← Book details Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 55

Sashe 31

Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Toh Mamy tunda ban miki laifi ba Dan Allah ki daina maltreating d'ina nifa 'yar kice"
Mikewa tayi Rai a mugun 'bace Tace "Ni ce ma nake Maltreating d'inki? Oooookaaay wata kin samu dama ina kula ki shiyasa kike fad'a min magana son ranki ko? Tashi ki fice min daga d'aki, Kuma ko da wasa na sake ganin kafar ki a d'aki na sai na karya miki su."

Ganin yanda mamy take mata fad'a ta tsorata matuka,Bata tab'a ganin ta a Haka na, hakan ne yasa ta fice da gudu tana kuka, Kanwar Tace ta bi Bayan ta tana tambayar ta "Aunty Ayrah Dan Allah ki fad'a min me ya Faru kullum cikin kuka kike"
'daga kai tayi ta kalle ta kana Tace " Babu komai" tasa hannu tana shara hawayen ta cike da kulawa Tace "Haba Aunty sai dai in baza ki fad'a min ba, na rasa dalili Duk sanda kuke tare da mamy sai kinyi kuka ko wani laifi Kika Mata ne?"
Kai a kasa Tace "Eh Nabila, nayi mata laifi kuma ta gindaya min wasu sharud'a Kan ta yafe min"

"To ai ni a gani na abu mai sauki ne tunda kin San abinda take so kiyi, sai ki aikata hakan"
"Uhmn lamarin Nan ya wuce tunanin ki, Amma ki tayani da addu'a insha Allah komai zai dai daita"
"Allahu yasa"
Ta amsa da "Amiin."

Ma'isha Bayan ta baro asibiti gidan Umma ta nufa, Bayan sun gama gaisawa Umma tace "Amma yau Kam zaki kwana mana ko? Kannen ki suna tambayar ki"
"Eh Umma kwana zanyi ina Twins d'in suke ne ma ban gan su ba?"
" Sun tafi islamiya"
"Haka Auta fa?" (Auta shine d'an da Umma ta Haifa Bayan kwanciyar Haisam zuwa yanzu yaron na da shekaru biyu a duniya da Yan watanni, sunan sa Aayan, amma suna kiransa da Auta).

Umma ta amsa da "Yana bacci kin San shi da son bacci"
"Wallahi yafi mishi ai, Ni da zan samu hakan ma ina so"
"Uhmn daughter Kenan, ki dai bi abin hankali ko da yake yanzu da sauki ma tunda kin kwana biyu ciwon ki bai tashi ba"
"Hakane Umma abin ne sai a hankali, gashi Daddy na son d'aura min wata damuwar Kuma"
Gyara Zama tayi tana kallon Isha tace "Me kuma ya Faru?"
"Umma Daddy wai aure zaimin Nan da sati biyu"
"To me abin tashin hankali anan ai dama tare da na Yayan ki za'a had'a rashin lafiyan naki ne yasa aka d'aga, ma'aruf sunan saurayin naki ko?"

'dan tab'e Baki tayi tace "Eh"
"Amma Isha me aibun sa naga yaron na da nitsuwa tunda yasha zuwa gidan na ganshi"
Cikin Muryar kuka Tace "To Ni Umma yaushe ni zan Sami abinda na ke so ni Wallahi bashi nake so ba, Ya Haisam nake so kuma shi nake so na Aura"

Umma Tunda Isha ke magana Baki a bud'e take kallom ta Muryar Mummy suka ji daga bakin kofa tace "Biri Yayi kama da mutum, Ashe dama Soyayya kuke da Yayan naki?"
Wuri ta samu ta zauna Umma tana mata Sannu da zuwa ta amsa a gaggauce kana ta maida hankalin ta ga Isha dake kuka tace "Isha dama kina son Yayan ki? Kika cuci Kanki Kar dai ma shine Wanda a dalilin sa Kika kamu da ciwon zuciya?"

