← Book details Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 55

Sashe 9

Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai kawai ya girgiza da kansa ya bud'e mata motar ta shiga sai turo baki take ita a lallai an 'bata mata raai, Yana shiga ya tada mota suka nufi hanyar gida, sai surutu yake Yana bata Labari bata kulashi sai da Tace Umm ko hmmm har suka Isa gida, suna Isa ta fice ta shige gida ba ta Tsaya jiransa ba kamar yadda suka Saba ba, mummy na ganin ta Tace "Ke Kuma yau ko sallamar ma baza ki iya ba"
Cikin sanyin murya tace " Sorry mummy na shafa'ane" wuri ta samu ta zauna tace "Mummy ina wuni"
"Lafiya daughter ya school d'in dai?"
"Lafiya Lau Mummy, ina Umma?"
"Tana part d'inta, yanzu ma tashi a inda kike zaune zatayi wanka zamu je saloon wanke Kai"
"Yauwa Mummy Nima zan biku"
"Ahhh yau Kuma ba yayan naki bane zai kai ki?"
"Eh zan biku"
Haisam da sallama ya Shigo mummy ta amsa har kasa ya tsuguna ya gaida ta kana ya nemi wuri ya zauna yace "Ni zan kai ki, aiki nane wannan"
Turo baki tayi Tace "Bana so zanbi su mummy"
Yace "In ko hakane baza ki ba don bazan bari ki fita a gidan Nan ba"

Mikewa tayi Tace "To an fasa wanke Kan" ta shige d'akin ta, Haisam yace " Kin ganta ko"

Mummy tayi saurin fad'in "Ah ah ba ruwan nikam kun fi kusa in sa muku baki ku kunyata ni ba dani ba" ta Mike ta shige d'akin ta itama Haisam Yar karamar dariya yayi ya bi bayan Ma'isha ya tarar da ita tana kwance a Kan gado tana kallon saman d'akin.

Turo kofar yayi a hankali tasan ba mai shigowa sai shi hakan yasa ta juya Masa baya, Murmushi yayiw ya zauna akan couch d'in dake d'akin ajiyar zuciya yace "Please princess kiyi hakuri duk da ban San laifin me nayi ba, don na tabbata fushin Nan da ni akeyi, Amma duk da hakan kiyi hakuri"

Hmmm kawai Tace ba tare da ta juyo ba, tashi yayi ya zauna a Kan couch d'in dake fuskantar ta, Kama baki yayi yace "Laaa ila kuka Princess? Me yayi zafi har Haka Dan Allah ki fad'a min laifi me nayi haka?"

A zuciyar ta Tace "Taya za'ayi na fad'a maka cewar ganin ka da nayi da watane ya sani kuka? Taya za'a yi na fad'a maka cewar bana son ganin wata mace ta rab'e ka? Taya za'a yi na fada maka ganin ka da wata da nayi cafeteria ne ya sani kuka?"

Cikin wani irin salo ya ambaci sunanta "Ma'isha!!! A hankali ta d'ago kanta ta sauke su akan kyakkyawar fuskar sa kasa jure kallon da yake mata tayi ta Kuma rufe idanun ta.

Yace "Ma'isha tell me please ko Nima so kike nayi kukan?"
Girgiza Kai tayi had'e da fad'in "A'a"
Yace "To tashi ki zauna"

Ba musu ta tashi ta zauna yace "Princess ina jinki Dan Allah me ya same ki?"
Shiru tayi sai kokarin 'boye hawayen da ke idon ta take Amma ta kasa, daga bisani ta fashe da kuka Mai sauti.

Haisam har cikin ransa baya jin dad'in kukan ta, musamman ma ace shine silar kukan nata ajiyar zuciya yayi yace "Dan Allah Dan Annabi na roke ki fad'a min dalilin kukan naki , bana jin dad'in ganin ki a hakan karya min zuciya yake Dan Allah kiyi shiru"
Bata ce mishi komai ba ta cigaba da rera kukan ta.

Mikewa yayi yace "Shikenan tunda ban kai matsayin da Zaki fad'a min matsalar ki ba na kyale ki, sannan yanzu nasan matsayina a wurin ki" har yasa hannu zai bud'e kofar d'akin yaji saukar Muryar Tace "Yaya kayi hakuri"
Murmushi yayi yasan hakan ne kad'ai zai sa ta kula shi, kin juyo wa yayi jin ta nufo shi ya had'a raai kamar bai tab'a dariya ba Tace "Yaya na"

Joyowa yayi Yana kallon ta , kanta a kasa tana wasa da yatsunta yace "Uhmn ina jinki?"

"Kayi hakuri Dan Allah"
"Hakurin me Kuma? Ni baki min laifi ba, kawai dai yanzu nasan matsayina a wurin ki Ni ba komai bane a wurin ki"
"Wallahi Yaya ba Haka bane ba , wallahi bayan mummy da daddy bani da Wanda ya fika a wurin Kuma Kai ma ka sani"

"In da hakan ne kamar yanda kikace ai da zaki fad'a min matsalar ki, da Allah fa nake ta had'a ki tun a hanya Amma kin ki kulani Kuma a hakan Zaki wani cewa ina da matsayi a wurin ki? In dai da Gaske ki ke ki fad'a min abinda ya same ki"

Turo baki tayi Tace "Ba Kai bane"
"Bani bane me?"
"Ai Kaine ka shanyani nayi ta jiran ka, ga Rana"
Murmushi yayi ya jaa hancin ta yace "yanzu dama don wannan ne kike uban kukan nan?"

