Sashe 24
Daren Aurena Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Inna Larai na dawowa daga gidan Baffa Usmanu ta tarar da Lado a kofar gida, ya ja ya tsaya sai huci yake yi kamar zai fashe, kallonsa tayi tana murmushi tare da cewa "jarumin d'ana ashe kana nan" Wani irin mugun kallo yayi mata tare da cewa "dole ki ce min jarumi tunda kina cuta ta, ai yanzu nasan komai kuma wallahi karki ga ke Innata ce sai kin biya ni, domin kuwa ban ga wanda zai ci min kud'i ya zauna lafiya ba" Inna Larai tayi masa kallon rashin fahimta tare da cewa "me ka ke fad'a ne, ban gane ba yi min bayanin yadda zan fahimta" Lado cikin hargagi da masifa ya ce "ina nufin kajin da kike zuwa kina siyar min, kina ce min mutuwa suke yi, to yanzu na san asalin gaskiyar" gaban Inna Larai neya fad'i "wa ya fad'awa Lado wannan maganar" ta fad'a a zuciyarta ba ta san maganar ta fito fili ba sai ji tayi ya ce "Amatullahi ce, ita ta fad'a min" Inna Larai ta kai kololuwa wajen k'ara tsanar Amatullahi "wato ita ce ta had'ata da gudan jininta, ai kuwa wallahi sai ta koya mata hankali" tayi maganar a zuciyarta.
Huce Lado tayi ta shiga gida dan har mutane sun fara taru suna son jin ba'asin meya had'a 'da da uwar, shima Lado bin bayanta yayi da sauri yana cigaba da yin bala'i tun daga zaure Inna Larai take kwad'awa Amatullahi kira da sauri Amatullahi ta fito tana cewa "Waye wannan yake min wannan kiran mafarautan?", "Uban ki ne shegiya".
Amatullahi ta mayar da fuskarta ta masu tausayi tare da cewa "Inna me nayi?" Inna Larai ta d'aga hannunta da niyyar marin Amatullahi, Lado yayi sauri ya rik'e hannunnata Yana cewa "Saboda ta fad'a min gaskiya shine zaki mareta, to wallahi karki kuskura" Amatullahi ta saka kuka tare da yin d'akinta tana shiga ta fashe da dariya "Kai Allah Mai yadda ya so, kad'an ma ku ka gani" hijabinta ta saka ta fito tsakar gida Babu kowa dan haka ta huce, ta fita daga gidan ta nufi gidansu Khadijatullah.
Tana shiga ta tarar da Aunty Murja ta zabga tagumi tana ta murmushi, abin ya ba wa Amatullahi mamaki sosai, tayi sallama kusan sau biyar, Amman Aunty Murja ba ta ma san tana yi ba.
K'arasawa tayi kusa da Khadijatullah wacce take zaune ita ma tana kallon Aunty Murja zuciyarta cike da tambayoyi domin ta ga kwana biyu Aunty Murja tana cikin farin ciki Amman da ta tambayeta sai ce Mata tayi bakomai, zama Amatullahi tayi kusa da ita suna kallon juna ta ce "bestyna meya faru da Aunty Murja ne, na ga na shigo Ina ta sallama ba ta amsa ba Kuma sai murmushi take yi" Khadijatullah ta ce "wallahi besty ban sani ba, nima yadda kika gan haka na ganta tun ranar da ta dawo daga gidan Hajiya Mama" Amatullahi tayi murmushi tare da cewa "to ko ta fad'a soyayya ne?","Ina tunanin haka gaskiya" Khadijatullah ta fad'a tare da kallon inda Aunty Murja take.
