Sashe 8
Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jabir ya ji haushin maganganun Hajiya Mama dan sunyi matuk'ar kona masa rai, koda ya ga alamar Aliyu baya gidan ya ja tsaki sannan ya fita daga gidan a fusace yana jin Hajiya Mama tana cewa "uwarka ka yiwa tsaki mara tarbiyya kawai". Haka ya shiga motarsa ya ja ta sa k'arfi sai huci yake kamar wanda yaje dambe, kai tsaye club ya nufa, yana zuwa bai shiga cikin club d'in ba ya huce hostel d'in d'akinsa ya huce ya bud'e ya shiga, fridge ya nufa ya bud'e ya d'auko giya ya balle murfinta cikin zafin nama ya shiga kwank'wad'arta har sai da ya shanye gaba d'aya, haka ya k'arasa kan gadon yana tangad'in ya fad'a gadon, yana kwanciya wani amai ya taho masa ya mik'e dakyar da niyyar ya shiga toilet ya zube a kan carpet ya shiga kwara wani irin bak'in amai, sai da ya gama sannan ya mik'e ya koma kan gadon bacci mai nauyi yayi awan gaba dashi.
*'BANGAREN KHADIJATULLAHI*
Alhamdulillahi jikinta yayi sauk'i dan har tana yin hira sama-sama dasu Aunty Murja, ganin yadda jikin nata yayi sauk'i ne doctor Halima ta rubuta musu takardar sallama, suka koma gida suka cigaba da lura da Khadijatullahi, b'angaren Inna larai kuwa tunda Amatullahi tayi mata wannan aika-aikar ta fita ta shiga kurma ihu da neman taimako tayi sa'a kuwa d'anta lado ya shigo gidan yaga yanayin da take ciki dan har fuskarta ta fara sabulewa, a gigice ya k'arasa gurin da take a bage yana tambayarta "Inna meyafara wa yayi miki wannan aika-aikan" cikin rawar muryar ta bud'e bakj dakyar ta ce "Ama....Amatullahi ce lado ka taimkeni ka kaini asibiti" lado kuwa ransa ya b'aci matuk'a "wato rashin mutunci Amatullahi har ya kai ga ta illatawa mahaifiyarsa fuska" ya fad'a a zuciyarsa a fili kuwa ya ce "Wallahi wallahi na rantse miki da girman Allah Inna kamar yadda Amatullahi ta kona miki fuska wallahi nima sai na kona mata", (Ni kuwa 'yar mutanan zazzau nace lado kayi sauri ka kai mahaifiyarka asibiti kar fuskar ta rub'e domin kuwa Amatullahi ba kanwar lasa bace dai-dai take da kai😂🤸🏽♀️).
Haka Lado ya d'auki mahaifiyarsa a hannunsa ya nufi waje yayi sa'a yana fita ya tarar da abokinsa Tanimu a cikin motarsa da alama fita zai yi, Lado ya tsayar dashi da sauri, Tanimu ya tsaya Lado ya saka mahaifiyarsa sannan shima ya shiga, yana cewa "Tanimu dan Allah kaimu asibiti mafi kusa damu wallahi wannan shegiyar yarinyar ce ta hankad'a Inna cikin mai", cikin nuna damuwarsa Tanimu ya ce "Subhanallahi gari yaya haka ta faru" tsaki Lado ya ja cike da takaici ya ce "to wannan hatsabibiyar yarinyar ma har a tambaya garin yaya hakan ta faru, wallahi wannan yarinyar idan bata yi wasa ba siyar da ita zan yi kowa ya huta", dariya ce taso ta kwacewa Tanimu amman ya had'iye a zuciyarsa yana cewa "Kai banda abin ka Lado ai wannan yarinyar wallahi bata siyu ba dan duk wanda ya siyeta ya siyi jafa'i dan da kansa zai dawo da ita ya ce ya fasa". Abin da yasa Tanimu ya ce haka akwai wata rana da kanwarsa taje ta tsokani Amatullahi har gida Amatullahi taje ta zagesu gaba d'aya tare da cewa Innarsu "bata iya bada tarbiyya ba", Wani asibiti mai suna *BUBA SPEACIAL HOSPITAL* suka tsaya Lado ya fita da Innarsa ya shiga asibitin yana kiran "nurse! nurse!! nurse!!" Nurses kusan biyar ne suka fito suna tura gadon da ake dora marasa lafiya, Lado ya dora Innarsa ya taimakawa nurses d'in wajen tura innar sukai d'akin tiyata da ita (Allah sarki Inna larai anji bala😂😆). Haka su Tanimu suka zauna har tsawon awa d'aya babu wanda ya fito domin sanar dasu halin da Inna Laran take ciki, Tanimu ya kalli abokin nasa ya ce "Abokina zanje gurin Mama saboda zan kai ta unguwa kuma na barta tana ta jirana" Lado ya sauke ajiyar zuciya ya ce "to Abokina babu komai dan Allah ka mik'a min gaisuwata gurin Mama", "Insha Allahu" Tanimu ya fad'a tare da nufar kofar fita daga asibitin, Lado ya zabga tagumi zuciyarsa cike da tsanar Amatullahi, da kuma d'aukar fansar abin da tayi wa Innarsa.
