Sashe 19
Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yar karamar dariya daddy yace "Ikon Allah daga ganin ta sau d'aya kace min ka kyasa?"
"Eh Mana love at first sight kake ji,look Yaya ka daina min dariya Kai da ya kamata kayi farin ciki ma"
"Sosai Kam,naji dad'i sama da 20 years kaki aure ai abin a duba ne,Kuma Insha Allah baka da matsala sabida Zainab bata da matsala ko kad'an tana da kirki"
Shafa kirjinsa Abba yayi had'e da fad'in "Alhamdulillah abinda nake son ji Kennan tunda ka yabe ta magana ta kare,yanzu dai ya za'ayi?"
"kar ka damu zansa Maryam ta Mata magana Insha Allah,Allah dai yasa ta amince"
"Amiin ya Allah Ni da kaina zanyi Mata magana ma, Maryam Uwar Maryam"
Fitowar Mummy Kennan ta ce "To me Kuma ya Faru naji ana Maryam Uwar Maryam nasan cuta ta za'ayi"
Dariya sukayi daddy yace "A'a ba cutar ki za'ayi ba alfarma Zaki Mana ko ince taimako"
Zama Mummy tayi Tace "Ahaaaf na sani ai da wala kin goro a miya, nasan ba a banza ba wannan kirarin"
Daddy ya Sanar mata da abinda Abba yake bukata, Murmushi tayi Tace "Kai Alhamdulillah finally addu'ar mu zata karb'u, a gaskiya idan ka auri Zainabu zan ji dad'i sosai sabida mutuniyar arziki ce, gata da tsoron Allah, mace Ce ta gari, fatana shine Allah ya Sanya alhairi yasa Kuma ta amince kasan dai baza'a mata Dole ba"
Abba yace "Nima ban bukaci hakan ba, in dai Bata so ki kyaleta Amma fa zanzo ki sa mata ra'ayi na gaskiya"
"Kar ka damu Insha Allah ma zata amince kaga Shikenan ta Zama ta gida Duk da dama Yan gida ne"
Nan sukayi ta hirar su har karfe 9:30 daddy da kansa ya kaisa Airport yaso ganin Umma Kan ya tafi Amma bata fito ba, Ma'isha Kuma da Haisam d'akin Haisam suka nufa suna ta Shan hirar su.
Suna cikin hiran ne Tace "Yauwa Yaya Kace Akwai maganar da kake son fad'a min, mene ne?"
"Yauwa kin tuna min, ba kince kina so na sama Miki aunty ba?"
"Eh hakane"
"To burin ki ya kusa ciki"
"Ban gane burina ya kusa cika ba? Soyayya ka fara ne?"
Murmushi yayi yace "Dad'i na dake kanki naja sosai princess, hakane soyayya nake Kuma ina sonta sosai"
Ma'isha jin maganar Nan dai dai yake da kamar wuka aka dab'a Mata a kirjinta ji take d'akin na juya Mata, shiru tayi kana tace "Wace Ce haka Yaya?"
Murmushin Jin dad'i yayi yace "Kin santa ai"
"Haba dai ya sunan ta?"
"Aysha!!!
A razane ta Mike Tace "Aysha?"
Shima mikewa yayi yace "Eh Aysha lafiya naga kin razana haka?"
Ma'isha a ranta ji take kamar ta shake mishi wuya ya Kuma cewa "Princess kuka, meyasa ki kuka?"
"Yanzu duk soyayyar da nake maka baka gani, da abun da zaka saka min Kennan? Baka san cewa ina sonka ba, me zakayi da wata Aysha? Dame ta fini?
Kiran sunan ta da yayi da d'an karfine yasa ta dawo daga tunanin da take ya Kuma cewa "Princess tell me please what happened, why are you crying?"
Cikin Muryar kuka Tace "Yaya ba Kai bane?"
"Me nayi princess?"
"Har zaka Fara soyayya ba tare da ka fad'a min ba"
Dafe Kai yayi ya sauke wani ajiyan zuciya "Na d'auka maganar Farukh zai tabbata ne Ashe ba hakan bane ba?"
