← Book details Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 54

Sashe 43

Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A zazzaune ya tarar dasu sun gama shirin su da alama shi suke jira Shahida ta ce "kai Yaya Aliyu Haidar shi ne ka shanyamu sai mun yi lating" Harara ya wurga mata sannan ya k'arasa gaba Hajiya Mama ya tsugunna ya gaisheta ta amsa tana sakar masa murmushi sannan ya mik'e tare da juyawa nan suka had'a ido da Khadijatullahi tayi saurin sunkuyar da kanta k'asa murmushi yayi tare da cewa "to muje ko darling sisters karku makara" Sai da su ka yi wa Hajiya Mama sallama sannan suka fita Aliyu yana biye da su a baya, suna zuwa motar Amatullahi da Shahida suka shige bayan motar Khadijatullahi za ta shiga Amatullahi ta ce ta shiga gaban motar ranta ya b'aci sosai wato wulak'ancin da za su yi mata kenan Aliyu ne ya bud'e mata kofar gaban motar babu musu ta shiga ya rufe ya za ga ya mazaunin driver ya zauna sai da ya kalli Khadijatullahi sannan ya ja motar ya nufi makarantarsu Khadijatullahi sai da ya sauke su sannan ya kai Shahida gurin aikinta shima ya huce na shi gurin aikin.

*Wannan kenan💃🏽*

*'BANGAREN SALIS DA NIHAL🌹💍*

Salis da Nihal wata iriyar sabuwar soyayya su ke nunawa junansu kamar su had'iye juna, kullum suna manne da juna kamar cingum, zuwa aiki ne kawai yake raba ta dashi nan ma idan zai tafi ta dinga yi masa kuka kenan ya tafi da ita, yau ma hakan take yayi shirinsa kyaf na zuwa aiki Nihal ita ma ta shirya ta saka hijabi har k'asa tana rataye da jakarsa a kafad'arta suna tafiya suna yin hirarsu ta masoya har suka iso gurin motar Salis Nihal tayi saurin shigewa gaban motar ta rufe, Salis ya saki murmushi dan kuwa ya fahimci kwana biyun nan wata iriyar sabuwar shagwab'a Nihal d'in ta ke ji.

Bud'e motar yayi ya zura kansa yana kallonta ita kuma sai turo masa baki take idanuwanta sun cicciko da kwalla za ta yi kuka ta ce "Yau ma ba za ka je da ni ba ko?" Tayi maganar hawaye na gangarowa daga idanuwanta, hannunsa yasa yana goge mata hawayen fuskarsa ta chanza zuwa yanayin damuwa ya ce "Am sorry Babyna na saka ki kuka, kin san ina sonki da yawa ba na son kowane banza ya dinga kalle min fuskar kyakkyawar matata, ina matuk'ar kishinki sosai kin ga Ma'aikatarmu gaba d'ayanmu maza ne, babu mata wannan shine dalilin" Nihal ta ce "to na ji zan zauna a mota" Salis ya shiga motar dan kuwa yasan daman idan Nihal tayi irin wannan rigimar sai yayi da gaske yake shawo kanta "Ta ya ya zan bar gimbiyata a cikin mota ni kuma na tafi office kina tunanin zan iya barinki a cikin mota, to Wallahi Nafisa ba zan tab'a tafi na barki a cikin mota ko da kuma na minti d'aya ne barantana na awanni.

Murmushi Nihal tayi jin ya fad'i sunata na gaskiya dan ba ta tab'a jin ya fad'a ba sai yau, irin yadda ya fad'i sunan nata cikin wani irin salo yayi matuk'ar sakata nishad'i kuma ta ji tana matuk'ar k'aunar sunan na ta, "to amman ni ina jin tsoron in zauna ni kad'ai a gidan nan" Murmushi yayi ya ce "to sai na ka na kai ki gidan Mama idan na dawo sai na biya na d'auke ki","Yawwa to shikenan" Fita Salis yayi ya koma mazaunin driver ya ja motar ya nufi gidan mahaifiyarsa, suna isa suka fita a tare suka shiga gidan, Mama tayi matuk'ar yin farin cikin ganinsu tare nan suka gaisheta sannan Salis ya tashi ya fita dan yayi lating ya shiga motarsa ya ja ya nufi ma'aikatarsu.