Kai ta d'aga alamun eh, Umma Tace "Haba Isha Amma baki kyauta Mana ba, Kuma kin cuci Kanki"
Cikin kuka tace " Umma ya kuke so nayi ne? Baku ga yanda Yaya yake sonta bane? Idan ma ya sani babu abinda zai Canza tunda ba Sona yake ba"
Umma Tace "Ai mune gaba daku Isha da kin sanar damu da Duk Wannan bai faru ba, Kuma da Yayan naki Bai Shiga comma ba"
"uhmn Umma Kenan, zafa ku raba su ne kuma yana sonta yanzun ma ai rashin natan ne yasa ya Shiga comma, Kinga da ko an gudu ba lallai bane a tsira."

Mummy Kam shiru tayi tana Jin tausayin Yar tatan chan sai ta ce "Idan bakya son Ma'aruf d'in zan fad'a wa mahaifin ki a kyale ki kawai"
Umma tace "A kyale ta Kamar yaya? Kina nufin ta cigaba da zama haka tana jiran babu?"
Cikin rashin fahimta mummy Tace "Ban gane babu ba?"

"Babu man Haisam da shi da Babu ai duk d'ayane, gaskiya to me a bar yarinyar nan tayi auren ta, wa yasan ranar da zai farka?"
Mummy Tace "Haba Dan Allah meyasa kike fad'in hakan, Haisam fa d'anki ne"
"Isha ma 'yata ce" kallon Isha tayi Tace "Daughter kiyi auren ki kiyi fatan hakan shine alhairi a gare ki dake da Haisam d'in baki d'aya"
Kirkirerren Murmushi tayi Tace " Shikenan Umma nagode Sosai Kuma na amince da auren Ma'aruf d'in"

Umma Tace "Masha Allah, Allah ya miki Albarka"
Ta amsa da "Ameen."

Girgiza kai mummy tayi tace "To dama Nazo ne muyi list na abubuwan da ya kamata mu saya mata in yaso zuwa next week sai muje turkey, muyi sayayyan a Chan"
Umma Tace "Ai a gani na ba sai munyi list bako?"
" Gara dai ayi kin San Akwai mantuwa"
"Eh hakane Kam" Nan suka shiga listing kayan d'aki da kayan kitchen d'in Isha mikewa tayi Tace "Nikam zan Shiga bacci nake ji" ta shige ciki abinta ba tare da taji abinda zasu ce ba.

Kwanciyar ta ke da wuya Ma'aruf ya Kira wayar ta da Kamar ba zata d'aga ba har dai da ya kusa yankewa ta d'aga bayan sun gama gaisawa yace "Am sorry Isha na tura gidan ku ba tare da sanin ki, Isha na gaji da ganin ki a haka ina sonki kuma ina tausayin ki sabida halin da Kika tsinci kanki a ciki"

Tashi tayi ta zauna Tace "Bangane kana tausayin halin da na tsinci kaina a ciki ba?"
"Uhmn Isha Kenan na Riga na San komai, Meerah ta Sanar dani halin da kike ciki and please Karki yi fushi da ita ko ranki ya 'baci a Kan hakan nine na takura ta Akan ta fad'a min Nan ma da kyar ta Sanar dani irin Soyayyar da kikeyiwa Yayan ki since from day one na fahimci hakan daga gare ki na d'auka Soyayya ce ta jini, Amma Dan Allah ina so ki bani dama na Shiga rayuwar ki ko da kuwa bazan iya maye miki gurbin sa ba zan kwatanta baki kulawa iya bakin karfina"

"Lallai Meerah wato shine ta je ta gaya maka ko zamu gamu"
"Yi hakuri ban sanki da fad'a ba"
"a a yanzun ma ba fad'a zanyi ba"
"Yauwa nasan nayi dace ai"
Murmushi kawai tayi yace "Isha Aurena da ke is in two weeks da fatan kina farin ciki da hakan?"
"Hmm eh"
"Dan Allah dagaske kike?"
"Eh dagaske nake"

"Kai Alhamdulillah ya kamata mu Fara Shiri ko?"

