← Book details Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 54

Sashe 53

Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Hajiya Asiya ce zaune a d'akinta tana tunanin mijinta Innarta ce ta shigo bakinta d'auke da sallama "Assalamu alaikum" Hajiya Asiya ta amsa mata "Wa'alaikumussalam Inna barkanki da zuwa" Inna ta ce "Yawwah nagode sosai" Hira suka d'anyi sannan Inna ta fita ta koma d'akinta, Hajiya Asiya ta d'auki wayarta ta shiga kiran layin Labahani ringing d'aya biyu ya d'auka "Assalamu alaikum" Daga chan 'bangaren aka fad'a "Wa'alaikumussalam Labahani ya dai ka gano inda 'yar uwata take?" Labahani ya ce "Eh hajiya na dai gano inda yaranta suke amman ita ta dad'e da mutuwa, kuma na gano cewar 'yar uwarki 'yar asalin wani k'auye ne kantum sanadiyar gobarar da garin yayi ne yasa suka tattaro suka gudo a hanyarsu ta guduwa daga garin aka kashe mata iyayenta gaba d'ayansu" hawaye ne suka shiga zubowa Hajiya Asiya ta ce "To ina zan sami yaran na ta?","Murja da Khadijatullahi gaba d'aya sunyi aure, ita Murja ta auri Alhaji Mansur jikamshi ita kuma Khadijatullahi ta auri d'ansa" Da sauri Hajiya Asiya ta mik'e daga zaunan da take jikinta na rawa tare da sakin wayar dai-dai lokacin Inna ta k'ara dawowa d'akin "Lafiya Asiya","Inna ashe Murja da Khadijatullahi yaran Hajara ne" Nan ta kwashe duk abin da Labahani ya ce mata ta fad'a mata Inna ta ji matuk'ar dad'i, Hajiya Asiya ta d'auki mayafinta ta fita Inna ta bita da kallo, Hajiya Asiya tana fita ta tari mai adaidaita ta shiga tayi masa kwatancen gidan Alhaji Mansur, suna isa ta fito ta biyasa kud'insa tare da nufar kofar gidan tana bubbuga gate d'in mai gadi ya bud'e mata ta shiga kai tsaye falon ta nufa ta shiga bakinta d'auke da sallama Abba da Aunty Murja suna falon suna kallo, Alhaji Mansur ya kalleta cike da mamakin meya kawota gidan nan kuma "Ku yi hak'uri na shigo muku gida babu izini, Murja gurinki na zo ya ya sunan mamanki?" Aunty Murja ta mik'e tsaye tare da cewa "Mamana kuma sunanta Hajara" Hajiya Asiya ta ce "Kenan da gaske ke 'yar Hajara ce k'anwata" Zaro ido Aunty Murja tayi shima Alhaji Mansur ya mik'e tsaye yana mamakin wannan lamarin "Hajara kuma?" Ya tambayeta cike da tsananin mamaki "Eh Hajara k'anwata da aka nemeta aka rasa" Aunty Murja ta ce "Mami kenan ke Yayar Mamana ce, kune 'yan uwanmu" Hajiya Asiya ta fad'a mata komai game da Mamarta da har zuwa guduwar da Hajaran tayi aka nemeta aka rasa, Kuka Aunty Murja ta fara yi inda Mami ta juya ta fita daga falon, Alhaji Mansur ya biyo bayanta anan ya tarar har ta fita daga gidan, motarsa ya shiga ya ja mai gadi ya bud'e masa gate ya fita adaidaitar da ya ga Hajiya Asiya ta shiga ya bi bayanta a dai-dai kofar gidansu ta sauka ta biya mai adaidaitar kud'insa ya ja ya bar unguwar tana shirin shiga gidan ta ji muryar Alhaji Mansur yana kiranta "Hasiya" Juyawa tayi da sauri tana kallonsa k'arasowa ya yi gurin da take suka kallon juna "Ki shiga ki je ki yi sallama da Inna ki zo mu tafi gida" Alhaji Mansur ya yi maganar yana kallonta "A'a ka bari kawai","ban gane na bari ba" Yayi maganar cike da b'acin rai "Ka yi hak'uri ban yi hakan dan na b'ata maka rai ba" Alhaji Mansur ya ce "Ki shiga ki fito ina jiranki" Ta amsa masa da "To" Anan ta shiga take fad'awa Inna yadda su ka yi da Alhaji Mansur d'in Innar tayi mata nasiha sannan ta fito murfin motar ya bud'e mata ta shiga ya bud'e ya ja motar ya nufi gidansa yana jin wani irin farin ciki a cikin zuciyarsa.

*'BANGAREN SAFNA😟🥰*

Duk da irin tsananin bak'in ciki da zafin kishin da take ji a kan Hafsa amman tunda ta shigo ta ga irin yadda take kula da Khalid da kuma yadda take girmamata yasa ta zubar da makaman kishinta, ta rumgumi Hafsa a matsayin 'yar uwa, komai na su tare su ke yi sun had'a kansu sosai suna kula da mijinsu yadda ya kamata, Safwan shi kansa hankalinsa ya kwanta sosai har wata 'yar k'iba yayi.

