← Book details Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 55

Sashe 16

Dangin Ubana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Umm umm ko don ke zan Shigo ai idan kin bukaci hakan"
Murmushi tayi Tace "Nagode Amma yallab'ai uwa d'aya uba d'aya kuke da ita ko naga Kuna Kama?"

"A a Yar Baffana ne"
"oh Masha Allah ka gaida min ita sai na Shigo d'in"
" Okay bye"

Ma'isha tana Jin su kamar zuciyar ta zata fashe Amma tayi kokoran saita kanta, ganin ya tada motar Tace "Ina kwana?"
Ya amsa da "lafiya" kawai yace mata a takaice, yasa wa motar key suka wuce makaranta.
_______________________
Please comment and share
Milhat ce
Yar tarewa

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._

🍃*DANGIN UBANA*🍃

Story & Written
By

Milhaart

Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne.

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________

*Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.*

Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

Page

27&28
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._

_Continuation.............._ Ma'isha ganin har sun Isa bai kulata ba cikin Murya kamar zatayi kuka Tace "Yaya yanzu Dan Allah baza ka kulani ba? Duk hakurin da nake baka baza kayi hakuri ba tsakani da Allah, bayan Kuma Kai ne kamin laifi"

Kallon kin Raina min hankali ya Mata sannan yace "Ni ne ma nayi Miki laifi?"
"Eh Kaine"
A dai dai suka Shiga School d'in sai da yayi parking kana yace "Uhmn ina jinki laifin me na miki?"
"Kasan time d'in da zan gama Lectures sannan ka kashe wayar ka bayan Nan Kuma kaje ka zauna da yarinyar Nan kana hiran ka hankali kwance ka ma manta dani" ta karasa maganar tana matsar kwalla.

Murza goshinsa yayi ya ce "Amma meyasa baki min magana ba?"
Bud'e kofar motan tayi Tace "Haka kawai" ta rufe kofar motan da d'an karfi yayi Kara har Saida yayi saurin rufe idon sa, hatta mutanen da ke tafiya da Wanda ke zaune suka kalli inda suka jie karar wasu suna magana kus kus.

Haisam kuwa fita yayi daga makarantar Sai da ya daidai ci lokacin da Aysha zata Shigo ya dawo,Bayan sun had'u suka Shiga hirar su har ta manta da wani abu Wai shi Lectures, ganin karfe 6 ya kusa yace ta tashi ta wuce gida maghrib ya kunno Kai, ba musu tayi yanda yace.

Har wurin motar ta ya raka ta sai da ta Shiga ta tada motar ya bar gun ya d'aga mata hannu ya nufi gun motar sa, daga nesa Ma'isha ta hango su girgiza kai tayi a tare suka nufi wurin motar, zagayo wa yayi ya bud'e mata ta Shiga ta zauna sannan ya rufe, kana yanzagaya Shima ya Shiga ya tada motar suka wuce gida.

*AFTER 1 WEEK*
Wata shakuwace mai karfi ta Shiga tsakanin Aysha da Haisam, yayin da tsakanin shi Ma'isha ina kwana ina wuni ne kawai.

Wata ranar lahadi, ta shirya ta Sanar da Mummy zata gidan su Ameerah Mummy ta mata fatan a dawo lafiya sannan ta jaddada mata kar ta dad'e, Haisam ta hango a garden d'in gidan kanta ta kawar kamar bata gansa ba, gun Driver ta nufa ta umurce shi da ya d'auko mota ya Kai unguwa, cikin sauri ya d'auko yayie parking ita kuwa ta Shiga gidan baya.

Haisam kallon ikon Allah yake a bayyane yace "Wato yarinyar Nan ta ganni Amma tayi kamar bata ganni ba, Kuma ma ina zata je da Rana tsaka haka?" Ganin ba samun amsa zaiyi ba ya zaro waya ya kirata.

Tana ganin call d'in tsaki tayi ta kashe wayar ma gaba ki d'aya, Haisam bin wayar sa yayi da kallon ganin ta danna Masa Line busy,ciza leb'en sa yayi,ya Shiga cikin d'akin sa ya d'auko key d'in motar sa ba fice daga gidan,basu d'au lokaci Mai tsawo ba suka Isa, sai da ta fita ta waigo ta kalli driver Tace "Baba kabiru kar ka manta karfe biyar Zako d'aukana"

A d'an rutsune yace "Inshallah rankashidad'e, karfe hud'u da rabi anan zata same ni"
Murmushi tayi Tace "To sai anjima"
Ta shige ciki.

Ma'isha ne zaune a Kan gadon Ameerah suna kallon juna, tana kwararo Mata bayani, sai da ta gama bata labarin duk abinda le faruwa tsakanin ta da Haisam kana ta fashe da kuka mai cin Rai.

