← Book details Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 54

Sashe 50

Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya Asiya ta sha matuk'ar wahala a hannun Alhaji Mukhtar tun da ya samu abin da yake so daga gareta, ya ke nuna mata tsantsar tsana kullum cikin dukanta yake, gashi matarsa ma haka zatai mata rashin mutunci kuma ta sakata wankin kayanta dana yaranta, duk rashin mutuncin Hajiya Asiya sai da bakinta ya mutu, nadamar abin da tayi wa iyayenta da mijinta ta shiga zuciyarta, tunani ta shiga yi yadda zata samu ta rabu da auren Alhaji Mukhtar ta koma gurin mijinta ta nemi gafarsa kuma ta je gurin iyayenta duk da cewa ta san ba lallai su yafe mata ba, domin tayi masu rashin mutunci kala-kala, hawaye ne ya shiga zubo mata "Allah na tuba, Allah ya ubangiji ka yafe min kasa su Innata su yafe min, nasan na zalince su kuma abin da nayi musu ne yake bibiyata, tabbas hausawa sunyi gaskiya da suka ce abin da ka shuka shi zaka girba, yau gashi ina girban abin da na shuka" Ta k'arasa maganar tana kuka mai tab'a zuciya, ta d'auki kusan mintina talatin tana kukan nadamar abin da tayi daga k'arshe ta tashi ta shiga toilet, wanka tayi sannan ta dora alwala ta dawo falon ta shimfid'a dadduma tayi sallah raka'a biyu, ta dad'e tana rok'on Allah ya yafe mata, ta mik'e ta koma kan gado ta zabga tagumi.

"Ke Asiya! Asiya dan ubanki kina ina ne?" A firgice Hajiya Asiya ta mik'e jikinta na rawa ta nufi kofar zata bud'e kamar ance ta lek'a ta window anan ta ga Alhaji Mukhtar ta wata sandar shan jini, gabanta ne ya fad'i, ta ja da baya, idanuwanta ne suka sauka akan wata 'yar k'aramar kofa da zata iya sadata da gate d'in da zata fita daga gidan, da sauri ta nufi wata drower ta d'auko key d'in kofar ta k'arasa gurin kofar ta bud'e ta fara gudu, Allah ya taimaketa gate d'in gidan a bud'e yake, tana fita ta ga wani mai adaidaita zai huce, ta tsayar dashi ta shiga tare da cewa masa "Ka yi sauri ka bar nan dan Allah zai kasheni" Mai adaidaitan ya ja da gudu sunyi nisa sosai, ya juyo yake tambayarta "Hajiya ina muka nufa?" Anan tayi masa kwatancen inda zai kai ta, suna k'arasowa, ta fita tare da ce masa "Ina zuwa yanzu zan shiga gidan, mai gadi zai kawo maka kud'inka" Mai adaidaitan ya ce "To shikenan babu damuwa" Juyawar da za ta yi suka had'a ido da Alhaji Mansur yana tsaye a bakin motarsa, da sauri ta k'arasa gurinshi tana kuka "Dan Allah Abban Jabir"........ "Ya isa Asiya ki yi min shuru, ba na buk'atar sake ganinki a rayuwata, tunda ke butulu ce baki san darajar d'an adam ba" Durk'ushewa tayi akan guiyoyinta tana kuka "Duk abin da ka fad'a min na san na chanchanci fiye da haka ma, zaka iya kirana da abin da ya fi butulu ma, Amman dan girman Allah Abban Jabir koda ace zaka yanke alak'ar da take tsakaninmu, ina rok'onka ka yafe min, na san nayi maka butulci ban kyauta maka ba, ka yafe min dan Manzon Allah" Alhaji Mansur jikinsa ne ya yi sanyi sosai, dan shi a rayuwarsa baya so ya ga matarsa tana kuk saboda shi "To na ji, ta shi tsaye" Mik'ewa tayi tana jin jiriri yana kok'arin kayar da ita, muryar Alhaji Mansur ta ji yana tambayarta "Wanchan fa, meya tsaya yi" Ya yi maganar yana nuna man adaidaita "Shi ya kawoni, kud'insa zan biya sa" Ta basa amsa kanta a sunkuye.

Zuwa ya yi gurin da mai adaidaitan yake tsaye ya d'auko naira dubu biyar ya mik'a masa, nan fa ya shiga godiya ya ja adaidaitarsa ya yi gaba, shi kuma Alhaji Mansur ya dawo gurin da Hajiya Asiya take tsaya ya ce "Yanzu ai kin ga abin da son zuciyarki ya janyo miki, ni dai yanzu na yafe miki Allah ubangiji ya yafe mana gaba d'ayanmu" Godiya Hajiya Asiya ta shiga yi masa tana kuka, ya dakatar da ita da cewa "Ya isa haka, ni yanzu ina da gurin zuwa zaki iya yin tafiyarki" Hajiya Asiya ta ce "To zan tafi amman dan Allah ina neman wata alfarma a gurinka, ina so ka zo muje tare na nemi yafiyar su Innata dan na san indai na je ni kad'ai ba za su saurareni ba" Alhaji Mansur bai mu sa mata ba ya ce ta shiga mota su je, ta shiga gurin mai zaman banza ta rufe, shi kuma Alhaji Mansur ya ja motar ya nufi gidan su Asiya.

To fa k'ak'ak'ara k'ak'a shin iyayen Hajiya Asiya zasu ya fe mata kuwa, ku biyoni dan jin yadda labarin zai kasance💃🏽.

