← Book details Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 54

Sashe 19

Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin Khadijatullahi yana k'ara girma dan yanzu watansa hud'u, duk da cewa yanzu ta rage yawan damuwa sai dai idan abin da Jabir yayi mata ya fad'o mata ta shige b'and'aki tayi kukanta mai isarta ta wanke fuskarta ta fito, ga laulayi ya sakata a gaba duk abin da ta ci sai ya dawo shiyasa kwana biyu basa zuwa makaranta ita da Amatullahi saboda Amatullahi ba za ta tab'a iya zuwa makarantar ba tare da Khadijatullahi ba, Hafsa kuwa tayi matuk'ar damuwar rashin zuwa makarantar da basa yi, shiyasa ita ma ta daina zuwa ya zamana kullum ita da Khalid suna gidansu Khadijatullahi, Aunty Murja da ta ga abin nasu ba na k'are ba ne, ranar wata Asabar bayan sun zo suna ta hira ta zauna tare da fara yi musu fad'a "Gaskiya mun ba ni mamaki sosai, yanzu ace kun daina zuwa makaranta saboda Khadijatullahi bata da lafiya bata zuwa, to insha Allahu gobe kowannan ku ya shirya zaku koma makaranta dan na gaji da zaman da kuke kullum kuka kullum cikin damuwa kuke ba za ku iya d'aukar k'addara ba kenan" Amatullahi ta kalli Aunty Murja cikin yanayin damuwa ta ce "Aunty Murja ba zamu iya zuwa makaranta ba tare da Khadijatullahi ba" Hafsa ta ce "Wallahi Aunty Murja gaskiya Amatullahi ta fad'a ba zamu iya zuwa makaranta ba tare da besty ba" Aunty Murja ta ce "Ai shine nace ku shirya gobe har Khadijatullahi dukkanku makaranta zaku tafi" suka amsa da "to shikenan Aunty Murja".

Haka kuwa aka yi washe gari kowannen su ya shirya suka fito su uku, kayansu iri d'aya motar Hafsa suka shiga drivernta ya ja su suka nufi makarantar, a makarantar ma haka Khadijatullahi tai-tayin Amai dan da har zasu dawo gida Khadijatullahi ta ce ba za ta koma gida ba har sai an tashi haka suka kyaleta har sai da aka tashi drivern Hafsa ya zo ya kai su har kofar gidan sannan ya nufi gidansu Hafsa, Amatullahi ta kama Khadijatullahi dan wani irin jiri take ji yana neman fad'ar da ita, suka shiga gidan kai tsaye d'aki suka nufa suka tarar da Aunty Murja tana share d'akin Amatullahi ta taimakawa Khadijatullahi ta kwanta a kan gadon, Amatullahi tayi wa Aunty Murja sannu da gida Aunty Murja ta amsa da "yawwa" Amatullahi ta ce "Aunty Murja zan koma gida zuwa anjima zan dawo naga jikin bestyna" Aunty Murja ta ce "to shikenan k'anwata sai kin dawo d'in" Amatullahi ta amsa da "yawwa" sannan ta fita zuwa gida.

Tana zuwa gidan ta tarar da Lado a tsakar gida yana zaman jiranta domin kuwa yanzu soyayyar bogin da suke yi tayi nisa sosai,yana ganinta ya washe baki kamar da gaske sannan ya tashi ya nufeta yana cewa "Sweety shine yau kika yi tafiyarki baki fad'a min ba" Amatullahi ta kalleshi sosai A zuciyarta ta ce "ji shashasha,mahaukaci wallahi ina nan ina had'a muku tarko kai da wannan shakatafin uwar ta ka, za ku san dawa kuke zancen, kayi tunanin zan fad'a tarkonka ne" amman a fili sai tayi wani irin kayatatcen murmushi tare da cewa "Sorry my love wallahi hankalina gaba d'aya baya jikina su besty suna jirana shiyasa" Lado ya ce "Allah sarki to shikenan ba komai kin san bakya laifi a gurina" haka suka jera a kan taburma suka yada zango suna ta hira kamar wasu masoyan gaske (kai Allah ya kyauta miki Amatullahi).

*'BANGAREN HAFSA*

Suna isa gidan ta fito daga mota Khalid ya nufota da gudu yana cewa "Mommy oyoyo" rumgumeshi tayi tare da sumbatarshi a goshinsa kamar ance ta d'ago sai ganin Yaya Safwan yayi a kusa dasu ya rumgume hannuwansa a k'irji yana kallonsu yana murmushi, mik'ewa tayi sannan ta kama hannu Khalid dan har yanzu haushin Yaya Safwan d'in take ji sosai kuma bata tunanin zata iya k'ara soyayya dashi har abada, har sun fara tafiya Khalid ya ce "Mommy kin ga Abbana fa tun d'azu ya zo yana jiranki" Kallon Khalid tayi sannan ta ce "zaka zo mu shiga gidan ne ko kuma suturu zaka yi min" Khalid ganin yadda Hafsa ta chanza masa fuska lokaci d'aya har hawaye yana kok'arin zubowa daga idonta ya ce "Mommy kiyi hak'uri bana son kiyi kuka saboda ni, ki yafe min" Hafsa tayi murmushi sannan ta ce "To mu shiga ciki ko yaron k'irki" Duk abin da suke fad'a Yaya Safwan yana jin su, da sauri ya tsaya a gaban Hafsa tare da saka guiwoyinsa a k'asa cikin muryar tausayi ya fara magana "Hafsa nasan nayi miki abubuwa da dama na wulak'anta soyayyarki na muzguna miki, Hafsa gani a gabanki kiyi min duk hukuncin da kike so zan karb'eshi hannu bibbiyu amman dan Allah ki karb'i soyayyata a karo na biyu wallahi ina tsananin sonki sosai ina k'aunarki Hafsa dan Allah ki tausaya min, karki yi watsi dani dan manzon Allah Hafsa" wani irin kuka Hafsa ta saka tare da jan Khalid suka shige cikin gidan, kai tsaye b'angarenta suka shiga ta fad'a kan gado tana cigaba da kuka, Khalid da ke tsaye a bakin gadon ya zuba mata ido yana kallonta shima yana kukan (Allah sarki soyayya), shi kuwa Yaya Safwan tashi yayi ya shiga cikin motarsa dan ya dad'e da zuwa gidan ya fito zai tafi shine ya ga dawowar Hafsa, Mai gadin ya bud'e masa gate ya fita daga gidan zuciyarsa nayi masa zafi.

