← Book details Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 55

Sashe 48

Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin Muryar Nabila ne yasa ya kalli inda take a tsaye bai ma lura da ita a gun ba, Yana kallon ta ya Gane Yar Mamy ce sabida duk yaran Kama da ita suke, hatta yaranta mazan ma Babu Wanda yayi Kama da malam Hassan, duk da shid'in bafulatani ne na usul Amma bakine, Nabila ce ma ta d'an d'auki kalar fatar sa, hakanne yasa duk ta fi su kyau, Kun San ance black is beauty.

Kallon ta yayi kana yace "Farida ko?"
Murmushi tayi kana Tace "A'a Nabila"
"oh sorry My Bad,Nabila amma Mami yarinyar Nan ta girma fa sosaiii"

Yar karamar dariya Mami tayi duk da haryanzu hawayene fal a idanun ta, Tace "Eh ta girma nan ma baka ga Auta ba"
Nabila turo baki tayi kamar zatayi Kuku, ita ta tsani daji ance mata wai ta girma, ganin yanda take ta kunkuni ba karamin bashi dariya yayi Amma ya gimtse dariyar tasa.

Babu Wanda ya Kuma cewa komai kusan na mintuna uku, mami Tace "Baka tambayi kanwar ka Ayrah ba"
Kai ya sane a kasa, kamar wani Mai nazari yayi ajiyar zuciya kana ya d'ago Kai ya kalli mami yace "Eh Mamy ban tambaya bane ba sabida ina da labarin abinda ya same ta"

" kaga Allah ko Haisam? Baka da hakkin su shiyasa Allah ya Kama su, ban San me ka terawa malam ba, babu yanda banyi dashi ba Akan ya d'auke ka kamar d'an cikin sa, Amma ina son zuciya da son Kai irin nasa ya rufe Masa Ido, bai tsaya a iya Nan ba ya had'a har da Yar sa wacce bata da ji ba bata gani ba yayi amfani da ita wurin biyan bukatar sa....... " Kuka ne yaci karfinta ta kasa karasa maganar, Nabila ce ta sa hannu tana d'an bubbuga mata baya alamun rarrashi, mamy hannu tasa ta share hawayen ta,kana ta had'e Hannayen ta wuri gudu alamun roko kana Tace "Haisam Dan Allah na roke ka ka yafe Mana a Karo na sau ba adadi, kila in ka yafe mana Rayuwar mu zata Koma dai dai" ta cigaba da kukan ta.

Haisam da d'an saurin sa ya nufo ta Yasa hannu Yana share mata hawaye, yace "Mami Wallahi ban tab'a rike Daddy a Raina ba ko da na minti d'ayane, Kuma maganar yafiya tun a ranar na yafe Masa wannan kadara tace Ni Musulmi ne na yarda da kaddara Mai kyau da Mara kyau,a ranar da Daddy yasa wa Abba guba na ganshi,Amma yace idan na kuskura na fad'awa,kowa sai ya kashe Ni ya kashe Umma,sannan a ranar da muka Koma gidan su Isha,na fito naje gidan mu don na d'auko Abu,babu Wanda ya sani daga ni sai maigadi,da idona naga daddy yana fad'a musu su sa petir ta ko ina,hmm su mutu kowa ya huta,a ranar na gane Isha is an Angel to me sends from the almighty Allah........." Ya d'aga Kai ya kalli Isha,da take ta matsar kwalla tana jin tausayin Yayan ta, ya maida kallon sa ga Mamy yace " let the bygones be gone Mamy, Allah baya barin wani don wani but am Very sure that ya barni a Raye ne to make things right and I'll surely do that insha Allah yanzu abinda ya Kamata muyi shine mu maida hankali gun Nemo Ayrah"

Fashewa Mamy tayi ta kuka Tace "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, Haisam kaga rayuwa, kaga rayuwa sabida dangin Uban ka, tun kana yaro kaga jarrabawa kalala"

Murmushi yayi yace "Kuma Yanzu ya zama tarihi ba, please Mamy ki daina kuka haka, nasan kin Soni tamkar d'an da Kika Haifa a cikin ki, har Yanzu ban manta lokacin da idan Kika sayo abu sai ki ja ni d'aki a 'boye ki bani sabida Kar Ayrah ta gani duk ina tune dasu Mamy"

Hannun ta ya rike ya zaunar da ita akan Plastic chair dake d'akin,ya durkusa a gaban ta Sannan ya Mika hannun ya d'auki bottle water ya bud'e kana ya Mika mata, ba musu ta Karb'a tasha, goran ta sauke kana sauke wani ajiyar zuciya, tana kallon Haisam da shima yake aikin kallon ta, shafo fuskar sa tayi had'e da fad'in "Allah ya maka Albarka"
Ya amsa da "Amin Mamy"

Kiran wayan Isha akayi, ta d'aga ji nayi Tace "Mun d'an zagayane Umma Amma ga munan muna dawowa" ta sauke wayan da ga kunnen ta tana kallon Haisam, mikewa yayi daga sugunawan da yayi yace "Mamy bari muje Umma ba neman mu" ya kalli Isha yace "Muje"

Ta juya ta fice, Mamy Tace "Tsaya muje tare naga d'akin da kake" Murmushi kawai yayi ya rike hannun ta suka fice.

Malam hassan najin sun fita ya d'ago Kai, yayi ajiyar zuciya, Nabila da sauri ta nufi inda yake tana fad'in "Daddy Lafiya? Kana son wani abune?" Girgiza Mata Kai yayi alamun a'a hawayena na zubowa daga idanun sa , da sauri ta d'auki tissue tana share Masa.

