Sashe 21
Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Murmushi Haisam yayi Wanda yake Kara bayyana kyawun fuskar sa yace "Mummy yanzu dama Akan wannan ne kike kuka Duk kuka tashi hankalin ku? Ni a ganina wannan abun ba abin tashin hankali bane ba, zanyiwa Umma magana Kuma Insha Allah zata amince, ko ba komai ai abun farin cikine wannan duba ga irin tsawon shekarun da Abba ya d'eba bayi da niyar aure ace Rana d'aya ya ce zaiyi, Kuma na tabbata Insha Allahu Abba zai rike ta da zuciya d'aya sabida na lura Shima Yana da son Mutane Shima kamar daddy, insha Allah zata amince fatan mu shine Allah ya tabbatar da alhairi"
"Kaai Amma naji dad'in maganganun ka son, Allah yasa ta amince d'in"
"Ameen Mummy"
Ma'isha da tun d'azu take kallon su Tace "Ni Idan akayi auren Nan ai barka na sabida Abba na auren mummy gidan su zan koma da Zama in huta da....... " Turo kofar da akayi ne da d'an karfine yasa ta kasa karasa maganar ta Duk su ukun suka Mike a razane mummy baki na rawa Tace "Al.... Alh..... Alhali Lafiya? Tana leka Bayan sa ganin ba kowa ta cigaba da magan "Alhaji Lafiya na gan ka a Haka?"
Rai a mugun 'bace yake nuna ta da d'an yatsa Yana fad'in "Haven't I warned you not to talk about it again? Haven't I?"
"Alhaji Amma...... "
"Shut up!!! Amma me? Nace amme? Akan me Zaki zauna kisa yaran Nan a gaba kina fad'a musu abinda bai shafe su ba iyee? Answer me?"
Mummy kasa magana tai ta sunkuyar da kanta a kasa tana kuka Mai cin Rai Duk yanda taso ta Hana kukan ta ta kasa sabida yanda daddy ya ke mata tsawa da fad'a a gaban yara, da su ya sune abun Sam bazai Dame ta ba.
Ma'isha Murya na rawa Tace "Daddy please Daddy kayi hakuri wallahi ba laifin mummy bane mune muka sata a gaba Dole tasa ta fad'a Mana, Kuma....... "
"Ma'isha!!! Ya Kira sunan ta a wani irin Murya Wanda hakan yasa ta rike bakin ta da hannun ba tare da tasan tayi hakan ba, ba tare da ya kalleta ba yace "Idan na Kuma Jin bakin ki a wurin Nan sai na 'ballaki"
Ya cigaba da fad'in "Taya za'a yi ni da gida in kafa doka Amma ki take shi? Yaushe Kika Zama Haka Maryam?"
Haisam cikin girmawa yace " Daddy please kayi hakuri Dan Allah Ni a gani na wannan abun ba abin tada hankali bane ba, yes kamar yadda princess Tace mune muka Masa wa Mummy Akan ta fad'a maana abinda ya faru sabida d'azu a gabana naga kana Mata fad'a, abinda ban tab'a gani ba Kennan tunda na dawo gidan, ta fad'a min ne sabida tasan Idan nayi wa Umma magana zata amince, sannan Abba nasan Idan hakan ta kasance zaka fi kowa farin ciki, Amma Dan Allah kayi hakuri"
Shiru Daddy Yana sauraron sa jikin sa Duk yayi sanyi, tabbas maganar Haisam hakane zaifi kowa farin ciki sannan idan Haisam yayi wa Umma magana babu Makawa zata amince, shiru d'akin yayi na d'an wasu lokuta Banda kukan mummy da na Ma'isha babu abinda ke tashi a d'akin jiki a sanyaye Daddy ya nufi inda Mummy me tsaye tana matsar kwalla, bai tsaya 'bata lokaci ba ku Jin kunyar su Haisam ba ya rungume ta Sam a jikin sa Yana d'an bubbuga Bayan