← Book details Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 55

Sashe 30

Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsaki Mamy taja Tace "Kuka ba? Baki ga komi ba tunda kin biye wa ubanki zaki ji dashi" tana Kai Nan ta fita, Mardiya ce tayi ta rarrashin ta tana Jin jina lamarin tabbas mahifin Ayrah abun tsorone.

Ayrah tun daga Wannan ranar ta Shiga tashin hankali mara misaltuwa tundaga wannan ranar take kiran layin Haisam Amma baya Shiga tayi kuka tayi kuka har ta godewa Allah.

Yau ta kudiri aniyar ko ta halin Kaka sai ta ganshi, har asibitin da yake aiki taje aka tabbatar mata da bayi da lafiya, jiki ba karfi ta fita a hanyar ta ta fita sukayi kicibus da Farukh.

Farukh na ganin ta ya kawar da kansa Kamar bai tab'a ganin ta , da sauri ta bi Bayan sa tana Kiran sunan sa baiyi niyar kulata ba ganin yadda take kiran sunan da ya ja attention d'in Mutane yasa ya tsaya, kallon ta yayi kana ya kawar da kansa had'e da fad'in "Lafiya kuwa kike ta bina?"

"Am Lafiya lau dama Kaima anan kake aikine?"
Kallon ta yayi yasa hannu a aljihun wandon sa kana yace "umm umm a specialist nake, tambayar Nan ce ta sa Kika tsayar Dani?"
Jiki a Sanyaye Tace "A a dama ina Kiran layin sa ne baya Shiga shine nazo neman sa aka ce min bayi da lafiya me ya same sa ne Haka?"

Ciza leb'en sa yayi cike da takaici yace "As if you care ta ina ruwanki da lafiyar sa bayan burin ki Kenan? To Haisam ya Shiga comma a dalilin ki kinyi farin ciki ko? Mtswww" ya tafi ya barta a tsaye a gun baki a bud'e.

Ta dad'e a tsaye a gun kana ta wuce gidan su mardiya ta sanar mata da halin da Haisam ke ciki "tab wai yanzu a dalilin ku, a gaskiya Wallahi Allah bazai bar ku ba, idan kuma ya Rasa ransa a dalilin ki kema kin Zama Kamar mahaifin naki"
"look mardiya nasan mahaifina ba mutumin kirkii bane ba, Amma that's not give you the right to disrespect him kin gane ko"
"Am sorry am sorry abun ne ya dameni, yanzu mene ne abinyi?"

Cikin Muryar kuka Tace " I don't know, I don't know am in a mess Wallahi, idan Haisam bai yafe min ba Nima bazan yafe kaina ba"
"kiyi ta istigfari Sannan muyi fatan Allah ya bashi Lafiya, kin san fa Allah ba ya yafe laifin wani wa wani"
"Ba Wannan ba, asirin Nan nake so a karya shi, don kin San Boka yace bazai tab'a daina Sona ba har ya mutu sai dai idan Mun tone abinda muka binne"
"Ta kwana gidan sauki sai muje mu cire shi"
"Shikenan hakan za'a yi zamu had'u gobe Insha Allah"

Ta Mike kana ta Tace "Ni zan tafi sai anjima Amma Banga Mama ba bata nan ne?"
"Eh sun fita da Ya Ma'aruf"
"Oh Ya Ma'aruf d'in kin Nan yaki aure ki had'a ni dashi Mana"

"Taaab d'i"
" Me na wani tabd'i?"
" umm babu babu muje na raka ki" a zuciyar ta Kuma Tace "Allah ya sauwake mu had'a jini da ke"

Har jikin motarta ta raka ta, sai da taga fitar ta ta koma cikin gida.

Ma'isha tundaga Wannan ranar kullum a asibiti take kwana take ta wuni idan ta koma gida to dalili ne Mai karfi dake a kwai bathroom na staffs hakan yasa ta kanyi wankan a Chan Amma ta fiye yi a gida, Bayan likitocin dake kula dashi ita kadaice ake bari ta Shiga kansa Nan ma sai ta sa wani irin rigar Wanda baya Kara dama an tanadar dashine sabida Shiga ICU sannan suna da takalmi na musamman idan ta Shiga takan d'auka wa Umma hoton sa ta tura mata ko kuma in taje gidan ta nuna Mata.

Duk sanda ta Shiga gunsa idan ta fito Sai tayi kuka, ga Nan mutum amma ba Hali yayi magana.

Kwan a tashi asarar Mai Rai, wasa wasa Haisam ya kaie shekaru har biyu bai tab'a motsi ba.

Daddy,mummy da Ma'isha ne zaune a parlor, gyara Zama Daddy yayi yace "Daughter na Kira ne don ina so muyi wata muhimmiyar magana"
"Toh daddy ina sauraron ka"
" Yaron Nan Ma'aruf magabatan sa sun Zo nema Masa auren ki Amma nace sai na ji ta bakin ki tukunna, kina son sa?"

