Sashe 4
Diya Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
DEDICATED to The Women Of Virtue
(group)
[12:29am, 5/1/2015] Khadija Sidi:
DIYA MACE
Tafiyar su Indo ma fa sai da dabara,sai da
su ka mata wayo wato su ka ce bari su
leka makota suna zuwa,ganin yayar Mairo
tare da Mairon sun shigo dakin na ta sai ta
yarda su ka tafi,ta saki jiki suna ta hirar su
kamar ba ita ce mai kukan dazu ba.
Kande
wacce ta ke sa’ar Indo amma ita bazawara
ce ta ce da mairo ta taya Hajjo hira ta na
zuwa.
Da fitar ta Hajjo ta ce yarinya kin ga
kayan salla na!ai Inna ta ce na fi kuwa a
kyawu,wai ina amaryar Garbatin na?
Mairo
ta ce lalle ma ke Hajjon nan!
Ga ba ki nan
ba!
Ba ki da wayo da ki ka yarda aka aura
mi ki yaya na Garbati!
Hajjo ta harare
ta,waya ce mi ki aurar Garbati na yi?
Allah
ya sitiri bukwi!
Mairo ta ce yarinya an sha
ki ai,ni ce fa na sa Jummala ta fasa auren
Garbati,wlh shekaran jiya da safe dan ban
sani ba na dan tankwabar ma sa da kokan
safe ya kamani yay ta jibga,ni kuwa da dare
yayi na je wajan Jummala na fada ma ta
gaskiya.
Cikin kaguwa ta ji Hajjo ta ce wani
gaskiya?
Mairo ta ce aw kema ba ki sani ba
ki ka yarda aka aura mi ki shi?
Hajjo ta ce
wlh Mairo za mu yi fada idan ki ka kuma
cewa an daura min shi!
Ni ki fada min
dallah!
Mairo ta ce hmmm ai Garbati mugu
ne,wlh mugun ma na gaske,dan ya sibirbide
ki ba wani aiki ba ne,gashi ba ya wanka da
buroshi sai ranar juma’a,warin Garbati sai
ya kar mutum har lahira…Hajjo ta toshe
hanci ta na fadin Allah da gaske Mairo?
Mairo ta ce kwarankwatsa da gaske na
ke,idan karya na ke ki kwace yar babyn roba
na,ke ki ma tambayi Kande ki ji!
Kande ta
shigo,Mairo ta ce yauwa dan Allah Kande
Garbati ba mugu ba ne?
Ai har kema bugu
ya ke ko?
Dan Allah ba baya wanka ba
ba…..ke Mairo!
Kande ta katse ta,ba ki da
hankali ko?
Na kuma ji sai na hada ki da
iyalle,kai wannan diya akwai surutu,karya ta
ke mi ki Hajjo kin ji ko?
Hajjo ta dubi Mairo,Mairo ta kifta ma ta ido
tare da kada ma ta kunne alamar dai Kande
karya ta ke.
Muryar Garbati su ka jiyo daga
waje,Kande ta ce ga angon nan ke Mairo ta
shi mu tafi,Mairo ta tashi da sauri Hajjo ma
tashi ta yi za ta biyo su,Kande ta ce ah ah
ai ke Hajjo nan dakin ki ne,ba ki san Garbati
mijin ki ba ne?
Hajjo ta yi zuru zuru da ido,ta ce wallahi
karya ne,ba miji na ba ne!
Kun ga na ce ba
na so…ni gun Inna zan tafi….kai su waye
cikin dakin nan?
Muryar Garbati suka ji ya
na maganar nan na shi kamar ya na yi da
sama,tini jikin Hajjo da Mairo ya fara bari!
Labule ya daga ya ce ke kande azo a wuce
daki ko?
Su ka kama hanya sim sim za su
fita Hajjo ta ruke Mairo,Garbati ya dube su
ya ce ke Hajjo!
Sau ta!
Ki sau ta na ce!
Kar
ki bata min rai na!
Jiki na rawa ta sake
ta,Mairo ta fice da sauri,Hajjo ta gama
tsorata da Garbati,ta bi bayan Mairo ya
daka ma ta tsawa,ke wai ke ina za ki?
