← Book details Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 54

Sashe 13

Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Hankalin Khadijatullahi ya fara kwanciya kuma ta fara rage damuwa da tunanin da take yi, kullum a makaranta zaka gansu su uku ko a aji ma su uku suke zama a banci Hafsa tana matuk'ar jii dasu Khadijatullahi yau ma kamar kullum suna zaune a kujerun roba farfagiyar makarantar a k'asan wata bushiya, Hafsa ta kalli kayan jikinsu Khadijatullahi wanda ya kasance iri d'aya ta ce "Gaskiya fa bana jin dad'in abin da kuke min kuna ware ni a cikin ku" Amatullahi ta kalleta fuskarta d'auke da mamakin abin da Hafsa ta fad'a ta ce "Haba hafsiyy ya za'a yi mu ware ki a cikinmu bayan komai tare kuke yi da ke", Khadijatullahi ta ce "wai ma tsaya me muka yi miki da kika fad'i haka" Hafsa ta ce "gashi nan kuwa komai na ku tare kuke yi kama daga kaya, mayafi, hijabi, d'inki , takalmi, amman ni sai dai ku barni ni kad'ai kayana daban" murmushi suka yi gaba d'aya, Amatullahi ta bud'e baki zata yi magana wayar Hafsa ta hau ruri, Hafsa ta duba screen d'in wayar lokaci d'aya yanayin ta ya sauya hawaye suka fara ambaliya a fuskarta,l m hankalinsu Khadijatullahi yayi matuk'ar tashi cikin rawar murya Khadijatullahi ta ce "Hafsa me yafaru?" kallonsu tayi cikin tashin hankali ta fara magana "ina cikin tashin hankali sisters sabida irin muguwar yaudarar da namiji yayi min" Khadijatullahi da Amatullahi suka had'a ido gabansu yana fad'uwa, Amatullahi ta ce "Hafsa kenan kema kina nufin kin had'u da bakin cikin d'a namiji", Hafsa ta yi murmushi mai ciwo tare da cewa "Amatullahi kedai bari kawai", Khadijatullahi cikin sanyi murya ta ce "ke kuma me namiji yayi miki Hafsa" Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa "Kamar yadda na fad'a muku sunana Hafsa Alk'asim mai fata kasancewar ni kad'ai ce a gurin iyayena suka d'auki son duniya suka d'ora min, na taso cikin gata babu abin da nake nema na rasa a lokacin da na kai shekara goma sha takwas, Yaya Safwan d'an k'anwar Abbana ya fara nunawa yana sona amman ni kuma ina basarwa, a hankali a hankali soyayyar Yaya Safwan ta ginu a cikin zuciyata har ina jin idan babu shi bazan tab'a iya rayuwa ba ko wuni nayi ban ganshi ba hankalina sai ya tashi inyi ta kuka har sai yazo na ganshi sannan zan sami nutsuwa, ganin irin tsantsar soyayyar da muke nunawa junanmu yasa su Abbana suka saka ranar aurenmu, kwatsam wata rana, ranar da bazan tab'a mantawa da ita a tarihin rayuwa ba Yaya Safwan yazo har gida ya sami Abbana ya fad'a masa wai bazai iya aurena ba, saboda ya gano cewa ni karuwa ce ina bin maza, kuma shi gaskiya bazai iya auren karuwa, lokacin da Abbana yazo ya fad'a mana abin da Yaya Safwan ya ce masa ban yarda ba hara sai da naje na sameshi har gida ya maimaita min irin abin da ya fad'awa Abbana, yayi min zagin cin mutunci nayi kuka nayi kuka har nagodewa Allah haka na kwaso k'afafuwana dakyar na dawo gida, Ummie mahaifiyar Yaya Safwan ta sako shi a gaba suka zo har gida amman Yaya Safwan ya ce shi ba zai tab'a aurena ba, amman in har aka tilasta masa ya aureni to tabbas a ranar da aka kai ni suzo su d'auki gawa ta dan wallahi kasheni zai yi, haka Ummie tayi ta kuka tana bani hak'uri Abbana ya ce mata babu komai suka tashi suka tafi, in takaice muku sisters har kwanciya nayi a asibiti ba na iya gane kowa,Allah ubangiji yasa dai akwai sauran kwana na a gaba, muka dawo gida Mommyna ta cigaba da rarrashina, ranar wata asabar sai ga mai gadin gidanmu ya shigo hannunsa rik'e da invitation card ya mik'awa Mommyna ya ce Yaya Safwan ne ya bada a kawo min nan da kwana uku masu zuwa za'a d'aura aurensa nayi kuka Mommyna tayi ta rarrashina, haka na k'arbi katin na yayyagashi nayi watsi dashi, na tashi na shige d'akina, bayan Auren Yaya Safwan da kusan wata hud'u shine aka samar min admission anan makarantar ana sauran kwana uku in fara zuwa makaranta ina zaune a cikin d'akina wayata ta shiga ruri ko dana duba sai naga number ce babu suna, na d'aga tare da yin sallama daga chan b'angaren ya amsa sallamar tare da kiran sunana gabana ne ya fad'i jin muryar Yaya Safwan da sauri na kashe wayar nayi wurgi da ita, na cigaba da yin harkokina a ranar sai ga Yaya Safwan yazo har gida, muna zaune a falo dani da Mommyna da Abbana muna hira yana zuwa gaban Abbana ya tsugunna yana kuka yana fad'ar wai ayi hak'uri da abin da yayi sharrin shaid'an ne, yasan yayi min sharri amman wallahi yana tsananin sona, takaici da bakin ciki ya lillib'e ni, ban san sanda na tashi nace ya tashi ya fitar mana daga gida, ya tashi zai k'araso gurin da nake na shiga d'akina da gudu tun daga ranar shine kullum sai ya kirani ni kuma bana d'agawa yanzu ma shine ya kirani" Hafsa ta k'arasa maganar tana kuka mai tsima zuciyar mai sauraro.

