← Book details Diya Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 41

Sashe 1

Diya Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Diya mace by
khadija sidi
Posted by UMMU-ABDOUL on OCTOBER 17,
2016
[16/10 21:43] .: 7/24, 11:46 PM] Salmah
Ateeku: [11:40pm, 4/30/2015] Khadija Sidi:
DIYA MACE
Jin an idda sallar isha’i,ga jama’a na ta
fitowa daga masallaci ya sanya Hajara
wacce ake kira da hajjo kara sauri,ji ka ke
kululu!

Karar kugin yunwa da cikin ta ke ma
ta kenan,silifas din ta hadin bauta,daya ya
tsinke saboda haka sai cire shi ta yi,ta ruke
a hannu.

Dauke ta ke da katuwar kwaryar
dawa wanda ta je aka niko domin Innar su
ta samu ta tuka mu su na dare,hajjo ta
dada sauri,cikin ranta fadi take yau dai Inna
za ta yi tuwan dare,wata kila ma sai
goman dare za mu ci,ko da yake mu ma
godewa Allah baba yau ya kamana dawa
mai tarin yawa,ma huta da shan garin rogo
kwana biyu.

Titi ta tsallaka,ta wuto ta wajan mai
shayi,kamshin tuyen wainar kwai ya daki
hancin ta,ba ta san san da ta mayar da
mugun yawu ba,ba ta da buri da ya wuce
ta gifta ta wajan,dan har dan tsayawa a
wajan ta ke,taitahura hanci,ita a lalle sai ta
shaki kamshin wainar kwai ko Allah ya sa
ta ji shi har cikin ta kamar ta ci ta koshi.

Wannan karan ma tsayawa ta yi ta na baza
hanci,ga wata bakar yunwa da ta addabe
ta,tini ta shagala ta ma manta da dawar da
ke kanta,ba ta ankara ba sai ga mahaifin ta
zaune cikin rumfar mai shayi,gaban sa
katan buredi ne,ga kuma wainar kwai
manya manya cikin faranti,ya na yagar
buredin ya na hadawa da wai nar kwai,ga
kuma shayin sa a gefe ya na korawa.

Da
sauri Hajjo ta matsa ta na fadin laa
Baba,Baba ne wlh,Baba!

A fusace ya waigo
ya dube ta,ganin Hajjon ce ba kunnen sa ke
zagi ba,ya daka ma ta tsawa,ke uwarki!
uwarki na ce!

Hajjo ta sha jinin jikin
ta,sauran jama’a da ke zaune cikin rumfar
su ka zubo mu su na mujiya.

Na ce Uwarki!

Ya ma ta dakuwa,shegiyar kaya!

Ki kai ma
ta dawar ba za ki kai ma ta ba kin tsaya
gantali!

Tafi gida dan uwarki!

Ya daka ma
ta tsawa,jiki na bari ta juya,har da tuntume
Allah ya sa ta ruko dawar ba ta zube
ba,Baba ya ce assha,kun ga dai
shashasha,maza zubar da dawar kwa yi
kwanan yunwa dan uwar ki!!

Ita dai Hajjo ta
ti maza ta kama hanyar ta,jiki na bari,ta
ma manta da wani kamshin wainar kwai da
ta ke bala’in so,shi ko Baba buredin shi ya
ci gaba da yanka ya na hadawa da wainar
kwansa ya kaiwa baki,sai gunguni ya ke
kamar kuturu!!

Tin da ta dau hanya,ba ta zame ko ina ba
sai cikin gida gaban Inna ta dire kwaryar
har lokacin jikin ta be daina rawa ba,Inna
ta dube ta tace sai yanzu Hajjo?

Layi ki ka
tadda a wajan ne?

Lfy ya na ganki ba
nutsuwa jiki na bari haka?

Hajjo ta zauna
ta na maida numfashi ta ce Inna wai fa dan
na ga Baba ya na cin buredi da wainar kwai
wajan mai shayi,ba fa emmin zance ya yi
ba,kawai dama magana dai kawai na ma sa
shi ne ya fatattako ni,kamar na ce ya
emmin!Inna ta dafa kafadar ta kema Hajjoo
me ya kai ki yi ma sa magana tin da kin
san ba ya so,yanzu haka sai ya time ki idan
ya dawo.