Koma ciki dallah!
Jiki na rawa ta yi baya ta
na wayyo Inna,ni gida zani!
Ta daga ido ta
dubi Garbati,ya kusan yin biyun ta ma,ga
tsayi ga jiki!
Garbati ya ja kofa karaf ya
rufe,ya daga fitar acibulbul da ke ci tsakar
dakin ya haska fuskar Hajjo,murya a sama
ya ce kan uba!
Ku ga kwailar da Baba ya
aura min dan Allah!
Hajjo dai gaba daya ta gama tsorata,dan
jikin ta har bari ya ke,gani take Garbati rufe
ta zai yi da bugu tinda dai Mairo ta ce halin
sa kenan!
Kamar daga sama ta ji ya ce
tube!
Ta yi zaton kunnan ta ke zagi dan
haka ta ce iye?
Ya ce ki tube rigar ki na ce
Hajjo!
Kar ki bata min rai na!!!!!!!!
Jiki na
rawa a gigice Hajjo ta ce wayyo Allah
wayyo Inna wai fa na tube!
Wlh ba zan tube
ba!
Ke Hajjo!
Wlh zan buge ki!
Kar ki bata
min rai na!!!
Ya dada ma ta tsawa,ya yiwa
Hajjo kwarjini,ba shiri sai ga Hajjo ta cire
rigar ta.
Garbati ya dada haske ta,ya ce ahaf!
Dama
wlh na san kwailace Baba ya aura min!
Ku
duba ku ga ko nawa ya fi nata!
Dirgan
dangin ma yanzu ta fara!
Dallah mai da
rigar ki!
Yo ni me zan yi da ke yanzu!
Wlh
Baba ya bata min rai na,ki sa rigar na ce!!!
Jiki na rawa ta mayar da rigar,ta fara shirin
fita,ya ce yo ke ina zaki?
Ta na kuka ta ce
gun Inna zani!!
Ya ce Innalo ba Inna ba!
Haye can ki kwanta!
Ya ma ta nuni da
karamin gado,ta ki hawa,ya ce kar ki bata
min rai na!!!!!
Ya daka ma ta tsawa,jiki na
rawa ta haye gadon ta na kuka,ya dada ma
ta wani tsawar ki min shiru kwaila!!!ko tarin
ki ba na son ji!!!Hajjo ta sa hannu ta toshe
bakin ta tana ta ajiyar zuciya,shi ko Garbati
gado mai rumfa ya haye,ba tare da ya cire
babbar rigar jikin sa ba,ko min ti biyar be yi
ba ya shiga numfashi kamar ba mutum
ba,bacci yayi gaba da shi…
DEDICATED to The Women Of Virtue
(group)
[12:33am, 5/1/2015] Khadija Sidi:
DIYA MACE
Jin munsharin sa ya sa Hajjo saukowa,cikin
sanda ta nufi kofa,ko da ta ja sai ta ki kam
ko motsawa kofar ta ki yi,Garbati ya
sakace,gashi sakatar can sama ne ko ta
taka kujera tsayin ta ba zai kai ba.
Nan ta
durkushe ta na kuka amma a hankali gudin
kar Garbati ya ji ya jibgeta,a haka bacci ya
sace ta.
Washagari sai karfe takwas rana ta fito
Garbati ya tashi,ko sallar asubahi dama ba
ya tashi,sai gari ya waye tangaradau ya ke
yi,ko da ya Hajjo kwance a kasa bakin kofa
sai ya tsallake ta abun shi cikin nuna ko in
kula yay ficewar sa.
Bayan kusan minti talatin cikin bacci ta jiyo
muryar Mairo ta na fadin Iyalle na. tafi
dandali sai na dawo!!!
A firgice Hajjo ta
tashi,ta ma manta inda ta ke,ita ma ta fito
a guje ta na fadin ke Mairo tsaya ni mana
dallah!Mairo tace tsaya ta na fadin toh ki yi
saurk ki wanke bakin ki da ido mu tafi dan
wlh Garbati ya na ciki ya na shan koko,cikin
sauri Hajjo ta dau buta tana fadin toh
Mairo….gidan ubanwa za ku?muryar Garbati
suka ji kamar daga sama,Hajjo ta saki buta
ya fadi kasa hannu na rawa.