*'BANGAREN JABIR*
Jabir bai tashi daga baccin ba sai wajen k'arfe uku, ya bud'e idanuwansa ya dorasu a kan wasu kyawawan yammata guda uku kowaccensu sanye take cikin kananun kaya riga da wando, wani kayatatcen murmushi yayi tare da kirawo sunansu "Leemsha, summy,Ammi" kowaccen su ta amsa da "Na'am sweety". Jawo su yayi jikinsa yana shafasu suma suna mai dar masa martani (Ni kuwa 'yar mutanan zazzau nace na shiga uku Jabir sai kace bursuru🙆🏼♀️),"Leemsha wacce ta kwanta a kan k'irjinsa tana tana kissing d'in lips d'insa ta ce "Sweetheart meyafaru da kai ne, dan naga kabar kofa a bud'e kuma nasan indai kazo kabar kofa a bud'e kana cikin damuwa ne"
Cikin wata iriyar murya mai wani irin salo mai d'aukar hankali ya ce "Wallahi wata tsohuwar banza ce ta b'ata min rai", Leemsha kuwa bata k'ara cewa komai ba, suka shiga yin bad'alarsu.
*'BANGAREN KHADIJATULLAHI*
Yanzu Khadijatullahi ta fara sakin jikinta kuma ta rage yin koke-kokenta Amman kuma kullum ne babu ranar banza sai tayi wa Jabir mugayen addu'o'i tare da tsine masa, Amatullahi kuwa tunda ta koma gida taga babu kowa tayi wata shegiyar dariya tare da cewa "Yau asibiti yayi d'iba kenan, ai Inna Larai kad'an kika gani indai zaki dinga zagin iyayena zan cigaba da baki wahala wallahi".
Yau kamar kullum suna zaune Amatullahi ta ce"Aunty Murja ya kamata mu fara shirye-shiryen makaranta domin nan da Sati d'aya insha Allahu zamu fara lecture" Khadijatullahi ta kalli Amatullahi domin kuwa ita har ta manta da sun sami admision ta ce "Amatullahi ni na hak'ura da zuwa makarantar kawai ke ki tafi" nan da nan hawaye ya fara zuba daga idon Amatullahi cikin muryar kuka ta fara magana da cewa "kina tunanin zan iya zuwa makaranta ba tare da ke ba, tun muna yara muke tare komai namu tare muke yinsa tun daga primary har zuwa yau babu abin da nake iyawa ba tare da ke ba yanzu kuma ina murna zamu fara zuwa makaranta zamu cigaba da kasancewa tare shine rana tsaka zaki ce min ba zaki je ba ai shikenan nagode sosai" tana gama fad'ar haka ta tashj ta fita daga gidan da saurinta tana kuka, hankalin Khadijatullahi ya tashi mik'ewa tayi ta d'auki hijabi ta saka duk sa cewa bata jin dad'in jikinnata haka ta bi Amatullahi domin ta bata hak'uri, Aunty Murja ta bisu da kallo tabbas k'awancen nasu yana matuk'ar burgeta "Allah ubangiji ya barku tare har abada". Ta fad'a a fili tana murmushi.