Umma da Mummy sai mardiya ne zaune a d'akin Ma'isha ta Shiga, sannan Haisam da Mamy a biye da ita, Umma na ganin mamy ta Mike a d'an razane tana kallon yanda Haisam ya rike mata hannu, Rai a mugun 'bace Tace "Haisam Ashe baka da hankali me ya Kai ka gun mugayen Nan?"

Saurin sakin Mamy yayi ya Shiga d'akin Yana fad'in "Haba Umma" juya Masa baya tayi Tace "Haisam kace matar Nan ta fice min daga gani bana son ganin ta na tsane ta da ita da duk wani abunda ya shafe ta"

" Harda ni?"
Cike da mamaki ta juyo tana kallon Haisam d'in kallon baka da hankali take Masa, ya Kuma maimaita tambayar sa a karo na biyu "hardani Umma?"

"What are you saying Haisam? Are you in your normal sense?" Umma ke Masa wannan tambayar.

"Of course Umma am okay, Umma have you forgotten who this woman is?" Yana nuna Mamy da d'an yatsa, "Itace fa matar da mijin ta ya kashe min miji, ya so ya kashe mu, sannan ya sa Shiga comma for almost five years"

"Alhamdulillah Mijinta Kika ce ba ita ba, and wannan matar Itace matar da take Kawo Mana abinci a 'boye ba tare da Mijinta ya sani ba, sannan itace matar da take kullar miki dani a lokacin da babu Wanda yake tare da ke, ta d'auki risk da dama akaina, shin Umma laifin wani na shafan wani dama?" Ya karasa maganar cikin sanyin Murya.

Shiru Umma tayi , Jikin ta ne yayi sanyi tabbasa mamy mutunce ta taimaka musu da ita da 'danta a lokacin da basu da kowa basu da komai, kosan da ta sayar a baya ma Itace ta bata jarin, tana cikin wannan tunaniin ne ta ji an Kama Mata kafa da sauri ta kalli a kasa, ganin Mamy tayi ta zube a gaban ta, tana kuka Tace "Dan Allah maman Yara kiyi Hakuri nasan an cutar dake, nasan Hakurin da zan baki bazai Canza komai ba, but please find a place in your heart to forgive and believe me, Wallahi I know nothing about this, hatta ita Ayrah ma bata San komai ba, you know how Hassan is he a very manipulative human being, yayi manipulating d'inta ne Wallahi bata San komai ba Yanzu haka maganar da nake miki ayrah ta 'bata kusan watanni hud'u kenan bamu San inda take ba ko ta mutu ko tana raye bamu sani ba, babban tashin hankali na ace ta mutu bamu gana ba sabida nayi fushi da ita tsawon shekarun Nan da muka rasa Haisam, Akan sai ya farka na yafe mata gashi ya farka and she is nowhere to be found" ta karasa maganar cikin kuka.

"Tabbas ni shaida ce, Mamy bata kula Ayrah, Wanda hakan ba karamin tada Mata hankali ba" duk suka kalleta, sai Kuma tayi shiru kamar ba ita tayi maganar ba, Haisam kallo d'aya ya mata ya gane ta, ya dad'e Yana kallon ta kamar Mai son gano wani abu, sai Kuma ya kawar da kansa.

Umma hannu tasa ta d'ago Mamy suka rungume juna, Umma na fad'in "Kiyi Hakuri Maman Yara, da na kasa fahimtar ki na manta duk abubuwan da suka faru a baya, na rasa madafa, Ina cikin tashin hankali"

" Ko kad'an Banga laifin ki ba, Amma Dan Allah ki yafe min"
"Allah ya yafe Mana duka"
Duk suka Masa da amin Amma fa Banda Mardiya da take ta taunan chewn gum tana latsar wayarta.

Duk wuri suka samu suka zauna, kasantuwar d'akin babba ne ya d'auke su, Hira suka Fara yi harda Mummy, cikin hiran ne suka yanke shawarar zuwa ganin Jikin malam hassan, Mummy, Umma da Mamy suka fita,suna fita Haisam ya Koma Kan gadon sa ya kwanta suna Hira da Isha,daga bisani sukayi shiru baka jin komai sai karar chewn gum d'in da Mardiya ke tauna.

Suna cikin wannan yanayin ne faruk da Meerah suka shigo, Isha na ganin Meerah da d'an saurin ta Mike ta rungume Meerah, Meerah d'an ture ta tayi tana fad'in "Kaaai mai ciki zungurina fa kike da tumbin ki" sai a sannan mardiya ta d'ago kai ta sauke Akan tumbin Isha, zaro Ido tayi tana kallon Isha, Meerah da ta lura da kallon da take mata Tace "Allah ya sauke ki lafiya mu samu Ma'aruf junior"

Mikewa tayi tana kallon Isha cikin Muryar kuka Tace "Ciki? Ciki kike dashi Isha? Cikin Yayana?"

Duk lokaci Guda ta jero mata tambayoyin Nan, Murmushi Isha tayi kana Tace "Uhmnn eh" mardiya Rungume Isha tayi ta fashe da kukan farin ciki.
_________________________
Please comment and share
Milhaat ce
Yar Terawa
[8/15, 8:02 PM] Miilhaat Writer✍🏻: 🍃 *DANGIN UBANA*🍃

Story & Written
By
Milhart

Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne.

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*

*Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.*

Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️

*BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM*

Page
Chapter 48 · 0% Book details