Amatullahi ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya ita dai lamarin maza yana bata tsoro, kwata-kwata babu tausayi ko imani a zuciyarsu tashi tayi ta matsa kusa da Hafsa tana goge mata hawayen fuskarta tana rarrashinta, Khadijatullahi wacce fuskarta tayi sharkaf da hawaye ta ce "wai meyasa maza zazzalumai ne, gaba d'ayansu basu da imani macuta ne" tayi maganar tana sharce hawayen da suke ambaliya a fuskarta, Amatullahi ta ce "Hafsa ki yi hak'uri tabbas Yaya Safwan ya yaudareki kuma yayi miki k'azafi amman da zaki ji abin da Jabir ya yi wa Khadijatullahi zaki san abin da Yaya Safwan yayi miki ba komai ba ne" Hafsa cike da k'aguwar son jin abin da Jabir yayi wa Khadijatullahi ta ce "Sister Khadijatullahi kema kenan kin had'u da bak'in cikin namiji? Amman ke meya faru dake?"

wani irin murmushin mai ciwo tayi sannan ta ce
"Kamar yadda kika sani sunana Khadijatullahi Abbakar Mai yak'i iyayenmu mu biyu suka haifa daga ni sai Aunty Murja wacce ta kasance yayata kuma mahaifiyata, Mahaifina Abbakar mai yak'i yana da rufin asirinsa dai-dai gwargwado domin yana tafiye tafiye zuwa wasu garuruwar ya saro shanuwa ya dawo ya siyar dasu anan garin kano, wannan abin ne yasa gaba d'aya 'yan uwansa suka tsaneshi duk da cewa ciki d'aya suka fito da su, suke nuna mana tsana sosai har ya kasance bama zuwa gurinsu, mahaifiyar babbana da mahaifinsa sun rasu tun kafin babbana ya yi aure sakamakon gobarar da suka yi a gidan cikin dare gaba d'aya suka k'one, ranar wata lahadi ranar da bazan tab'a mantawa da ita babbana ya yi tafiya zuwa zaria domin saro shanuwa, sai gawarsa aka kawo mana ya rasu sakamakon hatsarin da suka yi motar da su babbana suke ciki wata gingimari ta daki motar babu wanda ya rayu dan har driver mutuwa ya yi, lokacin da innarmu ta ga gawar babbana ta yanke jiki ta fad'i ko da muka kai ta asibiti aka shiga da ita emergency room muna nan zaune sai aka fito da ita fuskarta a lillib'e da sauri na k'arasa gurin likitan jikina na rawa nake tambayarsa meyasa suka rufewa innata fuska, ku yi hak'uri domin Allah ya karb'i abinsa abin da likitan suka ce mana kenan, nan Aunty Murja ta fasa ihu ta zube a k'asa tana rusa kuka, nima naje kusa da ita na k'ank'ameta ina kuka, haka muka dawo gida mak'obtanmu suka shigo aka yiwa inna da babba wanka aka kai su makwancinsu na gaskiya, haka rayuwarmu ta cigaba da tafiya muna zaune a gidanmu daga ni sai Aunty Murja duk duniyar tayi mana zafi" A dai-dai nan Khadijatullahi ta tsaya saboda jin k'arar kad'ai k'ararrawar komawa aji "to bari in tsaya anan idan mun fito lokaci bai k'ure ba sai in cigaba idan kuma lokaci ya k'ure gobe idan Allah ya kaimu sai in k'arasa miki" Khadijatullahi tayi maganar cikin muryar kuka.

Hafsa ta ce "Ko lokaci ya k'ure ma sai in bi ku har gida dan yau sai naji labarinki gaba d'aya sannan zan tafi gida" tayi maganar ita ma hawaye na kok'arin zubo mata share hawayen tayi sannan ta matsa kusa da Khadijatullahi ta kama hannunta ita da Amatullahi suka tashi suka nufi ajin zuciyoyinsu cike da bakin ciki.

Wajen k'arfe shida suka tashi daga makarantar suka fito bakin gate Hafsa ta kirawo Mommy a waya ta ce mata yau ba zata samu dawowa da wuri da zata biya gidansu Khadijatullahi da yake Mommy ta san labarin su Khadijatullahi dan haka ta ce to shikenan bakomai, mai adaidaita suka tara ya kai su har kofar gida Hafsa ta biya kud'in, suka shiga gidansu Khadijatullahi amman abin mamaki basu tarar da Aunty Murja ba, Khadijatullahi ta ce "To ina Auntyna taje" Amatullahi ta ce "haba besty kila taje wani gurin ne" haka suka zazzauna a kan taburmar Hafsa ta ce "wallahi har na k'agu in k'arasa jin labarinki" wani murmushi mai ciwo Khadijatullahi tayi sannan ta ce "Yanzu kuwa zaki ji labarina gaba d'aya" Khadijatullahi ta fad'a cikin wani irin yanayi sannan ta fara magana.
Chapter 13 · 0% Book details