← Book details Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 55

Sashe 45

Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nan ta Fad'a mishi incident d'in da ya faru, yaji tausayin ta matuka, Nan ta nemi alfarma ya bari ta Shiga a madadin Isha, bai Musa Mata ba, suka Shiga, suna Shiga taga Haisam a kwance sai rarraba idanu yake Yana son gane inda yake.

Idan sa ya sauke a Kan Meerah, Cikin tsarkewar murya yace "Prin.... Ceessss" (Princess) Kama baki Meerah tayi Nan da nan hawaye suka Fara kwararowa daga idanun ta, "wannan Wace irin shakuwace a tsakanin Ma'isha da Haisam,sabida nasan da sunan Princess yake Kiran Isha,tabbas ita yake son gani,tunda ya farka bai yi magana ba,sai da yaga kawar ta" Dr Ali ne yake ayyana hakan a ransa.

Da gudu Meerah ta fita, ta nufi ward d'in da Isha take, tana Shiga d'akin ta fashe da kuka su, mummy da Daddy suna tambayar ta ko Lafiya Amma sai kallon Isha kawai take, Isha ma kallon ta take.
________________________
Please Vote and comment
Milhaat ce
Yar Terawa

65&66

'''Continuation........''' daddy kallon ta Meerah yake cikin Muryar mai Sanyi yace "Meerah speak up Mana, what happened?"

Mummy ce ta karasa inda take, hannunta ta rike hadey da fad'in "Kina Lafiya tsorata mu Meerah, me ya farune kike kuka Haka? Wani mugun abune Kuma ya Faru, sabida a cikin Yan shekarun Nan duk kullum cikin tashin hankali muke da ga wannan sai wanchan"

Daddy yace "Kar kiyi sab'o Mana, Ko wani bawa da tasa kaddarar mu Tamu Kenan muyi fatan Allah ya bamu ikon cinye jarrabawar"

Meerah hannun tasa ta Shiga share hawayen ta, murmusawa tayi had'e da fad'in "Mummy wannan karon ba mumunar labarine ba, abinda Muka dad'e muna jira ne"

Cike da mamaki suke kallon ta, musamman ma Isha da ta kosa taji maganar dake bakin ta,mummy Tace "Please stop beating into the bush,just go straight to the point Mana"

"afwan mummy......" Kallon Isha tayi Tace "Haisam ya farka"
Isha da Bata San sanda ta Dirko daka gan gadon asibitin ba,bata tsaya tambayar ta komai ba ta yi hanyar fita,Duk suka bita da Kallo,Mummy Tace "Are you sure of what you're saying?"

"am sure mummy har sunan Isha ya Kira" daddy yace "Ta fita fa a haka jikinta ba ko mayafi" ai kuwa a sannan ne mummy da Meerah suka bi Bayan ta,a guje Mutanen dake gun sai aikin kallon su suke, suna Kiran sunan ta Amma inaaa kamar cewa suke ta Kara gudu.

Tana Isa ICU,zata Shiga aka hanata,ganin yanda take a birkice kamar mahaukaciya,Dr Ali ne ya karaso gun sabida hanyaniyar da yake ji,Yana ganin Isha ya bi Jikin ta da Kallo da ga sama har kasa ,a cikin kwana d'aya har ta lalace tayi baki ta rame, tabbas tana cikin damuwa.

Muryar tane ya Dawo dashi duniyar Mutane tana fad'in "Dr ka Fad'a musu su barni na Shiga please" tana maganar tana kuka hawaye ya wanke mata fuska, Dr Ali yace "Ai Haisam baya Nan Isha"

"Ban gane baya Nan ba?"
"Ina nufin Yana ward,an fitar dashi daga Nan,kizo muje na kaiki inda yake shima Yana tambayar ki" a dai dainan su mummy da Meerah suka Isa inda suke,suna ganin sun juya suka bi Bayan su ba tare da sunce komai ba,Isha tafiya take har tana kokarin fad'iwa.

