Sashe 33
Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun ranar da Talatu ta ji cewar Salis yana asibiti hankalinta a tashe yake amman tun da ta ji cewar wai saboda Mama ta je gidansu a kan ya saki Nihal shi ne ya fad'i aka kai shi asibiti ta ji wani irin kishi tare da jin haushin Salis d'in gaba d'aya tashin hankalin da take ciki gamai da rashin lafiyarsa ta nemeshi ta rasa, kuma ta shiga kulla sabon makirci domin kuwa ta rantse ba za ta barsu su k'ara kasancewa a matsayin ma'aurata ba kuma sai ta sakawa Salis d'in tsanar Nihal a cikin zuciyarsa, haka dai kullum cikin sak'a makirci take yi domin kuwa idanuwanta duk sun rufe hatta Salis ji take kamar ta kashe shi kowa ma ya huta.
*'BANGAREN NIHAL🥰*
Kamar yadda suka tsara ita da Khadijatullahi haka kuwa aka yi washe gari wajen k'arfe 4:00pm na yamma Nihal ta shirya cikin wata farar a atamfa da pupple sai shek'i take ta saka hijabinta har k'asa ta d'aura nik'af ta feshe jikinta da turarirrika kala kala masu kamshi sannan ta fito ta ce Hajiya Mama gida Mami zata je tunda ta dawo gida ba ta je ta ga Mamin ta ta ba, Hajiya Mama ta ce mata to sai ta dawo, saboda tasan idan ta fad'a mata gaskiyar in da zata je zata hanata zuwa, shiyasa ta ce mata hakan, ta fita kai tsaye asibitin da aka kwantar.
Doctor Sadiya ta kirawo a waya ta zo ta nuna mata d'akin da Salis d'in yake tayi mata godiya sannan ta shiga cikin d'akin da sallama a bakinta, da sauri Salis ya mik'e jin muryar babynsa domin kuwa ko da ace daga bacci ya tashi zai iya gane muryar Nihal, zama yayi yana sakin murmushi, tsugunwa tayi ta gaishe da Mama har k'asa, Mama ta amsa tana murmushi sannan Nihal ta ke tambayarta ya jikin Mama ta ce da sauk'i, "Allah ya k'ara sauk'i" Nihal ta fad'a tare da zama kusa da Mama wacce take zaune a kan k'atuwar taburma "Amin" Maganar Mama ta dawo da Nihal daga kallon Salis d'in da ta shagala tana yi.
Babu damar ta matsa kusa dashi, amman haka ma ta ji matuk'ar dad'i da ya kasance gata nan tana kallon babynta, mintuna ashirin Nihal tayi sannan ta tashi ta yi wa Mama sallama ta nufi gurin doctor Sadiya, Nihal tana fita Mama ta kalli Salis tana cewa "wannan yarinyar tana da hankali gashi ban san wacece ba","nima kam ban san ta ba Mama" Salis ya fad'a tare da komawa ya kwanta yana jin babu dad'i a zuciyarsa, saboda bai samu ya keb'e da babynsa ba.
Nihal kuwa tana zuwa gurin doctor Sadiya ta ba ta wata takarda ta ce ta ba wa Salis d'in sannan ta yi mata godiya ta nufi gida zuciyarta fal da farin ciki.
*Bayan wata d'aya*
Cikin Khadijatullahi ya kai lokacin haihuwa ko yau ko gobe Hajiya Mama ta dena barinta ta fita ko ina Allah ya taimaka lokacin an bada hutun makaranta na first semister wato hutun farkon zango, kullum tana jikin Hajiya Mama, Aliyu kuwa a b'angarensa kullum sai ya zo gidan Hajiya Mama yanzu kuwa da ya ga cikin Khadijatullahi ya kai lokacin haihuwarsa ya tattaro kayansa ya dawo gidan Hajiya Mama domin kuwa a cewarsa Khadijatullahi tana buk'atar kulawarsa shima ba iya kulawar da su Hajiya Mama suke ba ta ba, wani irin tausayinta yake ji kuma bai san meyasa ba duk sanda ya kalli Khadijatullahi sai ya ji wani abu a cikin zuciyarsa.