*'BANGAREN HAJIYA ASIYA👹*

Kwance take a gadon asibiti Alhaji Mukhtar wanda suke tare dashi a k'ungiyar matsafa yana zaune a kan kujera ya zabga tagumi yana kallonta, Alhaji Mukhtar jiya ya makara bai je gidan da wuri ba har bayan da Abba da Aunty Murja suka tafi sannan ya iso gidan yana shiga ya tarar da Hajiya Asiya kwance male-male cikin jini, bai tsaya yin wani tunani ba shine ya d'auketa ya sakata a mota ya kawota asibiti, wani irin sonta ne yake ji yana ratsa masa cikin jini daman ya dad'e yana son ya nuna mata yana tsananin sonta amman ya rasa yadda zai yi ya sanar da ita, amman abin da ya shige masa duhu shine meyafaru da gidan matsafan nasu ko da wani ne yayi musu lek'en asiri yayi musu shunan 'yan sanda? Amman bashi da me basa amsa dan haka ya watsar da tambayoyi ya shiga yin tunani a kan soyayyar da za su yi da Hajiya Asiya da zarar ta amince masa, shi kuma a shirye yake da yayi komai saboda ita.

Haka dai har wajen k'arfe biyar babu alamar Hajiya Asiya zata farfad'o ko da yake daman likitan ya ce masa zata jima sosai kafin ta farfad'o dan kuma ba k'aramin duka a ka yi mata ba, dan da ba'a kawota asibitin da wuri ba da zata iya rasa ranta, Alhaji Mukhtar ya tashi ya fita domin ya samarwa kansa abin da zai saka a bakinsa wani babban shago ya shiga yayi musu siyayya kusan leda biyar manya-manyan ledoji ne kuma gaba d'aya kayan ciye-ciye ne, ya dawo d'akin da aka kwantar da Hajiya Asiya ya zauna yana jiran farfad'owarta.

*POLY🏛️💕*

Tafiya suka suna hirarsu ta k'awaye suna dariya har suka iso gurin da suke zama, kowaccen su ta samu guri ta zauna Hafsa ta kalli Khadijatullahi ta ce "Amaryar Yaya Aliyu ina gaisuwa" Harararta Khadijatullahi tayi kawai ba tare da ta ce komai ba, sai jijjiga Affan ta ke yi Amatullahi ta ce "Lallai kuwa dai gwanda kema ki fad'a mata ta gyara halinta, dan kuwa duk wanda ya ce yana sonka ai ya gama yi maka komai","Wannan haka yake besty tabbas Yaya Aliyu yana matuk'ar son Khadijatullahi amman ita ta tsaya yi masa shakara (yanga)" Dariya Amatullahi tayi ta ce "Ai kuwa gwanda ta dai na dan kuma Aliyu d'aya ne tamkar da dubu, ba irinsa ake yi wa yanga ba","tabbas"Hafsa tayi maganar tana kallon Khadijatullahi.

Khadijatullahi ta ce " besty wai ba na ce miki shikenan ba"Tayi maganar cikin muryar kuka idanuwanta a kan Amatullahi, kallonta Amatullahi tayi ta ce "Ohh ni yau na ga abin da yafi k'arfina, ce miki nayi ki yi kuka" Khadijatullahi ta goge hawayen da suka zubo mata tare da sauke ajiyar zuciya, Hafsa ta dafata tana cewa "Besty wallahi Yaya Aliyu ba halinsu d'aya da wannan d'an iska kema iya zaman da ku ka yi dashi ya kamata ki fahimci hakan" Khadijatullahi ta kalli Hafsa ta ce "To shikenan Besty" Anan aka koma Aji suka tashi suka nufi ajin na su.