Ya nuna Mairo
da yatsa ke zan ci uban ki Mairo,ba ki san
Baba ya aura min ita ba?
Iyalle!
Ke Iyalle!
Sai ga mahaifiyar su Iyalle biye da ita
Kande ce sun fito daga daki da sauri dake
tsakar gidan daya ce,ba wani girma kuma
gare ta ba.
Iyalle ta bi su da kallo ta ce kaka an kayi
Garbati?
Garbati ya ce wlh Iyalle ki shiga
tsakani na da mairo,yo ban da rashin
mutunci Hajjo fa ta gayyata su ke
dandali,har da ta yo sauri ina ciki!
Iyalle ta
ce ke Mairo ba ki san ita Hajjo matar aure
ce ba?
Cikin gunguni tace yo ni na ce ta
biyo ni?
Ba ita ta ce in jira ta ba!
Karya ta
ke,makaryaciya!Garbati ya katseta,Mairo ta
murguda baki tace ba dai ni ba!
Hajjo kuwa
tini ido ya kawo ruwa.
Garbati ya yunkura
zai bugi Mairo Iyalle ta hana shi,ta ce Mairo
je ki abunki,haka kawai akan wata ba za ka
dakar min diya ba Garbati!Garbati ya ce wlh
Iyalle ke ki sa yarinyar nan ta na dada rai
na ni,Mairo ta juya za ta fita,Hajjo ta bi
ta,ina za ki?
Ya daka ma ta tsawa sai kuwa
ta sa kuka.
Iyyalle ta ce ni dai ba za ka
bugi diya ta ba,je ki abunki.
Hajjo ta na ji ta
na gani Mairo ta fice,Garbati ya fizgo
hannun ta ya wulga ta daki ya ja ya rufe ya
na fadin za ta dawo ita ma ta sa me ni ne.
Iyyale ta ce in ka taba Mairo sai na bata
ma ran ka!
Ta dubi Kande shige mu tafi kin
ji!
Su ka shigewar su ciki.
Garbati ya fice
shima ya huci,ita ko Hajjo inda ya jefa ta
nan ta durkushe ta na ihu,fadi take na shiga
uku na lalace!wayyo na shiga uku wayyo
Inna!
Su Iyalle da kande suna ji su ka mata
banza,har ta gaji ta yi shiru,sai ga Kande ta
shigo dauke da kwanan sha ta aje gaban
Hajjo,ta ce ga Koko da kusai inji Iyalle.
Hajjo ta ture ta ce ba na so,ni gidan mu
zani,ni wajan Inna zani!
Kande ta dube ta
ta ce yarinya zancen ki ke so,ta juyo tai
fitowar ta.
DEDICATED to The Women Of Virtue
(group)
[12:38am, 5/1/2015] Khadija Sidi:
DIYA MACE
Hajjo tana nan kwance ta jiyo sallamar
Indo,da.sauri ta tashi ta na fadin yauwa
Indo sai yanzu ki ka dawo wlh sai na hada
ki da Inna!
Ta bude kofa ta fito,sai ta hangi
Indo cikin dakin Iyalle suna gaisawa,ai kuwa
ita ma Hajjon kofar dakin ta nufa,ta tsaya
hannu a kugu ta na fadin ku gama gaisawa
ki fito mu tafi dan Allah!
Iyalle ta ce ina
ruwan Hajjo,har yanzu ba ta fahimci ta
girma ba,ki dai ma ta fada Indo,Indo
murmusawa ta yi ta na duban Hajjo,cikin
ranta kuwa sanyi ta ji dan daga ganin Hajjo
Garbati be ma ta komai ba,ashe dai ya na
da tunani.
Indo ta nisa ta ce zan ma ta
Iyalle,za ta gane inshaAllahu.
Iyalle ta ce
toh amen dai.