" Me Farukh d'in yace?"
Girgiza kai yayi had'e da Murmushi yace "Nevermind Amma princess Allah ya shirye ki komai kuka komai kuka gaskiya mijin ki zai Sha fama Kam, don wallahi aka Kai Masa ke raino zaiyi"
Murmushi tayi "Nikam bari na tafi Kan Abba...... " Ganin agogon dake d'akin yasa Tace "Wayyo karfe 10 da rabi" ta nufi kofa da gudu Haisam yace "Lafiya me ya Faru?"
"Abba zai tafi bamuyi sallama ba Kuma idan ya tafi sai yafi 3 years bai dawo ba"
Ta fita da gudu, parlor ta nufa, tana Shiga ta tarar da Umma da Mummy a zaune mummy da d'an fad'a fad'a Tace "lafiyan ki Kike Mana gudu a gida haka?"
"Mummy Abba da Daddy fa?"
"mtsww sun fita" kawai Tace Mata had'e da kawar da kanta.
Dafe goshin tayi Tace "Kai Amma naso mu yi sallama wallahi Amma ba komai zan kira shi a waya" tana Kai Nan ta shige d'akin ta, ba ta dad'e ba ta fito ta shirya cikin sutura mai kyau Tace "Mummy zanje gidan su Ameerah"
"Aikin Kenan ai bare yanzu kinyi mota"
Murmushi tayi Tace "Sai na dawo Umma sai na dawo"
Umma Tace "Ai Ni munyi fad'a dake"
Kama baki tayi Tace "Na Shiga uku Umma laifin me nayi kiyi hakuri"
"Uhmn wai ace a miki babbar kyauta haka Amma baki fad'a min ba"
Fad'awa jikin Umma tayi tana fad'in "Kiyo hakuri Umma wallahi d'azu ma da na Shiga da niyaan fad'a miki ne Amma Yaya yasa na manta kiyi hakuri kizo muje kiga motan"
"To na sani dai Dole mantawa kikai, kar ki damu kije sai kin dawo ki kaini d'ani"
Da murnar ta ta Mike Tace "To Umma sai na dawo d'in"
Ficewa tayi tana ganin Haisam hannu kawai ta d'aga Masa ta shige motar ta key ta sa wa motar ta fice abin ta girgiza Kai yayi ya Koma ciki wayar sa ya d'auka yan kirata tana gani taki d'auka a bayyane Tace "Chaap ina driving d'in zan d'aga call d'in ka sai na Isa"
Har ya katse Bata d'aga ba text ya tura Mata yace
```"Wato yanzu na Zama 0 a gun ki kinyi mota ba komai nagode"```
Bud'e text d'in tayi ta karanta Murmushi tayi parking tayi ta Masa ```"reply da ba Haka bane Yaya zanje gidan su Meerah ne, Kuma zan dad'e sai na dawo"``` ta ajiye wayar tana Isa gidan su Ameerah ta nuna Mata motar ta ta taya ta murna sosai, sai da suka gama kallon motan kana ta suka koma d'akin ta, wani irin Kallo Ameerah takeyi Mata Wanda yasa har ta Fara tsarguwa Ma'isha kallon kanta tayi Tace "Lafiya me ya Faru kike min Kallo haka?"
Cike da kulawa Ameerah Tace "Isha wai ke Dan Allah baza ki cire damuwa a ranki ba? Haka Zaki cigaba da Zama?"
Kirkirerren Murmushi tayi Tace "Me Kika gani ni Lafiya na Lau fa"
"Haba Isha na sanki fa over 10year you're my best friend ko da baki fad'a min ba na miki sanin da zan iya gane farin ciki da bakin cikin ki, tell me maganar Haisam d'in ne haryanzu?"
Ajiyar zuciya tayi sannan Tace "Shine kin San d'azu yake fad'a min wai Ashe soyayya suke da Aysha?"
"I said it, ai na fad'a miki ki cire shi a ranki ko Kuma ki fad'a masa Amma kinki and now it's late"
"Anya Ameerah kin San soyayya kuwa? Kar ki manta fa shi so halittace ba yin kaina bane wallahi abun ya fi karfi nane" ta karasa magani cikin kuka.
