← Book details Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 54

Sashe 3

Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da saurinsa ya fito daga motar ya nufi hanyar da zata sadashi da tafkeken falon, yana shiga ya tarar su Mami da k'annansa guda biyu dukansu mata ne Shahida da Nihal, wad'anda baza su huce shakara sha bakwai ba, da gudu Nihal ta k'arasa gurinshi tana fad'ar "Yawwa bro daman kai muke ta jira yanzun nan Mami take kok'arin kiranka" murmushi yayi tare da rumgume k'anwar tasa "to darling sister ai gani nazo kawai mu juya muje mu d'aukoshi k'ar jirgin nasu ya sauka, bamu k'arasa ba" Mami tayi murmushi tare da cewa "Ai yau dai kam naga ana kok'arin mantawa dani, dukkanku kuna d'aukin ganin d'an uwanku" da sauri Jabir ya saki Nihal yaje ya rumgume Mamin "haba Maminmu taya zamu manta dake you are so speacial to us" haka su Nihal da Shahida ma duk suka rumgumeta, Murmushi take ta faman sakarwa 'ya'yannata, "Thanks you so much my darlings ina 'kaunarku sosai, yanzu dai muyi sauri mu k'arasa Airport kar Aliyu su sauka bamu k'arasa ba, tunda ya ce 7:00am zasu sauka, yanzu kuma 6:30am daga nan suka dunguma zuwa Airport mota d'aya kawai suka d'auka, k'arfe 7:00am suka isa filin jirgi dai-dai lokacin jirgin su Aliyu yana sauka, haka ya fito cikin takunsa na isa da k'asaita sai zuba kamshi yake yi, kaii masha Allah kyau iya kyau Aliyu yayi domin duk irin kyan Jabir, idan kaga Aliyu zaka san gaskiya Jabir ma mummuna ne, domin kuwa ya ninka Jabir a kyau sosai idan ka ganshi za ka yi tunanin wani balaraben ne, Nihal da Shahida suna ganinsa suka tafi da gudu suka rumgumeshi "We really miss you darling brother" Wani kayatatcen murmushinsa mai tsada ya sakar musu, cikin muryarsa wacce kamar wanda yake yin rad'a ya ce "Me too i really miss you" ana dai suka k'arasa gurin Mami ya rumgume ta tare da sumbatarta a kuncinta, "Mum i miss you so much", "me too i miss you my son" Jabir wanda yake tsaye ya hard'e hannunsa a kan k'irjinsa ya ce "Lallai yau ina ganin san kai" sai a sannan Aliyu ya lura ashe har da Jabir a kazo "Wayyo Allah na, Bro Jabir ashe har da kai aka zo" ya fad'a yana k'arasawa kusa dashi da niyyar ya rumgumeshi, Jabir yayi saurin ja da baya tare da hararar Aliyun "A'a banda ni aka zo saboda tsabar rainin hankali ma baka ganni ba, ni na kasa bacci ina ta son gari ya waye nazo na ganka shine zakai min izza" yayi maganar cikin jin haushin Aliyun "sorry brother kayi min afwa nayi laifi kasan fa kaii d'in jini na ne" Murmushi suka yi gaba d'aya tare da rumgume junansu daga nan suka shiga mota, domin tafiya gida.

Suna zuwa Aliyu ya tarar da jerin abinci kala-kala a kan dining table, ai kuwa daman ya kwaso yanzu ya zauna, ya d'ebi fried rice wacce taji naman kaji ya shiga ci, suma duk suka zauna suna cin abincin suna yin hirarsu abin ban sha'awa.

