← Book details Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 54

Sashe 28

Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwanan Salis uku a asibiti bai san wanda yake kansa ba hankalin Mama yayi matuk'ar tashi, ganin tilon d'an nata cikin yanayin rayuwa ko mutuwa, kuka take yi sosai kamar ranta zai fita ta kama hannun Salis d'in tana cewa "dan Allah tashi duk abin da kake so zan yi maka, kasan kai ne kad'ai yarona kai nake kallo na ji dad'i "Ai baki fara kuka ba, domin kuwa duk halin da Salis yake ciki ke kika jawo masa, ki ka je kika rabasa da matarsa ai gashi nan yanzu sai ki dafasa ki cinyesa" Mahaifin Salis ya fad'a cikin fushi, Mama bata iya tankawa ba, sai kuka shi kuwa takaici ma ya hanasa zama ya fita daga d'akin zuciyarsa cike da bak'in ciki.

*'BANGAREN AMINAN JUNA AMKHAHAF😂💓*

Kamar yadda Safwan ya ce mata zai zo da sassafe ya kai ta gidan Hajiya Mama haka kuwa aka yi yana zuwa ko yarda ya shiga gidan ba ta yi ba, ta taresa a farfagiyar gidan bai musa mata ba ya juya ya nufi motarsa ya bud'e mata gurin mai zaman banza ta shiga ya rufe ya zagaya gurin driver ya shiga ya ja motar ya nufi gidan Hajiya Mama yana zuwa ya nunawa Hafsan gidan ta fita suka yi sallama ya nufi ma'aikatarsu kasancewar su Hafsa yau lahadi babu makaranta.

Ta shiga gidan da sallama a bakinta suna zazzaune a tsakar gida Amatullahi da Khadijatullahi suna ganinta suka tashi da sauri suka nufi gurinta suna murmushi rungumeta zasu yi tayi saurin dakatar da su cikin muryar fushi da cewa.

"Ba na buk'atar jin komai daga bakinku nagode sosai, kun ji nasan irin zaman da zan yi da ku" Tana gama fad'ar haka ta juya zata fita Amatullahi ta rik'eta sosai tana cewa "Wallahi ba inda zaki je, nasan a kan bikin Aunty Murja da ba'a fad'a miki ba shiyasa kike fushi, to ki tsaya ki saurareni dan Allah Hafsa wallahi! wallahi!! wallahi!!! Kin ji na rantse miki ko, mu kan mu ba mu san da bikin ba, sai da muka zo gidan Hajiya Mama sannan" Fizge hannun Amatullahi tayi daga jikinta ranta a b'ace ta ce "daman baku yi niyyar na zo ba, tunda ranar ma a school babu yadda ban yi da ku ba, a kan ku shiga mota a kai ku gida ku ka k'i, kuma lokacin da ku ka hau adaidaita Yaya Safwan ya bi hanyar da ku ka bi, sai gani na yi kun bii hanyar gida anan na tabbatar kawai daman bakwa buk'atar cigaba da mu'amalarmu".

Khadijatullahi jikinta yayi sanyi dan kuwa ta san bata kyautawa k'awarta ta ba domin ita ce da laifi Amatullahi babu ruwanta nan, rik'e hannun Hafsan tayi lokacin da ta juya zata fita, ta juyo da niyyar fizgewa sai ta ga Khadijatullahi ce kuma tana tsoron karta fizge ta je ta fad'i tunda cikinta yanzu ya tsufa sosai ya kai wata takwas, "me zaki ce min ke kuma?" Hafsa ta fad'a cike da masifa, "ki yi hak'uri dan Allah wallahi ba wai da niyya mu ka yi miki haka ba, kuma Amatullahi kwata-kwata ba ta da laifi ni ce nake da laifin dan mana k'aunar abin da zai sake had'a ni da wani namijin na tsane su, ba na son ganinsu, amman bikin Aunty Murja wallahi kamar yadda besty ta ce ba mu san dashi ba mu ma sai da muka zo ake fad'a mana, kuma lokacin ya ri ga ya k'ure shiyasa ki yi hak'uri".