Da sauri Dr Ali ya taro ta cikin sanyin Murya yace "Be careful"
Murmushi kawai tayi suka cigaba da tafiya, suna Isa kofar d'akin da Haisam yake yace "Ki Shiga Nan ne d'akin nasa"

Kasa motsi tayi tana kallon kofar, Meerah ve ta dafe ta a kafad'ar ta had'e da fad'in "isha kin dad'e kina jiran Wannan ranar, ki Shiga Mana"

"Meerah ina tsoron Shiga ne, bana so ya Kuma rufe idanun sa kamar na ranar idan ya sake rufe idanun sa na tabbata bazai sake tashi ba"

Dr Ali yace "No Isha Kar kice haka Mana, I told you d'an sarkin Saudi tun yana da shekara 17 a duniya yayi accident ya Shiga comma, tun 2014 Kuma a yanzu Muna 2022 bai farfad'o ba Kuma bai mutu, Kuma Haisam bai koma ba , tun da kiga mun dawo dashi nan, ya farka kenan" Mummy Banda kallon Isha babu abinda take yi,wasu zazzafan hawayene suke gangarowa daga fuskar ta tana mutukar jin tausayin Yar tata,fatan ta shine wannan ya Zama shine wahalar ta na karshe a Duniya.

Ajiyar zuciya tayi ta Fara 'daga kafa a hankali, ji tayi kafar ta ya mata nauyi Duk da babu takalmi a kafarta,Jan kafar ta farayi har ta sa hannu ta murd'a kofan ta bud'e, kamar baza ta Shiga ba, sai Kuma ta Shiga da d'an sauri.

Haisam naji motsin kofar ya waigo, don ganin Wanda ya shigo, Yana ganin Isha, kallon ta kawai ya tsayayi, itama kallon sa take Hannayen sa ya ware alamun come and give me a hug, cikin kuka da had'e da dariya ta nufi inda yake, ta rungume shi , wani ajiyar zuciya suka sauke a tare, Isha kuka take yayin da yake d'an bubbuga Mata baya alaman rarrashi Yana zubar kwallar Farin ciki, Shigowar su Mummy ne yasa tayi saurin janye Jikin ta.

Mummy wurin Haisam ta nufa, shafa kansa tayi cikin so da Kauna irin na uwa da d'anta, Tace "Son kana lafiya?"
Ya bud'e baki da niyar magana Amma ya kasa, Isha kallon Dr Ali tayi Tace "Ya baya magana Dr?"

"Eh ai dama bazaiyi magana Nan take ba, sabida shekarun da ya d'iba Yana bacci, yanzu Haisam ya zama kamar yaro babu abinda zai iya yiwa Kan sa"

Mummy Tace "For how long Dr?"
"Uhmn I can't really say gaskiya, Haisam have been sleeping for four years, so Allah ne Kad'ai yasan sanda koman shi zai Zama normal"

Haisam kallon su yake Yana mamakiin maganar da Dr Ali yake yi, Wai shi ne yayi bacci har na tsawon shekara 4,shi Duk a tunaniin sa Suma yayi ya farka, a Sannan ne ya tuna da a gun d'auri auren sa ne ya Suma, kokarin tashi ya Shiga yi, da sauri Dr yasa hannu ya kwantar da shi Yana fad'in "Calm down Haisam, Calm down"

Kuka ya farayi Yana kokarin tureshi, yace "Haisam me kake so? Akwai abinda kake so a Kawo maka ne?"
Murya a hard'e yace "Ayrah"

Isha, Mummy da Meerah kallon juna suka Kuma suka mayar da kallon su ga Haisam d'in, Isha fashewa tayi da kuka ta fice daga d'akin, tana fita suka ci karo da Daddy, Abba da Umma.

Daddy ne ya rike ta yace "Isha ina Haisam d'in"
Cikin kuka Tace "Yana ciki"
Umma tace "Ya Mutu ko Isha?"
Kallon Umma tayi a razane ta girgiza kai had'e da fad'in "A a bai mutu ba"

Abba yace "To kukan me kikeyi?"
"Kawai tausayin sa nake ji" tana Kai Nan tayi gaba suka bita ta da Kallo, d'akin suka Shiga, da sallama, haryanzu Yana kokarin ture Dr Ali,Umma na ganin Haisam cikin Muryar kuka tace "Haisam!!!"