Tsigar jikin Hajjo ya tashi tuno
dukan mahaifin ta,kana ta ce wlh Inna rai
na ne ya biya ban san sanda ma na ma sa
magana ba,ni dama ya emmin da yayyai ta
bugu na bazan damu ba ma,yunwa na ke ji
kamar na ci babu.

Inna ta ce inbe emmiki
ba ai ya emmiki bugu,yunwa kuma ga
danwake cen dazu da fitar ki yayar ki Indo
ta aiko ma na da shi sai…. ba ta jira Inna
ta gama magana ba ta tashi da gudu ta
nufi inda danwaken ya ke ta ja kwanan ba
tare da ta wanke hannu ba ta afka ma
sa,hannu baka,hannu kwarya,Inna ta bita
da kallo ta ce oh Hujja kamar kin shekara
ba ki ci komai ba?

Allah dai ya yanke ma
na wannan bakar wahalar da mu ke
ciki,amen.

DEDICATED to The Women Of Virtue
(group)
[11:49pm, 4/30/2015] Khadija Sidi:
DIYA MACE
Hajjo kenan,Hajara Mamman Mansur,diyar
Mallam Mamman Mansur,wanda suke
zaune a kauyen Kumurya,na yankin birnin
kano.

Wato Mallam Mamman wanda su
Hajjo ke kira da Baba mutum ne mai rufin
asiri matuka,ya na daya daga cikin ma su
kudin yankin,amma kash mako gare shi,be
san ya wadatar da iyalan sa ba,gidan sa
kullum cikin faci-faci ake,mafi munin halin
Baba shi ne kyamar haihuwan ‘ya’ya
mata,ya ki jinin ‘ya’ya mata dan a nashi
wahala ne kawai babu wata riba,a wannan
dalili ya sa ya auri mata shida ya na saka a
dalilin sun haifar ma sa diyoyi mata,duk
wacce ta haifi diya mace da sai ta bar ma
sa gida ita da diyar da ta haifa,wacce ta ci
sa’a Allah ya zaunar da ita ita ce Inna,uwar
gidan sa wato mahaifiyar su Hajjo,ita ma
din dan Allah ya nufe ta da haifar da namiji
a haihuwar ta na fari wanda aka radawa
Mahmud,ake kira Mudi,da wannan dalili ne
ya sa ya saki cikin sa ya zauna da
ita,bayan shekara biyu ta dada haifa ma sa
wani jinjirin Namiji mai suna Ayuba,murna
gun Baba ba a magana,ita kanta Inna sai
da ta zama yar gata dan cikin matan da ya
aura ita kadai ce ke haihuwar maza,ko da
Allah ya sake ba ta ciki a karo na uku,sai fa
Inna ta haifo diyar ta mace,bakin ciki gun
Baba kamar ya zaune diyar ya huta,yayyai
ta masifa da bala’i wai an haifo masa
jidali,wacce ba za ta amfana komai ba sai
dai kai ka amfana ma ta,ai ta dawainiya
ana jidali a karan banza a karan hofi,haka
dai ba dadi aka sanyawa yarinya suna Indo.

Tin daga nan Inna ta fara ganin
sauyi,abunda ta ke gani Baba ya na wa
matan da ya aura na shirin afkuwa kan ta.

A haka zaman ba dadi,sam be san rayuwar
Indo ba,sai dai na Mudi da Ayuba,su ka ci
gaba da zama,Baba na auran mata ya na
saki,gashi kuma kudira na Ubangiji har ya
yau babu wacce ta haifa ma sa da namiji in
ban da dai Innar.

A haka ba dadi har shekara goma ya
shude,an fidda rai da sake haihuwar
Inna,kwatsam sai Allah ya ba ta wani
cikin,tin ya na karami Baba ke ma ta
kashedi kar fa ta haifo diya mace,ya dai
fada ma ta,da ke abun na Allah ne bayan
wata tara Inna ta sillibo diyar ta mace,Baba
ranar har da zage zage,ai fa Inna ta kwashe
kayanta ta bar ma sa gida,da kyar yan
uwan sa suka sa baki ya bar ta,a fadar sa
ta ci darajar yaran ta maza.