*BAYAN WATA BIYU*

Amatullahi ce zaune a gaban Aunty Murja cikin nutsuwa Amatullah take magana "Aunty Murja daman nazo ne na nuna miki admission d'inmu na makarantar da muka samu" ta mik'a mata admission letter cikin nuna tsantsar farin cikinta mara misaltuwa Aunty Murja ta fara magana "Kai Alhamdulillahi masha Allah, Allah ubangiji ya tsareku ya baku sa'ar abin da zaku je nema" cikin jin dad'i Amatullahi ta amsa da "Amin ya rabbil'alamin" Aunty Murja ta ce "Amman wace makarantar ce? Kuma ke dawa kuka samu?" Wani kayatatcen murmushi Amatullahi tayi ta ce "Anan makarantar poly ta gadon k'aya, kuma ni da Khadijatullahi ne" ciki nuna mamaki Aunty Murja ta ce "wace Khadijatulla d'in?", Amatullahi ta nuna Khadijatullahi wacce take kwance tana jin duk abin da suka cewa, amman bata tanka musu ba, sai a wannan karon da taji k'awar ta ta, tazo musu da abin ban mamaki, da kyar ta samu ta mik'e idanuwanta na kan Amatullahi domin so take ta tabbatar da gaske take yi ko kuma wasa take musu, sannan ta ce "Aunty Murja wannan Khadijatullah d'in nake nufi, nayi hakan ne kuma domin na fahimci ta hakane kawai zamu samu ta rage tunani da koke-koken da tayi kullum ba dare ba rana, idan muna zuwa makaranta zata dinga samun sauk'in damuwarta" cikin zubar da hawaye Aunty Murja ta fara magana "Ni ban ma san da wane irin baki zan yi miki godiya ba, a gaskiya ke k'awa ce ta gari samun irin ki a wannan zamanin sai an tona domin zai yi wahala sosai mun gode mun gode sosai", hannu Amatullahi ta saka tana sharewa Aunty Murjan hawaye "Haba Aunty Murja menene na kuka ni na d'auke ku ne, tamkar 'yan uwana, dan haka komai nayi muku ku daina gode min dan Allah" Khadijatullahi ce ta rarrafo kusa da k'awar ta ta dakyar sannan ta kama hannayenta duka biyun tana kuka "nagode miki sosai, tabbas nasan kina sona sosai nagode sosai kuma....." aman da ya taho mata ne yasa ta kasa k'arasa maganar ta juya da niyyar ta shiga band'aki amman ina juyawarta kenan ta fara shek'a amai Aunty Murja da Amatullahi suka rik'eta, sai da ta gama shek'a aman sannan suka wanke mata jikinta inda ta b'ata suka kai ta kan gado ta kwanta, Amatullahi ta dawo ta gyara gurin da Khadijatullahin tayi aman sannan ta dawo ta zauna tana tambayar Aunty Murja "Aunty Murja bata da lafiya ne" Girgiza kai Aunty Murja tayi da alamun damuwa a kan fuskarta ta ce "Wallahi Amatullahi ban sani ba, dan bata ce min bata da lafiya ba" anan Amatullahi ta ce "to Aunty Murja mu tashi muje asibiti" da sauri Aunty Murja ta kalleta ta ce "haba Amatullahi ina nake da kud'in kai ta asibiti", "karki damu ni zan bada kud'in a dubata" haka suka samu suka d'aga ta da kyar akai sa'a kuwa suna fita suka sami mai adaidaita suka shiga sai asibitin nasarawa dake nan cikin garin kano, suna zuwa aka shigar da Khadijatullahi emargency domin duba lafiyarta sun d'auki kusan minti 40 suna jiran a fito a sanar dasu halin da Khadijatullah d'in take ciki, jin alamar da suka yi ana kok'arin bud'e kofar emargency room d'in ne yasa sukai saurin zuwa bakin kofar, doctor Halima ce ta fito tana ganinsu ta shiga sakar musu murmushi tare da cewa "ina tsananin taya ku murna, 'yar uwarku tana d'auke da ciki har tsawon wata biyu, kuma tana nan lafiya kalau dan yanzu na barta zaune tana hutawa, a yanzu ma zaku iya tafiya gida dan laulayi ne yasa tashiga cikin........" k'arar da suka ji an kwala ne ya katse doctor Halima k'arasa maganar da zata yi, juyawa sukai Khadijatullahi ce ta fad'i ta suma domin taji abinda doctor Halima ta fad'a Hankalinsu a tashe sukai kanta suna kiran sunanta

"Khadijatullahi! Khadijatullahi!! Khadijatullahi"

Amman ina bata ko motsi, haka doctor Halima ta shiga kiran nurses, suka zo da sauri suka ciccib'eta suka maida ita Emargency, Aunty Murja da Amatullahi suka koma gefe suka zabga tagumi fuskokinsu d'auke da tashin hankali mara misatuwa.
Tun k'arfe hud'u da aka shigar da Khadijatullah Emargency room har k'arfe 8pm na dare, Babu Wanda ya fito daga Emargency d'in daga nurses d'in har doctor Halima,hakan yasa Aunty Murja da Amatullahi suka shiga cikin matsanancin tashin hankali suna tunanin kodai Khadijatullahi ta mutu ne.

A b'angaren doctor Halima kuwa tunda suka shiga da Khadijatullahi suka shiga kok'arin ceto rayuwarta da ta d'an dake cikinta, yanayin Khadijatullahi ya tsananta domin numfashinta sai kok'arin d'aukewa yake yi, ga bugun zuciyarta sai bugawa yake da k'arfi tamkar ganga ake bugawa, gashi sai wata irin jijjiga take yi, sai da nurses kusan biyar suka rirrik'eta,hankalin doctor Halima ya tashi domin har ta fitar da ran rayuwar baiwar Allah, Anan take ta fara zubar da hawaye domin taga tashin hankali k'arara a fuskokin 'yan uwannata da suka kawota, yanzu idan aka ce ta mutu, ta san zasu shiga cikin mugun yanayi, anan take wani tunani yazo mata da sauri ta fita ta kofar baya office d'inta ta shiga taje ta had'o allurai ta dawo Emargency room d'in tayi mata, cikin ikon ubanjigi tana mata ko minti biyar ba'ayi ba, ta samu bacci, wata iriyar nannauyar ajiyar zuciya doctor Halima tayi tare da cewa "Alhamdulillahi Allah na gode maka" fita tayi domin ta koma office d'inta amman wannan karan ta kofar gaba ta fita, ai kuwa su Aunty Murja na ganinta sukai wajenta tare da wurga mata tambayoyi "doctor ya Khadijatullahi? Kodai ta mutu ne? Dan Allah ki sanar damu idan ta mutu" kamar had'in baki tambayoyin nasu suka zo dai-dai, "ku biyo ni office" tayi maganar a takaice, tare da yin gaba suka rufa mata baya da sauri, suna shiga doctor Halima ta huce kujerarta ta zauna, su kuma suka zauna a kujerar da ake ganin likita, bayan doctor Halima tayi d'an rubuce-rubucenta sannan ta d'ago tana yi musu bayani "A gaskiya 'yar uwarku tana cikin halin damuwa da kuma tsantsar tashin hankali, wanda a binciken da nayi na gano cewa ta dad'e a cikin wannan yanayin, kuma uwa uba wannan k'arar da ta suma ya k'ara sakata a cikin razana wanda har zuciyarta tana kok'arin bugawa, amman yanzu Allah ya taimaka mun shawo kan matsalar ta ta, amman in har zata cigaba da saka abu a ranta wanda har zai sakata ta dinga shiga damuwa to zata iya kamuwa da babbar matsala a zuciyarta kuma babyn cikinta zai iya samun matsala shima".
Chapter 3 · 0% Book details