← Book details Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 54

Sashe 35

Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani murmushin ya k'ara sakar mata sannan ya ce "me muka yi na rashin imani, dan mun nemi duniyarmu shine zai zama rashin imani, kuma zancen ki fita ai bai ta so ba, domin duk wanda ya shigo nan d'akin to sai na tabbatar ya zama d'aya daga cikin 'yan k'ungiyarmu sannan zan bar sa ya fita","to ni ba na buk'ata ana dole ne?" Tayi maganar cikin bala'i da masifa, murmushi yayi sannan ya ce "ba'a dole amman kuma zaki yi danasani mara adadi, domin kuwa zamu kashe 'ya'yanki ga baki d'ayansu, Jabir, Aliyu, Shahida da kuma 'yar autarsu wacce kika fi so Nihal, idan kina son ki tsetar da yaranki to idan kuma bakya buk'ata to ga hanya zaki iya tafiya"Ya k'arasa maganar tare da nuna mata kofar fita daga d'akin hankalin Hajiya Asiya ya tashi tabbas ba ta son wani abu ya faru da yaranta kuma tunda wad'annan mutane suka iya shafe kofar ta b'ace babu abin da ba zasu iya yi ba kallon saurayin tayi sannan ta ce "na yarda zanyi abin da kuke so, karku tab'a min yarana" Murmushi yayi sannan ya ce "shikenan ai kin tseratar da yaranki, tunda kin yarda" Anan dai wannan saurayin ya ba wa Hajiya Asiya wasu abubuwan na asiri wanda zasu kek'ashe mata zuciya ta ji ba ta tsoron duk abin da zata yi ko suka sakata tayi.

(tofa jama'a Hajiya Asiya ta shiga k'ungiyar masu asiri ya zata kaya kenan😎😳)

*'BANGAREN SALIS*

Jikin Salis ya dad'a rikicewa wanda a yanzu baya iya gane wanda ke kansa, babu abin da yake iya yi sai sunan Nihal da yake fad'a hankalin Mama yayi matuk'ar tashi ta rasa inda zata tsoma ranta, gashi doctor ya ce mata idan har ba'a ba sa abin da yake so ba to haka jikin nasa zai ta yi, ita kuma ta san Nihal yake son a dawo da masa da ita, dan haka babu shiri ta nufi gidan Hajiya Mama domin ta yi bikon Nihal.

Tana shiga gidan ta tarar da Hajiya Mama a tsakar gida tana shan iska su Nihal kuwa suna gidan Kawu Bala babu kowa a gidan ita kad'ai ce, Mama ta tsugunna har k'asa ta gaisar da Hajiya Mama bayan ta yi sallama ta k'araso gurin da Hajiya Mama take zaune,Hajiya Mama ta amsa mata cikin sakin fuska tare da yi mata izinin da ta zauna, ta zauna sannan suka d'an tab'a hirarsu ta duniya sannan Mama ta fara fad'ar abin da ya kawota "Hajiya Mama daman nazo ne a kan ina so Nihal ta koma d'akinta, saboda zamanta haka ba son shi muke ba gaba d'ayanmu" Murmushi Hajiya Mama tayi sannan ta ce "Ai wannan tsakaninku ne uwa da y'arta, yanzu dai suna gidan Kawunsu amman zuwa anjima zasu dawo zan turo miki ita" Mama tayi murmushi sannan ta ce ''to shikenan Hajiya Mama nagode sosai" Daga nan suka cigaba da yin hirarsu sannan Mama tayi wa Hajiya Mama sallama ta tafi, Mama tana fita Hajiya Mama ta ce "Ohh ni yau na ji ikon Allah, wato d'anki yana kok'arin mutuwa shine zaki rarrafo wani biko, to ko zata koma ma ba yanzu ba, sai nan da sati uku" Anan Hajiya Mama tai-tayin fad'a ta inda ta shiga ba tanan take shiga ba.