*'BANGAREN TALATU😂*

Lokacin da aka sanar da ita cewa Salis da Nihal sun koma gidansu kuma sun cigaba da yin rayuwarsu ta ma'aurata fad'uwa tayi ta suma har sai da aka kai ta asibiti haka tai-tayin zage-zage a asibitin nan da aka turasu asibitin mahaukata saboda irin yadda take dukan duk wanda ya matso kusa da ita, domin a cewarsu Talatun tana da matsala a kwakwalwarta.

*'BANGAREN ALIYU💔💍*

Da wuri ya dawo daga Office saboda ya d'auko su Khadijatullahi, ko gida bai je ba ya huce gurin da Shahida ta ke yin aiki ya kirata a waya ta ce masa yanzu zata fito ya jirata ta gama komai, ko minti d'aya ba'a yi ba sai ga Shahida ta fito gaban motar ta bud'e ta shiga, Aliyu ya ja motar ya huce makarantar su Khadijatullahi, ai kuwa yayi sa'a yana isa makarantar ana tashin su Khadijatullahi fitowa su ka yi daga motar suka jinjina a jikin motar, Khadijatullahi wacce tun fitowarta ta ga shigowar motar Aliyu gabanta yayi muguwae fad'uwa haka kawai ta ke jin wani irin abu a cikin zuciyarta, Amatullahi da Hafsa kuwa ba su gansu ba, sai da su ka zo daf dasu sannan Amatullahi ta gansu murmushi tayi tare da kallon Khadijatullahi "Besty ga mijinki ya zo d'aukarmu" Kallonta Khadijatullahi ta ce "Yaya Aliyu ai na ganshi tunda mu ka fito" Tayi maganar cikin wani irin yanayi dan ba ta son ran bestyn na ta ya b'aci.

K'arasawa gurin da suke tsaya su ka yi Hafsa ta rumgume Shahida tana cewa "Oyoyo sister ina Sister Nafisa" Shahida tayi murmushi ta ce "Nihal tana chan gidanta, ta koma yau satinta uku kenan da komawa" Hafsa ta ce "Allah sarki zan kirata kuwa" Sai kuma ta kalli Aliyu ta ce "Yaya Aliyu ina yini" Murmushi yayi sannan ya ce "Lafiya alhamdulillahi, ya karatu?",mun gode Allah" Hafsa ta fad'a tana kallon motar Yaya Safwan wacce ya kunno hancin motar cikin makarantar yayi parking sannan ya fito ya nufo gurin da su Hafsa suke dan ya gansu tun shigowarsa, hannu ya mik'awa Aliyu su ka yi musafaha Hafsa ta ce "Yaya Safwan wannan shine Yaya Aliyun da nake baka labarin cewar shi zai auri bestyna Khadijatullahi" Murmushi Safwan yayi ya ce "Ai na sanshi Aliyu Mansur Jikamshi"Aliyu ya ce "Wato Hafsyy har kin ba shi wannan labarin kenan" Yayi maganar cike da jin dad'in maganar Hafsa sannan ya dora da cewar "Ai mun san juna ni da Safwan sosai" Hafsa ta ce "Au to ai shikenan ma" Haka su ka yi d'an hira da bata huce minti biyu ba, Hafsa tayi musu sallama suka jera ita da Safwan suka shiga mota Hafsa tana d'agowa su Khadijatullahi hannu har suka fita daga makarantar.

Aliyu ya bud'ewa Khadijatullahi gaban motar ta shiga dan su Shahida tunda motar su Hafsa ta fita daga makarantar suka bud'e bayan motar suka shiga, suka bar Khadijatullahi a tsaye ita da Aliyu, shima zagayawa yayi ya zauna mazaunin driver ya ja motar suka nufi gida, Aliyu yana tuki yana satar kallon Khadijatullahi ita kuwa tana lura dashi dan tana kallonsa ta jefen idonta amman ta nuna kamar ba ta san abin da ya ke yi ba.
Chapter 43 · 0% Book details