← Book details Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 54

Sashe 6

Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin kuka Inna ta fara yi tana cewa "na shiga uku ni Indo ya ubangiji meyasa ka jarabceni da yarinyar da bata ganin mutuncinmu ni da mahaifinta", cikin muryar rarrashi Malam ya shiga bata hak'uri, har ya samu tayi shuru, Malam Kalla da Indo aure gida aka yi musu kasancewar iyayensu sun yaya da k'anine, tun daga ranar da ya aureta yake nuna mata soyayya har kawo yau da suka haifi 'ya'ya hud'u dashi kuma duka mata Asiya ce babba sai mai bi mata Hauwa,Hafsa, Hajara sai kuma k'aramarsu Na'ima, sam Malam Kalla baya k'aunar ganin bacin ran matar tashi ko kuma ganinta cikin damuwa shiyasa sam yake jin zafin 'yar tasu Asiya saboda kusan kullum sai ta saka Indo hawaye.

'bangaren Asiya kuwa tana fita kai tsaye bakin titi ta nufa ta tari mai adaidaita tayi masa kwatancen inda zai kai ta, a wani k'aton super market ya sauketa daman ta akwai ragowar kud'in da ta d'auka a jakar Inna naira 200 ta bashi ta nufi super market d'in, tana zuwa bakin kofar shiga super market d'in masu gadi suka hanata shiga, anan take ta k'ara jin haushin Mahaifiyarta da bata tsaya ta auri mai kud'i ba ta auri wannan matsiyacin Malamin, ta san yanzu da sun ganta da kaya mai tsada basu isa sun hanata shiga ba,amman kuma da ta tuna gurin wanda tazo kuma zata aura anan ba da dad'ewa ba, sai ta ji wani farin ciki ya lullub'eta, "Hmm da kun san wanda zan aura ba zaku tsayar dani,ku hanani shiga ba", d'aya daga cikin masu gadin ya ce "to mu ina ruwanmu da wanda zaki aura" Asiya ta bud'e baki zata yi magana kenan ta hango Alhaji Mansur ya nufo kofar fita daga super market d'in, cikin farin ciki da jin dad'in ganinshi ta shiga gyara mayafin dake jikinta, Alhaji Mansur yana fitowa idanuwansa suka sauka a kan masoyiyar tasa a nan take wani farin ciki ya lullub'esa "Asiya!" ya kirawo sunanta cikin wata iriyar murya,wacce take d'auke da wani irin salo, "Na'am Alhaji" tayi maganar cikin yauk'i da yanga, "Me kika zo yi anan" murmushi tayi tare da cewa "Bakomai" tayi maganar a takaice, "To shikenan muje in kai ki gida ko?" yayi maganar tare da yin gaba, ta bisa a baya kamar wata gela (ni kuwa 'yar mutanan zazzau naje Asiya ko kunya baki ji ba🤔).

Bud'e mata gurin mai zaman banza yayi ta shiga da sauri sanyi A.C ya daki fuskarta ta lumshe ido, "Arzik'i dutse takashi ake ni dai kam na taka nawa" tayi maganar a cikin zuciyarta, Alhaji Mansur ya zagaya ya bud'e wajen driver ya shiga ya ja motar ya nufi gidansu Asiyan, sun d'an yi nisa sosai babu wanda ya kuma yin magana daga cikinsu, har sun kusan isa gidan Alhaji Mansur ya ce "Sarauniyar mata da fatan kin ji sakona gurin Malam" ta ce "Eh Alhaji na ji" tayi maganar tare da sunkuyar da kanta "to kin amince" wani kayatatcen murmushi tayi a zuciyarta ta ce "Anzo gurin, banda abin ka Alhaji wacce macen ce mai kud'i irin ka zai ce yana sonta ta k'i amincewa" a fili kuma ta gyad'a kai alamar "Eh". Alhaji Mansur ya ji dad'in amsar da ta bashi, suna isa gidan sun d'an dad'e suna hira sannan sukai sallama ta fito ta shige gidan cike da farin ciki fal zuciyarta.

