← Book details Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 54

Sashe 30

Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka dai yayi ta rarrashin ta har tayi shuru ta raka shi ya shiga toilet dan yayi wanka ita kuma tana tsaye a bakin kofa tana jiranshi, yana fitowa ta tare shi da towel tana goge masa jiki dukka shima ya goge a cikin toilet d'in, ita ta zab'ar masa kayan da zai saka, sannan ta taimaka masa ya shirya ya fito a asalin angonshi ruwan tea d'in da ta had'e masa ta zuba masa ta bud'e fridge ta d'auko meatpie da cincin d'in da Hajiya Mama ta saka aka yi mata ta ajiye masa tare da cewa "ga wannan duk da nasan ba lallai ka koshi da shi ba","haba dai wannan kayan dad'in masu yawa ai sai kin taya ni ci ma dan yayi min yawa" Hannunta ya jawo ta zauna kusa dashi suka fara cin meatpie d'in hankalinsu a kwance sai da ta tabbatar ya koshi sannan ta kwashe plate d'in ta kai kitchen, haka suka jera a tare domin ta rakashi zuwa bakin mota ya tafi aiki, babu kowa a falon haka ta rakashi ya shiga mota har sai da ta ga ya fita daga gidan sannan ta koma ta shige d'akinta ta kulle da key.

*'BANGAREN SALIS😣*

Salis da taikamakon Allah likitoci suka samu suka yi nasara ya farfad'o amman duk da haka babu abin da yake iya cewa sai nishi da sauke ajiyar zuciya idan an ce masa ya jiki baya iya amsawa sai dai kawai ya gyad'a kai, bashi da wani tunani sai na babyn baby, kullum cikin addu'a yake Allah yasa tana cikin koshin lafiya, Allah ya bata kuwa juriyar rashin ganinsa da bata yi, yau kamar kullum yana kwance a kan gado Mama ta tafi gida domin dafa masa abinci babu kowa a d'akin.

Doctor Sadiya ce ta shigo d'akin domin duba yanayin jikinshi,bayan ta duba sa ta ga jikin nasa da sauk'i ta juya zata fita Salis cikin rawar murya yana maganar a harhard'e ya ce "doctor dan Allah taimakona nake so ki yi" Juyowa tayi tana murmushi jin yayi magana dan duk da ya farfad'o bai yi magana ba, sai dai kawai ya dinga bin mutane da ido "Wane irin taimako kenan?","wayarki na ke so ki ara min zan kira babyna" Babu musu ta mik'a masa wayar sannan ta fita daga d'akin, shi kuwa Salis ya saka number Nihal a wayar sannan ya kara wayar a kunnansa ring d'aya biyu ta d'auka tare da yin sallama "Assalamu alaikum","Babyna" Salis ya fad'a cikin yanayin farin ciki, Nihal wacce take cikin su Shahida duk ta rud'e hawaye suka fara zuba daga idonta "Babyn baby kai ne, ya jikin naka, ko har yanzu ba ka ji sauk'i ba na ji muryarka wani iri" Da kyar ya iya cewa "Babyna duk rashin ki kusa da ni ne ya saka ni, cikin wannan yanayin wallahi ina sonki sosai" Nihal ta k'ara k'ank'ame wayar dan ji take kamar idan bata rik'e wayar sosai da hakan zai nisantata daga mijin na ta, cikin shash-shekar kuka ta ce "Nima ina sonka sosai, kullum da tunaninka na ke kwana ba na iya bacci, yanzu shikenan saki na zaka yi, ba zamu k'ara zama a matsayin ma'aurata ba?","ba zan tab's iya sakinki ba Nihal domin kin ri ga kin zama wani b'angare na jikina, idan har nayi gangancin rabuwa da ke to tabbas kamar nayi gangancin rabuwa da rayuwata saboda ke ce rayuwata" Kuka ta saka sosai, Khadijatullahi ta rik'eta tana ba ta hak'uri shima Salis d'in kukan yake kuma bai kashe wayar ba, rarrashinta ya shiga yi da kalamai masu dad'i har ya samu tayi shuru, haka dai yayi ta yi mata kalaman soyayya ita ma tana mayar masa har sai da kud'in wayar ya k'are sannan Nihal ta ajiye wayar.