Ranar suna
aka radawa yarinya suna Hajara,shekara
biyar da haihuwar Hajara aka aurar da
yayar Indo wacce ta ke da shekara goma
shabiyar.

Kwanci tashi,yanzu Hajjo ta kai shekara
goma shabiyu cif a duniya,amma daidai da
rana daya Baba be taba fada ma ta magana
ta arziki ba sai kyara da tsangwama.

Hajjo
yarinya ce da ba ta fiya jiki ba,yar fiyot ta
ke kamar ka hure,kuma ba ta da wani
tsayin azo a gani.

Ba wani sifar kyau gare
ta ba,amma kuma ba laifi tana da wani irin
boyeyyen kyau wanda har ka kare zama da
ita ba dai ka ga munin Hajjo ba,sai dai ma
ka ga tana kara ma ka kyau.

Hajjo ba fara
ba ce,ba kuma baka ba,an fi danganta ta da
wankan tarwada,idanun ta ba manya ba ba
kuma kanana ba,haka zalika hancin ta be
da wani tsini,ba ba’a ba hancin na ta ya so
yayi gajarta sai Allah ya taimaka be yi
ba,ba ta da gashi,amma kuma gaban kan ta
rufe ya ke ruf da gashi .dan ko ta daura
dankwali gashin be buya kamar ta sa hula
ka ganshi lub lub a kwance kai ka yi zaton
irin mai gashin nan mai yawa na gaske ce.

Ba a kira ta mai karamin baki ba,amma
girman leben na ta ba me muni ba ne,shi ne
wanda turawa ke kira full lips,abubuwa biyu
da ke karawa Hajjo kyau shi ne lotsewar da
kumatun ta keyi duk sanda ya yi magana
bare kuma uwa uba fara’a,dama ga ta
gwanar murmushi,ga kuma yar wushiryar
wanda ke dada bayyana kyanta cikin
nutsuwa
DEDICATED to The Women Of Virtue
(group)
[12:01am, 5/1/2015] Khadija Sidi:
DIYA MACE
Washagari da safe Inna ta na wanki Hajjo
ta shigo a guje ta na waka..

“Wata tafi wata a gashi ko
Ni na fi a gashi,wata ta
Fi wata a hanci ko ni na
Fi a hannci…”
Ta fada bayan Inna ta na dariya,Inna ta ce
Hajjo hankali!za ki karasa min bayan
nawa,yau kuma wannan wakar aka yi a
dandalin kenan!Hajjo kyalkyale da dariya ta
ce wlh Inna shi aka yi,amma kin se me
Inna?

Inna ta ce sai kin fada auta,Hajjo ta
ce da ance wata ta fi wata,sai ki ga wata
ta fito ta ce ko ita tafi,Mairo ta ce ta fi a
gashi,Bintu a Ido,Hanse a hanci,ni kuwa ban
fito a kowani baiti ba,da aka gama na ce ni
me ya sa ba a bani nawa fitowar ba sai
Mairo ta ce wai ai ban da abun fitowar dan
babu abunda na fi su da shi,wai gani
kwakwido,kuma komai nawa kadan ne!

Inna ta murmusa,kyale su Hajjo,ai shi ya sa
ki ka fisu kyawu saboda komai na ki daidai
ne ba kuma kadan ba,dan haka ne ki kin fi
kowa a kyawu!

Hajjo ta saki Inna ta zura a
guje..ke ke ke Hajjo!

Ya ki nan!

Inna ta
kwalla ma ta kira,Hajjo ta dawo ta na
haki,cike da mamaki Inna ta ce ina kuma za
ki?

Cikin haki Hajjo ta ce zuwa zan yi na
fada mu su na fi su a kyauwu!

Inna ta
girgiza kai auta hankali!

Ki yi hakuri idan
kun sake haduwa anjima kya fada mu su,ko
fa karyawa ba ki yi ba,ga kokon ki da
dumame can maza ki dauka ki karya.
Chapter 1 · 0% Book details