Sashe 22
Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tunda ya d'ora idanuwanshi a kan Aunty Murja ya ji gaba d'aya hankalinsa ya kwanta da yarinyar domin kuwa tana da saurin shiga ran mutane, yau kwana uku kenan amman kullum da tunaninta yake wuni a zuciyarsa, shiryawa yayi kyaf domin kuwa yau zai je ya fad'awa Hajiya Mama abin da ke cikin zuciyarsa ga me da Aunty Murja, motarsa ya shiga mai gadi ya bud'e masa gate d'in gidan ya fita daga gidan ya nufi gidan Hajiya Mama.
Alhaji Mansur yana isa gidan Hajiya Mama yayi parking d'in motarsa ya shiga gidan bakinsa d'auke da sallama "Assalamu alaikum" babu kowa a tsakar gidan dan haka ya nufi d'akin Hajiya Mama ya shiga d'akin da sallama Aunty Murja ya gani zaune tana karatun wani littafi mai suna *Magajin masarauta* wanda *Murjanatu bintu Al'amin ce ta rubutashi* da sauri ta d'ago kanta suka had'a ido da ita zuciyar Alhaji Mansur ta shiga bugawa da k'arfi gaba d'aya ya shagala da kallo Aunty Murja ita kuma ganin irin kallon da yake mata duk gaba d'aya ta rikice ta kasa amsa sallamar da yayi sunkuyar da kanta k'asa tayi tana wasa da littafin da yake hannunta, Hajiya Mama ce ta fito daga bedroom d'inta ta tsaya tana kallon irin yadda d'an nata yake kallon Aunty Murja yana murmushi ko kifta idanuwansa ba ya yi, wani irin murmushin su na manya tayi tare da godewa Allah daman tana son ace d'an nata ya ga Aunty Murja ya ce yana sonta, kuma daman tana son ta yi masa magana a kan ya aureta, domin kuwa ta san zai more da mata kuma 'ya'yansa zasu taso cikin tarbiyya.
Gyaran murya tayi Alhaji Mansur ya d'ago yana sosa kai tare da cewa "Hajiya ashe daman kina nan nayi tunanin ai bakya nan" harara ta watsa masa tare da cewa "To yau kuma da sabon salon da ka zo kenan, ka tab'a ganin ka zo gidan nan ba ka same ni ba" murmushi yayi tare da neman guri ya zauna yana cewa "A'a Hajiya ai nayi tunanin ko suna ki ka je", "A'a dambe na je ba suna ba" wannan maganar da Hajiya Mama ta yi ba k'aramar ba wa Aunty Murja dariya ta yi ba har ta kasa b'oye dariyar sai da ta yi ta a fili, Alhaji Mansur ya kalli yadda Aunty Murjan take dariya, ya k'ara jin ta shiga ransa domin ita kanta dariyar ta ta abin tsayawa a kalla ce "Murjanatu kema maganar Hajiya ta baki dariya kenan" ya fad'a yana kallonta, Aunty Murja ta yi mamaki domin jin Alhaji Mansur ya fad'i sunanta "to a ina yasan sunana?" ta fad'a a zuciyarta.
Alhaji Mansur ranar da ya fara ganin Aunty Murja, ya ji Hajiya Mama ta kira ta da Murjanatu shikenan shima ya rik'e sunan, Kallonsa Aunty Murja ta yi sannan ta ce "Eh".
Hajiya Mama ta samu guri ta zauna tana cewa "to ai sai kuyi ta dariyar, idan kun zare na kai ku dawanau" dariya Alhaji Mansur ya yi sannan ya ce "To mun dena Hajiya. yau fa zuwan nawa na musamman ne, na zo neman wani abu mai muhimmanci ne ban sani ba ko zan dace na same shi ya zama mallakina".
Hajiya Mama duk da cewa ta san inda zancen sa ya dosa, amman sai ta nuna masa ba ta gane ma yake nufi ba ta ce "Wane irin abu ne wannan mai muhimmanci?"
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kalli gurin da Aunty Murja take zaune suka had'a ido a karo na biyu, gabanta ne ta ji ya fad'i gaba d'aya ta ji zuciyarta tana bugawa da sauri, tashi ta yi sannan ta ce "Hajiya bari inje tsakar gida na k'arasa tankad'en na san yanzu ruwan ya tafasa" Hajiya ta ce "to shikenan" fita tayi da sauri ta zauna a tsakar gidan tana tankad'en, Alhaji Mansur kuwa Aunty Murja tana fita ya juyo yana kallon Hajiya Mama yana cewa "Hajiya Mama kin san dai irin zaman da nake da Asiya, gaba d'aya ta lalata min tarbiyyar yara Shahida da Aliyu ne kad'ai suka fita zakka, kuma uwa uba Asiya sam bata k'aunar 'yan uwana,Hajiya Mama ina buk'atar na k'ara aure tunda dai ina da halin da zan iya rik'e mace sama da d'aya, kuma ina son na auri Murjanatu idan ba'ayi mata miji ba domin na yaba da halayenta"
Murmushi Hajiya Mama ta yi sannan ta ce "Alhamdulillahi daman ina da burin na ga ance yau kai ne zaka auri Murjanatu domin yarinyar tana da hankali sosai, kuma gaskiya ba na tunanin anyi mata miji saboda a yadda ta ba ni labari iyayensu sun mutu kuma ita kad'ai ce take kula da 'yan uwanta ita suke kallo a matsayin uwa kuma yayarsu" Alhaji Mansur ya ji matuk'ar dad'i ya ce "to yanzu Hajiya ya ya za'ai ina son nan da sati uku masu zuwa a d'aura auren saboda ba na son a ja wani dogon lokaci" Hajiya Mama ta ce "to ai sai ka bari muji ta bakinta ko?" Alhaji Mansur ya ce "Hakane kam Hajiya Mama" Hajiya Mama ta kira sunan Aunty Murja, ta amsa tare da ajiye tankad'en ta shigo d'akin har lokacin zuciyarta bata dena bugawa ba, zama ta yi a kujerar da ta tashi tare da sunkuyar da kanta tana cewa "Gani Hajiya" Hajiya Mama ta ce "Mansur ne ya zo min da wata magana wacce ta saka ni cikin tsananin farin ciki, da ina da dama da tun kafin ya rufe bakinsa zan basa abin da ya ke buk'ata amman ban da wannan damar shiyasa na ce bari in kirawo ki domin muji ta bakinki, Mansur yana so ya aureki kuma baya so a ja lokaci mai tsayi" Aunty Murja ta d'ago da sauri suka had'a ido da Alhaji Mansur wata iriyar kunya duk ta lillib'eta ta saka kanta a kan cinyarta tare da jan hijabinta ya rufe mata fuska, Hajiya da Alhaji Mansur murmushi kawai suka yi, Hajiya ta mik'e ta shiga bedroom domin ta basu guri su yi magana.