Suna isa gidan Hajiya Asiya ta ga gaba d'aya ya chanza mata ya koma irin na manyan masu kud'i ta san ko ba'a fad'a ba, Alhaji Mansur ne ya gyara gidan ya zama abin ban sha'awa, ta bud'e murfin motar ta fita amman me sai ta kasa motsawa daga gurin da take, wasu zafafan hawaye suna zubowa daga cikin idanuwanta yanzu da wane idon zata kalli iyayenata wanda rabon da ta saka su a idonta tun ranar aurenta da ta fita ta koma gidan k'awarta Aisha, Alhaji Mansur wanda har ya yi nisa ya juyo yana kallon Asiya, tabbas yasan tafi nadama amman ya kamata ya koya mata hankali sosai "Me ki ka tsaya yi anan? Kin kawo ni ne dan ki tsaya kina kuka" Tafiya ta fara yi inda Alhaji Mansur yayi gaba tana bin sa a baya, wani babban falo suka shiga inda nan take tayi ido biyu da iyayen nata, kuka ta saka tare da k'arasawa gabansu ta zube, magana take son yi amman ta kasa saboda irin kukan da ya ci k'arfinta, su kuwa Malam Kalla ido kawai suka zuba mata, "Dan Allah Inna da baffa ku yafe min abin da nayi muku, na san ban kyauta muku ba idan har baku yafe min ba, to tabbas haka rayuwata zata cigaba da tafiya cikin bak'in ciki da k'unci, ba zan tab'a ganin dai-dai ba, dan Allah ku yafe min na tuba" Alhaji Mansur ya ce "Baffa ku yi hak'uri ku yafewa Asiya tabbas tayi nadamar abin da tayi a baya, dan Allah ku yafe mata" Inna ta sauke ajiyar zuciya tare da cewa "Bakomai Mansur na yafe mata" Malam Kalla ya ce "Tabbas Asiya kin ci darajar Mansur yau da ke kad'ai ki ka zo gidan nan sai na b'alb'allaki, amman bakomai na yafe miki Allah ubangiji ya shiryeki" Nan Alhaji Mansur yayi musu godiya sannan ya mik'e tare da yi musu sallama, ya fita daga falon.

Inna ta cewa Hajiya Asiya "Tashi na nuna miki d'akinki","To" Tayi maganar tare da mik'ewa ta bi bayan Innar, suna shiga d'akin Hajiya Asiya ta ce "Innata ina 'yan uwana","Gaba d'ayansu sun yi aure, amman Hajara tun tafiyarki da 'yan kwanaki aka nemeta aka rasa har yau ba'a ganta ba" Zaro ido Hajiya Asiya tayi ta ce "Inna na shiga uku ina Hajara ta je?" Inna ta ce "Wallahi bamu sani ba, ni na rasa ma ya zan yi"Ta k'arasa maganar tare da fashewa da kuka "Kiyi hak'uri Innata ai na dawo zan je zan nemo duk inda 'yar uwata ta je, zan dawo da ita gida" Hajiya Asiya tayi maganar tare da rumgume Innar tana rarrashinta, har tayi shuru haka dai Innar tayi ta ba wa Asiya labarin irin neman da su ka yi wajen neman Hajara amman ba su sameta ba, kuma basu ji labarin komai a kanta ba "Ina tunanin wani ne ya bata labarinta, shiyasa ta gudu" Hajiya Asiya ta juyo cike da rashin fahimtar inda maganar Innar ta nufa "Inna ban gane ba, labarinta kuma, wane irin labari ne?" Inna ta gyara zama tare da cewa "Hajara ba 'yarmu ba ce tsintota Baffanku ya yi, mun b'oye muku ne saboda ba ma son ku nuna mata wani abu da zai sa ta fahimci ba iyayenku d'aya ba, musamman ke dan nasan indai kika san hakan za ki yi mata gori ne" Hawaye ne ya shiga zubowa Asiya "Innata insha Allah zan nemota, duk inda taje ai bai kamata tayi mana haka ba, ko da ace wani ne ya fad'a mata asalinta ya kamata,ta fad'a muku domin mu ta ya ta nemo iyayenta, bai kamata ta gudu ba" Haka dai Hajiya Asiya tayi ta kwantarwa da mahaifiyar hankali abin gwanin ban sha'awa, ni kam 'yar mutan zazzau nace Hajiya Asiya ko ke fa🤣.

*BAYAN WATA 'DAYA DA SATI BIYU🌼*

Jabir hankalinsa ya gama tashi ko bacci ba ya iya yi saboda tunanin Khadijatullahi, zuwansa gidan Hajiya Mama yafi sau ashirin dan ya samu ya ga Khadijatullahi ya nemi yafiyarta amman kullum yaje baya samun damar ganinta, zaune yake a cikin office d'insa kasancewa Abba ya bashi jagorancin ma'aikatarsa wacce ake yin shainkafa, ya zabga tagumi wayarsa ce ta shiga ruri ya kalli wayar wacce take ajiye a kan taburin office d'in *Bro Aliyu* shine ya bayyana a kan screen d'in wayar, Jabir cike da jin haushin Aliyu gami da wani a zababban kishi da ya taso masa, ya katse kiran Aliyun tare da sakashi a blacklist dan Shahida ta bashi labarin Aliyu ne yake son Khadijatullahi dan har an kusa saka ranar aurensu, tarin takaddu ne a gabansa wad'anda ake jira ya saka hannu, amman ya kasa duba koda guda d'aya baren tana ya saka hannun.
Chapter 50 · 0% Book details