Ma'isha ji tayi gabanta na duka uku uku baki na rawa Tace "Daddy aure Kuma?"
Mummy Tace "Eh Mana Ma'isha so kike mu zauna mu zuba miki ido kina abinda Kika ga Dama? Isha idan ma bacci kike ki farka kina neman kusan shekaru 29 a duniya Amma har yanzu kin kasa fidda miji Kuma bawai kin rasa mane ma ba"

Cikin Muryar kuka Tace "Mummy ni gaskiya ban shirya aure yanzu ba"
Mummy Tace "Kana ji ko Alhaji, kana ji ko? Yarinyar Nan so take ta jaa Mana zagi a gari shiyasa tun farko nace ba sai kaji ta bakin ta ba asa rana kawai"
"Hakane Hajiya sai yanzu na fahimci abinda Kika hango sabida haka Isha zan sa ranar auren ki da Ma'aruf Nan da 2 weeks ki Fara Shiri" Yana Kai Nan ya mike ya Shiga d'akin sa Mummy ma ta Mara Masa baya suka barta a zaune a gun ta rasa me ke mata dad'i abin duniya Duk ya bi ya ishe ta.
____________________________
Please comment
Vote
And share
Milhaat ce
Yar Terawa
[7/6, 1:26 PM] Miilhaat: 🍃 *DANGIN UBANA*🍃

Story & Written
By
Milhart

Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne.

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*

*Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.*

Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️

*BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM*

Page

45&46
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._

_Continuation........._ jiki ba karfi Isha ta fita, asibiti ta nufa Wanda shine ya zame Mata wurin wuni da Kuma Kuma kwana ko da kuwa ranar aikin tace ko ba ranar aikin ba achan ta ke Zama, Bayan ta Isa asibitin ne ta tarar da Meerah ta tashi, Isha hannun Meerah ta rike suka fita waje suka zauna a inda ba hayaniya Sosai Tace "Meerah ina cikin matsala Ina cikin tashin hankali"
"Kwatar da hankalin ki ai ko baki fad'a ba na fahimci hakan a tattare dake, Amma me ya Faru?"

"Uhmn Daddy ne Wallahi"
"Me ya sami Daddyn?" Cike da kulawa Meerah ke mata tambayar.
Isha Tace "Daddy wai aure zai min Nan da 2 weeks"
Murmushi tayi had'e da fad'in "Alhamdulillah Kai Amma naji dad'i Wallahi"
Wani irin Kallo ta mata Meera cikin rashin fahimta Tace "ikon Allah Wannan mugun kallon fa, nifa ina Taya ki murna ne"

"Zaki taya ni murna ne only if am happy with it"
"what do you mean if you're happy wi.....? Hold on kina so kice min bakya son auren ne, nasan Babu Wanda daddy zai aura miki a yanzu da ya wuce Ma'aruf"
"Bana farin ciki gaskiya Kuma eh Ma'aruf d'in ne"
" Meyasa bakya farin ciki?"
"Sabida bana son auren nan ke Kanki kin San Wanda nake so ba Ma'aruf ba, and yanzu fa Dole zasu min" ta karasa maganar tana matsar kwalla.

"Isha Kenan ke ma kin Samu zakiyi auren Amma Ni Kuma fa tunda na rabu da wannan d'an iskan shiru babu Wanda naga ya kwanta min"
"Uhmnn kefa issue d'inki daban nawa daban, yauwa that reminds me, ya maganar Farukh ne Kam?"
"Wai kina nufin Abokin Ya Haisam"
"Eh Mana Akwai wani Bayan shine"
"Yana nan kin San ya dage sai dai ya turo gidan mu"
"Then what are you waiting for? Then ki turashi Mana"
"Banfa Gama sanin wane ne shi ba tukunna so Ina bukatar lokaci gaskiya"

Zaro Ido Ma'isha tayi Tace "Wani irin sani kike bukata yau kusan 3 years Kennan fa da kwanciyar ya Haisam Kuma tun lokacin kuka fara Soyayya, ke dai kice bai miki bane kalas"
"Ba haka bane kin San ai gayen ya had'u ban San meyasa na kasa bashi dama ba"
"a gaskiya ki cire Duk wani kokonto Wallahi Yana da kirkii Sosai"
"To Shikenan inshallah zan duba na gani, Amma seriously Isha Kar ki tashi hankalin ki Akan maganar auren Ma'aruf Wallahi yana sonki"

"nifa bana son shi kin fi kowa sanin hakan, Haisam nake so kuma sho zan cigaba da so"
"Haka zaki zauna kina jiran ranar da Haisam zai farka? Kin San ranar da zai farka ne? Kibe abinda su mummy sukace shine kad'ai kwanciyar hankalin ki"
Ajiyar zuciya tayi Tace "Hakane I always have faith in Haisam will wake up sooner or later but it seems like...... " Kuka ne ya ci karfinta ta kasa karasa maganar dake bakin ta, Nan Meerah tayi ta rarrashin ta, sai da tayi ta bata baki har hankalin ta ya kwanta suka rabu.

"Mamy Dan Allah horon yayi yawa Dan ki yi hakuri ki yafe min"
Kallon ta tayi kana Tace "Ayrah na fad'a miki ba sau d'aya ba sau biyu ba, baza ki tab'a samun sakin fuska daga gareni ba har sai Haisam ya farka sannan ya yafewa miki, nifa baki min laifi ba"
Chapter 30 · 0% Book details