← Book details Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 54

Sashe 4

Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata iriyar wahalalliyar ajiyar zuciya suka sauke, doin tunda doctor Halima ta fara magana suka kafeta da idanu sai da ta gama bayanin, Aunty Murja ce ta ce "to doctor mun gode sosai,Allah ya saka da alkhairi, kuma insha Allahu zamu yi iya bakin kok'arinmu ganin mun fitar da ita daga cikin halin damuwar da take ciki".
Wata gajeriyar takadda ta mik'a musu Aunty Murja ta k'arb'a, doctor Halima ta ce "gashi nan magungunan da za'a siyo ne domin idan ta tashi sai a bata d'an ruwan tea ta sha ya d'an ratsata, sai ta sha maganin".
Godiya suka k'ara yi mata sosai sannan suka tashi suka fita, Emargency room d'in suka nufa domin ganin yaya jikin Khadijatullah d'in, d'akin da aka kwantar da ita suka tambaya wata nurse ta nuna musu, suka shiga da sauri Amatullahi ta k'arasa kusa da ita ta kama hannuwanta sai ta fashe da kuka tana magana ciki tashin hankali mara misaltu "dan Allah Khadija ki tashi kin barni a cikin matsananci hali, Allah ya isa tsakanina da Jabir bazan taba yafe maka ba, kai ka jawo mana duk irin halin da muke ciki yanzu da muna cikin kwanciyar hankali amman yanzu ka tsarwatsa mana farin cikinmu insha Allah sai kayi mummunan k'arshe sai kayi mutuwar da ba za'a iya gane gawarka ba shege,d'an iska, azzalumi mara tausayi, mara imani" duk tana kuka take yin wad'annan maganganu, dafata Aunty Murja tayi ita ma tana hawayen "haba Amatullahi ki daina irin wad'annan furucin a kan Jabir, tabbas mun san ya zalinceta amman haka Allah ya riga ya k'addara mana kuma kin san komai muk'addari ne, kuma kowane bawa akwai irin tashi k'addarar ki yi hak'uri kinji k'anwata" ta k'arasa maganar tana bubbuga bayanta, Amatullahi kuwa ta riga ta gama kaiwa k'arshe tabbas da ace Jabir zai bayyana a yanzu zata iya k'asheshi domin ta ramawa k'awarta abin da yayi mata, kallon takardar hannun Aunty Murja tayi wacce doctor Halima ta bata ta magunguna "Aunty bani takardar nan zan siyo magungunan kafin Khadijatullah ta tashi tunda ance tana tashi a bata tea sai a bata maganin" babu musu Aunty Murja ta mik'a mata domin daman ta ba san indai zata samu kud'in siyo magungunan ba, tana kan tunanin ko taje ta ari kud'i sai kuma Amatullah ta ce ta bata zata siyo, tashi tayi daman hijabi ne har k'asa a jikinta ta ce "Aunty Murja sai na dawo" kafin Aunty Murjan ta bata amsa ta fita da sauri.