Tun daga ranar soyayya mai k'arfi ta shiga tsakanin Alhaji Mansur da Asiya, ko sati uku basu yi da fara soyayya ba ya turo iyayensa aka saka ranar aurensu, wulak'anci da rashin mutunci Asiya ta shiga yiwa 'yan uwanta da iyayenta, domin kuwa har cewa take idan ta auri Alhaji Mansur suka sake, sukace zasu zo gurinta wallahi sai ta saka anyi musu korar k'are, shiyasa sam basa shshshige mata suka barta take hada-hadar bikinta ita kad'ai kuma kowaccensu tayi alk'awarin ko talauci zai kashesu ba zasu je gurinta da niyyar taimako ba ko ziyara.

Ana saura kwana uku d'aurin aure Asiya ta tattara kayanta wad'anda Alhaji Mansur ya bata kud'ad'e ta siyo su ta saka su a d'an k'aramin akwati ta fito kallonsu take yi d'add'e a wulak'ance tare da cewa "to sai anjimanku sai mun had'u a darussalam" ta fad'a tare da fita daga gidan Hajara cike da mamaki da tashin hankali ta ce "Innarmu wai Aunty Asiya yau ne bikin nata" cike da bak'in ciki Inna ta ce "Oho ita ta sani ai duniya ce ta isa kowa riga da wando wanda bai zo bama jiransa take" ina tak'arasa maganar tare da fashewa da kuka gaba d'ayansu sukai kanta suna rarrashinta da kalamai masu dad'i tabbas ta ji dad'i da ya kasance tana da wasu yaran dan da Asiya ce kad'ai 'yarta da bak'in ciki ya kasheta,Asiya kuwa tana fita gidan k'awarta Azima ta nufa daman har an ware mata d'akinta da zata zauna a ciki, Azima k'awar Asiya ce, ta gudo daga garinsu saboda auren dolen da iyayenta zasu yi mata tazo ta kama gida anan garin kano take zaune Alhazawa suna zuwa su d'auketa a tafi hutun yawon shak'atawada ita, wannan shine takaitatcen tarihin Azima k'awar Asiya, Anan gidan Asiya ta zauna har ranar d'aurin aure Azima ta gayyato k'awayenta 'yan bariki sukai ta shek'e ayarsu, har lokacin kai Amarya ya yi Alhaji Mansur ya turo motoci gidansu Asiya amman aka ce musu ba anan take ba, a kasa rakasu har gidan A ka fito da Amarya aka nufi makeken gidanta, suna zuwa suka kai ta har kan gadonta, sukai mata sallama domin suna da fita club yau akwai casun da za'ayi, suka tafi, Asiya ta yaye mayafin da aka lillib'eta ta shiga zata gidan lungu da sako tana dad'a godewa Allah, da ya mallaka mata Alhaji Mansur a matsayin mijinta, A babban falo ta ci karo da Alhaji Mansur murmushi suka sakarwa juna sannan Asiya ta koma d'akin da sauri shima ya rufa mata baya, daga nan suka shiga cin amarcin su har na tsawon kwana bakwai Alhaji Mansur yayi musu visa zuwa dubai, murna a gurin Asiya ba'a magana ta rasa inda zata tsoma ranta dan dad'i wai yau ita ake cewa zata je dubai,muryar Alhaji Mansur taji yana cewa "To gobe sai mu je ki yiwa su Malam da Mamata sallama tunda jibi zamu tafi" anan take Asiya ta b'ata rai ba tare da ta ce komai ba, domin kuwa tunda ta samu ta rabu da wad'annan iyayennata bata k'aunar sake ganinsu har abada, kuma uwar mijin nata ma bakyata tayi ba, domin akwai ranar da ta kira a waya ta ce ta bata su gaisa ta ce kunnanta ne yake ciwo ba zata iya amsa kira ba.