*'BANGAREN TEEMARH DA JABIR🤣*

Jabir babu yadda bai yi ba a kan ya shawo kan Teemarh ta fad'a tarkonsa amman Teemarh ta gama sanin wanene Jabir da kuma shaid'ancinsa, ya dena fita ko ina kullum yana gida dan ya samu ya yaudari Teemarh tayi tunanin kamar ya dena abin da yake yi, amman a banza domin kuwa Teemarh sam magana ma bata barin ya shiga tsakaninsu, fitowarsa kenan daga toilet yana d'aure da towel ya kalli Teemarh da take zaune a kan kujera tana kallon wani series a Arewa 24 na indian *'kaddarar rayuwa* "darling ki zo ki taimaka min in shirya kinji" Yayi maganar yana marairaice murya, Teemarh tayi kamar ba ta ji mai yace ba, dan ko kallo bai isheta ba, har sai da ya k'ara maimaita maganar da yayi sau biyu sannan ta ce "indai ni zan taimaka maka ka shirya ai kuwa zaka dad'e baka saka kaya ba" Tayi maganar ba tare da ta kallesa ba.

K'arasowa yayi har inda take sannan ya zauna kusa da ita suna fuskantar juna "darling" Ya fad'a tare da mayar da fuskarsa ta tausayi "menene?,wai Jabir me na tsare maka a duniya ka dameni?","babu komai kawai ina so na nuna miki irin yadda na ke sonki ne","hmmmm" Abin da Teemarh ta ce kenan, haka dai Jabir ya k'ara ci suturansa ya tashi ta je drower wasu kayan ball ya d'auko green colour a bayan rigar an rubuta Jabir d'in Teemarh, zama yayi kusa da ita suna yin kallon tare Teemarh dai kam ba ta da lokacin biye masa shiyasa tayi shuru ba ta ce masa komai ba.

*'BANGAREN KHADIJATULLAHI*

Zaune suke a falon Hajiya Mama dukansu sun sakata a gaba yau kwana uku kenan da Khadijatullahi ta haihu amman bata tab'a shayar da jaririn ba, da an zaunar mata da yaron ance ta shayar dashi sai ta saka kuka ta ce ita ba ta so, haka zasu yi su gama har su hak'ura Hajiya Mama ta kalli Khadijatullahi wacce sai kuka take yi sosai tare da cewa "Khadijatu yanzu haka ake rayuwa ace ba za ki shayar sa yaro ba, so kika ya mutu ne?" Ba ta ce komai ba sai ma k'ara sautin kukanta da tayi Aliyu wanda ya zuba mata ido yana kallonta ya ce.
"Dija me jaririn nan yayi miki, dan manzon Allah karki hukuntashi a kan laifin da ba na saba, ki sani fa shi yaro ne k'arami bai san meyafaru a tsakaninki da Yaya Jabir ba, ida da ace yaron nan zai girma a bashi labarin irin abin da Yayana yayi miki to wallahi sai ya fi ki shiga damuwa, tunda an wulak'anta masa mahaifiyarsa, dan Allah Dija ki karb'eshi ki shayar dashi kar ya mutu". Ya k'arasa maganar cikin yanayin tashin hankali zuciyarsa cike da bak'in cikin Halin da Khadijatullahi take cikin yanzu musamman da ya ga hawaye na zubowa daga idonta duk sai ya ji ya tsani duniyar da abin da ke cikinta, domin kuwa ya tsani ya ga tana kuka.

Karb'ar yaron yayi daga hannun Hajiya Mama ya mik'a mata, tare da cewa "Dan Allah ki tausaya masa ki bashi abinci kar ya mutu","ba na son shi" Amin da ace kenan tana kuka, "to na ji bakya sonshi, ina son ki shayar da yaron nan na wata bakwai ni kuma nayi miki alk'awarin ki fad'a min komai kike so zan yi miki shi" Kallonsa tayi tare da d'an tsagaitawa da kukan na ta "da gaske", kai ya gyad'a mata alamar "eh".

