← Book details Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 54

Sashe 32

Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nihal kuwa kwana yau da kewar mijinta ta tashi, dan haka da ta ji cewa Safwan bai mutu ba, haka ta faki idonsu Shahida ta shige bedroom d'in Hajiya Mama, ta kira number da Salis d'in ya kirawota jiya da ita ringing d'aya biyu doctor Maryam ta d'aga wayar tare da yin sallama, daman Salis ya fad'a mata cewa aran wayar doctor Sadiya yayi dan haka Nihal ta amsa mata sallamar tare da cewa "Ina wuni doctor","lafiya alhamdullahi da wa nake magana?" Murmushi Nihal tayi sannan ta ce "Nihal ce matar Salis, wanda ya ari wayarki jiya","Ohhhh nagane ya kike" Nihal cike da kosawa ta ce "Lafiya alhamdulillahi, dan Allah zaki iya had'a ni da babyn baby".
Murmushi doctor Sadiya tayi tare da cewa "me zai hana babyn baby" Wani irin kayatatcen murmushi Nihal tayi tare da cewa "To nagode Amman idan Mama tana nan kawai ki san dabarar da zaki Dan Allah ko muryarsa ne, naji dan nasan ba za ta bari munyi waya ba" Tayi maganar Cikin muryar kuka hawaye na zubo Mata, nan doctor Sadiya ta san da akwai matsala tsakanin wad'annan ma'auratan duk da ta ga irin yadda kowannan su ya damu da d'an uwansa.

"Meyasa bakya son Mama ta san kuna waya da mijinki","Saboda ta tsaneni, tana kok'arin rabani da babyna, Kuma saboda hakane Yaya Salis yake cikin wannan halin da yake a yanzu" Nan ta kwashe duk yadda suka yi ta fad'awa doctor Sadiya tana kuka tana ba ta labarin.

Doctor Sadiya tayi matuk'ar tausaya musu dan haka ta d'auki Alk'awarin taimaka musu a zuciyarta, Amman a fili rarrashin Nihal tayi tare da cewa "ki yi hak'uri kinji insha Allahu komai zai yi dai-dai Kuma Mama da kanta zata zo gurinki rok'on ki koma gidan Salis Allah yasa mudace","Amin" Nihal ta fad'a "Yanzu gaskiya Mama tana nan, Amman kamar yadda kike so zan shiga d'akin a zuwan duba yanayin jikinsa na zo yi na d'anyi Masa tambayoyi idan yayi magana hakan zai saka ki farin ciki ko?","Eh doctor nagode nagode sosai" Doctor Sadiya ta ce "karki damu".

Sannan ta nufi d'akin da aka kwantar da Salis d'in Bata kashe kiran ba, Amman ta cireta daga kunnanta,bata k'ara cewa komai ba ita ma Nihal d'in bata ce komai ba kawai dai ta rik'e wayar sosai a kunnanta.

Da sallama doctor Sadiya ta shiga d'akin, Mama da Salis Wanda yake kwance a kan gado Yana hutawa gaba d'aya kewar Nihal ta hana shi sukuni, suka amsa Mata sallamar "Mama barka da hutawa","yawwa doctor" Doctor Sadiya ta nufi gurin Salis tare da cewa "Sannu Salis ya jikin","doctor jiki alhamdulillah" Karaf idanuwansa suka sauka a kan screen d'in wayar number babynsa ya gani wani irin farin ciki ya kama shi.

Ya kalli Mama tare da cewa "Mama Ina son cin tuwo miyar busasshiyar kubewa","Wayyo yanzu Kuma Nafisa ta tafi gida, Amman Bari na je da kai na nayi na kawo maka" Murmushi Salis yayi tare da cewa "to Mama nagode" Fita Mama tayi daga Asibitin ta hau adaidaita ya suka nufi gidanta.

Salis kuwa Mama tana fita yayi saurin k'arb'ar wayar yana cewa "Nagode sosai Doctor","bakomai babyn baby sai a Sha soyayya lafiya" Ta fad'a tana dariya sannan ta fita daga d'akin.