Washe gari kuwa da duku-duku ta fara k'irk'irar rashin lafiyar k'arya domin karta je gurin iyayenta da kuma iyayen mijin nata,Alhaji Mansur hankalinsa yayi matuk'ar tashi jin matar tasa bata da lafiya, bayan ya bata abincin ya bata magani yaje shi kad'ai yayi musu sallama tare da basu uzurin Asiyan bata da lafiya ne shiyasa bata zo ba, shi dai Malam Kalla yana fad'a masa yasan k'arya take kawai bata son zuwa ne, washe gari da sassafe jirginsu ya d'aga zuwa dubai, watan su d'aya a dubai Asiya ta samu ciki zo kaga murna gurin masoyan biyu tamkar zasu had'iye junansu, haka sukai ta rainon cikin har ya kai watansa na haihuwa, a ranar wata labara ta haifi kyakkyawan d'anta mai kama da mahaifinsa, ranar suna a kasa saka masa suna Jabir a ranar da akai sunan da daddare Mahaifiyar Alhaji mansur ta kira a waya tayi ta masa fad'a a kan cewa yaje chan wata k'asa har matarsa ta haihu amman ba zan dawo a yi sunan a kano ba, hak'uri yayi ta bata ita kuwa Asiya tab'e baki tayi tare da jan ga gejeren tsaki, da yake suna da d'an tazara tsakaninsu Alhaji Mansur bai ji tsakin ba, haka ya katse wayar rayuwarsu ta cigaba da tafiya cikin farin ciki da walwala, Jabir ya taso cikin sangarci da gata daman ta yaya za'ai mara tarbiyya ace zata bawa wani tarbiyya dan haka Jabir ya debo gaba d'aya halayyar mahaifiyarsa a lokacin da Jabir yake shekara bakwai Asiya ta kuma samun ciki, suka dawo kano domin kuwa wannan cikin cewa Alhaji Mansur yayi a garin kano zata haifeshi kuma Jabir ya je ya ga kakanninsa domin ya sansu haka dai suka tahi ba dan ran Hajiya Asiya yaso ba, suna isa suka tarar har an gyara gidan haka aka zo ana tayi musu sannu da zuwa amman Asiya da ta gaji daga baya komawa tayi d'akinta ta kulle da mukulli, haka suka cigaba da rainon cikin har ya kai lokacin haihuwa ranar wata alhamis ta haifi d'anta namiji tun a asibitin jama'a sukai ta zuwa barka har aka sallamesu suka dawo gida, mutane suka cika gidan ai kuwa Hajiya Asiya ta d'aure fuska saboda ita sam bata son wani talaka ya rab'eta amman kuma taga a cikin dangin mijin nata har da talakawa, haka dai babu yadda ta iya kullum cikin zuwa barka ake a gidan har ranar suna yaro ya ci suna Aliyu, anyi shagalin suna sosai anci ansha sai wajen magriba kowa ya watse aka bar Hajiya Asiya daga ita sai yaranta sai kuma mijinta, haka suka cigaba da nunawa junansu da yaransu kulawa da soyayya Aliyu yana da shekara hud'u ta sami wani cikin amman wannan yayi matuk'ar bata wahala sosai dan haka Aliyu da Jabir aka kai su gurin Kakarsu ta wajen uba, ta rik'esu har sai da Asiya ta haifi yaranta 'yan biyu duk mata aka sakawa d'aya sunan mahaifiyar Alhaji Mansur Nafisa d'aya kuma sunan mahaifiyarta Aisha, Nafisa suke ce mata Nihal, Aisha kuma Shahida ranar da Asiya tayi arba'in aka kai mata su Jabir saboda irin matsawar da tayi a dawo mata da yaranta, suka cigaba da rayuwa cikin farin ciki da kwanciyar hankali.
Chapter 6 · 0% Book details