ta na kallan sa,wannan abu da me ya yi
kama?

Ganin Baba ya shige Hajjo ta kwaso
daddawar da ya zube,ta tashi da sauri ta
mi kawa Inna ba tare da ta san abunda ake
ciki ba,dan dama ta saba da ganin bala’in
Baba dan haka ba ta kawo komai a ram ta
ba,fadi take Inna ungo daddawar ai wannan
dan rainin wayon ne ya biyo wai dan ban
sani ba na buge shi manjan sa ya bare!

Maimakon Inna ta karba kawai sai ta fashe
da kuka,hakan ba karamin dagawa Hajjo
hankali ya yi ba dan ba ta taba ganin Innar
tata ba a cikin wannan hali,ita ma kukan ta
sa tana fadin wayyo Inna ta me ya same ki
ki ke kuka,ni Hajjo na shiga uku na lalace!

Baba dukan ki yayi Inna?

Baba ya na jiyo
su ya musu banza,Mudi da Ayuba su ka
shigo,sun dawo daga makaranta.

Gani uwa da ‘ya na kuka tini hankalin su ya
tashi,da kyar su ka shawo kan Inna ta yi
shiru ta fada mu su dalilin da ya sa su
kuka,Mudi da ke ya mallaki hankalin kansa
shi ya shiga bawa Inna baki,ya tura Ayuba
gidajen yan uwa domin sheda mu su
abunda ke faruwa,kan ka ce me?

Kafin
la’asar tini gida ya fara cika da yan uwa,ita
dai Inna ta zubawa sarautar Allah ido,bare
ita amaryar da ba ta ma san ana yi ba,tin
da ta samu Inna ta dai na kuka ta shiga
sabgarta irin na yara,Baba kuwa tin da ya
sa kafa ya fita be sake waiwayan su ba.

Yanda Baban yace haka ko aka yi,gado mai
rumfa ke aje shekara da shekaru aka fidda
aka shiga ma sa fenti,haka kuma Inna tace
a hada da gadon Hajjo mai spring,sai a
hada ma ta har shi,tinda dai amare ma su
gata gado biyu ake hada mu su.

Indo yayar
Hajjo ta karaso,gaba daya ranta yayi
matukar sosawa,daka su ka zauna ita da
Inna suna jin jina al’amarin.

Hajjo ta ci danmara,fuskar ta cike da
kwalliya an zane da gazar,ta faki idon
jama’a,ta fito sim sim,ba ta ankara ba ta ci
karo da Ayuba dauke da su langa tuwo da
miya da Inna ta aike shi ya siyo.

Wayyo
dan Allah yi hakuri Ayuba,yasin ban san ka
taho ba!Ayuba ya ce Hajjo hankali!

Dama
ina za ki san na taho?

Sai a sannan ya lura
da dammaran da ta ci,ga fuskar an bi an
zane,ya ce ke ina za ki wai?

Cikin yanga
tana tafa hannu ta ce ai Mairo ce ta
gayyace ni fatin yayan ta Garbati,ta ce ma
ba sai na kawo kudin fatin ba ma!

A fusace
ya ce ku ji shasha,fatin kaniyar ki,ba ki san
yanzu ke matar aure ba ce?

Ai kece
amaryar Garbatin!

Hajjo ta murguda baki
caf Allah ya sauwake!

Ya ma samo amaryar
sa kafin dare ya masa,ta yi gatsine.

Wuce
ciki kafin na bata mi ki rai!

Sakarya kawai!

Hajjo ta cije ta ki motsawa,ya ce ba da ke
na ke magana ba Hajjo?

Ta na buga kafa
bakin nan cure ta shige ciki Ayuba na biye
da ita,suna shiga Jama’a su ka fara waya
taba amarya?

Ta mu su banza,kai tsaye
gun Inna ta shige,ta tadda ta tare da
Indo,kan ciyar Inna ta zube ta na ihu an
hana ta zuwa fati!

Ayuba ya biyo ta ya na
fadin kiyi kukan jini ma ba inda za ki je!

Indo ta ce ayya mana Ayuba ka bi ta a
hankali dan Allah!

Ayuba ya ce anki a bita
din,yarinya ace har aure an daura ma ta
amma ta gaza hankali,ba dan Allah ya hada
mu ba ai da an tafka abun kunya,ganin ta
fa na yi za ta gidan sun Garbati wai Mairo
ta gayyace ta fati.

Inna ta kama baki,ai kuriciyar kenan
Ayuba,kuruci dangin hauka,shi ya sa gaba
daya hankali na ya gaza kwanciya kan
lamarin auren nan wlh,yi shiru auta,Allah
zai zama gatan ki.

Indo ta ce amen,amma
ba a kyautawa Hajjo ba gaskiya,ko nima sai
da na kai shabiyar aka min aure,bare kuma
Hajjo da ta ke shabiyu.

Ayuba ya aje langar
a gaban su,ya ce da Indo kar dai ki bari
Baba ya ji ki yarinya,za ki yi bayani.

Ya sa
kai ya fita Indo ta na fadin ya ji ni din,ba
gaskiya na fada ba!Inna ta ce kul Indo,ban
san tsaurin ido.