Ka ta d'aga Masa alamun eh, yace "Ai Saida nace miki kizo Kika ki zuwa, abinci fa nake ci princess, Amma kiyi hakuri na Miki laifi" yasa hannun sa biyu ya rike kunnuwan sa, Murmushi kawai tayi yace "Kin hakura? Idan baki hakura ba bazan sake kune na ba"

"na hakura"
Ajiyar zuciya yayi yace "Kai na gaji"
"Laa d'an rike kunnen ka da kayi da bai Kai minti d'aya ba har ka gaji?"

" Eh Mana da wahala fa"
Dariya tayi harda tafi Shima dariyar ya shiga yi yace "Zo mu je dining nasan princess d'in yayanta tana jin yunwa"

Tace "kamar ka sani Yaya"
Shima yace "Kamar ka sani Yaya" Yana kwaikwayon Muryar ta.
Dariya sukayi a tare suka fita, shigan su parlor yayi dai dai da shigowar mummy parlor baki a bud'e take kallon su suna Hira suna dariya Mummy Tace "Ahaaaf ni da sani za'a Rina ai, mutum ya shiga tsakanin ku kunya zaiji"

sosa keya yayi yace "Mummy in gaya miki da kyar da makerkyasa na rarrashe ta"
"Uhmnn to maza je ki d'auko mayafin ki mu je saloon d'in"

Cikin Muryar Shagwab'a Tace "A a mummy sai kun dawo Yaya zai kaini"
Mummy Tace "Kinci gidan ku ja'ira kawai Ni Zaki jawa raai" tsaki tayi ta fice a hanyar ta tafita suka had'u da umma hakan yasa suka juya kawai hannu Ma'isha da Haisam suka d'aga musu suna a dawo lafiya.

Mummy Tace "Yaran Nan sun maida mutane kamar kakannin su" Umma Tace "Bakamar Haisam bama sai a hankali"
Mummy Tace "Kin samin son a gaba wallahi ke Sam bakya ganin laifin yarinyar Nan ko kad'an"
"Hmm Hajiya Kenan ai ni gaskiya nake fad'a ke dai da son d'a ya rufe Miki Ido bakya gani" a haka suna Hira har suka Isa parking lot already dama driver yasan da fitan su yana hango su ya fito da motar a baya suka zauna, ya Danna wa motar key suka wuce saloon.

Haisam da Ma'isha suna zaune a dinning tana cin abinci shi Kuma sai tad'i yake ta mata tana ci tana dariya har kamar zata kware,kwasam wayaey sa ta fara ringing hannu yasa a aljihun rigar sa ya zaro wayan ganin sabon number yasa bai d'auka ba, sai da aka sake Kira a karo na biyu yayi picking sallama yaji jin Muryar mace ya sa shi tunanin Wace ce wannan da zakin Muryar da bai tab'a jin irin ta ba, a ransa yake ayyana hakan, ta sake sallama a karo na biyu ya amsa bayan sun gaisa daga d'ayan 'bangaren Tace "Ka gane mai magana kuwa?"
Yace "A'a " a takaice.

Murmushi tayi Wanda Yana iya jinsa Tace "Nice na karb'i number ka d'azu a Cafeteria d'azu, ka tuna"
Yace "Eh na tuna, ya kike? "
Tace "Lafiya, idan baza ka damu ba Dan In na so muyi wata magana dakai idan baka komai?"

" For now am busy gaskiya sai zuwa anjima when am less busy I'll call you"
Tace "promise?"
" Yeah Insha Allah"
"Okay sai na jika"
Kiit ya katse wayar, tunda ya fara wayan hankalin Ma'isha yake kansa Tace "Yaya who is that?"
Yace "A friend"
Tace "Okay"
Yace "Yau ina Baki Labari........ "
Nan suka cigaba da hirar su Saida ta cita koshi suka koma parlor suna kallon favorite series d'insu a zeeworld Mai sun I Do.
___________________________
Ina barar addu'ar ku fansa ina cikin wani yanayin da yake hanani komai hatta typing ma shiyasa kuka jini shiru.

Please Comment
Share
Milhat ce
Yar Terawa

🍃 *DANGIN UBANA*🍃

Story & Written
By

Milhaart

Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne.

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________

*Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.*

Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

Page

17and 18
Haisam da Ma'isha kallo suke hankali kwance har Saida aka Fara kiraye kirayen sallar maghriba, mikewa yayi ya kashe TV turo baki tayi Tace "Yaya meyasa zaka kashe min Kallo na?"

"Lokacin sallah yayi baki ji ana Kiran sallah ne?"
"To ai Ni bana sal...... " Sai kuma tayi shiru ta kasa karasa maganar dariya yaso yi sai Kuma ya matse yace "karasa abinda zakice bakya me?"
Mikewa tayi da sauri ta nufi d'akin ta tana dariya kasa kasa,dariya yayi ya kad'a Kai yasa Kai zai fita knn sai ga shigowar su Mummy, d'an Jaa da baya yayi ya basu wuri suka wuce Yana fad'in "Har kun dawo?"
Umma Tace "harne? Bayan munfi 2hours"
Yace "Naga kunyi sauri ne ai"
Mummy Tace "Son ana Kiran sallah kana Nan kuna ta aikin surutu ko?"

Murmushi yayi Yana Jin dad'in yanda mummy ke nuna kulawa a garesa tamkar ita ta haife shi yace "Yanzu Masallacin nayi"
Tace "To a dawo lafiya"
Ya amsa da "Ameen"
Sai yayi ficewar sa.

Ma'isha na shiga d'aki ta kwana abinta ta d'auki wayarta tana chatting da kawayen ta, Bata fito parlor ba har sai da ta ji shigowar Daddy, da gudu ta fito tana Masa sannu dazuwa.

Daddy yace "Daughter baki san kin girma bako, ya kamata ki rage Shagwab'ar nan Haka"
Chapter 9 · 0% Book details