← Book details Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 54

Sashe 37

Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To na ji Darling bakya sona kuma na san duk abin da kika yi min zuciyata ce ta jawo min tunda ta kasa dai na sonki" Yana gama fad'ar haka ya tashi ya futa daga d'akin, Teemarh ta bi bayansa da kallo sai kuma ta ji ba ta ji dad'in abin da tayi masa ba, zuciyarta ta k'arye ji take kamar ta bi sa ta ce masa ta hak'ura kuma tana sonshi amman kuma ta san Jabir farin sa ni ta ya ya zata yarda cewa ba yaudararta zai yi ba, kuma da gaske yana sonta, dole sai ta tabbatar da cewa yana sonta ba yaudararta zai yi ba sannan zata yarda dashi.

Da wannan tunanin ta tattara ta koma kan gado ba'a fi minti d'aya da kwanciyarta ba wani irin bacci mai nauyi yayi awan gaba da ita.

*'BANGAREN ABBA DA AUNTY MURJA*

Tunda ya fito daga d'akin Hajiya Asiya ya shiga d'akin Aunty Murja kwance ya tarar da ita tana karatun littafi tana ganinsa ta ajiye littafin ta tashi ta zauna tana kallonsa fuskarsa ta nuna mata cewa yana cikin damuwa dan haka ita ma lokaci d'aya ta shiga tsananin damuwa, zama yayi kusa da ita tare da zabga tagumi, hannu ta saka ta cire masa tagumin tare da girgiza masa kai alamar "A'a" sannan ta ce "Yaya hankalina ya tashi zuciyata ta shiga tsananin damuwa saboda, sarkin da yake mulkarta yana cikin damuwa, shin ya zan yi da raina".

Murmushi yayi sannan ya ce "to matata ki kwantar da hankalinki ina cikin koshin lafiya kawai dai lamarin Asiya ne yake ba ni tsoro kullum abin ta cigaba yake yi, kwata-kwata bata ba ni matsayina na mijinta" Ajiyar zuciya Aunty Murja tayi sannan ta ce "Addu'a ya kamata mu dinga yi mata, insha Allahu wata rana zata fahimci cewa kuskure take aikatawa kuma ina mai tabbatar maka da cewa zata gyara duk kuskurenta ka ji dan Allah karka saka wannan a ranka".

Wani irin farin ciki ne ya kamasa tabbas yana matuk'ar alfahari da Murjanatu domin kuwa duk sanda ta ganshi cikin damuwa hankalinta ba ya kwanciya har sai ta ganshi yana cikin farin ciki, "Allah yayi miki albarka matata","Amin mijina" Ta fad'a tare da sakar mata murmushi, daga nan suka koma kan gado suka fad'a duniyar soyayya.

*'BANGAREN SALIS*

Mama hankalinta ya tashi matuk'ar tashi tun ranar da ta je gidan Hajiya Mama take ta faman jiran ganin Nihal amman gashi yau sati biyu babu Nihal babu alamarta, Salis kuwa jikin na shi kullum k'ara tsananta yake yayi bak'i ya rame sosai, Baffa mahaifin Salis ne ya shigo d'akin bakinsa d'auke da sallama da sauri Mama ta k'arasa gurinshi tare da fashewa da kuka tana cewa "Malam ka taimaka min ka je ka dawo masa da matarsa kar ya mutu dan Allah ba ni da wani d'a shi kad'ai ne gareni ina matuk'ar sonshi sosai dan Allah ka taimaka min Malam" Mama ta k'arasa maganar tare da had'e hannuwanta guri d'aya alamun rok'o.