Indo ta ce na yi shiru
Inna,Inna ta duba fuskar Hajjo sai gani ta yi
ta yi bacci,ta gyara ma ta kwanciya zuciyar
ta cike da tausayin ta.

DEDICATED to The Women Of Virtue
(group)
[16/10 21:44] .: [7/24, 11:57 PM] Salmah
Ateeku: [12:22am, 5/1/2015] Khadija Sidi:
DIYA MACE
Biki dai gadan gadan yin shi ake,da daddare
aka yiwa amarya kunshi. washagari aka yi
jere da wuni,da magrib aka fara shirin kai
amarya sai aka nemi Hajjo aka rasa,da kyar
Ayuba ya gano ta cikin duhun bishiya ta na
ta shan mangaro,ya daka ma ta tsawa ta
sauko.

Da gudu ta shige dakin Inna,jama’ar
biki sai dariya su ke.

Ta na shiga ta ga an
aje kayan sallan ta bisa gadan Inna,Indo ta
ce maza ta sanya.

Hajjo ta daka tsalle ta
na fadin Indo yau sallah ne?

Ashe ban sani
ba!

Ita dai Indo banza ta ma ta,jiki na rawa
sai da ta yi tik sannan ta sanya kayan
sallan na ta,ta bazama za ta fita Indo ta
ruko ta ta na fadin ina kuma zaki amara?

Baki washe ta ce su Mairo zan je na
nunawa dama Inna ta ce na fi su a kyawu!

Indo ta ce ba sai kin je ba,dama mu ma
gidan zamu.

Hajjo ta ce Allah?

Za ku da ni?

Indo ta ce eh dole mu je da ke,ungo
mayafin ki sanya,Hajjo ta karba za ta ci
dammara,Indo ta dakatar da ita,ah ah Hajjo
ba haka ba,a ka za ki rufa,ta karba ta rufa
ma ta ruf,Hajjo ta yi saurin yayewa,ta ce
wayyo Allah,alquran tsoro na ke ji!

Indo ta
ce ke fa shasha ce Hajjo,Allah ki ka ci gaba
da kullar ni buge ki zan yi!

Inna ta shigo ta
na fadin yi ma ta a hankali Indo,auta yi
hakuri ki yafa,Hajjo ta ce toh Inna,ke ma da
ke za a gidan su Mairo?

Inna ta kwauda kai
ta ce ah ah.

Hajjo ta ce saboda me ya sa?

In ce ba iyalle ta aiko mi ki da cingam
ba….?

Kafin Inna ta ba ta amsa sai guda ya fara
tashi,da alama dai masu daukan amarya
sun zo,yayye da kannan Inna su ka shigo
suna fadi toh Hajjo Allah yayi lokaci
yayi,maza Innar ki ta karasa mi ki fada ku
yi sallama kuma sai watarana!

Inna ta
kwauda kai da alama kuka ne ya ciyo
ta,Hajjo ta ce fada?

Toh me na yi da za ta
min fada?

Daya daga cikin yayyen Inna ta
ce nasiha za ta miki,maza karasa gefan ta
ta mi ki.

Hajjo ta karasa wajan Inna ta ce Inna yi
min nisihan toh za mu tafi…..Inna ta fashe
da kuka!

Hajjo ta ce laaaa toh menene eh?

Ke ma so ki ke ki bi mu?

Yo ki biyo mu
mana ko Baba zai yi fada?

Da Allah ki bar
kuka Inna wlh zan rago mi ki kwili da kunun
zaki!

Gaba daya dakin ba wanda be tausaya
mu su ba,ita ko Indo tini itama ta sa na ta
kukan.

Yayar Baba ce ta kamo hannun
Hajjo ganin Innar ba ta da niyar yiwa Hajjon
nasiha,har sun kai kofa Hajjo ta fizge ta
dawo da gudu ta fada jikin Inna ta na fadin
ni ma na fasa zuwa alqur’an na fasa!nan fa
ana jan Hajjo Hajjo na dada kamkame Inna
da kyar aka samu aka bambare ta,Inna na
fadin Allah ya mi ki albarka,Allah ya zama
gatan ki,Allah ya sa ki je a sa’a Hajara.

Hankalin Hajjo ya tashi,ko by h da su ka
kai kofar gida sai ta cije,aka yi aka yi ta
saki kofa ta fito ta ki,ana haka sai ga
Mudi,ko da ya ga halin da a ke ciki,ya kuma
san halin Hajjo,idan ta kafe ko Baba be iya
tankwasa ta,sai kuwa ya cincibi Hajjo,ta na
buri ta na ihu,mata su ka sa su tsakiya,aka
nufi gidan su Garbati,gaba daya ta cika
kunnan jama’a da ihu.

A haka aka shigar da Hajjo har kuryar dakin
mijin ta.

Mudi na dire ta ya daka ma ta
tsawa,amma ko a jikin ta,ita dai ya mai da
ta gidan Innar ta!

Da dai ya ga jan ido ba
zai kai shi ko ina ba sai ya shiga rarrashin
Hajjo tare da alkawarin zai mai da ta gun
Innar sannan ta yi shiru,su Yayyen Inna da
Baba su ka sami damar damkata amana
gun uwar mijin ta wato Iyalle,shi ko Mudi
gida ya dawo abun sa.
Chapter 3 · 0% Book details