← Book details Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 55

Sashe 46

Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mamy yarfa hannu ta Shiga yi ta Kama habarta Tace "Oh Allah, Allahumma Ajurni fii musibati, Kinga rayuwar Nan ko, ita fa da Ayrah suka had'a Kai suka cutar da Yayan ku Haisam sabida hud'ubar uban ku, gashi duk Allah ya soma nuna musu ikon sa"

Nabila "uhmmmn" kawai tace..
Mamy Tace "Kira Mardiyar muji ko suna tare"
"To Mamy"

Ta Shiga Kiran layin Mardiya, mardiya naji wayan ta ya Fara ringing tayi Tsaki bata Duba wayar ba bare tasan Wanda ke Kiran an Kira har sau biyu na ukun ne tace "mtsww Wane ne hakane?"

Ganin sunan mardiya ya bayyana a fuskar wayarta tayi saurin d'agawa, ta'aziyya ta mata kana ta tambaye ta ko suna tare da Ayrah.

"A'a bata Zo ba, nayi tunaniin ma bata ji abinda ya faru bane ba"
"A a taji, har ta fita da motar ta Akan zata je gidan naku"
"okay bata iso ba maybe tana hanya ne"

"Anya kuwa tun fa lokacin da abin ya faru ta fita, ai ko barin gari zata yi Albarka"
"Hakane Kam, Kuma ko da taje gidan namu ma baza ta sameni a Chan ba"
" Toh Allah yasa Lafiya"
Ta amsa da amiin.

Mamy ce ta karb'i wayar suka gaisa ta mata ta'aziyya sannan ta mata nasiha, ta Kuma jaddada mata cewar kuka ba nata bane yanzu tayi ta musu addu'a kuka take sosai, Mamy na Jin hakan tayi saurin katse wayar, Mardiya kuwa ta Shiga rera kuka Mai cin raai.

Bacci take har ta manta Jikin ta , ruwan da aka watsa mata ne yasa ta farka a razane a had'e da dirkowa daga Kan gado, kallon sa take yi da d'an karamin bucket d'in dake hannun sa ta kalli Jikin ta, zaro ido tayi tana ganin jikinta har yanzu ba kaya da sauri ta sa hannu ta d'auko zannin gadon ta d'aura a Jikin ta.

"Mtsww me zaki 'boye anan me ban sani a Jikin ki ba?" Adnan keyi wa Ayrah wannan maganar
Kai ka sa tana matsar kwalla Sam bata ji dad'in maganar da yayi mata ba, yace "Ba Kya sallah ne? Bakiyi azahar da la'asar ba gashi magrib ta sako Kai, wato ma kinji dad'in abinda mukayi d'azu tunda har Kika iya bacci, to ki shirya anjima zamu sake, kije kiyi wanka" Yana kainan ya fice abinsa.

Bin bayansa tayi da Kallo tana Jin tsanar sa a cikin zuciyar ta, ajiyar zuciya tayi ta nufi hanyar ban d'aki, shigowa d'akin ya sake yi Amma wannan karon da wata Leda ne a hannun sa, wurga mata yayi yace "Kaya ne idan kin yi wankan kisa"

Bud'e ledar tayi, kananan kayane aciki, daga mini skirt sai wanduna da riguna sharara Wanda su da babu Duk d'aya, hawayebe masu zafi suke gangarowa daga fuskan ta Tace "Wai me ya maida ni ne?"

Ji tayi ya amsa da "Karuwa ta" kallon sa tayi tana mamakin yaushe ya shigo, Kuma ya akayi yaji abinda Tace ganin kallon da take Masa ne yasa ya kashe Mata ido had'e da fad'in "Ya akayi" Yana maganar cikin gadara da nuna Isa.
Wurgar da ledan tayi ta Shiga ban d'aki, tana ji kamar ta shake mishi wuya.
_________________________
Please comment and Share
Milhat ce
Yar Terawa

67&68
Continuation.......... Tana fita daga wankan jikin ta d'aure yake da towel,sai da ta leko taga baya nan kana ta sa Kai ta fita, ledan da ta yatsar ne ta tsuguna ta d'auka,zazzagen kayan tayi ta shiga dubawa wani wando ta gani Wanda shine d'an dama dama ta saka taga ya Kai gwiwanta, Wani riga ta d'auka ta sa, Wanda armless ne kamar vest Amma ya rufe mata cibiyar ta.

           Bayan ta gama sakawa ne ta hango kan gadon,da mamaki ta Kara gun hannu tasa ta d'aga ga mamakinta hijab ta gani girgiza kai tayi a bayyane tace "Adnan kenan,hijabi ya kawo min" ajiyewa tayi ta koma ban d'aki tayi alwala bata dad'e ba ta fito,sallayan da ta hango a bedside ne ta d'auka ta shimfid'a kana ta Sanya hijab din ta tada sallah.

             Ta yi raka'a biyu ta ji shigowar sa,har ta gama jero sallolin da ake binta kana ta sallame,tana d'aga Kai suka had'a ido dashi,tayi saurin kawar da kanta,murmushi yayi kana yace "Tashi muje muci abinci" mikewa yayi daga kwancen da yake ya fita, Yana fita ta bi bayan sa,a parlour ta tarar dashi ya zauna gaban shi da abinci kallon sa ta tsaya yi,Shima kallon ta yake yace "Kin tsaya kallo na zauna mana"

             Zama tayi tana mamakin a ina ya sami abincin,ta Kai hannun ta kenan yace "daga ta malama wai kina nufin a tare zamuci abinci? A kwano d'aya haba,matsayin ki bai Kai Nan ba" taji ba dadi hakan yasa ta mike cikin fushi ta nufi d'aki,da sauri yace "Gara ki zauna kici abinci,sabida bazan sake fita ba,idan ma na fita a chan zanci kayana,yanzun ma tausayin ki naji yasa na kawo miki take away,sannan inaso ki samu karfin d'auka na,ki ga take away chan...... "Yana nuna mata ledar dake gefen sa "ki d'auka rice and stew ne"

         Sai da ta gama kallon sa kana ta shige d'aki abinta,girgiza kai yayi had'e da Murmushi ya cigaba da cin  abincin sa,tana shiga ta sawa kofar key,zama tayi akan sallaya wayar ta ta shiga dubawa taga babu,hakan ne ya tabbatar mata da cewar ya d'auke mata, mikewa tayi ,tayi sallar Isha kana ta kwanta akan gado.