Murmushi Baffa yayi sannan ya ce "Sai yanzu kenan kika sauko kin ga yaronki yana kok'arin mutuwa ko? To ba da ni ba wannan abin kunyar gwanda............'' ,"Dan Allah Malam karka min haka ka taimaka min wallahi sharrin shaid'an ne da kuma matarsa Talatu da tazo ta fad'a min k'arya da gaskiya a kan Nihal ni kuma na zauna a kai, amman yanzu na gane gaskiya wallahi ba zan sake ba" Mama ta k'atse Baffa da maganar da yake son yi, Baffa ya ji tausayinta matuk'a dan haka ya kalleta sosai sannan ya ce "Zan je na bada hak'uri kuma zan yi kok'ari na ga na dawo da Nihal k'afata k'afarta amman sai kin yi min alk'awarin duk wanda ya sake kawo miki wata magana a kan Nihal k'arki ji ta, kuma ki yi masa kaca-kaca","Wallahi nayi maka alk'awarin zan doshe kunnuwana daga jin maganganun Talatu a kan Nihal".

Jinjina kai yayi sannan ya ce "to shikenan zan je na dawo da ita zuwa gobe","Allah ya kaimu" Mama ta fad'a cike da farin ciki "Amin ya rabbil'almin"Baffa ya fad'a sannan ya mik'e saboda jin kiran sallar da yayi ya ce "bari na je nayi sallah","to a dawo Lafiya" Mama ta fad'a Baffa ya fita da sauri ya nufi masallaci.

*'BANGAREN ALIYU❤️*

Kwance yake a kan tafkeken gadon da ke d'akin nasa idanuwansa suna kallon saman d'akin gaba d'aya hankalinsa da tunaninsa suna kan Khadijatullahi wani irin abu yake ji duk sanda ya dora idanuwansa a kanta, ko da ace yana cikin bak'in ciki ne idan ya dora idonsa a kanta sai ya ji wani irin farin ciki yana ratsa zuciyarsa, idan kuwa ya wuni bai ganta ba baya tab'a samun nutsuwa har sai ya dawo yayi arba da kyakkyawar fuskarta, a hankali ya furta "Dija ta" tare da sakin wani irin murmushi wanda yake nuna tsantsar farin cikin da yake ciki "wai daman ashe haka so yake? ban tab'a tunanin haka so yake da dad'i ba sai da na fad'a sonki wanda ni kai na ban san lokacin da na fad'a cikin kogin soyayyarki ba sai ganina na yi a cikinsa Dija ta" Yayi maganar a fili tare da juyawa jikinsa "Dija ta na san cewa kin tsani maza sosai, amman insha Allahu ni zan cire miki wannan tsanar da ki kai wa maza, zan tabbatar nasa kin fahimci cewa ba duka maza ne suke da hali irin na Jabir ba ina sonki babyna".

Khadijatullahi ta sauko daga iriyar muguwar k'iyayyar da take yiwa Affan har tana jin son yaron a cikin zuciyarta, Amatullahi kullum Affan yana gurinta ba ta ba wa Khadijatullahi shi har sai idan yana kuka alamar yana jin yunwa tana gama shayar dashi za ta karb'eshi tayi ta lallab'a yaron kamar wani kwai, Affan yafi sabawa da Amatullahi a kan Khadijatullahi, Nihal da Shahida kuwa ba'a magana dan kuwa kullum tare suke kwana dashi suna jin d'uminsa, ko kuka suka ga yana yi hankalinsu ya tashi har sai sun ga ya daina.

Zaune suke a tsakar gida kamar yadda suka saba kullum da yamma zasu shimfid'a taburma su yi ta hirarsu ta duniya, Aliyu ne ya fito daga d'akinsa sanye yake cikin wani yadi tsadadde brown yayi kyau sosai tafiya yake a hankali kamar wani mai sand'a har ya k'araso inda suke ya tsugunna har k'asa yana gaisar da Hajiya Mama "Ina yini Hajiya","Lafiya alhamdulillahi" Hajiya Mama ta fad'a tana sakar masa murmushi, guri ya samu ya zauna yana satar kallon Khadijatullahi wacce tun zuwansa ta had'e fuska kamar wacce ba ta tab'a yin dariya ba, Nihal ta kalli Aliyu tana murmushi ta ce "Yaya Haidar wai kwana biyun nan na ga ka na d'aukar wanka da yamma, ko dai an samo mana Aunty ne" Harara ya wurga mata sannan cikin muryarsa mai jan hankali ya ce "To ke kuma uwar 'yan sa ido, meye ruwanki da ni ko kuma so kike ki ganni kace-kace kamar wata ke" Zaro ido Nihal tayi tare da dafe k'irji kamar wacce tai gano ta ce "na shiga uku Yaya Haidar ni ce 'yar sa ido, kuma k'azama" Tayi maganar cikin muryar shagwab'a.