Murmushi tayi kana tace "Eh"
"Masha Allah, yanzu kina ina?"
"Ina gidan Umma"
"Okay ina zuwa yanzu Amma da Kanwata zamu Zo"
"To Shikenan sai kunzo d'in"
Bayan sallar la'asar yayi horn a mamakeken gate d'in gidan Abba, mai gadi bai tsaya 'bata Lokaci ba ya wangel musu gate d'in sabida zuwa yanzu yasan Ma'aruf da Kuma gun Wanda yake zuwa, Kamar kulluma kud'i ya zaro a aljihun sa ya Mika Masa kud'i ne sun kai kimanin naira dubu biyar murna ya Shiga yi yana kwararo Masa addu'a.

Kiran ta yayi akan sun iso, Yar aikin gidan ta aika ta Shiga dasu parlor bakin, kana ta kai musu abin sha da snacks bayan yan Mintuna ta Shigo bakin ta d'auke yake da sallama, Ma'aruf da Kanwar sa a tare suka suka amsa sallamar.

'dago kanta tayi don ganin wacce take sallama, ai ko tana ganin fuskar Isha ta Mike zumbur, Isha ma tayi mamakin ganin ta, Ma'aruf mikewa yayi yace "Ya dai Kun san juna ne dama?"

Kirkirerren Murmushi Isha tayi Tace "Eh kamar nasan fuskar Nan a wani wuri" shiru tayi tana kallon ta don tuna inda tab'a ganin ta, Yayin da ita Kuma jikinta sai rawa yake duk ta rasa sukunin ta, gani take kamar Isha tasan Duk Shirin su.

Muryar Isha ta tsinkayo tana fad'in "Yauwa kawar Aysha ko? Ko ince Ayrah?"
Murmushi kawai tayi bata ce komai ba Isha Tace "Zauna Mana" zama tayi kanta a kasa Isha Tace "Rankashidad'e Kai ma ka zauna Mana" Zama yayi yana kallon yadda yanayin kanwar tasa ya canza, Isha tace "Ya kike ya kwana da yawa da fatan dai an sami abinda ake so" Jin hakan tayi saurin d'ago Kai tana kallonta Isha ta d'aura da fad'in "Ina nufin an fita da result Mai kyau?" Ta maida kallon ta ga Ma'aruf Tace "kasan lokacin su suke bin mu a school"
Ajiyar zuciya yayi yace "Ai ni Duk kun tsoratani ne"
" Me abun tsoro anan don kawai Mun San juna"
"To baki ga yadda Mardiya bta sauya ba?"

"Oh dama sunan ta Kennan ai ban sani ba, ikon Allah Kenan back then ina ga sau d'aya ko biyune muka had'u dake ashe zaki Zama sister in-law na"

Mardiya da tun d'azu ta kasa cewa komai kirkirerren Murmushi tayi kana ta amsa da "Allah Kenan"

Wayar Isha ce ta fara ruri picking tayi Tace "Haba Dan Allah, to ki Shigo parlorn baki man muna ciki" ta ajiye wayan Ma'aruf yace "Wane ne?"
Ta amsa da "Meerah ce"
Ya amsa da "Oh okay"

Bata d'au lokaci Mai tsawo ba ta Shigo bakin ta d'auke yake da sallama, Zama zatayi ta kalli fuskar Mardiya Tace "What me ya kawo Wannan munafukar gidan Nan?"

Duk su ukun suka Mike suna kallon juna Meerah Tace "Isha me ya kawo Yar iskan yarinyar Nan gidan Nan?"
Murya na rawa Tace "Dama kin santa ne?"

Wani irin mugun kallo ta mata sama da kasa Tace "Nasan ta mardiya Kenan, itace wacce nake baki labari Wanda suka Shiga tsakani na da Bashir da kawarta Ayrah"
Kallonta mardiya Isha tayi Tace "Tirkashi to ai nima itace kawar Ayrah da sanadiyar ta Yaya na ya Shiga comma"

Ma'aruf Duk ya rikece ya kasa fahimtar inda maganar su ta dosa cikin rashin fahimta yace "Wai me ke faruwane Kun sani a duhu?"
Chapter 31 · 0% Book details