← Book details Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 54

Sashe 18

Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amatullahi ce ta fito daga d'akinta sanye da hijabi har k'asa kasancewar yau lahadi ne babu makaranta ta nufi hanyar fita Lado da ke zaune a tsakar gida shi kad'ai yana jiran fitowarta ya nufeta da sauri yana murmushi ya sha gabanta "K'anwata tun d'azu nake ta jiran ki fito, saboda akwai magana mai muhimmancin da nake so muyi da ke", "Lallai Lado anzo dai-dai gab'ar da nake so azo" ta yi maganar a zuciyarta a fili kuma ta d'an nuna alamun mamakia fuskarta kafin ta ce "Lado yau kuma da me ka zo?" Murmushi Lado yayi sannan ya ce "K'anwata babu da abin da nazo dashi sai alkhairi, domin a gaskiya ba zan iya b'oye miki ba tun ranar da kika gama secondary school d'inki naji soyayyarki ta shiga zuciyata amman ina tsoron in fitar miki dan karki k'i amincewa Amatullahi ina sonki sosai" Amatullahk tayi wani gajeren murmushi sannan ta ce "kana tunanin zan yarda da cewa kana sona? Bayan irin abubuwan da kake min hmmm Lado kenan" Lado ji yayi kamar ya kwad'a mata mari amman sai ya tuno indai yayi hakan shirinsu zai rushe dan haka sai ya da ke tare da cewa "Haba sweety da gaske nake yi ina sonki, idan kuma kina tunanin k'arya nake yi zan je in fad'awa Inna sai ta fad'awa Abba, ina ga hakan ne zai tabbatar miki da cewa da gaske na ke yi" Amatullahi ta ce "A'a ba sai ka yi hakan ba, zan je gidansu Khadijatullahi idan na dawo zamu yi magana" Lado ya ce "To shikenan, bari in taka miki" haka suka jera suna tafiya har sai da suka kusan zuwa gidansu Khadijatullahi sannan Lado ya koma gida zuciyarsa fal da farin ciki burinsu zai cika shi da Inna Larai, Amatullahi kuwa juyawa tayi tana kallon Lado tayi wata iriyar malalaciyar dariya sannan ta ce "Lado kenan ka ri ga ka fad'a tarkon Amatullahi, daga kai har uwar taka dai-dai nake da ku, d'an iska har da wani cewa sweety" ta ja wani tsaki tare da shiga gidansu Khadijatullahi, da sallama ta shiga d'akin "Assalamu alaikum" Hafsa da Khadijatullahi ta gani zaune a kan yaloluwar taburmar d'akin suka amsa mata sallamar a tare "Wa'alaikissalam" guri ta samu kusa da Khadijatullahi ta zauna tana tambayarsu "Ina Aunty Murja" Khadijatullahi ta ce "taje gidan Hajiya Mama" Amatullahi ta ce "Allah sarki Aunty Murjarmu tana kok'ari sosai wallahi" Hafsa ta ce "Wallahi kuwa sosai ma" Amatullahi ta ce "Besty ke kuma yaushe kika zo, ko kin yi tunanin yau akwai school" Hafsa ta ce "A'a wallahi besty kawai dai ba zan iya jira har sai gobe mu had'u ba shiyasa na zo" Murmushi Amatullahi tayi ta ce "Allah sarki besty mun ji dad'i kuwa" Khadijatullahi ta kallesu tana cewa "Ban baku labari ba jiya sai ga wannan d'an barikin Jabir ya zo gidan nan" Amatullahi ta wani daki bango tare da zaginsa sannan ta ce "uban me ya kawo shi gidan nan kuma shege dan gidan tambad'add'iya" Khadijatullahi ta kwashe duk yadda suka yi ta fad'a musu, Amatullahi ta ce "ai kuwa aniyarsa ta bi sa shege ai na gaba yayi gaba, wallahi da ace ban tafi ba had'u dashi sai na saka wallahi anyi mishi dukan tsiya na saka yara suyi ta jifanshi, nima ina nan muna shirya wata babbar drama a gidanmu" Hafsa ta ce "Wace iriyar drama kuma?" Nan Amatullahi ta kwashe duk komai ta fad'a musu bata b'oye komai ba ta d'ora da cewa "Sun yi tunanin zan iya fad'awa tarkonsu ne, ai yanzu wasan ya fara" Khadijatullahi da Hafsa ban da dariya babu abin da suke yi "Kai besty wallahi ke 'yar drama ce wato tsiyar da kika tafkawa Inna Larai shiyasa ranar kika ce wai na ganta amman ban gane ita ba ce" Khadijatullahi tayi maganar tana cigaba da dariya, Hafsa ta ce "Allah ya shiryeki besty kina zuba kamshi fa" Amatullahi ta ce "Wallahi ku tsaya ku ga yadda za'a buga wannan babban game d'in" Hafsa ta ce "besty muna biye da ke wallahi" Amatullahi ta ce "ya labarin yaya safwan kuwa?" Hafsa ta tab'a baki sannan ta ce "bai zo ba ya bar min yaronsa yau kuma da sassafe ya aiko masa da kayansa a akwati" Dariya suka saka sannan a tare suka ce "Mommy Hafsa" harararsu tayi sannan ta chanza hirar zuwa ta makaranta, sai wajen k'arfe 2pm na rana driver Hafsa ya zo ya d'auketa suka tafi gida, ko minti biyar Hafsa bata yi da tafiya ba sai ga Aunty Murja ta dawo suka yi mata sannu da zuwa ta zauna ta ajiye kwanon silban a k'asa sannan ta bud'e shi jollof d'in taliya ce da macaroni ga nama da yawa haka suka had'u suka cinye abinci, hira suka zauna suna yi abin gwanin ban sha'awa.