Hannun Khadijatullah ta kama ta taimaka Mata ta tashi sannan suka k'arasa gurin da Aunty Murja take domin Amatullahi tana son tambayarta meke damunta zama suka kayi gaba d'ayansu kusa da ita, dafata Amatullahi tayi tare da Kiran sunanta "Aunty Murja" Firgita tayi ta d'anyi murmushi ta ce "Amatullahi yaushe kika zo","ban dad'e da shigowa ba, Aunty Murja me yake damunki?" Aunty Murja ta ce "me kika gani, bakomai","Dan Allah Aunty Murja ki fad'a mana kwana biyu Khadijatullah ta ce kina cikin farin ciki, Amman kin k'i fad'a mana mu ta ya ki farin cikin".
Tabbas ba za ta iya b'oye musu ba, saboda su d'in jininta ne, Dan haka ta fara yi musu bayani "D'an Hajiya Mama ne, Alhaji Mansur ya ce Yana sona zai aure ni" wani irin tsalle Amatullahi tayi tare da furta "Alhamdulillah Allah Kai ne Allah, Auntynmu Ina ta ya ki farin ciki" ta fad'a tana rumgumeta sosai, Khadijatullah ma tayi farin ciki sosai a hankali ta furta "ina ta ya ki murna Auntynmu, Allah ya Baku zaman lafiya","Amin" Amatullahi ta fad'a haka sukai ta farin ciki dan ji suke kamar su zuba ruwa a k'asa su sha.
*'BANGAREN SAFWAN DA HAFSA🥰*
Tafiya take yana biye da ita a baya yana Kiran sunanta "Amrish Dan Allah ki tsaya, ki ba ni ko minti 1 ne nayi miki bayani" ba ta tsaya ba Kuma ba ta da niyyar tsayawa dan kwata-kwata ba ta k'aunar ganin Safwan a rayuwarta, wannan maganar da yake yi mata ji take kamar garwashin wuta ake watsa Masa a zuciya.
To masu karatu nasan wasu zasu ce to menene Amrish d'in, to idan aka ce Amrish ana nufin masoyiya.
Gabanta ya sha, hawaye suka fara zuba daga cikin idanuwansa, "Amrish" ya fad'a cikin wata iriyar murya, shuru tayi tare da kawar da kanta gefe, domin zuciyarta ta fara k'aryewa da ganin hawaye na zuba daga cikin idon Yaya Safwan d'in, ya cigaba da magana "Amrish wallahi ina sonki sosai, Ina k'aunarki, abin da ya faru a baya sharrin shaid'an ne da Kuma na matata.
Da sauri Hafsa ta kallesa domin tabbatar da abin da ya ce, Kai ya gyad'a Mata alamar "Eh" sannan ya ba ta labarin duk irin mak'ircin da Safna tayi ta raba su "wallahi Amrish ban miki haka wai dan ba na sonki ba, Ina tsananin sonki sosai".
Hawaye ne suka fara zuba daga idonta tare da cewa "Amman Yaya Safwan, nayi tunanin kafi kowa sani na, ka san ba zan iya yin irin wannan ba, ka ba ni mamaki ban yi tunanin haka daga gurinka ba", ta fad'a tana kuka Mai tsuma zuciya "na sani ban kyauta ba, ki yafe min insha Allahu hakan ba zai sake faruwa ba","Shikenan ya huce Yayana" wani irin farin ciki ne ya kama shi haka suka jera har wajen motarsa, sun dad'e suna hirarsu ta masoya daga k'arshe kuma suka yi sallama Hafsa ta koma gida zuciyarta cike da farin ciki, daman ta fito daga gidan ne saboda ba ta k'aunar su yi magana da Yaya Safwan d'in shine ya biyo ta, d'akinta ta shiga ta tarar Khalid ya kwanta Yana bacci fad'awa kan gadon tayi ta lula duniyar soyayya.
*WASHE GARI☄️*
Nihal ta farfad'o Shahida ta kira Hajiya Asiya ta fad'a mata babu shiri ta fito kamar wata korarriya tana zuwa Asibitin ta rumgume Nihal d'in tana kuka "yarinyata" Teemarh wacce take tsaye dan yanzu ta ji sauk'i tun da aka yi Mata allurai da k'arin ruwa ta Warware sosai, Baki ta tab'e Hajiya Asiya ta kudurce a zuciyarta Nihal ba za ta sake komawa gidan Salis ba sai ya saketa sai dai duk abin da zai faru ya faru.
