← Book details Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 54

Sashe 16

Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Khadijatullahi tayi dariya ganin irin yadda Hafsan take hararar Amatullahi fuskarta a murtuke, drivern Hafsa ne ya zo suka nufi motar gaba d'aya, haka suka nufi layin gidansu Khadijatullahi suna isa, tun kafin su fito daga motar Khadijatullahi take bin wata mota mai numfashi da ta gani a kofar gidansu mamaki ya cika zuciyarta, haka suka fito daga motar bayan sunyi sallama da Hafsa, Amatullahi ta kalli Khadijatullahi ta ce "besty yau bazan shiga gida ba ki cewa Aunty Murja zuwa anjima zan dawo akwai abu mai muhimmancin da zan yi ne" Khadijatullahi ta ce "to shikenan besty" Amatullahi ta nufi hanyar gidansu domin kuwa yau su Inna Larai sai ta tabbatar ta koya musu hankali, Khadijatullahi haka ta nufi kofar gidansu zuciyarta na buguwa, Jabir kuwa yana ganin Khadijatullahi ya bud'e motar ya fito idanuwansu suka had'u Jabir yana mata wannan Shu'umin murmushin nasa, Khadijatullahi tayi baya zuciyarta na bugawa idanuwanta suka firfito jikinta ya maka rawa tana nuna sa da yatsa tana kok'arin kiran sunan "jaa.....ja....jabir".
Jabir ya nufi inda Khadijatullah take tsaye idanuwansa a kan cikinta "naji ance wai kina da ciki" sai Kuma yayi wani irin murmushin mugunta tare da ya mutse fuska sannan ya ce "Wayyo ni Jabir ina da k'arfin jini ace daga kwanci da mace sau d'aya har ta harbu ciki ya bayyana" cikin dakewa Khadijatullah ta fara magana "kaii tsinanne kayi gaggawar barin kofar gidan kafin na saka an jagaliya suyi min yaga-yaga da naman jikinka, shege d'an gidan shegiya" tayi maganar cikin zafin nama domin kuwa yau zata koyawa Jabir hankali zai san ita ma bawai k'anwar lasa ba ce Jabir ya kalleta sosai ya ga irin hucin da take kamar tsohuwar zakanya ya shek'e da wata iriyar dariya sannan ya ce "duk ki gama zagina karki ga nazo nan kofar wannan matsayacin gidan naku ki ce zaki yi min rashin mutunci ai kin san waye Jabir kuma kin san ba k'aramin aikina ba me wallahi yanzu a gaban kucakan 'yan layin naku nayi miki abin da ya faru ranar Asabar 26 ga wata march k'arfe 1 zuwa 2 na dare" wani irin a zababben mari ta wanke shi dashi hagu da dama sai da ta jera Masa sau biyar sannan fara magana "Eh tabbas nasan waye kai, Kai d'in ba kowa ba me in Banda dabba, Kuma ka sani idan a wanchan ranar kayi min ba yadda zan yi to yanzu baka Isa ba Jabir nima d'in nan da ka ke ganina ba k'aramar tantiriyar mara mutunci ba ce, wallahi Jabir na tsane ka na tsani duk wani Abu da ya dangance ka, Jabir idan baka bar nan kofar gidan ba zan iya kashe ka" magana take cikin wani irin yanayin bak'in ciki muryarta duk a shshshak'e, Jabir yaji matuk'ar jin zafin Marin da Khadijatullah tayi Masa domin kuwa tunda yake babu Wanda ya tab'a Marin shi, cikin zafin nama yake nuna Khadijatullah da yatsa Yana cewa "ba ni kika mara ba, wallahi ki jira zaki ga abin da zai biyo baya Kuma ki rubuta ki ajiye ni Jabir zan k'ara aurenki a Karo na biyu Kuma sai nayi miki abin da yafi Wanda nayi miki a baya" Yana fad'ar haka ya nufi motarsa ya bud'e zai shiga ya ji maganar Khadijatullah "Lallai Jabir sai yau na tabbatar Kai ka fi dabba ma, wa zaka aura?to Ina Mai tabbatar maka ni Khadijatullah na fi k'arfin ka, sai dai ka auri wannan shashashar uwar ta ka domin ita ce dai-dai kai, banza a jawo dak'ik'i Kuma insha Allahu sai kayi mutuwar da sai ana tattaro naman jikinka sai kayi mutuwar da ba za'a iya gane gawarka ba, na tsane ka na tsane shege Mai hali timakai" tana gama fad'ar haka ta shiga gida da gudu tana kuka, Jabir kuwa murmushi yayi domin kuwa yasan Yana zuwa gurin wad'annan kawun nata ya basu kud'i dole ko tana so ko Bata so a d'aura auren (ni kuwa 'yar mutanan zazzau nace Jabir ka makaro😂)