Hafsa tayi shuru tabbas ita ma ranar sai da ta raya wannan abin a zuciyarta cewa Khadijatullahi ba ta son ganin maza shiyasa ta k'i shiga motar "Shikenan ya huce" Hafsa ta fad'a tana murmushi, murmushin su ma suka yi gaba d'ayansu.

Aliyu ne ya shigo gidan idanuwansa a kan Khadijatullahi duk ya ji abin da suka fad'a zuciyarsa ta shiga bugawa magana Khadijatullahi ta girgiza shi ba ma shi kad'ai ba har da su Hajiya Mama domin kuwa sun san Jabir shi ne silar da yasa Khadijatullahi ta tsani maza, "Assalamu alaikum" Ya fad'a har lokacin idanuwansa na kan Khadijatullahi, amman ita tun da ya shigo ta kawar da kanta domin kuwa wata iriyar muguwar tsanar Aliyun take ji saboda tsananin kamannin Jabir da take gani a fuskar Aliyun ji take kamar Jabir d'in ne.

Suka amsa masa sallamar amman ban da Khadijatullahi d'akin Hajiya Maman ta shige tayi kwanciyarta, "ko me ya kawo shi nan, banza kawai" Tayi maganar zuciyarta kamar zata fashe saboda tsanar maza da tayi mata katutu a cikinta.

Hafsa da Amatullahi kuwa k'arasa suka yi suka zauna Hafsa ta gaisar da Hajiya Mama cike da girmamawa Aliyu ma ya gaishe da ita ya zauna kusa da ita suna yin hirarsu irinta jika da kaka, Hafsa kuwa hira suka shiga yi su da Shahida,Nihal da Amatullahi, zuciyar Amatullahi ta karkata a kan ta je ta ga wace wainar ake toyawa a gidansu domin kuwa ba ta k'aunar ace Lado da Inna Larai sun shirya, tashi tayi tana cewa "Sisters zan je na dawo yanzun nan","ina zaki je besty" Hafsa ta tambayeta.

"Ginin da na fara yi ne nake tsoron kada ya ruguje" Hafsa ta gane abin da Amatullahi take nufi dan haka ta fashe da dariya tana fad'i "gaskiya ne besty, gwanda ki je ki duba shi kar ya ruguje duk aikinki ya dawo baya" Khadijatullahi da take cikin d'aki tana jin su ita ma dariyar take yi sosai har suna iya jin dariyar Hafsa ta ce "Ahhh besty ke ma dole ki yi dariya, tana tsoron kar ya ruguje aikinta ya dawo ba, kin san fa besty akwai ta da iya tsara gini mai kyau","Ai kuwa dai kam" cewar Khadijatullahi.

Wannan maganar ta su ta saka su Hajiya Mama a rud'ani har Amatullahi tayi musu sallama ta fita, da Hajiya Mama ta gaji ta tambayi Hafsa "me take nufi da kar gininta ya ruguje?" Nan Hafsa ta fad'a musu abin da take nufi da hakan, Nihal da Shahida dariya suka saka sosai har da hawaye "Ai daman na fuskanci sister ba k'aramar 'yar drama ba ce" Shahida ta fad'a "wallahi kuwa other half" Hajiya Mama dai girgiza kai kawai tayi Aliyu kuwa yana son yin dariya ya basar, suka cigaba da yin hirar ta su.

*'BANGAREN INNA LARAI,LADO DA KUMA AMATULLAH*

Cikin sauri sauri ta k'arasa gidan tana saka kanta a sauron gidan ta ji muryar Inna Larai tana cewa "dan Allah kayi hak'uri mana Lado tunda ya ce a wannan satin zai turo kud'in sai ka tsaya satin idan ya huce ka ga bai turo ba, sai ka fad'i duk abin da zaka ce, tunda dai kasan k'aryar da nayi masa cewar ginin d'akina ne ya fad'i na gyara ban bada kud'in ba, kai ma kasan zai turo kud'i" Amatullahi tayi wani irin murmushi "lallai kam da ace ban dawo ba, da tuni ginina zai ruguje, amman yanzu na dawo zan d'ora daga inda na tsaya" Tayi magana a zuciyarta.