*BANGAREN GIDAN HAJIYA MAMA🌸*
A yau ranar talata tun da asuba Khadijatullah ta fara jin wani irin sauyi a tare da ita, Amman ta daure ba tare da ta fad'awa kowa ba, gashi Hajiya Mama ta su Nihal sun fita gidan Kawu Bala matarsa ta haihu kuma baya garin, gidan ya rage daga ita sai Amatullahi sai Kuma Aliyu dan shi kam k'in bin su yayi domin kuwa yana tsoron ya fita kuma Khadijatullah ta tashi nak'uda baya kusa da ita.
Wajen k'arfe 8:00am na safe Khadijatullah ta fito daga d'akin ta d'auki buta dan tana son ta kama ruwa, toilet ta nufa tana tafiya a hankali tana yi tana cije Baki a dai-dai kofar shiga toilet d'in ta saki buta tare da kwalla k'ara, a firgice Aliyu ya fito daga d'akinsa ya k'arasa kusa da ita tare da tambayarta "menene?","cikina ka taimaka min" Amatullahi ce ta fito daga d'aki da gudu har tana zabga tuntub'e kama Khadijatullah tayi tana cewa "besty haihuwar ce?" Aliyu ya ce "Amatullahi d'auko Mata hijabi ko mayafi mu tafi asibiti" Yana gama fad'ar haka ya shige d'akinsa ya d'auko mukullin mota Daman sanye yake da jallabiya fara ce sol kallo d'aya zakai mata kasan tsadaddiya ce sosai Yana fitowa ya tarar da Amatullahi har ta d'auko Mata mayafin, Amatullahi ba za ta iya kamata ba, dan haka Aliyu ya rumgumota suka fita har wajen da motarsa take, a bayan mota ya sakata sannan ya shiga mazaunin driver Amatullahi ta shiga bayan sannan ta rufe kofar motar Aliyu ya ja motar da k'arfi sai Asibitin Abbansu *MANSUR SPECIAL HOSPITAL*.
Amatullah ta dinga raya abubuwa da yawa a ranta tana ji dama ace Aliyu shine mijin bestynta domin kuwa ta Yaba da hankalinsa shi Sam bashi da hali irin na wannan shashashan d'an uwana sa Wanda bai San ciwon kansa ba.
Suna isa Asibitin sai ga wasu nurses da gadon d'aukar mara sa lafiya dan tun a hanya Aliyu ya kira waya a kan suna nan zuwa Asibitin, tare da nurses d'in aka fito da Khadijatullah wacce duk ta gama fita daga hayyacinta, haka aka dorata a kan gadon suka nufi Labour room da Khadijatullah, Aliyu ya so ya shiga Amman babu dama saboda shi ba likita ba ne, shi soja ne Jabir kuma engineer.
Haka sukai ta yawo a filin gurin Amatullahi kuka take tana fad'in "Dan Allah besty karki mutu Ina sonki sosai" Zama tayi a kan wata kujera tana cigaba da kukanta, Aliyu ma ji yake kamar yayi kukan Amman wannan lokacin ba lokacin kuka ba ne, dan haka ya shiga yi mata addu'ar Allah ya sauketa lafiya.
Sun d'auki kusan awa d'aya a haka Babu wani likita da ya fito, hankalinsu ya tashi, ji sukai tana kok'arin bud'e kofar labour room d'in da sauri suka nufi gurin kofar wata nurse ce ta fito rik'e da jariri a hannunta fuskarta d'auke da murmushi, "nurse ya jikin dija"Aliyu ya tambayeta a gaggauce "ta haihu lafiya an samu d'a namiji ga yaron ma" Ta yi maganar tare da mik'a Masa yaron k'arb'ar yaron yayi tare da k'ura Masa ido kamarsu d'aya sak da Jabir kamar an tsaga kara.