*'BANGAREN JABIR ANGO DA AMARYARSA TEEMARH*

Jabir kwata-kwata duk yadda yake tunanin Teemarh ta huce hakan domin gaba d'aya ta chanza masa, sam yanzu bata nuna masa soyayya kalaman soyayyar da take yi masa da yanzu bata yi idan ya shigo d'akin sai dai ta bi sa da wata muguwar harara kuma abin da yake bawa Jabir haushi shine Teemarh ta daina barin sa ya kwanta a kan gado sai dai a kan kujera ya ke kwana abinci kuwa idan an raba an basu bata ajiye masa sai dai ta ci iya cinta sauran ta kaiwa mai gadi, tana zaune a kan gado ta mik'e k'afa Jabir ya banko kofa ya shigo yana ta faman huci, Teemarh tayi masa wani wulak'antatcen kallo tare da cewa "Kai meye haka zaka shigo min d'aki kana wani huci kamar tsohon mahaukaci" Jabir ya gama fusata gaba d'aya jikinsa rawa yake yi ya ce.

"Teemarh sai yau na tabbatar baki da mutunci, ashe ana baki abincina shine kike kai wa su wad'anchan matsiyatan, to wallahi baki isa ba tunda ba ubanki ne yake siyo abincin ba, shashasha 'yar gidan matsiyata" Jabir yayi magana yana cigaba da huci, Teemarh ta ce "To ai kai ne babban matsiyacin dan kuwa sun fika komai da komai wallahi, kuma da kake cewa ba mahaifina ne ya siya ba, na ji daman nace Abbana ne ya siya kuma haka nayi niyya su nake son na bawa abincin dan haka banga wanda ya isa ya hanani bawa su baba mai gadi abinci ba, kuma da kake ce min shashasha 'yar gidan matsiyata to sannu mai kud'i dan gidan k'aruna", Teemarh ta k'arasa maganar tana harararsa, Jabir ya gama fusata ya gama kaiwa k'arshe cikin zafin nama ya jayota yayi wurgi da ita kan kujera har sai da ta bugu da hannun kujerar goshinta ya fara zubar da jini, Jabir ya nufi kanta gadan-gadan Teemarh tayi saurin tashi tana nuna shi da yatsa "Jabir wallahi zaka san ni ka wurga kan kujera kuma...." bata k'arasa yin magana ba taji ya zabga mata mari har sau biyu hagu da dama ita ma kuwa tana d'agowa ta rama marin sai da ta jera masa sau hud'u sannan ta nufi hanyar fita da gudu tana kuka domin kuwa yau sai tayi wa Jabir sharrin da bazai tab'a mantawa da ita ba.

A babban falo ta tarar da mutanan gidan gaba d'aya ta je gaban Abba ta zub'e tana k'ara saka sabon kukan, Abba ya kalleta ya ce "Fatima meya faru" cikin kuka ta ce "Abba na shiga uku Jabir zai kashe ni, wai kawai yana shigowa d'akin ya fara dukana ya gwara min kai na a bango" Jabir da ke tsaye yana jin duk abin da ta fad'a dan Teemarh tana fitowa shima ya biyo bayanta "Wallahi Abba k'arya take yi wai fa dan......"wani irin mari Abba ya d'aukeshi dashi yana fad'ar "Ok k'arya take yi wannan jinin da yake zuba daga goshinta fa, shima k'aryar ne ko kana nufin ita da kanta zata jiwa kanta ciwo" ya rasa abin cewa domin kuwa Teemarh tayi amfani da wannan ciwon wajen yi masa sharri, haka ya juya jikinsa a sanyaye ya nufi d'akinsa, Abba ya kalli inda Teemarh take durkushe ya ce "ki yi hak'uri kin ji Fateema, Aliyu kira doctor ya zo ya dubata" Aliyu ya Amsa da "to" haka ko minti d'aya Aliyu bai yi da kiran doctor d'in ba sai gashi yayi sallama ya shigo da yake a unguwar yake, bandegi ya saka ya had'e mata goshin sannan ya rubuta musu magungunan da zata dinga sha, yayi musu sallama ya koma gidan shi, Teemarh ta ce "Nagode Abba Allah ya saka da Alkhairi" Abba ya ce "Amin ya Allah" haka ta tashi ta bi bayan Jabir zaune ta tarar dashi a kan kujera ya zabga tagumi, Teemarh ta shek'e da wata iriyar mahaukaciyar dariya tare da tafa hannu tana cewa "Jabir kenan ai yanzu wasan ya fara tagumi yanzu ka fara yin shi, ai wallahi sai ka gane kurinka, banza kawai" Jabir yayi murmushi tare da cewa "Teemarh kenan nii Jabir d'an tuwa kika yi wa wannan abin ko? To wallahi zan nuna miki cewa nii babban d'an iska ne, karki ga wai ina tagumi kiyi tunanin wai tsoron ki nake ji, to wallahi ba'ayi macen da zan ji tsoronta ko kuma ta takura min ba, Teemarh ki rubuta ki ajiye Jabir yana nan sai ya rugu rayuwarki gaba d'aya" Teemarh ta zauna a kan kujera tana murmushi tare da cewa "Me kake cewa maimaita inyi hadda" tsaki ya ja ya fita daga d'akin kai tsaye gurin da aka tanada dan ajiye motoci ya nufa ya ja motar da gudu har yana kok'arin kwarfe mai gadin da motar Allah ya taimaka ya kauce masa (ni kuwa 'yar mutanan zazzau nace wai Jabir an had'u da k'arfen k'afa ko nace gaba da gabanta Aljani ya taka wuta😂).

~*BAYAN WATA DAYA*~
Chapter 18 · 0% Book details