             Tunanin halin da Nabila zata shiga ne yake damun ta,Fatan ta shine Allah yasa su gane sace ta akayi,kuka ta fara yi ganin yanda Adnan ya Maida ta tamkar matar sa a Rana d'aya kawai Kuma ta tabbata zai Kuma Neman ta shiyasa ma ta rufe kofar, tunani take mai kyau da mara kyau tana da na sanin abubuwan da ta aikata,ta dad'e a haka kana bacci ya d'auke ta,chan cikin bacci taji alamun ana cire mata wando,a razane ta Farka tana jaan jikinta,ganin Adnan ne hakan ya Kara tsoratar da ita,kuka ta shiga yi tana Masa magiya akan Kar ya mata haka Amma ina baya ma sauraron ta,a haka har ya raba ta da kayan dake jikin ta,ya afka mata bakamar d'azu ba da Saida ya yi wasanni da ita,zafi taji sosai tana kokarin tureshi Amma ta kasa sabida Adnan na mijine kakkarfa,yafi karfin ta,sai da yayi mai isarta kana ya kyaleta, tare suka kwana a wannan ranar idan yayi barci da zaran ya Farka sai ya afka mata yayi hakan kusan sau Hud'u kan gari ya waye,sai da aka Kira sallar asuba kana ya kyaleta ya koma d'ayan d'akin,ya watsa wa jikinsa ruwa yayi sallah kana ya koma baccin sa,ayrah kuwa ko motsi Mai kyau ta kasa yi,i wani azabebben zazzab'ine ya rufe ta,ta ja bargo ta rufe jikinta tana rawar sanyi.

             Sai karfe 10 na safe ya tashi daga bacci Nan ma yunwace ta tashe shi, weekend ne hakan yasa bazai fita aiki ba,d'akin da take ya nufa Yana shiga ya hango ta tana rawar sanyi da sauri ya karasa inda take ga mamakinsa zufa take had'awa Amma kuma tana rawar sanyi, first aid box ya d'auko ya bata maganin zazzabi dakyar ta karb'a Tasha zaunar da ita yayi Yana kokarin d'agata,wani Kara ta saka Wanda yasa ya razana bargon ya d'aga yaga irin aika aikan ta yayi zanin gadon duk ya 'baci da jini,dafe Kai yayi a zuciyar sa yace "What have I done?" Cike da Jin tausayin ta ya Mike ya d'aga ta Chak sai ban d'aki ruwan wanka ya had'a mata tana tsaye a rigingine tana kallon sa, had'e da ciza leb'en ta magana yake mata Sam bata Jin sa,ganin hakan kawai ya d'aga ya saka ta acikin bathtub da already ya had'a ruwa Mai zafi,wani nkarabta saka tana kokarin fita ya danne ta da dukkan karfin sa,Yana mata sannu kuka take sosai har ta fara Jin dadin ruwan bayan ta d'auka tsawon mintuna kana ya cire ta,ya Mika mata towel ya fita,bed sheet d'in ya cire ya canza wani a dai dai Nan ta fito,kallon ta yayi ya fice daga d'akin.

          Tun daga wannan ranar yake tausayin ta ya d'an d'aga mata kafa,sai da ta warware kana ya d'aura daga inda ya tsaya.

         Mardiya tana samun kulawa sosai agun Umma ta d'auke ta kamar Yar da ta Haifa a cikin ta,haka ma su Twins sun saba da ita sosai, idan suka dawo daga school sai su zauna a d'akin ta suyi ta cika ta da surutu,wannan dalilin ne yasa ta d'an saki ranta a gidan.

*AFTER ONE MONTHS*

        Haisam na samun kulawa sosai from both families,musamman ma Isha tafi kula dashi sama da kowa,Ayrah kuwa cigiyan ta ake sabida alamu sun nuna sace ta akayi an samu motar ta a pake a bakin hanya Amma an kasa gano Indo take.

             Adnan kuwa duk lokacin da yaji amfani da ita zai afka mata ba dare ba rana,da safe zai fita yaje gun aikin sa da dare kuma ya dawo,wasu lokutan kuma ita kad'ai take kwana tafiya yake ya barta Amma baya barin ta ba tare da ya ajiye mata abinda zata ci ba,sau dayawa idan ta shiga d'akin sai ta rufe Amma cikin dare sai taji motsin sa hakan ne ya tabbatar mata da cewar Yana da wani key d'in daganan ta hakura,kullum cikin kuka take tana rokon sa akan ya kyaleta ta tafi gida,Adnan na matukar Jin tausayin ta kuma yana kaunar ta shi Kansa bai San dalilin da yasa yake mata haka ba,har cikin ransa Yana so ya bar ta tafi,Amma idan ta tafi ya zaiyi,ya Saba da ita,Yana sonta Yana kaunar ta sannan Yana son kasancewa tare da ita,hakan yasa ya yanke shawarar bazai tab'a rabuwa da ita ba.
Chapter 46 · 0% Book details