Shahida ta ce "Ai Other half wallahi Yaya Aliyu Haidar ya fad'a mai zurfin baki ga kwana biyun nan ba sai ki ga yana ta wani smiling shi kad'ai" Dariya su ka yi gaba d'ayansu amman ban da Khadijatullahi wacce har lokacin fuskarta babu alamar murmushi "Awww har da ke ko darling sister"Aliyu yayi maganar tare da satar kallon Khadijatullahi "Eh mana Yaya Aliyu Haidar ai ina kula da kai sosai yanzu fad'a mana wannan wace mai sa'a ce tayi sa'a sace zuciyar Yayanmu, zuciyar da take da matuk'ar tsada 'yan mata da yawa suna son su ga cewa wannan kyakkyawar zuciyar ta so su","hmmm! Shahida kenan kawai ku ta ya ni da addu'a kun ji, dan ina tsananin buk'atar haka a halin da nake ciki yanzu" Nihal ta kalli Aliyu sosai, ta fuskanci yana cikin tsananin damuwa "To Yaya Allah Ubangiji ya fitar da kai" Nihal ta fad'a tana cigaba da kallon d'an uwan na ta, Shahida ta ce "Amin ya rabbi".

Amatullahi da ta fuskanci inda maganar Aliyu ta dosa dan ta fahimci cewa Aliyu yana tsananin son Khadijatullahi, saboda irin yadda yake nuna kulawarsa a kan ta, da kuma yadda yake sadaukar da abubuwa da yawa a kan ta, amman kuma tana tausaya masa saboda ta san cewa Khadijatullahi ba lallai ta yarda ta so shi ba, kuma ko da zata yarda gaskiya sai an kai ruwa rana "Yaya Aliyu Allah ya fitar da kai ya dora ka a kan wacce ka ke so, tayi maka son da ba ka tab'a tunani ba, ta so ka da dukkanin zuciyarta" Murmushin jin dad'in Addu'ar da Amatullahi tayi masa yayi sannan ya ce "Amin Allah ya sa sister nagode sosai","Amin" Suka amsa gaba d'ayansu.

Hajiya Mama tana jefe tana jin su ita dai ba ta ce musu komai ba dan kuwa ita ma tuntuni ta fahimci cewar Aliyu yana son Khadijatullahi, ta ji dad'i sosai amman kuma ta wani b'angare na zuciyarta tana tausayawa Aliyun saboda Khadijatullahi ba lallai ta so shi ba, ta tsani maza bayan haka kuma ta tsani Jabir wanda hakan ya shafi Aliyu shi ma ta tsane shi, Aliyu ya tashi daman ya zo ne ya ga Khadijatullahi ya kalli Hajiya Mama tare da cewa "Hajiya zan je gidan Musaddik ba zan dad'e ba zan dawo","to A dawo lafiya" Aliyu ya ce "Allah yasa'' Sannan ya fita daga gidan motarsa ya shiga ya d'auki hanyarsa zuwa gidan Abokinsa Musaddik.

Hajiya Mama suka cigaba da yin hirarsu har sai da aka kira sallar magriba sannan suka tashi kowannansu ya doro alwala suka gabatar da sallar magriba, ko da suka gama suka yi addu'o'in da ake yi bayan anyi sallah sannan suka dora hirarsu daga inda suka tsaya.

*'BANGAREN TEEMARH DA JABIR💕🥀*
Chapter 37 · 0% Book details