← Book details Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 54

Sashe 47

Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Haka Alhaji Mukhtar ya dawo gida jikinsa na rawa dan yau burinsa zai cika, dole Asiya ta amince dashi yanzu ko ta k'i ko ta so, kai tsaye d'akinsa ya nufa inda ya tarar da Hajiya Asiya tana kwance a kan makeken gadon d'akin, hannunta rik'e da waya tana daddannawa, da kallo ta bi Alhaji Mukhtar har ya k'araso kusa da ita ya washe baki tare da cewa "Hajiyata an d'aura fa" Hajiya Asiya ta ya tsine fuska "To yayi" Tayi maganar tare da cigaba da danna wayar "To yanzu dai ai zancen 'boye-'boye babu shi, tunda kin zama mallakina" Ya k'arasa maganar tare da fad'awa kan gadon, a gigice Hajiya Asiya ta mik'e tana kallonsa tare da dafe k'irji tana cewa "Me zan gani, me ka ke shirin yi min, to karka so ma ka ji na fad'a maka ban shirya ba" Wani irin kallon kin raina min hankali Alhaji Mukhtar ya ke bin Asiya dashi "Lallai ma Asiya ba ki san ma wanene Mukhtar Sa'id Baba ba, ki je ki tambayi Sadiya za ta fad'a miki wanene ni, indai ina son abu to dole fa sai na same shi ko ta wane irin hali ne, wallahi Asiya tunda aka d'aura mana aure to a yanzun nan sai na samu abin da na ke so gwanda ki shafawa kan ki ruwan sanyi, ki amince tun kafin ki ga ba dai-dai ba" Wata iriyar mahaukaciyar dariya Hajiya Asiya tayi tare da cewa "Ka na tunanin zai amince ka kusance ni ne, to idan mafarki ka ke gwanda ka farka don kuwa ni Asiya wallahi na fi k'arfinka, ba zan iya amincewa d'an mafiya ya kusance ni ba, ko kuma nace matsafi" Ai tana k'arasa maganar ta ji ya d'auketa da wasu zafafan mari tun ina argawa har sai da na gaji na daina na ce Allah ya k'ara wallahi🤣.

Har sai da ta fad'a kan gadon sannan ya cire kayan jikinsa ya kama doguwar rigar jikinta ya yaga ta "Yanzu za ki fahimci wanene ni ke har kin isa ki ce min matsafi to wallahi sai kinyi danasanin haihuwarki da uwarki tayi yau d'in nan" Tun Hajiya Asiya tana iya tureshi har ta fara gazawa haka tana ji tana gani Alhaji Mukhtar ya samu abin da ya ke so, ya tashi ya shiga toilet yayi wanka ya dawo ya shirya cikin tsadaddiyar shadda ya fita daga gidan.

Hajiya Asiya kuwa tashi tayi ta shiga wanka zuciyarta babu alamar nadama wanka ita ma tayi sannan ta dawo ta shirya cikin atamfa blue colour doguwar riga ce, kwanciya tayi a kan gadon tare da lumshe idonta, har bacci ya fara d'aukarta ta ji saukar duka a jikinta, ta yunk'ura da niyyar tashi amman ta kasa sakamakon d'aure hannuwanta da k'afafuwanta da aka yi da sauri ta d'aga kai Alhaji Mukhtar ta gani a kan ta rik'e da wata dorina mai kauri, ta bud'e baki za ta yi magana ta ji saukar wata bulalar haka yayi ta jimgarta tun tana ihu har sai da ya zama ta kasa yin ihun sai dai hawaye da ya ke bin fuskarta, sai da ya gaji dan kansa sannan ya durgar da bulalar ya fita a fusace, kuka Hajiya Asiya ta ke yi mai tsima zuciya gaba d'aya jikinta rad'ad'i ya ke yi mata, fatar jikinta duk ta yi ja, tayi rud'u-rud'u.

*'BANGAREN HAFSA✨*

Yau sauran wata d'aya a d'aura auren Hafsa da Safwan wata iriyar soyayya suke nunawa junansu kamar su cinye juna kullum suna tare, yana zaune kusa da Safna ya d'auki wayarsa ya kira Hafsa ringing d'aya biyu Hafsa ta d'aga wayar tare da yin sallama "Assalamu alaikum Sweetheart" Murmushi Safwan yayi ya ce "Wa'alaikumussalam Ga ruhina za ku gaisa da ita" Yayi maganar tare da sakawa Safna wayar a kunne, Safna idanuwanta suka cicciko da k'alla tana kallonsa a hankali hawaye suka fara gangarowa, Safwan ya d'aure fuska tare da kawar da fuskarsa da kallonta ya fara kok'arin tashi ya bar ta, ganin haka yasa Safna dai-daita kanta "Assalamu alaikum Amarya" Hafsa tayi murmushi dan da taji shuru ta d'auka Safna ba za ta yi mata magana ba "Wa'alaikumussalam Aunty Safna ina yini" Safna ta ce "Lafiya alhamdullahi Ya shirye-shiryen biki","Alhamdullahi Aunty Safna" Safna ta ce "To Allah ya kaimu lokacin sai anjima" Bata jira mai Hafsa za ta ce ba ta ajiye wayar ta nufi d'akinta da gudu tana kuka.