"Ina son Jabir ya wulak'anta, ina son yayi mutuwar da ko gawarsa ba za'a iya ganewa ba, sai ana tattaro naman jikinsa saboda irin yadda ya ragargaje kuma..............." Saukar marin da Aunty Murja tayi mata ne, yasa ta rik'e gurin kuma ta kasa k'arasa abin da take son ta fad'a kuka ta saka tare da yunk'urin tashi Aunty Murja ta hankad'ata ta koma ta zauna ta karbi yaron daga hannun Aliyu ta dora mata a cinyarta "ga shi nan idan kin ga dama karki shayar dashi, tunda ke kwata-kwara baki da hankali ki je ki yi duk abin da zaki yi dan kin ga an zauna ana lallab'aki to dan manzon Allah karki shayar dashi ki barshi ya mutu shashasha kawai mara tunani" Tana gama fad'ar haka ta fita ta zauna a kan taburma a tsakar gida wani irin haushin Khadijatullahi take ji, saboda irin maganganun da tayi a gaban 'yan uwan Jabir d'in.

Amatullahi ta kalleta tare da cewa "Ai kin huta tunda har kin sa Aunty Murja fushi saboda wannan bak'ar zuciyar ta ki ai sai ki yi ta yi, dan Annabi tsabar tsanar da kike yi wa Jabir ki kashe jaririn idan kin kashe shi, shi ba asararsa ba ce, tun da bai san ma kina yi ba kuma ko yau jariri ya mutu ko a jikinsa, amman ki yi abin da kika ga dama tun da haka kika zab'arwa kanki".

Ita ma Amatullahi fita tayi kusa da Aunty Murja ta zauna tana raya abubuwa da yawa a ranta, tana son d'aukarwa bestyn ta ta fansar abin da Jabir yayi mata dan yanzu ma shirin da take yi kenan, amman yau bestyn ta ta taba ta haushi sosai, saboda Amatullahi ranta yana matuk'ar son jaririn dan har suna ta bashi Affan dan da haka take kiranshi.

Khadijatullahi kuwa kukanta ya k'ara sauti tana kallon Aliyu shi ma d'in ita yake kallo, yana durkushe a gabanta, "ka ce musu zan shayar dasu su yi hak'uri ba zan k'ara ba","to idan kina son na fad'a musu to ki shayar dashi yanzun nan dan na fad'a musu, kuma na basu hak'uri, kin ga sai kuka yake yi" Aliyu ya fad'a idanuwansa na cikin na ta.

Kallon jaririn take yi wanda sai tsala kuka yake yi ta saka shi a cikin hijabinta sannan ta shiga shayar dashi, shuru Affan yayi yana tsotsar abincinsa, Hajiya Mama,Nihal,Shahida da Aliyu ajiyar zuciya suka sauke tare da godewa Allah da Khadijatullahi yau ta shayar da Affan.

Tashi Aliyu yayi gurinsu Aunty Murja yake basu hak'uri kuma ya fad'a musu Khadijatullahi yanzu haka tana shayar da Affan ne, sun ji dad'i sosai suka tashi suka shiga d'akin Khadijatullahi tana ganinsu ta saka kuka tana cewa "dan Allah ku yi hak'uri ku yafe min na dena" Zama Amatullahi tayi kusa da ita tare da rumgumeta ta ce "Ai yanzu komai ya huce indai zaki dinga kular mana da Affan d'inmu babu wanda zai dinga jin kanmu","Hakane kam indai kina so mu shirya to ki kula da Affan amman wallahi na k'ara jin kina tsangwamar yaron ko kina cewa bakya sonshi to wallahi idan na tafi ba za ki sake ganina ba" Aunty Murja ta fad'a fuskarta babu alamun wasa.
Chapter 35 · 0% Book details