Shi kuma Salis a b'angarenshi ya samu sauk'in abin da yake ji a ranshi kuma ya samu nutsuwa doctor Sadiya ta shigo ya ba ta wayar tare da cewa "sai dai kuma mun k'arar miki da credit kuma gashi babu waya a hannuna da na saka miki","Laaa babu komai wallahi" Ta fad'a tare da fita waje, shi kuma ya kwanta wani irin bacci mai dad'i yayi awan gaba dashi.

*'BANGAREN NIHAL💔😰*

Shuru tayi tana jin wani irin sabon son Salis d'in yana k'ara ratsata, Shahida ta ce "to romeo sai ki daina kukan haka ko?" Amatullahi ta ce "Ahhh kin ji mu da wannan tsohuwar ba dole tayi kuka ba ana shirin rabata da kunun zak'in zuciyarta" Khadijatullhi ta ce "Allah ya shiryeki besty wallahi ke ko, meye wani kunun zak'in zuciya da yake duk salon magana kin san shi" Dariya sosai suka dinga yi dan kuwa maganar Khadijatullahi ta basu dariya Hafsa ta ce "wai besty ya kuwa ginin na ki?","Wallahi Allah ya taimake ni, yana daf da rugujewa na isa na samu na k'ara had'eshi da juna","Allah ya shiryeki to" Khadijatullahi tayi magana tana dariya haka dai sukai ta hirarsu abin ban sha'awa wajen k'arfe hud'u Safwan ya zo d'aukan Hafsa har bakin motar suka raka ta, Khadijatullahi ta so ta nok'e tak'i zuwa Hafsa ta b'ata rai shiyasa a dole ta bi su, suka gaisa da Yaya Safwan d'in sannan suka koma gida.

Hajiya Mama wacce take zaune a kan kujera ita da Aliyi suna hira ta kallesu ganinsu reras ta ce "Ohhh ai kuwa idan na zo aurar da ku zan sha kud'i dan ma d'aya daga cikinku ita tana da aure" Tab'e baki Khadijatullahi tayi sannan ta shige d'aki dan ita ba ta son duk abin da ya danganci aure ko kuma namiji "to matar d'aki d'azu kin fito yanzu daga maganar aure shi ne zaki koma"Hajiya Mama ta fad'a tana bin bayan Khadijatullahi da kallo ma d'akin suka nufa Amatullahi ta ce Hajiya Mama "ai ke dai bari wallahi ni zan dinga tara miki kud'in ma, ki dinga shan farfesu" Ta yi maganar tare da shigewa d'akin.

Hirarsu suka shiga yi daga k'arshe Nihal ta ce "ya kamata mu je gurin Aunty Murja yau kwananta d'aya kar ta ga ba mu je ba","hakane kam" Amatullahi ta fad'a "ku bari sai gobe kun ga yanzu yamma tayi sosai" Khadijatullahi ta fad'a "Allah ya kai mu goben lafiya" Shahida tayi maganar tana murmushi "Amin ya rabbi" suka amsa gaba d'ayansu.

