Sashe 42
Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Malam ka matsa min daga hanya zan huce" Tayi maganar cikin tsawa, "Haba Dija ta wai ni menene laifina, wallahi ni da gaske nake ina sonki kuma auren........." Saukar marin da ya ji ne yasa shi yin shuru bai k'arasa maganar ba, ya dafe gurin yana kallonta cike da mamaki, "Idan baka fita a harka ta ba, to wallahi kad'an ma ka gani, kuma idan ka cigaba da dorawa kanka soyayyata to tabbas za ka mutu ko kuma nace lokacin mutuwarka yayi, dan ni ba zan tab'a sonka ba na tsaneka kai ba ma kai kad'ai ba gaba d'aya mazan duniyar nan na tsanesu" Tana gama fad'ar haka ta wuce fuuuu ta shige falon saukar bak'i.
Aliyu kuwa wasu zafafan hawaye ne suka shiga zubo masa ya d'auki kusan mintina talatin a tsaye har sai da ya ji k'afafuwansa suna rawa sannan ya samu ya lallab'a ya koma d'akinsa zuciyarsa kamar zata fashe ga wani irin zafi da ya ji zuciyar ta sa take yi masa, sai bugawa ta ke yi da k'arfi.
Kwanciya yayi a kan gadonsa tare da runtse ido hawaye na cigaba da zuba daga idanuwansa babu abin da yake maimaitawa sai innalillahi wa inna ilaihi raju'un a haka har ya fara jin sauk'i a cikin zuciyarsa, wani irin bacci mai nauyi yayi awan gaba dashi, Allah sarki Aliyu ka ba ni tausayi Allah ya kawo maka sauk'i.
*'BANGAREN JABIR😂*
Tun da su Abba suka fita hankalinsa ya k'i kwanciya dan kuwa a kan idonsa suka fita gashi Abba yayi masa gargad'i a kan kar ya biyosu, wannan dalilin ne yasa bai bi bayansu ba, yana nan zaune a falo jugum yana jiran ganin Abba dan kuwa Jabir ya d'auki alk'awarin duk wanda ya sake ya sha jinin mahaifinsa to tabbas sai ya tabbatar ya kashe shi koma d'an gidan uban waye, Shigowar su Abba da Aunty Murja ne yasa Jabir mik'ewa da sauri yana sakin wata aijiyar zuciya tare da yin murmushi "Abbana kun dawo kai amman na ji dad'i sosai hankalina ya kasa kwanciya, dan ban san halin da ku ke ciki ba" Abba yayi murmushi tare da cewa "muna lafiya ya kamata ka je ka kwanta dare ya yi" Jabir ya ce "to Abba" Sannan ya shige d'akinsa Aunty Murja ta bi bayansa da kallon dan kuwa wani irin haushin Jabir d'in ta ke ji,duk san ta ganshi sai abin da yayi wa Khadijatullahi ya fad'o mata a rai, Alhaji Mansur ya kama hannunta suka shige d'aki, ni kuwa dijartyy nace ba sai na shiga d'akin ba, dan babu kyau shiga hurumin da ba na ka ba😂
Jabir yana shiga d'akinsa Teemarh ta rumgumeshi tare da kissing d'insa a kunci tana cewa "Darling shi ne ka tafi ka bar ni a d'aki" Tayi maganar cike da shagwab'a, Jabir ya ce "Ki yi hak'uri darling kin ji ki min uzuri yau d'in ne na shiga tension" Teemarh ta ce "Allah sarki darling sannu" Abin da ta ce kenan a kan kujera suka zauna Teemarh ta kwanrar da kanta a kan k'irjinsa tare da lumshe idonta shi kuma Jabir abin nema ya samu babu a kan haka ya shiga kissing d'inta har sai da ta kai su sun koma kan gado, ni kuma ina ganin sun nufi kan gado nayi saurin fitowa daga d'akin na koma gidan Hajiya Mama wajen Khadijatullahi.
*'BANGAREN KHADIJATULLAHI🤔*
Tana shiga d'akin ta ci karo da Amatullahi tana tsaye ranta ya gaba b'aci da lamarin Khadijatullahi nan ta shiga zazzaga mata masifa ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba "Wallahi kin ba ni mamaki k'warai da gaske yanzu har za ki iya d'aukar hannu ki mari Aliyu saboda kawai ya ce yana sonki, to insha Allahu wallahi tallahi zan je nayi magana da Aliyu ba zai sake tun kararki da maganar soyayya ba kuma sai na fad'awa Aunty Murja duk abubuwan da kike aikatawa, saboda anan kin ga Hajiya Mama da Shahida suna kyaleki shine har kika samu damar marin Aliyu wai me kike tak'ama dashi ne, kin tsani maza ko, to da ke da tsanar sai na had'a ku na zazzageku wanne ai wulk'anci ne da rashin sanin darajar d'an adam" Amatullahi ta k'arasa maganar tare da zama a kan kujera sai huci ta ke yi.
Ita kuwa Khadijatullahi hawaye ne ya shiga zubo mata saboda maganganun Amatullahi sun yi matuk'ar tsaya mata a rai kuma sun bata haushi sosai ashe akwai ranar da za ta zo Amatullahi tayi mata irin wannan rashin mutuncin zaunawa tayi a k'asa tare da rumgume Affan tana kuka tare da cewa.
