← Book details Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 55

Sashe 27

Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ma'isha sai da gari ya Waye kana ta farka, mikewa tayi ta Shiga ban d'aki ta wasa ruwa    kana ta d'auro alwala Sannan ta Shiga jero sallolin da ake binta, Bayan ta idar ne ta sauko parlor Jin muryar su Mummy a dinning room ne ya sa ta nufi gun, da sallama ta karasa inda suke ta jaa kujera ta zauna dukkanin su kallon ta suka Shiga yi cike da mamaki Umma tace "d'azun Nan fa na leke ta tana bacci, Amma gashi ta fito."

Abba ne cike da kulawa yace "Daughter ya jikin naki?"
Ta amsa da "Sauki Alhamdulillah"
Daddy yace "Sannu daughter"
Ta amsa da "Yauwa nagode Daddy."

Mummy mikewa tayi ta shafa kanta had'e da tab'a wuyan ta Tace "Jikin naki da d'an zafi har yanzu"
"Uhmn da sauki mummy"
Haisam kuwa gyaran murya yayi yace "Princess ya jikin naki? Da fatan bakya jin komai yanzu?"

Kirkirerren Murmushi tayi kana tace "Eh bana jin komai , sai Kaine da yake d'an sarawa kad'an kad'an"
"Allah ya sauwaka, shima zai daina a hankali."

Duk suka amsa da "Allah yasa"
Kallon Mummy Ma'isha tayi Tace "Mummy nima a Samin abincin"
Jika na rawa ta sa mata abinci, kallon ta suka tsaya yi Murmushi tayi Tace "Dan Allah ku daina kallo na haka sai ku sa na kware."

Haisam yace "Ai Dole ne mukalle ki, Duk da Yan kwanaki kikayi bakya cikin mu, ji muke Kamar shekara kikayi" ya maida kallon sa ga su Umma ya d'aura da fad'in "Ko ba Haka ba" Umma ta amsa da hakane, dariya sukayi suna ta hirar su, dukkanin su sunji dad'in ganin Ma'isha a haka.

Sai da aka Fara kiraye kirayen sallar azahar ,Duk mazan Suku fice zuwa Masallaci, Bayan sun idar da sallar kuwa asibiti suka nufa, Haisam office d'insa ya bud'e musu suka zauna kana ya fita, bai wani dad'ewa ba suka ya Shigo Meerah kuwa na biye da shi.

Har kasa ta durkusa ta gaida daddy ne yace "Tashi ki zauna" Yana nuna mata kujerar dake fuskantar su, Bayan ta zauna ne ya Fara magana yace "Meerah nasan Daughters bata da kawar da ta wuce ki, sannan nasan kin San sirrukanta Dan Allah ina so ki fad'a min abinda Kika sani game da Wanda take so"

Kai ta d'aga ta kalle shi kana ta maida kanta kasa Tace "Daddy ban sani ba, ban San Wanda take so ba"
Abba yace "Please ki fad'a Mana gaskiya nasan Dole Akwai abinda Kika sani akai"

Meerah har cikin ranta take so ta Sanar dasu gaskiya Amma idan ta tuna alkawarin da tayi wa Ma'isha sai ta fasa Tace "Abba da na sani wallahi zan fad'a Muku"

Haisam ransa ya yi mugun 'baci cikin 'bacin Rai yace "Wallahi karya take Daddy, da kunne na fa naji lokacin da suke maganar Amma yanzu Kuma don ta Raina Mana hankali tace bata sani ba"
Daddy yace "Son calm down"
Abba yace "Kinji ko Ameerah, Dan Allah ki fad'a mana wane ne, kece kad'ai zaki taimaka Mana wajen sama wa zuciyar ta abinda take muradi"
Shiru tayi tana matsar kwalla, a tsawace haisam yace "Shegen taurin Kan tsiyane da ita, ranar babu yadda banyi da ita ba Akan ta fad'a Min Amma taki, na rantse da Allah idan wani abu ya sami princess...... "

Daddy ne ya d'aga Masa hannu yace "Ya Isa , ya Isa " mikewa yayi ya kalli Abba yace "Mu tafi ko?" Abba Rai ba dad'i ya mike yana girgiza Kai, Sai da suka Isa kofar fita, Abba ne ya juyo ya kalle ta yace "ki yiwa girman Allah ki ceci rayuwar Isha wallahi tana cikin wani matsanancin hali dan Allah ki fad'a mana gaskiya wane wannan wanda Isha take so a ina yake kuma d'an waye?"

Cikin Muryar kuka Tace "Wallahi ban sani ba,da na sani da na fad'a Muku"
Girgiza Kai Daddy yayi yace "Allah shi kyauta" suka fice Haisam Rai a 'bace yace "Tirrr da qawa irin ki, Wallahi ko kaffara bazan yi ba kin San komai"
"Ya Haisam ban....... " A tsawace yace "Get out of my office" a tsorace tayi hanyar fita sai da ta kusa fita yace "Kuma ki sani idan wani abu ya same ta kece sila" cikin kuka ta fice.