*'WASHE GARI💥🔱*

Hankalin Safna a tashe yake gaba d'aya ta kasa tsaye ta kasa zaune, saboda tun da jiya da ruhinta ya fita bai dawo ba, kuma da dare yayi ta ga bai dawo ba ta shirya ta tafi gidan su Hafsa ta ga ko yana chan tana zuwa ta shiga gidan da sallama duk a firgice take dukansu suna falo har da Abbansu Hafsa tana rumgume da Khalid tana yi masa wasa, kai tsaye gurin Hafsa ta nufi tana tambayarta "Hafsa ina ruhina","wanene kuma ruhinki" Hafsa ta tambayeta dan gaba d'aya ta yi tunanin Khalid ta zo d'auka "to ya zaki tambayeki ki fito min da mijina" Sai a sannan Hafsa abin da Safna take nufi ta ce "ni tun jiya da ya kawo ni gidan wajen k'arfe hud'u ya ce gida zai tafi ban sake ganinshi ba","ki ka ce tun jiya ba ki ganshi ba?" Safna ta fad'a hawaye na zuba daga idanta Khalid ya matso kusa da ita yana cewa "Mommy ina Abbana","Ban san inda yake ba, tun jiya da ya dawo d'aukar wata takarda ban sake ganinshi ba" Safna ta fad'a tare da zubewa tana kuka, Khalid ma jikinta ya fad'a yana kuka yana kiran "Wayyo Abbana" Hafsa tun da ta ji abin da Safna ta ce hankalinta ya tashi, mikewa tsaye tayi ta nufi d'akinta da gudu tana kuka, Mama da Abba ne suka lallab'a Safna ta tashi da kyar tare da zaunar da Khalid d'in ta fita daga gidan, haka ta koma gidan zuciyarta babu dad'i, ba ta iya yin bacci ba, har gari ya waye yadda ta ga rana haka ta ga dare.

"Ruhina ina ka tafi, kasan ba zan tab'a iya rayuwa ba tare da kai ba, idan har ban ganka ba rayuwata zata lalace, dan Allah ka dawo gareni" Haka tai tayin sambatu abin ban tausayi, t.v da ke manne a falon wacce tun jiya da yamma wajen k'arfe uku da Safna ta kunnata tana kallon bbc hausa ba ta kashe ta ba, ta ji abin da ya saka ta tashin hankali, sanarwa ta ji anyi a kan jiya da yamma anyi hatsari a wajen club road kuma ta san tanan Ruhinta yake bi kullum idan zai dawo gida.

Anan fa aka shiga nuna gawarwakin mutanan da suka mutu hango motar Safwan tayi a gefen titin duk ta farfashe wata iriyar gigitatciyar k'ara ta kwalla tare da zubewa a k'asa sumammiya...................!😉💕

Hafsa ce ta shigo gidan a firgice saboda ita ma ta ga hatsarin da aka nuna a bbc hausa k'afafuwanta babu takalmi ko mayafi ba ta tsaya d'auka ba wata huta ce a kan ta, haka ta fito daga gidannasu tana gudu kamar wata mahaukaciya har ta iso gidan Safwan d'in.

Kai tsaye falon ta nufa tana gudu, tana shiga ta ga Safna ta baje a k'asa, ta nufeta tana girgizata tana kiran sunanta Amman shuru, wata dabara ce ta fad'o mata da sauri ta nufi fridge ta d'auko ruwa Mai sanyi ta shek'awa Safna, ai kuwa sai gashi ko second d'aya Safna ba ta yi ba, ta farfad'o tare da rushewa da wani irin kuka, rumgumeta Hafsa tayi sukai ta rara kuka.

Mama,Abba da Khalid ne suka danno cikin gidan daman gate d'in gidan a wangale yake domin kuwa, saboda dokar da Safwan ya sakawa mai gadin cewar idan lokacin dawowarsa yayi to ya dinga bud'e gate d'in dan baya son ya dawo gidan yayi tayin hon,shi kan shi mai gadi a gigice yake, tun da ya ji labarin hatsarin, a parking space sukai parking, kowanne daga cikinsu hankalinsa a tashe yake, sun fito kenan sun nufi hanyar da zata sadasu da falon gidan sai jin tsayawar mota suka yi a bayansu, ba su iya juyawa ba,sai ma cigaba da tafiya da suka yi sai jin muryar Alhaji Yahaya mahaifin Safwan yana kiran sunansa, da sauri suka tsaya tare da juyawa.
Chapter 30 · 0% Book details