Haisam naji Muryar Umman sa ya d'ago ya kalli inda yaji Muryar ta, cikin tsarkewar murya yace "Umma"
Da sauri ta nufi inda yake, Dr Ali na ganin hakan ya jaa da baya, rungume shi tayi Yana kuka tana kuka.

Meerah na ganin hakan ta fita tabi Bayan Isha, hango ta tayi ta durkusa tana ta kuka mai tsuma zuciya, cike da Jin tausayinta ta d'ago ta tana fad'in "Isha kuka?...... Tasa hannu tana share mata hawaye " please ki daina kuka Isha, nasan ambaton Ayrah da yayi ne ya saki kuka ko?"

'dago rinannun idanun ta tayi cike da mamaki Tace "Ya akayi Kika gane hakan"
"Hmm haba Isha we have been friends for a very long time, ya za'a yi bazan gane ba?"

" Hakane Amma Meerah abun ya bani mamaki, Amma meyasa ya ambaci sunan ta, hakan na nufin asirin da ya mata bai Karye ba?"
"A a baki ga actions d'insa ba, ya tuna abinda ya faru ne, don na tabbata Haisam zai d'auka kamar bacci yayi ya farka, ya Kamata ki Masa uzuri kinji, bazai ma so Ayrah ba sai dai ya tsane ta sabida abinda ta aikata masa"

Hijab ta saka Mata kana ta ajiye Mata ta kalmi, sawa tayi, Meerah riko hannun ta tayi suka koma cikin d'akin.

Dukkanin su murna suke sosai yau Haisam d'insu ya Dawo.

Mardiya tana kwance a d'akin da Mummy ta ajiyeta, taji lokacin da suke waya da Mummy Akan Haisam ya farka, kuka ta Shiga yi tana fad'in "bazan tab'a yafe miki ba Isha, kin kashe min Yayana da Iyeye na, gashi Yayan ki ya farrka wayyo Allah na, ya zanyi na Shiga uku na lalace" kuka take sosai kamar ranta zai fita.

Kwankwasa kofar da taji akeyi ne yasa ta tsagaita kukan nata, hannu tasa ta share hawayen ta kana ta Mike ta nufi kofar d'akin, bud'e kofar tayi tana kallon ta.

Tace "Hajiya Lafiya naji kina kuka?" Mai aikin Umma ke yi Mata wannan tambayar.
Kirkirerren Murmushi tayi kana Tace "Lafiya Lau, nagode" ta koma ciki had'e da rufe kofar.

"mtswww Amma Ayrah bata da mutunci na tabbata taji labarin abinda ya same Ni, tun da safe Amma har yanzu Bata Kira ni ba bare tazo inda nake"

Dialing numberta ta Shiga yi Amma swich off, cike da mamaki take kallon wayan nata a bayyane Tace "Yau Wace Rana? Wayar Ayrah a kashe?" Tab'e baki tayi ta wurgar da wayar a gefe ta yi tagumi tana tunaniin yanda rayuwar ta zata kasance, ba uwa ba uba ba yayanta Wanda yaje sonta fiye da komai, ta cigaba da rera kukan ta.

"Nabila wai yau ina Ayrah ne, tun safe da na Zo ban ganta ba, wato dama haka takeyi Bata Zama a gu d'aya?" Mamy kiyi wa Nabila Wannan tambayar.

"A'a Mamy kullum tana Nan Wallahi, Sunusi ne ma ya daina zuwa kwata kwata"
" To ina taje?"
"A Facebook muka gani Wai gidan su Mardiya ya kone, shine ta fita don taje ta Duba ta Amma haryanzu bata Dawo ba, Kuma na Kira Layin ta baya shiga"

"Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, Ashe dama gidan su Mardiya ne? Ance fa Duk mutanen ciki sun mutu"
"Eh Mamy gidan sune"
Chapter 45 · 0% Book details