Amatullahi kuwa tana fita bata zame ko ina ba sai bakin titi ta tari mai adaidaita tayi masa kwatancen inda zai kai ta, sun kai a kalla mintina 10 suna tafiya kafin su isa wani tafkeken gida, ta sauka ta biya mai adaidaitan kud'insa sannan ta d'auki wani k'aton dutse ta nufi gate d'in gidan cikin zafin nama take buga gate d'in gidan, cikin hanzari mai gadi ya nufo gate d'in yana jaraba yana bud'ewa Amatullahi ta bangajeshi ta shiga cikin gidan nan mai gadi ya biyota yana mata bala'i "ke baki da hankali ne kin shigo gidan mutanan kiyi maza ki fita ki yanzun nan nayi miki shegen duka" cikin zafin nama Amatullahi ta juyo ta d'auke mai gadin da wani wawan mari sannan ta cigaba da tafiya, duk da cewa bata san kan gidan ba, amman hakan bai bata damar tsayawa ba tayi tafiyar kusan mintuna 40 sannan ta hango wata kofar glass wacce da alama ita ce kofar shiga falon gidan nufar kofar tayi a kayi sa'a a bud'e take tana zuwa bakin kofar, ta bud'e da kanta, ta shiga ko sallama bata yi ba, hangosu tayi a chan falo gaba d'ayansu sun zauna suna kallon wani indian film, kawai taje ta tsaya a gurin tana yi musu wani irin wulak'antatcen kallo, su Mami da suke falo dukansu suka mik'e suna kallonta "ke kuma daga ina? Uban waye ya baki izinin shigowa har falon nan?" Nihal tayi maganar cikin jin tsiwa "Ubanki ne dan Uwanki" Amatullahi ta fad'a cikin zafin rai, sai kuma ta juya gurin Jabir "Dan ubanka, dan uwarka yarinyar sa ka wulak'anta ka tozarta yanzu tana da ciki dan haka ina fad'a maka da babbar murya kasan inda dare yayi maka domin kuma dole ka d'auki dawainiyarta" cikin mamaki da zafin jin zagin da tayi mata Jabir ya ce "ke kuma daga ina da har zaki zo har ciki gidanmu kina ci mana mutunci", "daga gurin uwarka" ta fad'a jikinta har rawa yake saboda bala'i Nihal ta nufota cikin tsiwa ta cakumeta, ai kuwa Amatullah ta cakumeta ita ma ta had'ata da bango, ta saki wata iriyar gigitatciyar k'ara, a rud'e Mami ta matso kusa da ita da niyyar ta cakumeta Aliyu ya rik'eta, sannan ya matsa kusa da Amatullahi wacce ta shak'e wuyan Nihal sai ihu take ya ce "ki yi hak'uri ki saketa muyi magana" sakinta tayi ta fad'i a k'asa tana rik'e da wuyanta, "ki zauna" Aliyu ya fad'a a takaice "ni ba zama ya kawo ni ba" ta bashi amsa fuskarta a murtuke, "na sani amman ki zauna domin muyi magana" zama tayi tare da hard'e hannayenta, Mami ta ce "kai Aliyu tayi mana irin wannan cin mutuncin amman ka dinga wani lallab'ata kamar kana jin tsoronta", "Mami dan Allah ki zauna, bai kamata ba hakan" yayi magana cikin sigar rarrashi zama suka yi gaba d'aya cike suke da jin haushin Aliyu, shima ya koma ya zauna sannan ya fara magana "baiwar Allah bai kamata ki shigo mana gida babu sanarwa kuma......." hannu Amatullahi ta d'aga masa tare da cewa "a fuskata kaga alamar nazo gidannan da niyyar mutunci, ai 'yan mutunci sune ake sanar dasu tun kafin azo gidansu, kuma wallahi ka ganni nan ba mutunci ne gareni ba, d'an uwanku ne ya sakani nazo har gidannan idan ba haka ba me zanzo nayi a wannan banzan gidan da har wani za'a ce sai na sanar, ina matuk'ar ganin mutuncinka da sai nayi maka abin da ba zaka tab'a mantawa dani ba", wani kayatatcen Murmushi Aliyu yayi ya ce "ki yi hak'uri amman ni ban gane me kike nufi ba, kin ce dan uwanmu ne ya saka ki, ki ka zo anan gidan me yayi miki haka", Amatullahi tayi masa wani matsiyacin kallo sannan ta ce"Ka tambayi d'an uwanka wannan Jabir d'in mai zumin shegu" ta fad'a tana nuna Jabir da yatsa, cikin rashin fahimta Aliyu ya ce "Bro me ya faru ne" domin shi Aliyu bai san Jabir yayi aure ba dan babu wanda ya fad'a masa, Jabir yayi wani gejeran murmushi sannan ya ce "ni da ban fahimci mai ya kawo ta gidannan ba, amman yanzu na fahimta wata yarinya ce wallahi da muka tab'a yin auren wucen gadi da ita a kan ta take magana", Amatullahi za ta yi magana Aliyu ya dakatar da ita ta hanyar cewa "dan Allah ki yi hak'uri duk da cewa ban san me ya faru a tsakaninku da Jabir ba, ina mai baki hak'uri ina zuwa" yayi maganar tare da tashi ya shiga d'akinsa bandir d'in kud'i ya d'auko tare da dawowa falon ya mik'a mata tare da cewa "gashi nan kuje kuyi amfani dashi", tashi tayi ta d'auki takardar da ta zurgawa Jabir a k'asa ta nufi kofar fita ko godiya ba tayi masa ba, haka tayi tafiya mai tsayi sannan ta kai bakin kofar gate d'in ta fita tayi sa'a kuwa tana fita sai ga mai adaidaita yana sauke wasu mata ta tsayar dashi ta shiga ta ce masa "Asibitin nasarawa zaka kai ni" mai adaidaita ya amsa mata da "to hajiya".