Alhaji Mansur ne yake tafiya cikin motarsa a nutse yake tukin gidan Hajiya Mama ya nufa domin shi bai San ma abin da ya faru da Nihal d'in ba, Yana zuwa ya tarar da Aunty Murja tana wanke-wanke yayi sallama tare da ja ya tsaya Yana kallonta, tabbas nan da sati mai zuwa zai yi kok'arin ganin an d'aura aurensu domin ba zai iya hak'ura ace har sai sati uku ba, Aunty Murja ta d'ago suka had'a ido dashi murmushi ya sakar Mata tare da cewa.
"Amincin Allah ya k'ara tabbata a gareki ma'abociyar nutsuwa da hankali kyakkyawar Matata wacce nake saka ran a cikin wannan satin zan fara tunanin samun 'ya'yana daga gareki".
Murmushi kawai tayi tare da sunkuyar da Kai, Amman kalmar da ta tsaya mata ita ce da Alhaji Mansur d'in ya ce a cikin wannan satin zai fara saka ran samun 'ya'ya, to shine ta rasa gane meyake nufi.
'yar k'aramar kujerar k'arfe ya d'auko ya ajiye kusa da ita ya zauna, da sauri ta kallesa domin kuwa gurin da rana sosai "ka tashi daga nan akwai rana sosai, karka sami matsala","A'a na k'i" ya fad'a yana mak'e kafad'a kamar wani k'aramin yaro, abin ya ba wa Aunty Murja dariya sosai, tsayawa yayi Yana kallonta tare da cewa "Murjanatu dariyarki tana saka ni nishad'i fi ye da yadda bakya tunani".
Kallonsa ta yi sosai ta ce "Kai ne ai ka ke ba ni dariyar, nagode sosai Kuma......" Sai kuma tayi shuru tare da yin wasa da zoben hannunta, Alhaji Mansur ya k'ura Mata ido tare da cewa "Kuma me?","Bakomai"ta bashi amsa har lokacin tana wasa da zoben hannunta, "ba za ki fad'a min ba ko?", Kai ta girgiza Masa alamar "A'a".
Mik'ewa yayi fuskarsa ta chanza zuwa yanayin fushi ya nufi hanyar waje, da sauri Aunty Murja ta bi bayansa a gabansa ta tsaya tana cewa "Dan Allah ka yi hak'uri","to fad'a min kuma me?" Aunty Murja ta ce "Daman godiya kawai zan maka" ta fad'a dan ba za ta iya fad'a masa abin da ke ranta ba, tana jin tsananin kunyarsa.
"Shikenan nagode miki sosai, kuma nasan matsayina a gurinki tunda kin k'i fad'a min kin nuna min ban kai matsayin da zan san abin da ke ranki ba" Yana gama fad'ar haka ya huce ya fita motarsa ya shiga ya ja ya bar unguwar, Aunty Murja tsugunnawa tayi a k'asa tare da fashewa da kuka gaba d'aya haushin kanta take jii a kan meyasa ba ta fad'a masa ba, har ta bari yayi fushi da ita.
Hajiya Mama kuwa duk abin da suka yi tana jin su, domin kuwa tana cikin toilet ne ta shiga kama ruwa kuma tsakanin toilet d'in da inda suke babu nisa, murmushi tayi sannan ta koma d'aki ba tare da ta bari Aunty Murjan ta ganta ba, a zuciyarta tana cewa "sai yanzu Mansur zaka san zakai aure".
Ita kuwa Aunty Murja haka ta gama shan kukanta sannan ta tashi ta k'arasa wanke-wanken ta kifesu a kwanbo sannan ta shiga d'akin Hajiya Mama ta yi Mata sallama ta fito ta nufi gida zuciyarta a cunkushe.
*POLY🚴🏽♀️🏦*