"Babyna Ashe dai zai ji muryarka yau" Murmushi Salis yayi ya ce "Eh mana babyn baby, Ina cikin tsananin kewarki sai Kuma gashi nan zan samu kewarta ki ta d'an ragu dan kuwa waya ba zai saka ni na daina kewarki ba, babyna I really miss you badly, yaushe zaki zo ki duba babynki yau satina d'aya a asibiti Amman ace babyna ba ta zo ba","Ka yi hak'uri Ina tsoron Mama ne shiyasa Amman Ina son na zo gurinka, Kuma Nima nayi kewarka sosai" Salis ya ce "Ohh saboda Mama ne shine ba zaki zo ki duba babynki ba, ai shikenan" Yayi maganar tare da kashe wayar.

Nihal ta kira wayar kusan sau goma Amman Salis bai d'aga ba, hankalinta yayi matuk'ar tashi ta rasa inda zata tsoma ranta, kuka ta zauna tai-tayi "haba babyn baby meyasa zaka min haka, kai ma kasan ina tsananin son na zo na ganka" Ji tayi an dafata da sauri ta juya tana kallon wacce ta dafata Khadijatullahi tana bin ta da kallon tausayi, zama tayi kusa da ita tare da cewa "Sister na san dole ki ji ranki babu dad'i, amman duk da nasan Mama ba ta son ki tare Salis, ya kamata ki je ki duba yadda jikinsa ya ke hakan zai saka shi cikin farin ciki","to ya ya zan duba shi Sister ko so kike na je ta wulak'antani" Murmushi Khadijatullahi tayi sannan ta ce "menene amfanin nik'af" Wani irin farin ciki ne ya kama Nihal ta ce "kai Sister na ji matuk'ar farin ciki da wannan shawarar","Amman ya kamata ki bari sai gobe, sai ki saka hijabi har k'asa ki saka nik'af babu mai gane ki","to shikenan Allah ya kaimu goben Auntyna" Dariya Khadijatullahi tayi sannan ta ce "Amin amman dai ki ce min Sister zan fi son haka","to shikenan Sister".

Haka dai suka tashi suka fito zuwa falo inda su Amatullahi da Shahida suke zama suka yi suka shiga yin hirarsu ta duniya.

*'BANGAREN INNA LARAI DA LADO😂*

Lado ya gama d'agawa Inna Larai hankali gashi ko da ta je domin ta kirawo Malam Shu'aibu ta ji ya bai turo kud'in ba har yanzu, amman kiran duniya tayi masa ya k'i d'agawa, 'yar yaloluwar katifar d'akinta ta kira wata dillaliya ta shiyeta a dubu biyar, haka dai ta samu ta lallab'a Ladon ta bashi naira dubu biyar d'in bayan sun yi yarjejeniya a kan cewa idan ta d'auki adashinta wani satin zata cika masa kud'insa, ta ce masa ta yarda sannan ya karb'a, amman duk da haka kullum sai yayi mata masifa, haka dai take toshe kunnuwanta.

Inna Larai ta cigaba da kok'arin kulluwa Amatullahi makirci saboda tana zargin cewa da hannunta wajen k'in turo da kud'in da Malam Shu'aibu yayi, saboda mai kiran wayar ya fad'a mata cewa Amatullahi ta zo gurinsa ta kira waya ammam bata yi magana a gabansa ba, sai da ta matsa nesa dashi, ai kuwa Inna Larai ta k'ara jin tsanar Amatullahi ta ji zata iya yin komai dan ta ga ta wulak'anta, gashi abin takaicin Lado yanzu baya sauraronta ya ce idan ta ga ya fara sauraronta to ta biya shi ragowar kud'insa, sannan sai su koma kamar da.