A b'angaren Jabir kuwa Amatullahi na fita ya kalli Aliyu cikin jin haushinsa ya ce "Amman wallahi baka da hankali wato har da d'aukar kud'i ka bata" sai kuma ya ja tsaki, Mami kuwa mikewa tayi ta zabgawa Aliyu mari hagu da dama har sai da tayi masa sau bakwai sannan ta rufe shi da bala'i "Amman ban tab'a tunanin zaka iya yarda ayi wa 'yar uwarka rashin mutunci kana kallo ba tare da ka d'auki mataki ba kuma kana jii shashashar yarinyar nan har ni sai da ta zageni amman shine ka goyi da bayanta" Aliyu kuwa cikin jin haushin marin da Mamin tayi masa ya shige d'akinsa a fusace ba tare da ya ce komai ba, haka Mami ta matsa kusa da Nihal ta d'aga ta tare da cewa Shahida "Shahida dan Allah kamata ki kai ta d'akinta" ta ce "to Mami" haka ita ma Mami ta juya ta nufi d'akinta a ka bar Jabir shi kad'ai yana ta sake-sake a cikin zuciyarsa.

Amatullahi kuwa suna isa Asibitin ta sallami mai adaidaita sannan ta nufi gurin da ake siyar da magunguna ta basu takardar suka mata total d'in kud'in magungunan gaba d'ayansu dubu ashirin 20k ta arga ta basu sannan ta nufi d'akin da aka kwantar da Khadijatullahi tana shiga ta tarar har ta tashi tana zaune, tayi sallama ta shiga, Aunty Murja ta amsa mata ta k'arasa ta zauna a bakin gadon tana yiwa Khadijatullahi sannu "sannu besty ya jikin naki" cikin muryar rad'a ta amsa mata "da sauk'i" Amatullahi ta bawa Aunty Murja ledar magungunan tare da ragowar kud'in, cike da mamaki Aunty Murja take kallo Amatullahi tare da wurga mata tambaya, "Amatullahi a ina kika samu wad'annan kud'ad'en masu yawa haka.

Amatullahi ta ce.
"Aunty Murja gidansu Jabir naje domin kuwa in sheda musu da cikin da ke jikin Khadijatullahi ba zai yi ace ga mari ga kuma tsinka jaka ba, dole su d'auki dawainiyyar babyn har ta haihu, anan ta fad'a musu duk yadda suka yi daga farko har k'arshe", Aunty Murja tayi shuru kawai tana kallon Amatullahi har ta gama yi musu bayani, sannan ta nisa ta ce "A gaskiya ban san da wane irin baki zan gode miki ba, ke d'in ta daban ce, amman daga yanzu karki k'ara zuwa gidan saboda kin san halin Jabir tantirin d'an iska ne, dan Allah kinji k'anwata k'arki k'ara zuwa tunda dai kin riga kin je kin sheda musu hakan ma yayi".
Chapter 4 · 0% Book details