← Book details Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 54

Sashe 17

Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tunda ta shiga gida duk inda tayi Khalid yana biye da ita kamar jela, haka tai ta jiran Yaya Safwan domin ya zo ya d'auki Khalid su tafi gida amman har wajen k'arfe 10:30pm na dare babu alamar zuwan Yaya Safwan,ta kama hannunsa suka nufi b'angarenta domin suyi bacci, a kan k'aton gadonta suka kwanta Khalid ya rumgumeta sosai, yana tayi mata labarin makarantarsu "Mommyna kin ga a class d'inmu na fi kowa kok'ari, Abbana har keke ya siya min da nazo ta d'aya" Hafsa ta ce "Kai masha Allah yaron k'irki gaskiya dole Abbanka ya siya maka keke" murmushi Khalid yayi sannan ya ce "Mommy kinga an kusan fara exams idan nazo ta d'aya ke me zaki siya min?" Hafsa ta ce "Me kake so na siya maka?" Khalid ya ce "Ina son ki siya min waya na dinga yin games" Hafsa ta ce "to karka damu insha Allahu zan siya maka waya" cike da jin dad'i Khalid ya ce "da gaske Mommy" Hafsa ta ce "Eh mana, amman Khalid meyasa ka ke ce min Mommy?" Khalid ya ce "Abbana ne ya ce in dinga ce miki Mommy saboda kema Mommyna ce" shuru Hafsa tayi tana kallon yaron, "Lallai wato kitumurmurar da Yaya safwan yayi mata kenan, hmm Allah ya kyauta" tayi maganar a zuciyarta haka suka cigaba da yin hira har bacci ya kwashe su.

*******************************************************

*'BANGAREN AMATULLAHI😂*

Fans dole in dara anzo wajen fa🤣🤣Amatullahi iyayen bala'i bari muji yau da me zata jewa su Inna larai😂😂

Haka Amatullahi ta shiga gidan ta tura kai zata shiga tsakar gidan sai jin Inna Larai tayi tana cewa Lado "wannan yarinyar ba zamu tab'a barinta ba wallahi dole ne, mu kulla mata wata kitumurmurar da zata saka ubanta ya tsaneta" Lado ya ce "kamar me kenan?" Inna Larai ta shek'e da wata iriyar mahaukaciyar dariya sannan ta ce "za ka nuna cewa kana sonta zaka aureta, sai mu sanar da mahaifinta daga nan sai in fad'a maka shirinmu na gaba" Lado ya ce "Inna kin tabbatar wannan shirin naki zai saka mu rabasu" Inna Larai ta ce "rabuwa ta har abada kuwa". Amatullahi tayi wani gajeren murmushi sannan ta shiga gida da sallama sam bata nuna musu cewa taji abin da suka fad'a ba haka ta nufi d'akinta ta kwanta tana murmushi "Lado da Inna Larai kenan wallahi ni Amatullahi na fiku shaid'anci ina nan ina jiran ka furta ka na sona na yarda da soyayyarka daga nan wasan zai fara"

Wayyo ni 'yar mutanan zazzau😂🤣😂Amatullahi da Lado za'a fara soyayya🤣🤣🤣ba zan iya daina dariya ba wayyo cicina😂😂😂Ummu Juwairiyya kina jin wata drama ko😅😅

*'BANGAREN GIDANSU JABIR*

*WASHE GARI⚜️🔱*

Misalin k'arfe sha d'aya na safe Abba ya fito daga d'akinsa ya shirya tsaf cikin wata tsadaddiyar shaddarsa teal blue ko minti biyu Abba bai yi da fitowa ba Aliyu ya fito daga d'akinsa shima shadda ya sa royal blue, Abbah ya ce "Aliyu yi da sauri mun makara fa, suna ta jiranmu" Aliyu ya amsa "to Abba" fita suka yi daga falon suka nufi wajen da aka tanada dan ajiye motoci, suka shiga kai tsaye suka nufi masallaci domin d'aura auren Jabir da Teemarh, masu karatu nasan zaku ce yaya aka yi Abba ya gano iyayen Teemarh har ya je musu da maganar d'aura auren yau, tun jiya da Abba ya shiga d'aki ya k'uduri aniyar d'aura auren Jabir gobe,Aliyu yana zaune Abba ya kirashi a waya ya ce "ya gano masa a ina yarinyar take? kuma su waye iyayenta?" Aliyu bai gane wace yarinyar Abba yake nufi ba sai da yayi masa bayani, sannan ya gane a daren Aliyu ya yi bincike suka yi sa'a kuwa gidansu Teemarh ba wani 'boyayyan gida ba ne, wani abokinsa mai suna Jafar da yake a layin yake shi ya nuna musu gidan, Aliyu ya kirasa a waya domin ya taimaka masa da binciken, da yake Jafar yana ganin Jabir yana zuwa kofar gidansu Teemarh anan yake sanar da Aliyu ai yasan yarinyar dan yana ganin Jabir d'in a gurinta kullum, a daren Abba da Aliyu suka je gurin Jafar ya rakasu har kofar gidansu Teemarh ko da mahaifin Teemarh ya fito Abba ya sanar dashi abin da ya kawosu Mahaifin Teemarh Alhaji Lamid'o yayi matuk'ar farin ciki domin daman bashi da wani buri a yanzu irin ya ga ya aurar da Teemarh domin wannan Harkar barikin da take yi yana matuk'ar kuntata zuciyarsa, haka suka yi sallama ya shiga gidan yake sanar musu Teemarh kuwa tayi farin ciki matuk'a kuma nan da kudiri niyyar sai ta kuntatawa Jabir sai ta gigita rayuwarsa zai san ita ya cewa karuwa haka tayi ta saka irin wahalar da zata bashi da kuma rashin mutuncin da zata dinga yi masa, wannan kenan.