Teemarh ce zaune a kan gadonta ta zabga tagumi Jabir ya shigo d'akin ya k'ura mata ido, ya zauna a bakin gadon tare da hurgo mata tambaya "Yaushe kika dawo? Meyasa baki dawo jiya ba?" Teemarh ta ce "Jiyan na dawo" Ta bashi amsa tana kallonsa "Meyake damunki? Bana son ki yi min k'arya" Teemarh idanuwanta suka ciko da kwalla "Bakomai darling" Jabir cikin fushi ya ce "Ba za ki fad'a min ba" Teemarh ta ce "Ni ba zan haihu ba kenan" Tayi maganar hawaye na zuba daga idanuwanta, shuru Jabir ya yi yana kallonta wato kenan Teemarh saboda ba ta haihu ta shiga damuwa "Waya ce miki ba za ki haihu ba, zaki haihu mana ai kin san komai lokaci ne kema lokacinki yana nan zuwa","to Allah yasa" Jabir ya yi murmushi yana cewa "Ko kefa darling" Anan suka shiga yin hirarsu ta masoya har sai da Jabir ya tabbatar Teemarh ta fita daga cikin damuwar da take ciki.

*'BAYAN WATA HUD'U🤙🏾*

Gaba d'aya amaren suna zaune cikin farin ciki da kwanciyar hankali, Aunty Murja ta haifi 'yarta mace inda aka sha suna kamar ba gobe, dare ya yi kowa ya koma gidansa, a cikin watan kuma Amatullahi da Khadijatullahi suka shiga yin laulayi koda aka tabbatar musu da cewa suna da ciki Jabir ya yi murna amman da ya tuna irin damuwar da Teemarh take ciki akan rashin haihuwar da ba tayi ba, duk ya ji jikinsa ya yi sanyi ya san idan Teemarh ta ji Khadijatullahi tana da ciki to zata shiga damuwa fiye da wacce ta shiga a baya, amman ya san koda bai fad'a mata ba dole ta sani "Ya rahim" Ya fad'a tare da dafe kansa, haka dai ya shiga gidan nan Khadijatullahi ta huce 'bangarenta shi kuma ya huce gurin Teemarh yana shiga nan ya tarar da ita tana bacci ya k'arasa kusa da ita tare da shafa kanta yana murmushi, daga k'arshe ya fita ya koma gurin Khadijatullahi.

Bayan wata biyu yau ya kama za'ayi bikin 'yar Kawu Bala haka kowannansu suka ta ho gidan Hajiya Mama,Nihal, Amatullahi, Shahida,Khadijatullahi da kuma Hafsa da yake ita ma ta zo gida shine ta biyo gidan Hajiya Mama da yake ta san su Amatullahi zasu zo gidan gaba d'ayansu suna da ciki har ya fito ma, Teemarh tana zaune wacce ita kad'ai ce ba ta da cikin hankalinta ya tashi ta ware kanta a gefe tana tunanin ita ma ya za'ayi ta samu cikin? Amman ta rasa mafita Jabir da Aliyu ne suka shigo Idanuwan Jabir ya sauka akan Teemarh wacce ta ware kanta "Zahra" Ya kira sunanta d'agowa tayi da sauri tana kallonsa bata iya amsawa ba saboda kukan da ya taho mata "Ki zo falon bak'i ina son ganinki" Yana gama fad'ar haka ya fita daga falon, Teemarh ta mik'e ta bi bayansa tana shiga falon bak'in ta zauna a kan kujera "Darling nayi mamaki sosai, wannan abin da ki ke yi fa kamar kina jaa da hukuncin ubangiji bai kamata kina damun kanki ba, haihuwa Allah ne mai badawa kuma ina da tabbacin kema zaki samu ciki ki daina damun kanki dan manzon Allah darling" Teemarh hawaye suka fara bin kuncinta "Shikenan badamuwa" Abin da ta ce kenan tana goge hawayen fuskarta haka dai yai-yi ta rarrashinta har tayi fara walwala daga nan suka fito tare dashi a gurin Hajiya Mama ta zauna a tsakar gida Jabir ya bita da kallo ya girgiza kai kawai ya shiga falon, haka aka yi bikin aka gama kowannansu ya koma gidansa.

Khadijatullahi yau ne cikinta ya kai watan haihuwarta tun da safe Jabir ya kai ta Asibitin, inda anan suka tarar da Aliyu ya kawo Amatullahi har an shiga da ita labour room, ita ma Khadijatullahi ana shiga da Amatullahi ta fara labour nan ita ma aka an ta ya ta labour room, ni kam nace Amatullahi Allah ya sauke ku lafiya🥲.
Chapter 53 · 0% Book details