Amatullahi kuwa cikin farin ciki mara iyaka ta ce "Alhamdulillah, nurse yanzu zamu iya ganinta?","Eh zaku iya" Nurse d'in tayi maganar tana kok'arin barin gurin Aliyu ya kirata ta dawo aljihunsa ya saka hannu ya d'auko kud'i naira dubu hamsin ya Bata, tayi Masa godiya sannan ta koma gurin aikinta.
Shiga d'akin suka yi Khadijatullah suka tarar ita kad'ai tana kwance a kan gadon d'akin tana hawaye kwata-kwata bata k'aunar yaron, tun da ta samu ta haifeshi ta ji zuciyarta tayi mata haske domin kuwa ta rabu da k'aya.
Zama suka yi a kan kujerun dake d'akin na roba sai a lokacin Aliyu ya tuna su Hajiya Mama ba su san Khadijatullah ta haihu ba, wayarsa ya d'auko a aljihunsa sannan ya shiga kiran layin Nihal tana d'agawa yake fad'a mata Khadijatullah ta haihu, ihun murna tare da godewa Allah ta shiga yi sannan ta kashe wayar ta fad'awa su Hajiya Mama ai kuwa babu shiri suka fito daga gidan Kawu Bala suka nufi Asibitin a hanya Shahida ta kirawo Aunty Murja take fad'a Mata da yake Abba yana gida dan haka suka shirya suka nufi asibitin, a harabar Asibitin suka tarar da adaidatan da ya d'auko su Hajiya Mama suka k'arasa gurin da suke bayan sunyi parking d'in motarta su suka tsugunnawa har k'asa Abba da Aunty Murja suka yi suna kwasar gaisuwa gurin Hajiya Mama, ta amsa musu cikin sakin fuska sannan suka nufi d'akin da Khadijatullah take duk inda suka huce sai ma'aikatan gurin da likitoci sun tsugunna suna ta kwasar gaisuwa suna shiga Amatullahi ta nufi gurin da Shahida da Nihal suke ta ce "kun kira besty kuwa?","A'a yanzu zan kirata" Shahida tayi maganar tare da d'auko wayarta Hafsa ta kira take fad'a mata Hafsa ta haihu,babu shiri ta fito ta Ado driver ya nufi da ita asibitin da yake asibitin ba wani boyayye ba ne, a cikin awa minti talatin asibitin ya cika damkam da jama'a Jabir,Teemarh da mahaifiyarsa Asiya kuwa ba su san abin da ke faruwa ba, kuma babu wanda yayi gangancin sanar dasu, domin a cewarsu ba yanzu ya kamata su san komai ba, akwai abin da Hajiya Mama da kuma Alhaji Mansur suke shiryawa wanda babu wanda suka sanar sun barshi a cikin zuciyarsu.
*'BANGAREN SAFWAN DA SAFNA*
Safna wata iriyar kulawa ta musamman take ba wa Safwan kullum tana manne dashi, ji take wannan karayar dama a k'afarta take ba a tasa ba, wani irin sonshi da k'aunarshi take ji suna k'ara ratsata domin kuwa Safwan kullum cikin kasheta yake da kalaman soyayya ita kuma sai k'ara narkuwa take a cikin kogin soyayyarta, yau ma kamar kullum tana zaune a kan kujera kusa dashi ta dora kanta a kan kafad'arsa idanuwanta a lumshe ta kama hannayensa duka biyun ta rike "Ruhina" Safwan ya kirata cikin wata iriyar murya mai rikita zuciya "Na'am Ruhina'' Safna ta amsa tana mai bud'e idanuwanta tare da d'ago kanta tana kallonsa ido cikin ido tana sakar masa wani irin murmushi.