Hannu Ameerah tasa a goshin Ma'isha Tace "Akwai zazzab'i a jikin ki"
Mikewa tayi ta d'auko BP apparatus kasantuwar ita d'in a school of Nursing take tana final year yanzu, gwada BP d'inta tayi ta Kuma gwada har sau uku zaro Ido tayi Tace "Isha jinin ki ya hau sosai har 200 Inna wa Inna ilaihirraji'un, gaskiya dole in fad'a wa Ya Haisam gaskiyar magana bazan bari ki cutar da kanki" wayar ta d'auka zata Kira shi Ma'isha tayi saurin kwace wayan Tace "Me haka Ameerah me kike Shirin aikatawa haka?"
"Ke zan tambaya Isha me kike Shirin aikatawa, zaki ja wa kanki matsala a banza Bayan wannan matsalar idan kina so a Yau d'in Nan za'a yi maganin sa"
"kince na cire shi a Raina Insha Allah zan cire shi I just need some time please"
Hawaye wani na bin wani haka ya rik'a fita daga cikin idon Ma'isha,ta kalli Ameerah ta rik'e hannunta tace "Please Dear ki taimaka min dan Allah karki fad'a,baki san irin son in da yaya yake ma Aysha ba ,haka itama wallahi suna son junansu bani son lalata masu farin ciki muna k'aunar junanmu ni da d'an uwana"
Haushi yasa Ameerah ta fara magana cikin fad'a "oh kenan kin fiso ki mutu?kina so mu rasa ki kenan?shin keda Aysha wa ya fara son yaya Haisam? tun kafin ya dawo gidan ku a school baki da wata magana sai tashi shin idan ba'a fito fili an fad'a masa gaskiya ba ya kike so muyi?kina so ki dawwama cikin damuwa Kenan?"
Kukanta a yanzu ya fito fili ta saka hannayenta ta rufe fuskarta tace "alkawari kika d'auka Meerah karki manta girman alkawari da mahimmancin sa ki rufa min asiri"dan Allah karki fad'awa kowa"
Itama Meerah kuka ta fara, ta jingina kanta a kafad'ar Ma'isha ta cigaba da fad'in "karki damu da duk halin da nake ciki ni dai fatana karki fad'awa kowa kamar yadda kikayi alk'awari"
"Shikenan Insha Allah bazan karya alkawarin da na d'auka ba Amma kema kimin alkawarin Zaki cire shi a ranki"
"Insha Allah."
"Hajiya wai kina nufin Kanin Alhaji ne wannan ko da yake na d'an ga kama Kam"
"Eh kanin sane uwa d'aya uba d'aya....... " Nan fa Fara bata labarin sa da halin da ya Shiga girgiza kai Umma tayi Tace "Allah sarki na tausaya mishi, wato Duk halin da ka Shiga a Rayuwa idan Ka ga na wani sai ka Raina naka"
Mummy tace "Wannan hakane" riko hannun Umma mummy tayi Tace "Please Zainab ki taimake mu ki maye Masa gurbin abinda ya rasa"
Cikin rashin fahimta take kallon ta, "ban gane na maye Masa gurbin abinda ya rasa ba?"
Nan mummy ta kwararo mata bayanin yanda sukayi da Abba a razane ta Mike tace "Gaskiya bazaiyu ba, bani ba aure kice Masa bana son sa ban amince ba, Kai baza ma na tab'a son sa"
Mummy mikewa tayi ta fara Mata magiya, hakan yayi dai dai da Shigowar Daddy a tsawace yace "Maryam!!!
Ba Mummy ba har ita Umman ta tsorata , sai da ta maso inda suke, sai Kuma yayi kasa da murya yace "Ba haka mukayi dake ba Akan me Zaki matsa mata Tace Bata so then let her be" sai ya wuce d'akinsa, Haisam kuwa Jin Muryar daddy ya Shigo da gudu, karaf maganar da daddy yayi ya sauka kunnen sa.