Tana fita shima ya fita, rufe kofar office d'in yayi ya nufi gun su Daddy dake tsaye a jikin motar sa suna jiran sa , hakuri ya basu Duk suka shige motar suka koma gida, Bayan ya ajiye sune ya koma office don cigaba da aikin sa.

Daddy da Abba ganin Isha na walwala hakan yasa suka d'an ji dad'i, ta wuni cikin farin ciki sai fara'a take,Nan suka Cigiba da shirye shiryen biki, Isha kuwa Duk lokacin da ta Shiga tashin hankali sai ta Rika ambaton '''la'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu Minal zalimin''' hakanne yasa ta ji sauki abun Sosai.

Rana bata karya sai dai uwar d'iya taji kunya, yaune ranar da Haisam da Aysha suke jira, shine ranar da yafi shekaru har hud'u yana jiran wannan ranar, Bayan sallar jumma'a za a d'aura auren amma a kofar gidan su Aysha za a d'aura dalili kuwa shine mahaifin Aysha ne ya bukaci hakan.

Bayan sallar jumma'a jama'a sun taru, ga Nan waliyin Ango Amma babu waliyin amarya, Abba ne ya bukaci da a d'an jira su, wurin shiru yayi kwasam suka jiyo horn d'in mota da gudu motar ta karasa rumfar da Mutane suke zaune, Kura motar ta tada mutanen daga masu Allah ya wadai sai masu zagi, sai wa'anda Kuma suke kokarin toshe hancin su.

Kowa hankalin sa a Kan motar take kowa son ganin Wanda ke cikin motar suke son gani, ai kuwa Mahaifin Aysha suka gani da Kanin sa, inda su daddy suke suka zauna, Haisam kuwa fararen jamfa da garen sa Sannan kansa bakar hulace Kamar yadda takalmin sa yake Baki,sai baza kamshi yake,  Murmushi yake abokanan sa na tsokanar sa babu ma Kamar Farukh, Malamin da zai d'aura auren ne yayi hamdallah zaiyi magana mahaifin Aysha ya dakatar dashi malam yace "Lafiya dai ko?"
Ya amsa da "Uhmn lafiyar Kenan Akwai Wanda ya kamata ku gani kamun a d'aura auren na"
Abba yace "Wane ne? Kuma yana ina?"
Hannu ya d'aga ya nuna Masa jikin motar, Haisam, Abba da Daddy naga sun mike Daddy ne yace "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un"
_____________________________
Naji dad'i Sosai da addu'oin kuyi hakuri ban samu damar muku reply ba nagode Sosai Allah ya saka da alhairi.

Please comment and share

🍃*DANGIN UBANA*🍃

Story & Written
By

Milhaart

Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne.

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________

*Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.*

Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

Page

41&42
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._

_Continuation........_ Abba kallon su Daddy yayi ya dafe kafad'ar sa had'e da fad'in "Yaya Lafiya naga Duk kun rud'e"
Haisam cikin rawar murya yace "Kanin Mahaifiyi na" a dai dai lokacin Malam ya iso Haisam karo zaro idon sa yayi da ganin Aysha a bayan sa, cikin kid'ima yace "Habibty dama kin San shine?"

Yar karamar dariya tayi tace "Na San shi mana"
"Amma.... Amma ta yaya? Kin San shi Kuma baki sanar dani ba? Why?"
"Yaya Haisam kenan, Dole na sanshi sabida jinin sa ke yawo a jinin jiki na"
Tana maganar tana kallon jikin ta, Haisam kama baki yayi Nan da Nan zufa ya keto masa yace "Kina nufin...."
Tayi saurin katse shi da fad'in "Eh mahaifina ne, Nayi mamaki da ba ka gane kanwar ka ba"
Zaro Ido yayi waje yace "Ayrah!!!

Dariya tayi Tace "Yaaap you got it right, d'azu ka tambayeni meyasa ban fad'a maka na San shi ko?" Shiru yayi Yana kallon ta bashi kad'ai ba kowa da kowa na son Jin dalilin ta, gyaran murya tayi Tace "To ga amsar ka Nan, nayi hakan ne saboda na karya maka zuciya, na sa maka soyayya ta a ranka sabida na ga bayan ka"

Idon sa fal da kwalla Yana Fara magana suka fara gangarowa yace "Amma me na miki what have I done to deserve this?"
"Oh so you don't know? Kar ka rainawa kan ka hankali mana don't act innocent"

Murmushin gefen baki Malam hassan yayi yace "Just tell him Yar daddy, fad'a masa ya kamata ki tunatar dashi"
"Toh daddy" kallon ta ta maida ga Haisam Tace "Dr Haisam, wannan shine sakamakon tozarta mahaifina da kayi ka kwace Masa dukiyar sa sabo son zuciya irin naka"

Daddy Rai a 'bace yace "Dukiyar sa? Ko Kuma dukiyar Haisam?" Kallon mallam Hassan yayi yazo ya tsaya gaf dashi yace "Bayan ka kashe shi yanzu Kuma so kake ka kashe d'an sa?"
Chapter 27 · 0% Book details