ta a hankali, yace "Am sorry Maryam, am sorry please wallahi raina ne ya 'baci jin kalaman Zainab a Jan d'an uwana Sai na kasa jurewa yanda na ga ta ki Abdallah karara naji zafi sosai da kalaman ta, Amma bani da ikon da ita bazan iya tirsasata ba, na d'au lokaci Mai tsawo na ganin irin wannan ranar da Abdallah zai kawo min maganar aure, nayi matukar murna sosai Allah Allah nake na dawo gida don Jin labari Mai dad'i sai Kuma najie akasin hakan, ke Kuma da na hanaki magana akai sai Kuma Kika ki jin magana Amma maganar da Son yayi sai na gane kuskure na" d'an d'ago Kan Mummy yayi yasa hannu Yana goge mata hawaye yana fad'in "am sorry am sorry"
Haisam d'an Buge kafar Isha yayi da kafar sa ta juyo ta kalle sa murya kasa kasa yace "Kinga ko mijin ta ya rarrashe ta,Yana share Mata hawaye ta daina kukan, gwamma kiyi shiru don ba Mai rarrashin ki anan"
'dan Buge shi tayi da kafan ta yana gumse dariyar da ke kokarin kwace Masa.
Mummy zare jikin ta tayi a hankali daga jikin daddy tasa Bayan hannun ta, ta share hawayen ta kana ta gyara murya Tace "Son kaci gidan ku" Kama baki yayi yace "Laaaa Ashe ta ji" da gudu ya fita isha ta Mara Masa baya, Tace "Ja'irai kawai" suka bar daddy dashi da Matar Nan, suka Shiga soyewa abinsu.
Haisam da Ma'isha kuwa a parlor suka zauna Banda dariya babu abinda suke yi, su Haisam harda rike ciki itama Isha dariya take sosai ba kakkautawa tana cikin dariyar ne kwasam ta Mike a zabure ta wuce d'akin ta da gudu, Haisam kuwa baki ya sake Yana kallon ta har ta haura d'akin ta sai da yaga ya daina kallonta kana ya kawar da kansa Yana mamakin Shagwab'a irinta Ma'isha , a bayyane yace "Mutum bata da aiki sai kuka"
Ma'isha kuwa tana Shiga d'akin ta ta had'a kai da gwiwa ta fara rera kuka son ranta, tunawa tayi da Haisam na son wata ita ba, yanzu duk dakon soyayyar sa da ta dad'e tana yi ya tashi a banza Kenan?
Karar shigowar Kira taji ya shigo wayar ta mikewa tayi ta duba fuskar wayar ta ganin sunan Meerah yasa ta daina kukan ta yi picking ba tare da Tace komai ba, Meerah Tace "Hy Isha kin koma gida kalau, da fatan kinsha maganin da muka saya d'azu?"
"Nikam Na manta da wani magani" a ranta ta ayyana hakan Amma a bayyane Kuma Tace "Uhmmn Nasha"
"Subhannallah Isha kuka kikayi yana ji muryar ki haka Lafiyan ki kuwa?"
"Uhmn Lafiya na Lau daga bacci na tashi"
"oh sorry na tashe dama so nake na ji ko kinsha maganin nakin gudun kar jinin naki ya sake Hawa"
"Kar ki damu Nasha"
"Tohm Shikenan zan Zo gobe Insha Allah na gwada BP naki ko ya sauka, da fatan baki da Lectures gobe?"
"Akwai But da safe ne zuwa la'asar zan dawo"
"alright sai mun had'u goben please take care"
" Insha Allah thank you" a tare suka katse wayar d'ago kanta da tayi ta sauke kanta a Kan haisma da tun da ta Fara wayar Yana tsaye Yana kallon ta, Murmushi tayi Tace "Yaya ka Shigo Mana"
Girgiza Kai yayi yace "Ba Zama ya kawo ni Nan ba, Princess meyasa ki kuka? Kuma ke da wa kike waya naji kina maganar kinsha? Me ke damin ki baki da lafiyane?"