Ya shiga motarsa ya ja ya nufi gidansu kawun Khadijatullah, ko da ya je ya ga gidannasu gaba d'aya an ruguje shi, Nan ya tambayi wani saurayi a kan meya faru aka ruguje gidan Kuma Ina mutanan gidan, nan saurayin ya fad'a Masa duk abin da ya faru sannan ya d'ora da cewa "yaran gidan Kuma tun ranar da aka kawo gawarsu Kawu Sani suka tattara suka bar garin babu Wanda yasan inda suka je" Yana gama sanar dashi ya juya yayi gaba Jabir ya daki motarsa yanzu shikenan sai ya auri Teemarh damar abin da yaso shine ya samu a mayar da aurensa da Khadijatullah hakan ne zai saka ba zai auri Teemarh ba, gashi duk Shirin da yayi Yana nema ya ruguje, haka ya shiga motarsa ya nufi gida zuciyarsa cike da tashin hankali, Yana zuwa gidan ya tarar gaba d'ayansu suna falo Abba sai zagaye yake a falon kallo d'aya zaka yi masa ka tabbatar Yana cikin fushi ga Hajiya Asiya a gefe sai kuka take yi ita da Nihal saboda yau Alhaji Mansur tunda ya tashi ya tambaya Ina Jabir? Aliyu yace ya ganshi ya fita nan ya saka Hajiya Asiya a gaba yana Mata bala'i a kan ita ta saka shi a kan wannan tarbiyyar, Kuma yake shaida musu cewa Aure zai k'ara domin ya samarwa 'ya'yansa uwa ta gari shine fa suke ta kuka ita da Nihal, (ni kuwa nace wallahi Alhaji Mansur ka min dai-dai👏😂) Shahida da Aliyu basu ji haushi ko bakin ciki ba domin kuwa sun San tabbas Abbansu Yana buk'atar macen da zata kula dashi saboda Mami Sam Bata damu da ta kula dashi ba ita dai kawai tana zaune dashi ne saboda Yana da kud'i.

Jabir tunda yayi musu kallo d'aya ya watsar haka ya nufi d'akinsa yana cika yana batsewa kamar zai fashe, Abba ya k'are masa kallo daga sama har k'asa wai ace wannan d'ansa ne yake irin wannan shigar ya fita waje sai kace tsohon shaid'ani (ni kuwa nace Abba ai Jabir wallahi yafi shaid'an🤣) cikin zafin nama ya nufeshi gadan gadan ya jawoshi ya kifa masa mari wanda har sai da ya rasa ganinsa na tsawon dak'ik'a guda ya fad'a kan kujerar da take kusa da kujerar da Aliyu yake zaune, Abba ya ce "dan ubanka ina ka je tun safe sai yanzu ka dawo" Jabir ya d'ago ya kalli mahaifinnasa da rinannun idanuwansa ya ce "Club naje kuma......" Ai jin wani sabon marin da ya ji a fuskarsa yasa yayi shuru da maganar da zai k'arasa, haka Alhaji Mansur ya rufeshi, Aliyu ya tashi ya rik'e Abban yana bashi hak'uri shi kuwa Jabir tashi yayi sai da ya kusan shiga d'akinsa ya juyo ya kalli mahaifinnasa ya ja tsaki tare da tofar da yahu, nan fa Alhaji Mansur ya fusata yana kok'arin fusge rikon da Aliyu yayi masa, amman Aliyu ya riga ya rik'eshi sosai Jabir ya shiga d'akinsa ya saka mukulli, Abbah ya ce "to wallahi ka shirya goben nan za'a d'aura maka aure da wannan k'aruwar yarinyar shege gantalallan banza d'an iska mara kunya mara tarbiyya" Jabir duk yaji abin da mahaifinnasa ya ce dan da k'arfi yake magana, kwanciya yayi a kan gado yana tuna maganganun da Khadijatullahi ta fad'a masa "na tsaneka insha Allah sai kayi mutuwar sai ana tattaro naman jikinka sai kayi mutuwar da ba za'a iya gane gawarka ba" bai san meyasa ba wannan maganar ta tsaye masa a rai kuma ya ji son cikin da Khadijatullahi take dashi a zuciyarsa, tsaki ya ja tare da cewa "aikin banza" haka ya cigaba da sake-sake a cikin zuciyarsa.

Abbah kuwa dakyar Aliyu da Shahida suka lallab'ashi ya shiga d'akinsa su ma suka shiga nasu d'akin, Mami da Nihal kuma abin duniya duk ya ishe su, haka dai suma suka nufi nash d'akin kowannan su zuciyarsa cike da bakin ciki da tashin hankali.

••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••

*'BANGAREN KHADIJATULLAHI*

Tana shiga gidan da gudu tayi gurin da Aunty Murja take zaune tana tankad'an garin tuwo ta fad'a jikinta tana kuka cikin jijicewa Aunty Murja ta ce "Khadijatullahi meyafaru? Wani abun aka yi miki?" cikin kuka mai tsima zuciyar me sauraro ta fara magana "Aunty Jabir Jabir ne" zaro ido Aunty Murja tayi tare da cewa "A'uzubillahi minashshed'anir rajim Allah kayi mana tsari dashi, a ina kika ganshi" anan ta kwashe labarin duk yadda suka yi dashi ta fad'a mata, Aunty Murja ta ce "to aniyyarsa ta bi sa wallahi mun fi k'arfinsa, ki daina damuwa kin ji k'anwata ina tare dake ba zan tab'a bari ki wulak'anta ba" haka Khadijatullahi ta kwanta a jikin Aunty Murja, dakyar Aunty Murja ta iya k'arasa tankad'an sannan ta tureshi gefe d'aya, domin ji tayi ma ba za ta iya yin tuwon ba, daman akwai ragowar garin kwaki da sugar suka jik'a suka sha shi, suka shiga d'aki domin yin bacci haka suka kwanta kowanna su da abin da yake sak'awa a cikin ranshi.

```'BANGAREN HAFSA🥴```
Chapter 16 · 0% Book details