Taro yayi taro an d'aura auren Jabir da Teemarh a kan sadaki naira dubu d'ari haka su Abba suka biya ta gidan su Teemarh domin da ita zasu koma gidan, suna zuwa aka suka tarar har an shirya Teemarh cikin wani tsadaddan lace wanda Alhaji Mansur ne ya saka aka kawo mata kayan lefe akwati goma sha biyu, fuskarta a lillib'e da mayafi aka saka ta mota Aliyu wanda shi yake driving d'in ya ja motar suka nufi gida, suna isa mai gadi ya bud'e musu gate d'in tafkeken gidan suka shiga Aliyu yayi parking, Aliyu ya fito ya bud'ewa Teemarh motar ta fito fuskarta har lokacin a lillib'e take Abba na gaba suna fiye dashi a baya har suka shiga cikin babban falon gaba d'aya suna falon suna kallo Jabir ya dora k'afarsa a kan center table d'in falon, "Assalamu alaikum" suka yi sallama suka shigo, Shahida ce kad'ai ta amsa sallamar tare da yiwa musu sannu da zuwa, suka amsa mata da yawwa Jabir ya kallesu gaba d'aya sannan ya bi yarinyar da fuskarta take lillib'e da mayafi da kallon mamaki zuciyarsa cike da tambayoyi gabansa yana fad'uwa tsoro da firgici suka shigeshi mikewa tsaye yayi yana cigaba da kallon yarinyar, Mami ta kallesu sannan ta fara magana fuskarta kunshe da mamakin wacece wannan "Abban Jabir wacece wannan?" Wani irin kallo ya wurga mata domin gaba d'aya haushinta yake ji kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce "Matar Jabir ce Fatima" Jabir da ke tsaye cike da razana ya ce "Abba wace Fatima kake nufi, ba dai Teemarh kake son ka ce min ba" Abba yayi murmushi sannan ya kalli Teemarh ya ce " 'yata bud'e fuskarki domin su ganki" Teemarh kamar jira take ta yaye mayafin idanuwanta a kan Jabir tana yi masa wani irin kallon zaka gane kurinka, Jabir yayi baya jikinsa na rawa ashe daman jiya da Abba ya ce yau za'a d'aura auren da gaske yake shi gaba d'aya ya yi tunanin kawai fad'a yake yi, "Abba karka min haka dan la'ilaha illallahu ka ce min wasa ka ke min, Abba ba zan iya zama da karuwa ba" magana yake cikin yana yin tashin hankali, Abba bai bi ta k'ansa ba ya juya ya shige d'akinsa.

Nihal kuwa gabanta ya shiga dukan uku uku domin kuwa tasan Abba zai waiwayo kanta dan baya tab'a furta magana ba tare da ya aikata ta ba, hawaye suka shiga zuba daga idanuwanta, ta k'ank'ame Shahida da ke kusa da ita tana cigaba da kuka, hankalin Shahida ya tashi ta shiga rarrashin 'yar uwar ta ta haka ta kama hannunta suka shige d'akin Nihal d'in, Mami ma jikinta a salub'e ta nufi d'akinta, Falon ya rage daga Aliyu sai Jabir sai kuma Amarya Teemarh.

Aliyu ya kalli Teemarh tare da cewa "Aunty Fatima nikam zan huce Allah ya bada zaman lafiya, ina nan ina jiran babies da yawa nan da 'yan shekaru" murmushi Teemarh tayi sannan ta ce "To nagode Aliyu haidar" haka Aliyu ya huce yana kallon Jabir yana murmushin jin dad'i domin kuwa hakan ne ya kamace shi.

Teemarh ta kalli Jabir sannan ta fara matsawa kusa dashi tana magana tana hurga masa harara ta had'e fuskarta kamar ba ita ce ta gama murmushi ba "Jabir d'an tuwa, kai k'aramin k'waro ne kuma zaka san nii Fatima Lamid'o ka cewa karuwa sai na gigita maka rayuwarka kai baka ji ma kunyar kirana da karuwa ba to kasan ni kai ne ka fara lalata ni dan haka dole ka zauna dani a matsayin matarka, kuma ina k'ara fad'a maka da babbar murya cewa idan ka k'ara kirana da karuwa to a wannan ranar zan nuna maka nii cikakkiyar karuwa ce zan bar maka mugun tab'o a rayuwarka" tana gama maganar ta shige d'akin Jabir d'in haka Jabir ya zauna dab'as a k'asa tabbas Abba ya auro masa masifa da bala'i amman kuma dole ya san matakin da zai d'auka dan ba zai tab'a zama da yarinyar da ya gama da ita ba, babu abin da bai sani ba a jikinta, haka dai ya d'auki key d'in motarsa ya fita daga gidan zuciyarsa cike da ba'kin ciki.

*'BANGAREN KHADIJATULLAHI DA AMATULLAHI*
Chapter 17 · 0% Book details