Yar karamar dariya tayi Tace "Yaya irin wannan tambaya haka wanne zan amsa a ciki?"
"Dukka" ganin ba wasa a fuskar sa Tace "Uhmn dama kaina ne yake ciwo"
"Uhmn sai akayi Yaya? Da wa kike waya?"
"Ameerah ce dama da naje gidan su ne, saai.... Umm kaina ya Fara ciwo shine ta bani magani Nasha Akan in na dawo na Sha, shine ta Kira taji ko Nasha"
"Toh naji shi Kuma kukan na mene ne?"
"umm... Ummm..... Kai na.... Kaina ne yake ciwo"
"Ciwon Kan ne ya saki kuka?"
Kai a kasa ta amsa da "Eh shine" ganin ya kure Idanun sa yana kallon ta Yana kokarin gaskata maganar da.
"Ya ciwon Kan, kin Sha maganin?"
"Eh Nasha"
" Alright, sai ki samu ki kwanta kar na Dame ki, good night" ya jaa kofar ya rufe Mata bai tsaya Jin abinda zata ce ba.
Ajiyar zuciya tayi Tace "That was closed I thought yaji" girgiza Kai tayi ,ta Shiga ban d'aki ta yi wanka tana fitowa ta Sanya sleeping dress d'inta ta kwanta sannan ta kunna datarta, ta Shiga WhatsApp, ganin Haisam a online yasa ta Masa "Hy Yaya ba kayi bacci ba?" Sai da ya d'auki kusan 5 minutes kana ya mata reply da "Eh banyi ba me ya hanaki bacci?"
Emoji na kuka ta jero masa had'e da tura masa "Sai yanzu Zaka kulani?"
"am sorry Video call muke da auntyn ki"
Tana bud'e wa ta kashe datar ba tare da ta Masa reply ba, ta gyara kwanciyar ta tana ta tuna abubuwa dayawa daga bisani bacci yayi awon gaba da ita.
```Washe Gari```
Haisam ne ya Shigo ya tarar da mummy da Daddy a parlor suna karyawa gaishe su yayi suka amsa kana ya tamabaya Ma'isha fa.
Mummy ce ta amsa Masa da "Bata fito ba kana da Lectures ne?"
"Eh Umma Lectures na karfe takwas nake dashi" ya maida kallon sa ga daddy yace "Daddy naga jaka tafiya zakayine?"
"Eh son zani abuja zanyi 3 days a Chan"
"Gaskiya daddy sun sa makan Kai a gaba Sam baka Zama Ni na manta ranar ma da kayi one week a gida"
Dariya yayi irin tasu ta manya yace "To ya zanyi Dole ce tasa"
Haisam ya ce "Hakane Allah ya dafa maka daddy"
"ameen son Mike ka Duba ta kar ku makara, mikewa yayi da sauri ya haura sama, a hankali ya tura kofar had'e da lekawa ya hango ta Akan gado ta na sharar baccin ta hankali kwance, a bayyane yace "lallai yarinyar Nan"
Ban d'akinta ya Shiga ya bud'e tap ya d'an Tara da hannun sa ya fito ya watsa Mata a fuska a razane ta farka tana ambaton sunan Allah ganin Haisam yasa Tace "Haba Yaya me Haka" ta koma ta kwanta.
"Princess ya haka baki da Lectures ne ki tashi please Karki makarar da mu"
Ido a rufe ta amsa Masa "Sai 10 kaje kawai sai anjima zan Shigo"
'daga kafad'a yayi ba tare da yace Mata komai ba, Yana fita yaga mummy na shigowa ciki yace "Har ya tafi?"
"Eh "
"Allah ya tsare, sai na dawo" ta amsa da "a dawo Lafiya"
Ya shige motar sa ya fice daga gidan ya wuce school.