"Besty meyasa ki ka yi min haka, saboda..........." Cikin masifa Amatullahi ta dakatar da ita da cewa "Ba na son ki ce min komai saboda ni ba na mu'amala da wacce ba ta san darajar d'an adam ba, kuma tabbas sai na tabbatar na fad'awa Aunty Murja duk abin da ki ke yi" Tayi maganar ba tare da ta kalli Khadijatullahi ba, "Dan Allah ki yi hak'uri ki fad'a min abin da zan yi dan na gyara kuskurena karki yi fushi da ni amman ni na yarda ki fad'awa Aunty Murja tayi min duk hukuncin da ya dace da ni amman dan Allah karki ce za ki dai na min magana dan hakan zai saka zuciyata cikin tsananin damuwa" Ta k'arasa maganar tana had'e hannayenta guri d'aya alamar rok'o tana cigaba da yin kukan.
"To idan kina so kar inyi fushi da ke, ki je ki ba wa Yaya Aliyu hak'uri kuma ki karb'i soyayyarsa idan kuma ki ka k'i to babu ni babu ke har abada" Amatullahi tayi maganar fuskar nan ta ta a d'aure, Khadijatullahi cikin rawar murya ta ce "zan yadda ki ke so" Amatullahi ba ta k'ara ce mata komai ba ta d'auki Affan wanda ya ke kan cinyar Khadijatullahi ta shige bedroom ta bar Amatullahi zaune tana kuka, duk da cewar ta tsani Aliyu amman ya zame mata dole ta je ta nuna masa ta amince da soyayyarsa kuma ta bashi hak'uri saboda Amatullahi kar ta yi fushi da ita, dan haka ta barshi a zuwan idan gari ya waye sai ta je har d'akinsa suyi magana.
Shahida duk abin da suke fad'a duk tana ji dan bata wani jima da tashi ba, tayi farin ciki sosai duk da cewar ita Khadijatullahi ba'a son ranta zata karb'i soyayyar Aliyu ba, amman ta san hakan zai faranta ran d'an uwan na ta kuma daga wannan lokacin Khadijatullahi za ta san ba duka maza ne suka taru suka zama d'aya ba kuma halin Jabir da Aliyu sam ba d'aya yake ba, shi Aliyu yana da kyakkyawar zuciya kuma ita gaskiya tunda suke dashi bai tab'a yin wata budurwa ba, dan 'yan mata ba sa gabanshi, a haka dai wani sabon baccin ya kwasheta wanda yake cike da mafarkai kala-kala a kan Khadijatullahi da Aliyu.
Misalin k'arfe 7:30am na safe Khadijatullahi ta gama had'a musu breakfast ta shirya cikin wata shadda pink ta saka hijabinta har k'asa ta d'auki abincin Aliyu ta nufi d'akinsa a bakin kofar ta tsaya tare da kwankwasawa, Aliyu wanda yayi shirinsa na zuwa office amman saboda irin damuwar da yake ciki, ji yake duniyar tayi masa zafi dan a halin yanzu gaba d'aya baya cikin nutsuwarsa, jin ana kwankwasa kofar ne yasa ya zauna a kan kujera tare da cewa "Shigo" Dan shi a tunaninsa Shahida ce ta zo kawo masa breakfast d'insa.
Khadijatullahi ta shiga d'auke da sallama a bakinta, da sauri Aliyu ya mik'e jin muryar zab'in zuciyarsa dan kuwa ko a mafarki ya ji wannan daddad'ar muryar to tabbas sai ya farka daga baccin nasa, "Dija ta" Aliyu ya fad'a tare da kafeta da manyan idanuwansa yana murmushi hawaye na kok'arin zubo masa, Khadijatullahi ba ta amsa ba har sai da ta ajiye masa abincin a kan table d'in da yake tsakiyar d'akin sannan ta dawo gurin da yake tsaye tasa guiwoyinta a k'asa tana cewa "Dan Allah Yaya Aliyu ka yi hak'uri da abin da nayi maka d'azu, ba zan sake ba" Wani irin farin ciki ne ya shiga ratsa zuciyar Aliyu ya k'ara fad'ad'a murmushinsa, shima ya tsugunna suna kallon juna ido cikin ido da sauri Khadijatullahi ta kawar da kanta dan jin wani irin abu da ya tsarga mata zuciya saboda Aliyu yana da matuk'ar kwarjini ba za ta iya jurewa su yi kallon ido cikin ido ba.
"My Heartbeat yau ke ce da kanki ki ka zo ki ba ni hak'uri gaskiya na ji matuk'ar dad'i fiye da tunaninki ina sonki sosai dan haka tun lokacin da abin ya faru na mance dashi na d'aukeshi tamkar mafarki na yi muku na farka fatana shi ne ki karb'i soyayyata" Murmushin yak'e Khadijatullahi tayi "nagode sosai ni zan tafi besty tana jirana zamu tafi makaranta" Aliyu ya ce "to ai nima Office zan je, ai sai na sauke ku a makarantar","to shikenan" Abin da kawai Khadijatullahi ta fad'a sannan ta tashi tayi masa sallama ta fita.
Aliyu kuwa ya rasa inda zai tsoma ransa ji yake tamkar anyi masa albishir da gidan Aljanna haka ya zauna ya bud'e abincin soyayyan dankalin turawa ne sai kuma kwai da aka soya shi daban ya ci sosai dan ji yayi kamar kar ya daina ci, "gaskiya matata ta iya girki" Yayi maganar a fili yana murmushi, jakarsa ya rataya a kafad'arsa sannan ya fita zuwa d'akin Hajiya Mama.