Haka Khadijatullah ta bi bayan Amatullah tana kiran sunanta Amman Amatullah ta k'i tsayawa har sai da suka kusan isa gidansu Amatullah, Khadijatullah ta tsaya tana sauke numfashi domin cikin nata Yana tsananin bata wahala, wannan tafiyar ma da tayi ji take tamkar k'afafuwanta zasu fita daga jikinta, ganin Amatullahi tana kok'arin shigewa gidan yasa Khadijatullah ta fara tafiya a daddafe har ta Isa gidansu Amatullah, shiga gidan tayi bakinta d'auke da sallama, "Assalamu alaikum" jin ba'a amsa Mata ba tayi tunanin Babu kowa a gidan Amman tana shiga tsakar gidan ta ga Lado da wata Mata fuskarta nannad'e da band'egi, ta tsugunna ta gaisar da wannan matar Amman Bata amsa Mata ba, sai ma jan tsaki da taji matar tayi, Lado kuwa cike da jin haushi ya ce "to munafuka zaki tashi ki bar nan wajen ko sai na kwarfeki" Khadijatullah ba tare da ta cewa Lado komai ba ta tashi ta nufi d'akin Amatullahi, tayi sallama ta shiga d'akin zaune ta tarar da Amatullahi tana kuka a kan d'an k'aramin gadon d'akin nata, Tsugunnawa Khadijatullah tayi a gabanta ta rik'e hannunta ita ma tana kukan "ki yi hak'uri k'awata nasan nayi miki laifi Amman Dan Allah ki yafe min, na amince zan je makarantar in dai hakan zai saka ki cikin farin ciki, Dan Allah ki daina kukan nan haka ya isa, zan je wallahi da gaske nake" Amatullahi ta juyo fuskarta d'auke da murmushi ta ce "da gaske kike besty" Kai Khadijatullah ta gyad'a Mata alamar "Eh" Amatullah ta d'agota ta taimaka Mata ta zauna a kan gadon kusa da Amatullahi hannayensu suna had'e da juna, Amatullahi ta ce"kin ga yanzu kaya iri d'aya zamu dinga sakawa, kuma ya kamata muje kasuwa domin muyi siyayyar makarantar" Murmushin yake kawai Khadijatullah take yi dimples d'inta suna lotsawa,ba tare da ta ce komai ba.
Haka Amatullahi tayi ta tsara musu yadda zasu dinga yin shiga idan zasu je makarantar ita dai Khadijatullah "Eh", "A'a shine kawai abin da take cewa, har wajen k'arfe 8:00am na dare Khadijatullah ta tashi ta ce "To besty zan tafi gida" Mik'ewa Amatullahi tayi tana cewa "Lallai kam yau Maman baby ta dad'e a gidan nan tun 5:00 na rana gashi yanzu karfe takwas na dare" harararta Khadijatullah tayi sannan ta ce"wacece Maman babyn?" Amatullahi ta saka duka hannuwanta a kunnuwanta alamun bada hak'uri ta ce "Am so sorry besty, ai nice Maman baby kin ga idan kika haihu ni zaki bawa babyn" Khadijatullah ta ce "Ai gwanda da kika gyara zancenki dan ni bazan tab'a son cikin nan ba" Amatullahi Bata ce komai ba suka gera suka fita daga cikin d'akin a tare, nufar kofar gida suka yi Khadijatullah ta juyo ta kalli Amatullahi dai-dai lokacin da ta saka k'afafuwanta zata fita daga gidan tare da cewa "Yau ban ga Inna ba ko Bata nan" Amatullahi cikin dariyar mugunta ta ce "kin ganta mana kamanninta ne suka chanza miki shiyasa baki ganeta ba" shuru Khadijatullah tayi Bata ce komai ba Amman zuciyarta ta cika da mamakin abin da Amatullahi ta fad'a, ta juya ta cigaba da tafiya ita ma Amatullahi ta bi ta a baya sai da suka kusan isa gidan sannan suka yi sallama da juna, Amatullahi ta koma gida ita Kuma Khadijatullah ta k'arasa gidan, tana zuwa ta tarar har Aunty Murja ta kwanta bacci ita ma ta kwanta a bayanta duk da cewa ba baccin take ji ba Amman ta lumshe idonta ta kusan awa a kwance bacci Mai nauyi yayi awon gaba da ita.
*'BANGAREN GIDANSU JABIR*