← Book details Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 54

Sashe 29

Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Safwan ya shigo falon domin ya manta wata takardar wad'anda suka siya kaya kuma ake binsu bashi, kallon Safna yayi cike da tausayi tabbas shi kansa ya san Safna tana sonshi sosai, amman kuma Hafsa ita ma tana matuk'ar son shi bai san a cikinsu waya fi son shi ba wannan Allah ne kad'ai yasan hakan, har ya huce sai kuma ya dawo domin bai zai iya barinta cikin yanayin da take ciki ba a yanzu.

Zama yayi a kusa da ita tare da kama hannunta yana murzawa, kamar jira take ta fad'a jikinsa tare da fashewa da wani irin kuka ta k'ank'ameshi kamar wanda aka ce mata idan ta cika shi guduwa zai yi, shi kuwa Safwan shafa gashin kanta ya shiga yi a hankali yana bubbuga bayanta "Yi shuru babyna ba na son kina yin wannan kukan, yana ta da min da hankali sosai","Ba ka so na yanzu, ka fi son Hafsa duk irin abin da nake maka baya burgeka shi ne zaka k'ara aure" Tayi maganar cikin kuka "Wa ya gaya miki cewar ba na sonki, na fi son Hafsa, kuma ke a tunaninki saboda na gaji da ke ne shine zan k'ara aure, ke sanin kanki ne, Hafsa tun kafin na aureki muke tare da ita 'yar uwata ce" Ya saka hannu ya d'agota yana share mata hawayen fuskarta sannan ya cigaba da cewa "Ina sonki sosai Amaryata","da gaske" Tayi maganar cikin farin ciki, kai ya gyad'a mata alamar "eh" sannan ya cigaba da cewa "ko da na auri Hafsa matsayinki ba zai tab'a chanzawa ba, saboda ke ce ruhina ita kuma ita ce rayuwata" Murmushi tayi tana mai jin farin ciki a zuciyarta.

Yanzu kam ta fara samun sassauci a kan zafin da take ji a zuciyarta, sambatarta yayi a kuncinta yana fad'ar "Baby nayi mantuwa ne, shiyasa na dawo zo muje ki ta ya ni d'auko takardar","to" Ta fad'a tare da mik'ewa hannunsu yana rike da na juna suka shiga d'akin ya d'suki takardar sannan ta rakashi har bakin motarsa zai shiga motar ta rumgumeshi ta baya "Baby ka tafi da ni" Murmushi yayi sannan ya juyo ta dora kanta a kan k'irjinsa "Baby ina kishinki sosai ba zan iya tafiya da ke office ba, saboda akwai maza sosai" Murmushi tayi tare da janye jikinta daga na shi tana cewa "To shikenan baby yau da wuri zaka dawo amman ko?" Kai ya gyad'a mata alamar "eh" ta marairaice fuska cikin shagwab'a tace "to k'arfe nawa zaka dawo?","6:00pm dai dai" Nan ta fara kukan shagwab'a "gaskiya ni ban yarda ba, k'arfe 4:00pm na ke so ka dawo","to rigimammiyar matata yadda kike so haka za'ai zan dawo k'arfe 4:00pm insha Allah zan yi kok'arin ganin na gama aiki da wuri" Dariya tayi sosai tare da cewa "to a dawo lafiya" Mota Safwan ya shiga ya ja har ya fita daga gidan Safna tana d'aga masa hannu.

Sai da mai gadin ya rufe kofar san ta nufi falon zama tayi a kan kujera ta lumshe ido tunda dai Safwan yace ita ce ruhinsa ai shikenan yanzu dai ta san ita ma tana da matsayi mai girma a gurinshi kuma ta san abubuwan da Safwan yake so da wanda baya so dan haka ta haka zata bi ta kwace mijinta ko da kuma Hafsan ta shigo ba ta isa ta fi ta a gurinshi ba dan ta san ba lallai ne ita ta san abubuwan da yake so da wanda baya so ba, murmushi tayi sannan ta tashi ta shiga gyara gidan wanda yayi kaca-kaca, nan gidan yayi kyau ta shiga kitchen nan ma ta gyara shi sannan ta dawo falon ta kwanta kafin k'arfe uku tayi ta dora girki ta san wajen hud'u ta gama sai ya dawo ya ci abincin da zafinsa.

*'BANGAREN GIDANSU JABIR*

Da sassafe Aunty Murja ta tashi dakyar tana dafa bango cikin sand'a take tafiyar dan kar ta tashi mijin nata daga bacci, shi kuwa Alhaji Mansur tun lokacin da ta tashi shi ma ya farka wani irin farin ciki ne ya kama shi tabbas tun kafin aje ko ina Murjanatu tana shayar da shi zumar soyayya wacce ya gaza samunta a gurin Hajiya Asiya kitchen ta shiga dan d'akin har da kitchen a cikinsa komai akwai a cikin kitchen d'in dan haka ta fere dankalin turawa ba tare da ta yanyanka shi ba, ta fasa kwai ta saka masa tattaruhu da albasa da su maggi da curry ta shiga tsoma wannan dankali tana soyashi har ta gama ta saka ta wani kwanon kas ta fito dashi ta ajiyeshi a kan teburin ta koma kitchen d'in ta dora ruwan tea ta saka masa citta,kanin fari da masoro sannan shima ta zuba a flask ta d'aukoshi ta ajiye kusa da wannan kwanon dankalin, toilet ta shiga tayi wanka sannan ta had'a masa ruwan wanka ta fito ta shirya cikin wata atamfa kofi colour d'inkin riga da siket tayi kyau sosai zama tayi kusa da Alhaji Mansur d'in dan ta tashe sa yayi wanka ya ci abinci kada ya makara gurin aikinsa.

