← Book details Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 54

Sashe 52

Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan sati uku aka sallami Jabir suka daga gidan Hajiya Mama dan ya ji sauk'i sosai, yana iya tashi da kansa kuma raunikan da ya ji sun fara warkewa, kullum yana tare da Teemarh da Khadijatullahi a gefensa dan bai yarda d'aya daga cikinsu tayi nesa dashi ba, Affan kuwa kullum yana mak'ale dashi, a yau aka saka ranar auren Khadijatullahi da Jabir da kuma Amatullahi da Aliyu wanda babu wanda ya san da haka gaba d'ayansu, Shahida ce ta fad'o falon da gudu tana tsalle, kallonta su ka yi gaba d'ayansu Aliyu wanda yake zaune yana chatting da abokinsa ya ce "Lafiya kuwa kodai duk a cikin gwaurancin ne" Dariya Jabir ya yi ya ce "Wallahi kuwa bro wannan yarinyar ai sai ana yi mata uzuri" Amatullahi da Khadijatullahi suka fashe da dariya "Kaiii sister ce fa, ita ma ta kusan shiga daga ciki Ammar zai yi wuff da ita" Khadijatullahi tayi maganar tana kallon Shahida wacce ta had'e ranta jin ance Ammar "Allah Aunty kina yi min wulak'anci sosai ni fa ba na son wannan mutumin" Teemarh ta ce "Kin ga kyalesu me ki ka zo fad'a mana na san wannan bakin na ki akwai news da yawa" Shahida ta ce "Yawwah Aunty Fatima shiyasa nake sonki da yawa, A yau ne ranar laraba da misalin k'arfe hud'u da rabi na rana aka saka ranar auren Amatullahi da Yaya Aliyu sannan kuma aka saka ranar auren Khadijatullahi da Yaya Jabir inda za'ayi bikin nan da sati d'aya" Amatullahi a firgice ta ce "Ke! Sister dan Allah ba na son irin wannan wasa ki daina" Shahida ta bud'e baki zatai magana suka ji muryar Nihal tana cewa "Sannan kuma aka saka ranar Aisha Mansur jik'amshi wacce aka fi sani da Shahida da kuma angonta Ammar Muhammad wanda za'ayi bikin rana d'aya da su Yaya Aliyu" Duk da irin yadda Khadijatullahi da Amatullahi suka shiga cikin firgici amman da suka ji abin da Nihal ta ce suka fashe da dariya "Wayyo cicina" Khadijatullahi tayi maganar tana kallon Shahida wacce ta shiga zubar da hawaye, Teemarh ma dariyar ta ke yi "Kai wannan sanarwar tayi min dad'i sosai" Ta yi maganar tana kallon Shahida.

"Nifa ba na son shi, wallahi ba zan au"........"Karki rantse Sister dukkanmu nan mun san bakya son shi, amman ya kamata ki yi hak'uri ki sani fa ai duk wanda yace yana sonka yafi wanda zai ce maka baya sonka Ammar yana sonki sosai to menene aibunsa da ke ba za ki so shi ba, me ya yi miki da kika d'auki tsanar duniya kika dora masa, ya kamata ki yi yak'i da shaid'anin da yake cikin zuciyarki yana kissa ki yi tsanar wanda bashi da wani aibu a rayuwarsa" Khadijatullahi tayi maganar tana kallon Shahida, Nihal ta ce "Dan Allah ki barta Aunty ai sai tai-tayi, tunda ita ma ta koyi wulak'anta mutane" Aliyi ya ce "Zo nan kinji k'anwata" Shahida ta k'arasa gurin da Aliyu yake ta zauna tana kuka "Yi shuru kin ji, karki yi kuka kan yi ya yi miki ciwo" Yayi maganar yana goge mata hawayen kan fuskarta "Yaya Aliyu ta ya zan iya zama dashi bayan ba na son shi" Aliyu ya ce "Shin Ammar akwai abin da ya tab'a yi miki ne? Ko kuma kun tab'a samum sab'ani dashi?" Ta girgiza kai alamar A'a "To meyasa bakya son shi" Shahida ta ce "Kawai Yaya Aliyu nima ban sani ba" Jabir ya ce "Kawai wulak'anci ne wallahi" Aliyu ya ce "Ina son ki yi min alk'awari guda d'aya" Shahida ta ce "Menene shi?","Ina son ki so Ammar kamar yadda yake sonki, idan kuma ki ka k'i to ba zan k'ara yi miki magana ba Yaya Jabir ma haka" Jabir ya ce "Ai ni tun yanzu babu ni babu ita, tunda wulak'anci take ji dashi" Shahida ta ce "Ku yi hak'uri zan aureshi" Aliyu ya ce "Yawwah ko ke fa" Daga nan suka d'an tab'a hirarsu abin sha'awa.