Safwan ya d'auki wayar su kayi sallama da Hafsa, ya bi bayan Safna yana shiga d'akin ya ganta kwance a kan gado tana kuka, ji ta ke zuciyarta kamar za ta fashe (Ni kam nace Safna kin yi namijin kok'ari wallahi ba za iya ba🤣) d'aukarta yayi gaba d'aya ya zauna a kan gado sannan ya dora a jikinsa yana rarrashinta dan kuwa yau Safna ta burgesa sosai ya san saboda kar yayi fushi da ita tayi haka "Ruhina ki yi shuru dan Allah ba na son ki na yin wannan kukan kin ji sarauniyata" Murmushi tayi mai ciwo ta ce "Ruhina dole nayi kuka, dan Allah ka bar ni idan nayi kukan zan ji dad'i a zuciyata, ina jin zuciyata kamar za ta fashe" Ta k'arasa maganar tana kuka, tausayinta ya kamasa "Babyna nasan kina tsananin kishina, amman za ki iya yi min wani alk'awari?" Safna ta d'ago idanuwanta tana kallonsa tare da cewa "Eh zan yi maka" Wayarsa ce ta hau ruri yayi sauri zarota daga aljihu tare da d'agawa yayi sallama ban ji mai wancan d'in ya ce ba sai ji nai ya ce "To insha Allahu ranka ya dad'e gani nan zuwa" Ya fad'a tare da kashe wayar kallon Safna yayi "Ruhin ki yi min afwa mai gidana yana kirana akwai lissafin da za mu yi dashi mun fara to ba mu k'arasa ba kuma uzuri ya kama shi, idan na dawo zamu kin ji Sarauniyata dan Allah ki yi min alk'awari ba za ki daina wannan kukan, zuciyata tana raya min cewar ni mara adalci ne indai na ganki ki na kuka" Yayi maganar cikin yanayin damuwa, murmushi tayi ta ce "Allah sarki ruhina kai ba mara adalci ba ne, kuma zan dai na kuka ka ji ka tafi kawai karka damu","Kinyi min alk'awarin za ki dai na kuka?" Kai ta d'aga masa alamar eh, haka ya tashi ya shirya Safna ta rakashi har gaban mota ya shiga, Safwan ya kafeta da ido yana kallonta ta ce "Allah ya dawo min da kai lafiya","Amin" Har ta juya ta fara tafiya Safwan ya kirawota "Ruhina" Da sauri ta juyo tana kallonsa tana murmushi "Na'am" Shima murmushin yayi mata sannan ya ce "Ina sonki sosai" Yana gama fad'ar haka ya rufe murfin motar ya ja mai gadi ya bud'e masa gate d'in gidan ya fita ya nufi hanyar ma'aikatarsu, Safna kuwa murmushi tai-tayi har ta koma cikin falon ta kwanta tare da kunna kallo.

Sai wajen k'arfe 9:00pm na dare Safwan ya dawo da sauri Safna ta tashi daga kwanciyar da tayi tunda ya tafi tana yi masa sannu da zuwa murmushi yayi tayi zuciyarsa fas, rumgumeta yayi tare da cewa "Da fatan kin cika min alk'awarina ko?" Safna ta ce "Eh na cika ban yi kuka ba" Safwan ya ce "Yawwa er aljanna" Zama su ka yi a kan kujerar da ta tashi sannan ya ce "To yanzu za mu yi maganar alk'awarin da na ke so ki yi min" Safna ba ta ce komai ba sai dai gaba d'aya ta tattara hankalinta a kan sa da jin wane alk'awari kuma ya ke son tayi masa "Ina son ki yi min alk'awarin ba za ki sake yin kuka a kan auren nan da zan yi ba, dan idan na ganki ki na yin kuka ba na jin dad'i a cikin zuciyata dan Allah ruhina ki daure ki yi min alk'awarin nan ko na ji dad'i dan Allah ki daina yawan kukan nan kin ji dan Allah" Safna dai shuru tayi hawaye suna shirin zubowa, amman sai ta daure ta mayar dasu tana kallonsa "Yaya Safwan duk alk'awarin da ake cewa nayi maka, ina yi indai na ji bai fi k'arfina ba amman wannan ba zan iya ba dan ni kai na wani lokacin ban san lokacin da kukan ya ke zuwar min ba sai dai kawai na ji ina yi" Tayi maganar cikin muryar kuka, rumgumeta yayi sosai yana bubbuga bayanta tare da yi kalamai masu dad'i, daga nan suka tashi suka shiga d'aki.

*'BANGAREN INNA LARAI🤦🏽‍♀️😩*
Chapter 47 · 0% Book details