(Lado uban son kud'i wayyo cikina🤣hawan ruwan Inna Larai zai tashi😂🚴🏽‍♀️)

*'BANGAREN GIDANSU JABIR🤏🏾😎*

Zaune take a cikin d'akinta wata doguwar riga ce a jikinta pink mai ratsin blue a jiki ta d'aura mayafin rigar a kanta hannunta rik'e da littafin hausa tana karantawa hankalinta kwance, fizge littafin da aka yi ne yasa ta juya bayanta da sauri Alhaji Mansur ne fuskarsa d'auke da murmushi "Wato mijinki ma ya dawo ba ki sani ba kina karatu ko?" Sunkuyar da kanta tayi tana wasa da 'yanyatsun hannunta tana cewa "ka yi hak'uri wallahi ban san ka shigo ba, kuma ban fara karatun ba har sai da na ga lokacin dawowarka yayi ba ka dawo ba".

Mik'a mata littafin yayi yana cewa "to na hak'ura, kuma yau aikine yayi min yawa shiyasa ban dawo da wuri ba, na gaji sosai", Sannu ta shiga jera masa, zama yayi a kujerar da ta tashi sannan ya kamo hannunta ya jawota jikinsa yana wasa da ita cikin wani irin salo.

Bugun kofar da ake yi ne kamar za'a k'aryata, yasa su dawowa daga duniyar soyayyar da suka lula, Aunty Murja ce ta tashi ta nufi kofar sannan ta bud'e Hajiya Asiya ce, tana ganin an bud'e kofar ta bangaje Aunty Murja sannan ta nufi gurin Alhaji Mansur gadan-gadan "Mansur" Ta kirawo sunansa da k'arfi kai ka ce uwarsa ce ita, wani irin mugun kallo ya watsa mata bai ce mata komai ba ya kawar da kansa gefe "ina fad'a maka da k'akkausar murya ka saki wannan karuwar yarinyar tun kafin nayi maka rashin mutuncin da ba za ka iya dashi ba","to sannu uwata Asiya ban tab'a tunanin ke dabba ba ce sai yau na k'ara tabbatarwa, ko ba rashin mutunci ba bismillah karki fasa yi min, kuma ina sake fad's miki idan kika sake ki a fusata ni to zaki koma inda kika fito shashasha mai shashashar zuciya jahilar banza jahilar wofi" Wasu irin hawaye ne suka zubo mata, lallai ma wato har Mansur ya isa ya gaya mata haka, ai kuwa sai ta tabbatar ya biya abin da yayi mata haka ta fita daga d'akin fuuuuuuuu kamar wata kububuwa, tashi yayi ya nufi kofar ya saka mata mukulli sannan ya kalli Aunty Murja wacce take tsaye kamar an dasata ta kasa ko da motsawa, hannunta ya kama suka nufi kan gadon domin kuwa yana buk'atar ya jita a jikinshi a halin yanzu.

Aunty Murja ta bashi had'in kai domin kuwa ba ta da wani buri irin ta ga ta faranta ran mijinta, haka suka tsunduma duniyar soyayya.

Hajiya Asiya kuwa tun da ta fita ta shiga d'akinta ta kasa tsaye ta kasa zaune, hankalinta duk a tashe gashi har 'yar wata rama tayi saboda halin da take ciki "ya zama dole na nemi mafita dan kuwa wannan gidan da kuma duk kadarorin Alhaji Mansur nawa ne ni da yarana" Wayarta ta d'auka ta shiga kiran number k'awarta Hajiya Suhaima amman a kashe take wani irin mugun tsaki ta ja sannan ta zauna ta tura mata text kamar haka _Shegiya sai ayi ta kiranki wayarki a kashe to idan kin kunna wayarki, ina son yin magana da ke domin akwai matsala, kuma wannan tsohon najadun ba zai bari in fito yanzu ba_ tana gama rubuta sakon ta tura mata tare da kishin gid'a zuciyarta nayi mata zafi, bacci b'arawo ne yayi awan gaba da ita.

*'BANGAREN TALATU😂*
Chapter 32 · 0% Book details