Ameerah taji tausayin kawar tata sosai, ta Shiga rarrashin ta har sai da tayi kuka mai isan ta don kanta tayi shiru.

Ajiyar zuciya Ameerah tayi Mai d'an sauti tace "Isha gaskiya Yayan ki bai kyauta ba tun ba yau ba nake fad'a miki kin nunae damuwa sosai akan shi na miji ba a mishi haka, in fact ma d'an Adam haka yake idan ka nuna masa ka damu dashi sosai sai ya d'auka duk duniya baza ka tab'a samun irin sa ba ko Kuma baza ka iya Rayuwa babu shi ba, Ni shawarar da zan baki shine ki cire Shi a ranki alamu sun nuna Yana son So Called Aysha d'in Nan, Don iya abinda Kika fad'a min Haisam a matsayin kanwa ya d'auke ba masoyayi ba"

Murmushin takaici Ma'isha tayi Tace "Nayi kokarin fahimtar hakan Ameerah Amma na kasa ke Kanki kin sani tun muna makaranta nake crushing d'insa, in fact tun muna primary, Har Saida muka Isa SS 3 da ya bani amsar tambayar da ake kana na Samu damar Shiga rayuwar sa, yanzu Kuma kice na rabu dashi?"

"To Isha fad'a min me zakiyi idan baki hakura ba? Cutar dake zaiyi Isha, na damu da lafiyar ki"
"Gaskiya Ki kawo wata shawarar banda wannan rabuwa da Haisam tamkar rabuwa da numfashi nane"

"Hmm isha Kenan" mikewa Ameerah tayi ta nufi Yar karamar fridge d'in dake d'akin ra d'auko ruwa Mai sanyi da Hollandia, had'e da glass cup ta dawo ta zauna Tace "wanne zan sa Miiki?"

"Hollandia" kawai a takaice zuba mata tayi ta cika cup d'in kamar zai zuba ta Mika Mata, Ma'isha tasa hannu ta karb'a, bismillah tayi ta kafa a bakin ta bata sauke ba har sai da ta shanye Tass.

Ameerah Tace "Should I add more?" Cike da kulawa
Girgiza Kai Ma'isha tayi had'e da fad'in "No Thanks"
Tissue ta zaro a jakar ta, tagoge bakin ta.

Ameerah Tace "As I was saying isha, rabuwa da Haisam is the best solution, cos Haisam baya son ki ya kamata ki gane hakan"
Kallon ta Ma'isha tayi sai Kuma ta sunkuyar da kanta kasa.

Dafe kafad'ar tayi Tace "Isha!!"
'dago kai tayi a hankali ta na kallon ta, Tace "I know how you feel son Wanda baya sonka babbar matsala ce but you can't force him to love you"

Cikin Murya kuka Tace "Kin fad'i gaskiya, Dole na rarrashi zuciya ta" sai Kuma tayi Murmushi bayan hannun ta tasa ta share hawayen dage gangaro wa a fuskar ta d'aya nabin d'aya kana ta d'aura da fad'in "Insha Allah zan cire Ya Haisam a raina please ki taya ni da addu'a"
"Insha Allah dear"
Ma'isha Tace "Kwana biyu ba mu had'u ba ba wani gulma ne?"
"Hahaha Allah ya shirye ki Isha kina cikin damuwar ma baza ki Canza Hali ba?"
"Ahhh ya zanyi to? Kefa Kika ce min na cire shi a raina to it starts from now"
Dariyar ta Kuma yi Tace "Akwai su dayawa har sai kin gaji da fatan wuni zakiyi?"
"Eh sai 5 zan koma"
"Kai Amma naji dad'i wallahi"
Murmushi kawai Ma'isha tayi bata ce komai ba.

Ameerah Tace "Yauwa mutumin ki kullum sai ya tambayeni ke"
Cike da rashin fahimta Tace "Wa Kenan?"
"Ma'aruf Mana"
"Mtswww wai dama yana Nan? Ni wallahi na ma manta da wani ma'aruf"
"Hmm to na tuna miki, please give him a chance"
" I can't dallah,Ni yunwa nake ji ma me Akwai?"

Girgiza kai Ameerah tayi ta fahimce ta so take ta kawar da maganar sabida tun shigowar ta Tace zata kawo mata abinci tace a koshe take, riko hannun Ma'isha Ameerah tayi had'e da fad'in "Zo muje kitchen mu duba me suka girka don dama Nima tun breakfast ban ci komai ba"

Nan suka nufi hanyar kitchen, a hanyar su ta Shiga kitchen suka ci karo da mahaifiyar Ameerah har cikin girmawa wa ta gaida ta ,ta amsa ba yabo ba fallasa, suka shige cikin kitchen.
Chapter 16 · 0% Book details