Shiga gidan tayi ko kad'an ba ta nuna ta ji abin da suke fad'a ba, ta saki wani irin murmushi tare da cewa "sannunku da hutawa Inna, my love nayi missing d'inka" Tayi maganar tana kallon Lado fuskarta tana nuna alamun tsantsar damuwa.

Lado ya k'ak'alo murmushin dole ya wanzar a kan fuskarsa "nima haka my love" Ya fad'a tare da mikewa tsayi yana cewa "zan fita waje na d'an sha iska my love ki kula da kanki" Yana gama fad'ar haka ya fita ransa a b'ace shi sam baya k'aunar yi wa Amatullahi magana kuma duk Inna ce ta jaaa masa gashi ta zamar masa k'arfen k'afa.

Ita kuwa Amatullahi d'akinta ta shiga tayi wanka, sannan ta fito wata doguwar ce a jikinta blue tayi mata matuk'ar kyau tamkar dan ita aka yi rigar, fita tayi daga gidan ta nufi gurin mai kiran waya ta biya shi kud'in sannan ya bata wayar ta saka number babanta sannan ta matsa chan nesa da mai kiran wayar domin kar ya ji abin da zata ce, ring d'aya biyu ya d'aga tare da yin sallama "Assalamu alaikum" ta amsa masa sallamar "Wa'alaikumussalam Babana Amatullahi ce","Allah sarki yarinyata nasan kinyi kewar babanki ko?" Yayi maganar cike da jin dad'in kiran da tayi masa "Eh babana nayi kewarka sosai da sosai kullum sai na ji dama nima ace na dawo gurinka mu dinga yin aikin tare","Allah sarki yarinyata karki damu na kusan dawowa insha Allahu na zo na ganki" Amatullahi ta ce "to Baba Allah ya dawo da kai lafiya","Aamin ya Allah" Sai kuma Amatullahi ta numfasa ta fara kora masa jawabi "Babana na ji wai Inna ta kira ka a kan cewa ginin d'akinta ya ruguje, ta kirawo mai gyara an gyara bata bada kud'in gyaran ba","Eh wallahi gobe ma nake shirin turo mata da kud'in dan ta biya shi kud'insa" Amatullahi ta ce "to wallahi Baba k'arya Inna take babu wani ginin da ya ruguje, so take ta damfare ka, kuma idan ka na tunanin ba gaskiya nake fad'a ba zaka iya zuwa ka duba ka gani da kanka" Shuru Malam Shu'aibu yayi domin a duniya babu abin da ya tsana irin kayi masa k'arya, gwanda ka fito fili ka fad'a masa gaskiyarka "Kin tabbatar babu ginin da ya ruguje","wallahi Baba da gaske nake yi maka" Amatullahi ta fad'a cikin fara'a, kashe wayar Malam Shu'aibu yayi ransa duk a b'ace kuma ya k'uduri niyyar ba zai bata kud'in ba kuma ko ta kirasa ba zai d'auka ba, Amatullahi kuwa mayarwa da kiran wayar tayi da wayarsa sannan ta shiga adaidaita ta nufi gidan Hajiya Mama.

*'BANGAREN SAFNA*

Tun ranar da ta ji labarin cewar Safwan da Hafsa sun shirya kuma yanzu soyayya suke yi, kuma ta fuskanci duk irin abubuwan da take yi a gidan dan ta kuntatawa Safwan d'in sam bai dameshi ba, nuna mata ma yake yi kamar bai san tana yi ba, hankalinta ya tashi zuciyarta ta shiga yi mata zafi, ta shiga neman hanyar da zata bi ta mallake Safwan d'in ita kad'ai kuma ta cusa masa tsanar Hafsa a cikin zuciyarsa amman kwata-kwata ta gaza samun hanyar, kullum cikin kuka gashi kuma kamar k'ara ruru mata wutar son Safwan d'in ake yi a zuciyarta, yau ma kamar kullum tana zaune a falo tana shan kukanta.
Chapter 28 · 0% Book details