Shirye-shirye bikin ake yi dan sauran kwana d'aya a d'aura aure, bikin yazo dai-dai dana Hafsa dan haka aka ce za'a had'a party aka kama babban guri dan komai yazo musu da sauk'i, Teemarh ita ce uwar biki dan ita ce take shirya yadda take son bikin ya kasance dan har gurin da aka kama ita ta ce aje nan ayi partyn sai yafi, yau da misalin k'arfe hud'u za'ayi partyn Teemaeh ta shirya cikin wani material tayi kyau sosai yadda kasan ita ce amaryar, ta zauna a falon Hajiya Mama ta zabga tagumi komai take tunani oho, Jabir ne ya shigo falon ya tarar da ita zama ya yi kusa da ita yana kiran sunanta amman sam bata ma san yana yi ba, dan tayi nisa sosai wajen tunaninta, hannunta ya kama ya sauke mata tagumin da tayi da sauri ta kalleshi tana murmushi "Darling ashe kai ne, ka ba ni tsoro sosai" Jabir ya ce "Babyna na san dole zaki ji babu dad'i saboda zan yi aure, amman ki yi hak'uri kema ina sonki sosai wallahi" Teemarh tayi murmushi tare da cewa "Haka nace maka saboda za ka yi aure ne, na tsorata karka damu ka ji kawai ka cigaba da shirye-shiryen bikinka, Allah ya bamu zaman lafiya" Tayi maganar tare da mik'ewa ta fita daga falon, Jabir ya bita da kallon yana jin babu dad'i a zuciyarsa.

Wajen k'arfe hud'u aka kawo motoci sama da guda hamsin aka tafi gurin party, amaren gaba d'aya kowannansu kalar kayansa d'aya da angonta, sun yi kyau sosai Safna ita ma tazo bikin duk da cewa ba'a son ranta ta zo ba, Haka aka tashi daga party bayan anci an sha, suka koma gida kowannansu ya tafi d'akinsa dan ya yi bacci, Teemarh kuwa tun da ta shiga d'akin da aka bata take kuka wanda ni kai na ban san na menene ba, haka ta sha kukanta ta shiga toilet tayi alwala tayi sallah sannan ta koma kan gadonta ta kwanta a hankali bacci mai nauyi yayi awan gaba da ita.

Washe gari da misalin k'arfe sha d'aya na safe aka d'aura auren Khadijatullahi da Jabir, Amatullahi da Aliyu da Hafsa da Safwan da kuma Shahida da Ammar, Baban Amatullahi ya samu halattar d'aurin auren 'yar ta sa, inda bayan sun dawo daga gurin d'aurin auren ya saka aka kirata yayi mata nasiha mai ratsa zuciya, daga nan yayi sallama da ita ta koma cikin gidan, shagalin bikin ake yi ba ji ba gani har lokacin kai amarya yayi Jabir ya shigo gidan inda yayi ido biyu da Maminsa duk da cewar yana tsananin fushi da ita sai da ya sakin mata murmushi, ya k'arasa gurin da take ya gaisheta, ta amsa masa tana mai maidar masa da martanin murmushin na sa "Ina Teemarh tun jiya ban ganta ba?" Jabir ya yi maganar yana waige-waige ko zai ga giftawa Teemarh "Yanzu nan ta shiga d'aki za ta yi wanka" Hajiya Mama ta bashi amsarsa, Jabir dai bai ce komai ba dan ya fahimci Teemarh tana cikin damuwa kuma ta k'i bari su had'u tun jiya yake son suyi magana da ita fita Jabir ya yi jikinsa a sanyaye.

*7pm*

Motocin kai amarya suka cika layin, haka aka cika motocin gaba d'aya aka nufi gidan amaren, gidan Khadijatullahi suka fara zuwa inda Jabir yayi katafaren gini aka kai ta har cikin bedroom d'inta suka zaunar da ita a kan gado tare da yi mata nasiha, sannan aka fito aka nufi gidan Amatullahi komai iri d'aya ne da na gidan Khadijatullahi, ita ma sukayi mata nasiha sannan suka huce gidan Shahida shima babban gida ne sosai nasihar ita ma sukayi mata sannan suka koma gida, Jabir yana shiga gidansa yayi sallama kai tsaye 'bangaren Teemarh ya shiga amman abin mamakin a kulle ya tarar dashi, "To ina Teemarh ta ke? Kodai tana gidan Hajiya Mama?" Duk tambayoyin nan a fili yake yin sa, haka ya nufi 'bangaren Khadijatullahi jikinsa a sanyaye k'arasawa kan gadon da take ya yi inda ya yaye mayafin da ta lillib'e fuskarta dashi "Sweetheart" Ya kira sunanta yana murmushi, Khadijatullahi bata iya amsawa ba dan wata iriyar kunyarsa take ji haka dai suka raya wannan daren wajen nunawa junansu soyayya.
Chapter 52 · 0% Book details