Kallonsa wata iriyar kunyarsa take ji tun jiya, murmushi tayi tare da shafar fuskarsa, idanuwansa ya bud'e ya zuba su kanta suka had'a ido tayi saurin saka hannuwanta ta rufe fuskarta tana dariya, tashi yayi zaune ya jawo ta jikinsa yana kok'arin cire hannuwanta daga fuskarta, Hajiya Asiya ta banko kofar d'akin da k'arfi idanuwanta suka sauka a kan su ganin Aunty Murja a kan cinyar Alhaji Mansur shi kuwa ya rumgumota jikinsa suna ta kokawa wani irin ihu ta kwalla.

Babu wanda ya ji ihun domin kuwa kowa yana d'akinsa kuma akwai tazara mai yawa tsananin d'akin Abba da sauran d'akunan, Aunty Murja ta bud'e ido k'irjinta sai bugawa yake amman a fili ba ta nuna tsoro ko fargaba ba, ta shiga kok'arin tashi daga jikin Alhaji Mansur d'in amman bai ba ta izinin yin haka ba, ya rumgumeta sosai dan ko motsi ma bata iya yi, Hajiya Asiya zuciyarta kamar zata fashe "to tsohuwar 'yar bariki ke har kin isa har kina da matsayin da zaki zauna a jikin miji, to wallahi yau sai kin gammace da baki auri Mansur ba" Tayi maganar cikin yanayin tashin hankali.

Juyo da fuskar Aunty Murja, Alhaji Mansur yayi suna kallon kallo wani irin murmushi yake sakar mata ita ma tana mayar masa da martani "meyasa ki ka je kika yi wanka ba tare da kin tashe ni mun yi tare ba" Abba yayi maganar yana kallon cikin idon Aunty Murja, ita kuwa duk sai ta ji kunya a wani b'angaren kuma ta ji babu dad'i domin Hajiya Asiya tana nan kuma ta san ta ji abin da ya ce mata.

"Ka yi hak'uri ba zan sake yin makamancin irin haka ba, na ga ka na bacci ne shiyasa" Ta bashi amsa domin ta san inda tayi shuru zai ji haushi, kuma yayi fushi da ita,ita kuma a duniyar nan ta tsani Alhaji Mansur yayi fushi da ita, dan ba za ta iya jurewa ba.

"To daga yanzu ba bacci ba ko mai kika ga ina yi indai zaki yi wanka ki tashe ni muyi tare","to insha Allahu zan yi yadda kace Yaya" A dai-dai kumatunta ya sumbaceta tare da k'ara rumgumeta.

Hajiya Asiya kuwa ta ji duk abin da suka ce, cike da b'acin rai ta ce "dabba kawai abin da ka iya kenan shashasha kawai wanda bai san meyake ba, kuma wallahi ba ka isa ba" Nufarsu tayi gadan-gadan ta d'auki wannan kwanon dankali ta bugashi a k'asa ya tarwatse gaba d'aya a k'asa, cikin zafin nama Alhaji Mansur ya tashi da niyyar yayi mata dukan tsiya.

Aunty Murja ta rik'oshi tana murmushi "dan Allah ka barta bai kamata daga tashinka ka fara da b'acin rai ba, kasan ba na son ranka ya dinga b'aci dan Allah ka kyaleta kaji Yaya" Wani irin mari Hajiya Asiya ta zabgawa Aunty Murja wanda sai da ta ji shi har tsakiyar kanta ai kuwa kafin ta sauke hannunta daga fuskar Aunty Murja ita ma ta ji saukar na ta marin a fuskarta wanda ya gigitata har sai da ta saki ihu, haka Alhaji Mansur ya finciketa har sai da suka isa bakin kofar ya hankad'ata ya mayar da kofar ya saka key.

Dawowa yayi gurin Aunty Murja tare da dafe gurin da Hajiya Asiya ta mareta sumbatarta yayi a gurin sannan ya rumgume abarsa tare da zama a kan gadon, a kan k'irjinsa ta kwantar da kan ta tare da fashewa da kuka, hankalin Alhaji Mansur yayi matuk'ar tashi ya rasa inda zai tsoma ransa ya ji dad'i d'agota yayi idanuwansa sun kad'a sun yi jajahur "Haba Murjanatu dan Allah ki taimake ni ki yi shuru ki dena kukan nan kin san ina sonki sosai ba na son ganin zubar hawayenki" Goge mata hawayen ya shiga yi amman wasu na k'ara zubowa cikin muryar kuka Aunty Murja take cewa "ni Yaya ba wai marin da tayi min ne yasani kuka ba, irin abin da ta ce maka ne yasani kuka" Murmushi yayi tare da cewa "to ki daina kukan nan ya isa haka,ai idan ita ta fad'a min maganganu da ba su dace ba, ke na san zaki faranta min rai ki sa na manta da abin da ta ce min".
Chapter 29 · 0% Book details