*'BANGAREN GIDANSU JABIR*

Yau aka d'aura auren Nihal da wani yaron Alhaji Mansur mai suna Salis, matarsa d'aya da d'ansa namiji sunansa Khamis, iyayen Salis talakawa ne kuma shi kad'ai ne suka haifa da yake Baban Salis yana gadi a ma'aikatar Alhaji Mansur shine ya nemi Alfarma da ya kawo d'ansa domin ya samu aikin yi shima Alhaji Mansur bai k'i ba ya amince aka d'auke shi aiki wannan shine takaitatcen tahirin Salis.

Alhaji Mansur ya yaba da hankalin Salis shiyasa har ya bashi auren Nihal, lokacin da labari yazowa Nihal fad'uwa k'asa tayi sumammiya, Shahida ta d'auko ruwa mai sanyi ta watsa mata nan fa ta farfad'o ta rumgume Hajiya Asiya wacce take gefenta tana kuka, "Mami dan girman Allah ki cewa Abba zan dinga yi masa duk abin da yake so kuma ba zan sake fita daga gidan nan ba har sai idan shine ya bani umarni Amman dan Allah kice a fasa auren nan wallahi bana son shi" ta k'arasa maganar tana kuka kamar ranta zai fita, Teemarh take zaune tana kallonsu kawai ta ja tsaki ta kawar da kanta Abba ne yayi sallama ya shigo d'akin Aliyu da Ango Salis suna biye dashi a baya, Teemarh da Shahid suka amsa sallamar tare da yi musu sannu da zuwa zama suka yi suna amsa musu da "Yawwa" Salis kuwa tunda ya shigo yake kallon Nihal wacce take ta shan kuka zuciyarsa cike da farin ciki, Abba ya fara magana cike da farin ciki bayan yayi addu'o'i ya ce.

"Nihal kamar yadda nasa aka shaida muku an d'aura aurenki yanzun nan to haka yake shiyasa ma nazo tare da mijinki domin ku tafi tare dashi" Amman yayi maganar cikin sanyayaryiyar muryarsa.

Hajiya Asiya tana kuka ta ce "haba Abban Jabir a ina aka tab'a yin haka, ka aurar da yarinya ba tare da ka sanar da ita ba, kuma maimakon ka bari ta fito da zab'in ranta kawai sai ka aura mata wannan matsiyacin" Mami ta k'arasa maganar cike da bak'in cikin mijin nata.

Alhaji Mansur ya ji matuk'ar zafin yadda ta ci mutuncin Salis d'in abin yayi matuk'ar k'ona masa rai amman ya da ke tare da cewa "Ai da ba'a san asalin balbala ba da sai ta ce daga madina take" yayi maganar yana harararta, Salis ma ya ji matuk'ar bak'in cikin yadda Hajiya Asiyan ta ce masa matsiyaci, amman zai tabbatar mata da cewa shi d'in matsiyaci ne a kan 'yarta, sai kuma yayi wani murmushi da ban san ma'anarshi ba.

Hajiya Asiya kuwa mutuwar zaune tayi jin abin da mijin nata ya ce mata tun da take dashi bai tab'a yi mata gorin cewa ita 'yar talakawa ce ba sai yau, tsoronta d'aya kada yaranta su gane cewa ita 'yar talakawa ce dan kuwa idan suka gane ba za ta tab'a yafewa Alhaji Mansur ba, ganin babu wanda ya fahimci abin da Abba ya ke nufi yasa ta sauke ajiyar zuciya a b'oye, tare da godewa Allah.

Muryar Alhaji Mansur ce ta dawo da Nihal daga dogon tunanin da take yi fuskarta shab'e-shab'e da hawaye, "Ke Nihal tashi taje ki shirya ki zo ku tafi domin k'afarki k'afar mijinki" haka Nihal ta mik'e jira na kok'arin d'ibanta ta fara tafiya tana dafa bango, Salis ya bi ta da kallo yana ra ya abubuwa da yawa a zuciyarsa, fuskarsa kuma har yanzu kunshe take da wannan murmushin nashi.

Nihal tana shiga d'akinta tayi saurin shiryawa dan tasan halin Abbanta idan ta dad'e sai ya shigo har d'akin yayi mata dukan tsiya, cikin wata atamfa coffe brown ko mai bata shafa ba ta yafa mayafi ta fito, Salis ya mik'e suka yi sallama da Abba da Aliyu ya saka Nihal a gaba suka nufi gurin da yayi parking d'in motarsa, ya bud'e mata murfin motar ta shiga wajen mai zaman banza, sannan ya mayar ya rufe ya zagaya mazaunin driver sai da ya kalleta ya ga fuskar nan babu alamar murmushi ta had'e fuskar nan kamar bata tab'a murmushi a duniya ba.
Chapter 19 · 0% Book details