Alhaji Mansur ya ce "Murjanatu ki d'ago domin ki ba ni amsa, kina sona? kuma zaki aure ni?" bata d'ago ba domin gaba d'aya ji ta yi kamar ta nitse a gurin saboda kunya "Dan Allah ki d'ago ki ba ni amsa kinji ki cire kunya domin in san in da na dosa" d'agowa ta yi kanta a k'asa dan ba za ta iya had'a ido da shi ba, murmushi yayi sannan ya ce "yawwa gimbiyata yanzu fad'a min na ji ra'ayinki" , "Eh zan iya auranka" abin da ta ce kenan sannan ta fita da sauri gidansu ta nufa wani irin farin ciki duk ya cika zuciyarta, Alhaji Mansur kuw murmushi yayi sannan ya shiga bedroom d'in Hajiya Mama yana cewa "to Hajiya Amaryata fa ta tafi, nima tafiya zan yi" ya fad'a yana zama kusa da ita.
Hajiya Mama ta ce "Lallai Murjanatu wato tafiya babu sallama" Dariya sosai Alhaji Mansur yayi "haba Hajiya kiyi mata uzuri yau dan kuwa kunya ce ta sa ta tafi ba sallama" tashi yayi sannan ya ce "Hajiya nima zan huce", "to shikenan sai ka dawo". Fita yayi daga gidan ya shiga mota ya ja zuciyarsa cike da farin ciki, kai tsaye ma'aikatarsa ya huce.
*'BANGAREN NIHAL*
Zaune take a kan kujera tana chatting da Shahida tana mata korafin tunda ta zo gidan Salis d'in bata tab'a zuwa ba ko ta daina sonta ne?, Shahida ta shiga bata hak'uri da kawo mata uzurin yanzu tana zuwa aiki ne kuma bata dawowa da wuri shiyasa bata zo ba, amman zata kawo mata ziya nan zuwa wani satin insha Allahu
Salis ne ya shigo ya ganta tana zaune tana chatting a bayanta ya tsaya, tare da rumgumota ta baya, a zabure ta mik'e ganin shi ne yasa ta sauke ajiyar zuciya, "kai Yaya Salis ka ba ni tsoro wallahi" murmushi yayi tare da cewa "Sorry baby nayi sallama ne na ji baki amsa ba, kin shagala da chatting", "Eh wallahi da Shahida na ke chatting shiyasa ban ji sallamar ba" matsawa kusa da ita yayi yana kok'arin jawo ta jikinshi, cikin muryar d take nuna alamar za ta yi kuka ta fara magana "Dan Allah Yaya Salis yau ka bar ni, dan manzon Allah", Kallonta yake ido cikin ido ya ce "wai me yasa kullum idan na zo gurinki domin ki biya min buk'ata ta sai kin wulak'anta ni" kuka ta fashe dashi tare da durkushewa tabbas tasan wannan duk alhakin Khadijatullahi ne yake bibiyarta Allah ya had'ata da Jarababben namiji, tsugunnawa yayi kusa da ita ya d'auketa cak be za me da ita ko ina ba sai kan gado, ya kwantar da ita domin shi ba zai iya jira wai ya bi ta ta lallami ba, haka ya fara tsotsar ko ina na jikinta ita kuma tana kuka, tabbas ta yarda alhak'i k'uikuyo ne gashi sun d'auki al'hakin baiwar Allah tun yanzu ita ta fara ganin sakamakon abin da Yayansu Jabir ya aikatawa baiwar Allah, haka Salis ya yi abin da ya kawosa ya d'agata ya shiga toilet ya yi wanka, ya fito d'aure da towel yana kallon inda Nihal d'in take sai wani irin nishi take ta yi matuk'ar ba sa tausayi, ta nufi inda take kwance ya d'agata ya d'auke ya kai ta toilet ya saka ta a cikin ruwan zafin da ya tara, ta kurma wani irin ihu tana kok'arin tashi zata fita daga cikin bahon wanka amman Salis ya rik'eta sosai kuma ya dannata cikin ruwan ta yadda ko ina na jikinta zai gasu sosai.